🌼’YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA
26-30
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN
MASU AUDIO DUK WACCE TA MAIDA MIN NOVEL AUDIO BA IZININA TACI HAKKI NA TACI HAKKIN WACCE TA SIYA,KUJI TSORON ALLAH.
PAKE NAKU NE
Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children’s wears shoe’s and bag’s.
Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage’s din kawai duk inkazo
R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.
Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo
Masu bukata ga number. 0703 455 9202
https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx
Kwashe kayan karton Cele tayi tare da na Maheerah sannan ta Kama kunnen kwarton tace wato Kai kunnen kashi ne dakai matar wani kake bi har gidan mijinta Kai ga tsohon bunsuru,kasa magana yayi ya hade hannaye biyu Alamar bada hakuri Cele ta Kama gashin gemun ta yanke rabi ta bar Masa rabi tace kana motsawa Dan ubanka wlh sai na tsaga ma jikinka,bai San me tace ba ya mike zai gudu ta zabga masa duka a dokin wuyansa tace zauna,So yake ya kwaci Kansa shi ba lusari bane gani yayi da gaske Cele zata wulakantashi ya tashi ya kwaci kayansa ta karfi Yana zage zage,ya duka Yana kokarin saka wandonsa Cele tasa kafa ta daki duwawunsa ya tintsira Saura kadan ya fadiya juyo a zuciye ya Mari Cele sabo da kwallon Dan Iska ne bashi da mutunci,Cele haushi yasa tasa Rezar ta tsaga Masa bille kato a barin duwawunsa daya, larabawa da kwailo ihu ya saki ya kwalla Kara ko wandon Bai karasa sawa ba ya fice da gudu,Ahsan Yana Palo yaga kwarton ya fito da wando a hannu da riga Yana Kare gabansa, Maheerah Cele ta kalla ta fada toilet da gudu ta kulle da key Cele tace Zaki fito ne wallahi ko ba yau ba kafin na bar gidan Nan sai na Miki billen Yan fulani.
Maheerah ta tsorata yanda taga Cele ta tsagawa Saurayinta duwawu cikin dare ta fice daga gidan gaba daya ta tafi gidansu Kai Kara gwara a dauki mataki akan cele gaskiya ta gaji.
Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document
Ahsan ne ya shigo dakin Cele da lalube Yana so zata bashi shayi ta fito da wanka zata Yi Shirin bacci ta ganshi zaune a gefen bed dinsa tace gaskiya makafi da basira suke ji yanda ya gane Yana iya zuwa da Kansa,ganin baya gani Cele tace su Saluhu ba a gani me Zan zauna Ina wahala ta cire towel din ta jefar sintir da ita,Ahsan dariya ta kamashi ya boye ta a ransa ya sake zooming idanuwansa Yana ta Shan kallo a hankali yanda baza ta ji ba ya furta Astagafurillah,Cele taje jikin mudubi harda karewa kanta kallo tayi girgiza tace Kai cika fa nake duk na bude sai kiba nake kalli jikina ga cikina tumbini ko cuta ce oho, Abubuwa haka Kai Cele kinfa hadu sai babban Alhaji, Ahsan ko kyafta Ido bayayi ya manta shi makaho ne,Jin zaiyi loosing control ya rufe idonsa har Cele ta shirya ta gama komai ta saka kayanta Riga da skert sannan tazo gabansa tare da rike Masa hannu tace Allah sarki Dan makahon Maheerah,Idonsa ya Bude a hankali yayi wani ja,Cele tace Kai Kuma lafiya uhm ta ja shi ya mike tsaye,Mutumin ba hakuri hannunta ya fisgo ta fado kirjinsa ya rungumeta sosai abinda bai taba ba,Cele tayi lakwas tana shakar kamshinsa,kanta ta dago a hankali tana kallonsa tace Haram,Kamar ta tsikara Masa Allura ya matsa da sauri daga jikinta yana istingifari,dariya ya bata yace uhm ta rike hannunsa Suka fice
Washe gari Ahsan ganin Maheerah bata gidan komai Cele sai taga Yana yi da Kansa normal ya dawo Yana gani,Ido Cele ta zaro Murmushi ya saki ya nunawa Cele da hannu Wai Yana gani dama amma tayi Shuru da bakinta,Cele tunawa tayi jiya ta gama tsirara a gabansa Takaici ya kamata da kunya ta tashi ta gudu daki ta buya tana cewa wayyo ya ga komai nawa shike nan,dariya Ahsan yayi yasan me ta tuna.
