Uncategorized

Cikin fushi Ummi Zeezee ta mayar wa da wani matashi martani ko me yayi zafi

 “An ba ni kambun fitacciyar jarumar Kannywood da ba a taba samu ba a mujallar Madubi.” – Zeezee

 Ummi Ibrahim Zeezee ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta soki wani mai sunanta, mutumin ya buƙaci masoyanta na Facebook da su daina kiranta a matsayin fitacciyar jarumar Kannywood.  An ji ta tana takama cewa ba za a iya cire mata wannan laƙabin ba.

KARANTA: “ADO GWANJA NEW ALBUM AMADA 2021”


 An jiyo ta tana cewa “A shekarar 2005, Mujallar Aminu Shariff Momo mai suna (Madubi) ta ba ni mukamin fitacciyar jarumar Kannywood.  magoya baya sun bar taken, wanda ba zai yiwu ba”.

 Fitacciyar yar wasan kwaikwayon ansanta da rashin kyale abu a cikint kina, domin kuwa duk wanda yayi mata maganar da bata yi mata daɗi ba a take zata maida martani. 

 Jaruma Ummi Zeezee tana cin ganiyarta a duniyar social media, cikin kyawawan tufafi na alfarma, sai dai har yanzu jarumai ita bata yi yunƙurin dawowa tsohuwar sana’arta ta Kannywood ba.

KARANTA: “BAZAN BAR ‘YA’YANA DA MATA TA SU YI FIM BA – ABUBAKAR MAISHADDA”


Ko a kwanakin baya Ummi Zeezee ta yi yunƙurin kashe kanta saboda dafararta miliyoyin nairori da wani mazambaci yayi mata, bisa alƙawarin za su fara harkar danyen man fetur, kuma daga bisani ya gudu da kuɗin.

Back to top button