Tunda ta buya bata fito ba sai da me karatu tazo Hajiya Hauwa tazo ta koya Mata ta rubuta sosai ta tafi ta bar Cele da hadda.
Baffa Yana zaune ya hakimce,takun mutum yaji ana taga steps a hankali,wani kamshi na musamman ya daki hancinsa,a hankali ya juya Suka Yi Ido biyu da Mami,Ido ya zuba Mata ta wani tsare gida wai aji ita,Sallama tayi Masa ya amsa da fara’a ta zaune ta wani kame, ko gaisuwa babu ne Baffa ya tambaya,Mami Fuska ta yatsina ta dauke kai, Haba ranki ya dade tuba nake yi har yanzu baza ki yafe min ba ne, haba my Uniform ko Ina Zan Shiga sai dake,me farar aniya, idan ba ke a rayuwa ta bazan taba rayuwa ba cikin Jin dadi,shifa tuwo duk darajarsa sai an Sanya miya,bazan sake rikon ki da Wasa ba har abada,kece me sharen min hawayena bazan sake saka ki kuka ba,Dan Allah kiyi hakuri ki yafe tunda na ganki karfin da nake ji ko Zaki albarka, bazan Kuma rike ki da Wasa ba,Zan baki komai da kike so sabo da kece farin cikina,a kanki na San Mene so ma Kuma daga ke bazan sake ba na rufe kofa,waccen ma kaddara ce amma idan badan ma barbade aka min ba ta ya za ayi na iya juya Miki baya,Ina tabbatar Miki asiri aka Mana Ina ji a jikina to wallahi karyar makiya Yan bakin ciki Allah ya sake hada mu har abada Muna tare, kiyi hakuri ki yafe min dan Allah ki sai na sake durkusawa Baffa ya zube gwiwoyinsa a kasa,Mami kanta ya wani Kara girma,Baffa yace haba yar budurwata…Mami duk yanda ta Kai da danne dariyarta ta kasa Wai budurwa Murmushi tayi ba tare data shirya ba,ya sake cewa My Baby,the love of my Life, Sweetheart,my Angel,my Sugar cake,Mami sai dariya take tace Ni dai ka zauna karka dameni,Kin bani dama na zauna ya tambaya? tace ae yace ato idan baki bada dama ba nayi ta Zama a Haka Zan iya kwana ma..
Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document
Mami ce ta Fara magana cikin salo da kashe murya ka tsaneni babu dalili,na soka na kaunaceka babu misali Amma Kai baka ganshi ba,ba irin rokon da ban maka ba Amma kaki min uzuri sai da ka sakeni ka dinga sakina har igiyoyina Suka Kare wannan wanne irin cin mutunci ne,idan za ayi sulhu ba a tuna baya Salma,dan Allah Ni dai na gane kurena naci kwal ubana na horu haka ki yafe min idan ba so kike zuciyata ta buga ba to ki hakura a bar zancen tuna baya yanzu mu maida auren mu ko ya Kika ce,Harararsa tayi tace ya wuce kawai badan halinka ba sai dan yarana,yace naci albarkacinsu hakan ma na gode Allah ya biya,Mami ta mike tace Ina zuwa ta Shige kitchen,Baffa tana kulewa yace yessss….Finally Alhmdllh,kayan ci da sha data shirya Masa ta kawo Masa ta jera sai kallonta yake yace Allah ya Kara Miki lafiya da tsawon rai,Ameen Mami ta furta tana cewa saura ka kara bata min rai dan ma dai Kawai ka samu Ina sonka,soyayyarka a zuciyata ta Zama ciwo shi yasa,Baffa yace ai ko babu kafa na tako da gudu wajenki Matukar kece, ya dai kamata ka sani so ba kudi ne ba bare ka debo ehe,Baffa yace na tabbatar Yana bude abincin,ta zuba Masa yace ai Baki Isa ba tare zamu ci,spoon ta sa suna ci tare suna hirarsu kamar matasa,suna hada Ido da Baffa zaice I love you,tace itama much more Dear,Nawwar da Ni sai Auta Muna part dinmu Muna jira Baffa ya fito amma Shuru Shuru har bayan Sallar Isha sannan ya fito ya Kira Auta yace yazo su tafi,Auta ya bishi suka tafi,Auta yace Baffa Yaya? Yace haba tuni aikin gama ya gama ai mu indai muka je waje to ba a iya Mana musu,Auta dariya yayi yanda Baffa ke zuga Kansa,Auta yace ka bata kudi? Ba Dole ba ai shine makamin yakin namu Auta Suka Yi dariya abinsu.
Mami tun daga ranar ta Fara gyaran jiki dama tana yin abinta sabo da Balarabe ya Mata Illa,Nawwar ne ya samu Baffa yace Baffa Wai baza kuyi test na aure ba? Baffa yace test din uban wa lafiyar mu kalau ko Sanda muke saurayi da budurwa bamu Yi ba sai yanzu ko kanjamau ce da ita ko ni ai sai dai mu shafawa juna mu wuce lahira, karka kawo min Iskanci a nan Kai dama komai sai kayi Wasa a ciki sa’anka ne ni, yanzu da Auta ne zance zamuyi na hankali da shi,Nawwar dariya yayi dama tsokanarsa yayi yasan haka zai ce Auta shine na kirki,yace to Ni Zan kawo Amaryar taka? A’a zanje in dauko kayata ni na saka nace ka kawo min Mata gida dan Sa Ido, Auta yana zaune Yana ji yace Baffa Alkawarina fa? Gashi aure ya kusa tabbata,Karka damu Auta ko Yar gidan uban waye ka kawota sai dai duniya ta zageni akan aurenka ace anyiwa yaro aure da wuri amma ko wace Zan aura maka,Auta yace to Baffa dama akwai wata yar ajinmu yanzu ita nake so sunan larabawa ne da ita sunanta Sahar,Baffa yace Kai dai kayi shuru tunda Candy ya matso ai kana shiga University sai aure,yace to Allah ya kaimu,Nawwar yace Wai da gaske wannan mahaukacin yaron zaku biyewa kuyiwa aure,aure fa ba Wasa bane fisabilillahi kamar Auta fa 23yrs shi ba wani me jikin girma sosai ba sai yazo ya kasa rike aure,aure fa akwai wahala Auta kayiwa kanka fada wannan iskancin da kake ji gwara ma ka hakura,Baffa yace Kai Ina ruwanka,Nawwar yace shike nan ni dai Kar a sani a ciki wlh ba ruwana ba sa hannuna a ciki Kamar Auta nawa yake me ya sani ma a duniya Ina wannan yaron ina mace, Auta ya bata rai yace ni dama bance kasa baki b….rashin kunya zaka min Nawwar ya nufe shi zai make shi Baffa yace karka ta min dana ba ruwanka da shi ka kyale mu muyi zancen mu,Kai Auta bana son rashin kunya Yana magana kana yi,ai gani yake kanmu daya tunda Kuna daure masa gindi,Auta Murmushi yayi yace waye zai daure min abuna abuna kalau yake ba Wanda ya daure shi,ko Nawwar yaso yayi dariya dan shi har ga Allah hausarsa yayi ya manta ma sunan Antena ne,Auta Kuma yace shi ba a daure Masa kayansa ba,Auta tashi yayi sum sum ya fice abinsa,Nawwar ya fice ya koma gida wajen Mami yace yanzu da gaske auren za ayiwa Auta? Mami tace Wai me Auta ya tare maka ne da yarona ya lalace ai gwara a Masa auren,tunda Auta ya damu mutane Kawai idan da Hali ayi Masa Kar yazo ya fada harkar banza yaje yaci Karo da lalatattu, Kai da kake salihin ji nake da su Miracle ka hadu da tuni ma baka lalace ba badan Allah ya Kare ba shine zaka dame ni,Nawwar yace Mami Rabin tawa Zaki zaga,Ni ai ba zaginta nayi ba ai ta kirki ce gaskiya na fada,yace shike Nan ayiwa Auta aure lafiya ni dai ba ruwana ko daurin aure bazan je ba,karka je Mana dama wa ya gayyaceka cewar Mami.
Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document
Kaka Kuwa kwana Suka Yi suna tafiya a mota daga nan aka shiga jirgi da shi ta Jedda,Kaka tsoro ya kamashi Addua Kawai yake ya zaci wata state din zasu je a jirgi a ransa yace wata jahar zamu je Ina Jin lallai me kamafanin nan Yana da kudi ta wani bangaren Kuma zuciyar kaka a tsorace take sai da Suka Yi tafiya a jirgi ta Kai awa shida sannan Suka sauka a kasar Qatar Ashe kasar Qatar aka kawo Kaka za a siyar dashi azzalumai matsafan wasu larabawan suke Neman wani abu na sassan jikina mutum shine bakar fata shine marar gata shi za a kai a kashe shi Kamar ba Allah ne ya halicce shi ba,Mutumin bayan sun fito daga airport Kaka dai binsa yake dunkum dunkum Babu me jin yaren daya,a jikin wani shago mutumin ya tsaya tare da siyowa Kaka lemo da Madara da nama,Kaka ya samu waje ya zauna ya cika cikinsa dam,mutumin yayiwa Kaka Alama da ya jirashi
Kaka ya nuna ba matsala mutumin Yana tafiya kaka ya fece ya dinga gudu gudu sauri sauri bai San Ina ya nufa ba bai San Ina aka kawo shi ba tunanin Kaka ma duk a Kasar Saudiyya yake wata state din har dare Kaka bai daina tafiya ba Kawai bi yake ta ko wanne lungu da sako,Mutumin Yana dawowa ya nemi kaka ya rasa Takaici da bakin cikin irin kudin da zai samu Kaka ya cuce shi ya gudu,haka ya ja kwafa ya sake dubawa bai ga Kaka ba babu alamarsa yasan tabbas ya gudu masauki ya tafi cike da bacin rai,Kaka Kawai tafiya yake sai da ya kwana Yana zaga gari Bai San Ina yake ba kafafunsa duk sun kumbura,waje ya samu ya zauna domin ya huta,tagumi ya zuba yace Ni da kasar waje har abada me za ayi da wata kasar waje,yanzu Kaka ya zaiyi ma ya koma garin Makkah shi yake tunani ba gida Nigeria ba,yace banga riba a wannan tafiyar ba,Cele tawa ta bata,na Sha wahala gashi da alama an kawo Ni nan a cuce ni,Yana ta maganganu shi kadai sai ga wani babban mutum bahaushe yace Sannu Malam,Kaka yace Kai masifa Kai bala’i ko Ina kaje sai kaga bakar fata sabo da shishigi da jaraba ko wacce kasa bakar fata sun taru sun cike gari jama’a muyiwa kanmu fada mu zauna a kasar mi Ina riba cikin wannan masifa,sai da Kaka ya Gama sannan ya dago ya kalli mutumin yace yanzu nan ma Kuna nan Wai bawan Allah nan Ina ce? Yace Kai baka San inda kake ba? Kaka yace ni nasan sadai a Saudiya nake Makkah wani balarabe ya min hanyar aiki yace zamu je a koya min aiki Jan dinga Jan motar Yogourt ya hadani da wani mutum balarabe sai naga mun dauki hanyar jidda a mota Muka shiga jirgi sai Muka zo nan bawan Allah wannan wacce Jaha ce a Saudiya? Mutumin yayi dariya yace ai Nan kasar Qatar kake cikin birnin Alqahira,Kaka yace Jar uba dan nan kayiwa Allah ka taimaka min na koma Makkah Dan Allah,Mutumin yayi dariya yace karka damu zuwa gobe kana Makkah Inshaallah,Kaka Yana ta murna Yana godiya mutumin waya ya dakko ya Kira wasu larabawa suna ta larabci Kamar ba bahaushe namu ba ashe shima sake cinikin Kaka yayi shi Kuma can dai Riyad za a Kai Kaka a siyar da shi,shi Kuma ba masu Luwadi za a bawa su siya in Suka Gama da mutum su sake shi ko su hallaka shi,shima bahaushen da shi ake hada Kai ana cutar bakar fata Dan uwansu bahaushe Kuma musulmi sabo da shi ya Zama hamshakin me kudi yafi shekara ashirin a zaune a Qatar sana’arsa kenan Luwadi har suke siyar da mutane ana Basu kudi a lalata su ba tsoho ba yaro ba matashi kowa Suka samu dama a kansa damawa suke,shima tafiya yayi da Kaka a gidansa Kaka ya kwana yaci ya sha da safe Kaka yayi wanka mutumin ya bawa Kaka Jallabiya sabuwa ya canja sannan ya hadashi da wani matashin balarabe me suffar Dan daudu ya tafi da Kaka aka sake shiga Jirgi da Kaka tare da juyawa da shi Saudiyya,suna zuwa Jedda Kaka murna ta kamashi Yana cewa naka sai naka ji bahaushe Dake dan uwa ne ya tallafa min gani a Jeddah Hauwa kulu Majadan Alhmdllh,Balaraben ya shiga mota da Kaka a zuwan zai kaishi Makkah sai ya wuce da shi Riyad,Kaka Kawai yaga bai yarda da tafiyar ba tun kafin su bar gari su Shiga daji yace a tsaya zaiyi fitsari ya nuna musu gabansa,ganewa sukayi Suka tsaya dai dai inda akayi toilet na mutane ka tsaya ka shiga Kaka ya fita Yana waige waige ya Shiga toilet ya fito ya lallaba yabi ta baya ya arce da gudu ya Sha kwana basu sani ba,Taxi ya tare ya shiga ya Fadi address din gidansu na Makka Basu ma karasa Makkah dinba ashe Driver ya Kai Kaka har kofar gida Kaka ya biya driver kudi ya fada gidansu cikin daki ya haye saman gadonsa ya ja bargo ya lulluba yana Nishi da hakkin wahala Wai ya buya kenan.
Download>>>Â Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document
Dagaci ana ta cin duniya da tsinke har sunyi kyan gani,Rabi ta sake Aiko musu da kayan sawarta data cire zata bayar tace a bawa Gaji,Gwaggo sauki ya samu sosai tana iya Dan tafiya kadan kadan itama sai data zabi manyan riguna a ciki Wanda zasu shigeta,Gaji sai daukan wanka ake yi ana neman bazawari,Asirin Zayya matar Danbinni ya karye tuni Danbinni ya saketa ya auro wata bazawara me hankali suna zamansu haka Yana lallaba rayuwarsa ya daina iya shegen da yake yaran Zayya biyu suna hannun matarsa suna zamansu,Babu kukan da Zayya bata Yi ba da roko yace wallahi baza ta dawo gidansa ba ya tsaneta yanzu baya sonta,Dole ta hakura ta tashi a tutar Babu ba tsuntsu ba tarko.
Sabreen ce taje wajen Mama ta samu Mama duk ta rame ta canja,tana ganin Sabreen sai data Yi kwalla tace na jawa kaina,Sabreen tace yo haka Kika zaba dai Mama gashi nan kin rasa Mami ta rasa amma ki sani Mami Aurenta za a maida da Baffa,kema baki kyauta ba dama idan kana tunanin kayiwa wani to kanka kayiwa gashi ni bani da auren ke Babu gashi kowa baya ta tamu shima Papa ya auri matarsa baya son laifinta ta Gama da shi bazai iya Mata kishiya ba Mata Muna sani mu dinga cutar kanmu da kanmu gashi yanzu inda Muka Kare Wanda Muka zalunta Kuma sune a sama,Ni gaskiya na gane gaskiya Shaye shayen ma so nake na daina na kusa hakura da shi duk da ban daina ba Nan gaba Zan daina,Mama ta kasa magana ma bata da abin fade Dan ma Allah yasa gidansu suna da rufin asirinsu dai dai gwargwado ba rashin ci Babu rashin Sha.
Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document
Omaira ke Omaira Abba Yana kwala Mata kira Shuru Omaira bata sani ba bacci ma take ita ,Uwa Babar Abba tace ai wannan yaran idan kana Jin jarabar duniya to su kenan,ai Kai Kam Ismail baka yi Dace ba ka haifi jaraba,Abba yace kyale su Watarana sai na bar gidan nan naga uban Wanda zasu raina,sun gaba talautani bani da farcen susa,Omaira ce ta fito tana mika tace Umma tace kana kirana? Mari ya kawo Mata ta kauce,Uwa tace yawwa nadawa Yar iska duka,Umma ce ta fito tace wallahi duk Wanda ya taba min ‘ya sai ya Gane kurensa,to fitsararriya kina bakin ciki Dana zai Sha shayi da Madara shi yasa Kika hana yarsa tazo ta je aikensa,Umma tace madarar me yan madarar burar….ta narko ashar,ai ke kin Zama mayya badan haka ba an sakeki zaman me kike Yi a gida shekara da shekaru har da Kai Kara kotu kice ba inda zaki je kotu ta baki damar zama a gidan tsohon miji kinji kunya dai ana korarki kina mannewa marar zuciya,zaman yarana nake Yi Kuma Dole ya ciyar damu karya kuke wlh baku Isa kuga bayana ba marasa godiyar Allah jahilai Allah ya baku baku so Inshaallah a yarana sai an samu wasu sun muku ranar da duk duniya babu Wanda zai iya muku ita,Dariya Uwa tayi tace a hakan? Ana kawo talakawan duk ba na kirki a yaran naki,Bilkisu ce ta shigo gidan tayi Sallama itace Babba a dukkan Yaran da aka Haifa sai ka dauka kanwar Umma ce,tana shigowa Abba ya fice daga gidan ma gaba Daya yasan bala’i tazo da kanta yanzu za ayi batacciya,ita kanta Uwa Shuru tayi ta wayance tare da furta Allah Yana Nan, Hayaniyar me nake ji? Bilkisu ta tambaya tana zazzare Ido ita dama kana ganinta kasan Kalar bala’i ce,badai Umman mu ake zagi ba? Umma tace gasu nan abinda Suka Saba kullum tunda aka aureni suke min haka gashi har na girma Kuma an sakeni ma baza a kyale ni ba ta karasa da hawaye,Bilkisu tace Abba ne Kawai zamu kyale sabo da mu cika da Imani billahillazi tsohuwar wani ba tamu bace ko Kaka uwa ce,Omaira tace never Bilkisu tace to tunda hakane a raba gida Bari kotu tazo ta tsagawa uwarmu sashenta kowa ya ji da Kansa zamu katange mata bangarenta kofa kowa da tasa mun gaji, Omaira tace Ina cikin masu buga bulo da ni za a buga bulo Aunty Bilkisu tace Allah yaji Kan Cele badan ta mutu ba da yanzu an wuce wajen nan na so Cele a gidan nan take da tayi min maganin wannan tsohuwar, Omaira tace kice da yanzu ta farfasa Mana jiki.
A ranar Aunty Bilkisu ta Kira sauran Yan uwan Suka hada kudi ciki kwana uku aka kawo yashi da siminti Kamar gidansu Abba bashi da ikon magana sunfi karfinsa, Suka taru dukkansu su takwas cif aka Kira ma’aikata masu buga bulo baza su siyo ba yayi tsada gwara a buga musu bulo, Masu buga bulo dukkan matan suna wajen sai kac fore maza ana farawa Bilkisu aka fara zubawa kwaben bulon ta buga guda daya Suka Yi tafi da ihu,sai Sai Nazifa da Nazira Suma Yan biyu ne,sai Safiyya da Sufia Yan biyu ne su ma Suka buga har Kan Omaira sai twins Suma Rahma da Raheema,sauran Suka barwa ma’aikata suna ta fama a ranar Suka buga bulo,Cikin dare Uwa ta fito da tabarya kowa Yana bacci gaba daya tasa tabarya ta doke bulo din kaf bata bar ko guda Daya da lafiya ba ta koma ciki tayi kwanciyarta sai da safe su Omaira Suka ga bulo a farfashe gaba daya an tarwatsa su,ransu ya baci ga asarar kudi sunyi dama su ba wani kudi ba,gida ta dawo ta fadawa Umma,Umma tace kyale su dan Allah nasan Babu me Yi sai kakar ku Allah Kuma zai saka Mana Allah Yana kallon su,baya bamu ci da sha ga wulakancinsu sabo da sun sa ya sakeni,abin haushi ma Wai abin nasu duka danginsu na rasa me na tare musu a duniya haihuwa laifi ce,Omaira tace kiyi hakuri Umma komai zai wuce Allah ya Mana arziki zasu ga tsiya.
Karanta>>>Â Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata
Umma tace badan ku ba da naga wulakanci a duniya a gidan nan to Allah ya min arzikin Yara Ni ko yanzu sai dai nace Alhmdllh.
Nazifa ce ta shigo tace me nake ji haka Wai an rushe mana bulo? Uwa tana ji tayi mukus,Nazifa tace ko waye Allah ya tsine Masa Albarka ba shi ba rahamar Allah ai mu bama kisan mummuke a fito fili Mana a fasa a bainar jama’a a gani,wallah ko waye Allah ya tsinewa uwarsa,Uwa tana ji tasan da ita suke sun San ma itace da ubansu baza su zage shi ba ko me yayi musu kyale shi suke Yi amma ita da sauran dangi basa kyalewa,Kannen Uwa ne Suka shigo su biyu Sa’ade da goshi, Nazifa tace kannen wata ma matane duk gidansu Mata sunfi yawa namijj daya ne tal Kuma tambadadde ne ma namijjin gashi nan duniya duk tayi Masa Ruku’un Dila,Sa’ade tayi dariya ba shiri tace shegun Yara Baku da aiki sai bakar magana yanzu Baballlen kanin Uwa shine tambadadde duniya ta Masa Ruku’un Dila, Nazifa tace to mene shi dan kwaya bama gwara Mata masu tausayi ba mazan wasu duk gasu nan daga sunyi aure sai matansu da Dangin matansu mace ma me tausayi da Jin kai baza ayi Addua Allah ya bada dana gari masu Albarka ba sai maza maza mace ba mutum bace sabo da jahilci ku Kuma da kuke son maza wace ta haife ku idan ba mace ba,ku sai ku canja kanku ku koma mazan ai Jahilcin banza idan ance muku jahilai kuce ku ba haka ba,Omaira tana fari da rangwada tace mu da muke da baiwa ma iri iri mune fa farin cikin mazan su taba mu ma Dadi ne,Umma ta kwade Omaira tace ke a gaban namu ne,nace dan basu San Miracle bane da fitsara bane,haka ranar Suka yini suna Shige da fice a gidan suna tijara iri iri idan wannan tazo ta tafi gidan mijinta sai wannan tazo Uwa sai barin gidan tayi ranar sai dare ta dawo shima Abba guduwa yayi sabo da jarabar yaran nan,Umma Kuwa da tana Hana yaran ta gaji yanzu Ubansu Kawai zasu yiwa ta taka musu birki sabo da mahaifi mahaifi ne ko ne yayi musu basa ce Masa kala in Banda Cele itace kadai take fada Masa abinda taga dama shima da dalili abinda ya mata dole tayi.
Auta ne ya tambayi Mami ana gobe zata tare yace zai je Kaduna Birthday din abokinsa,da kyar Mami ta bari Suka tafi da abokinsa amma tace sai dai su tafi a jirgi Suka ce to,a ranar Suka Isa Kd da yamma da abokansu Suka hadu abokin Auta Afif a gidansu Suka sauka Suma masu kudi ne, da yamma yawo Suka fita a motar Yayan Afif su uku,Auta yace Wai ku baku da classy Girls ne haba gari kayau haka, Yana yarfe hannu Yana duba ogonsa da Wise ta bashi kyauta me tsada,Afif yace wanannan agogon yayi,Nawaf yace tsohuwar Babyna ce ta bani, tayi aure? Yace tayi aure Mana kanin Baffa ta aura,suka ce gaskiya kana Shan takaici,yace ba kadan ba Allah ya bani zuciya me karfi badan haka ba da tuni ciwon zuciya ya kamani,Suna ta dariya suna tafawa su a Dole samari,Afif ya danni pics din wata katuwar budurwarsa yace kalli wannan mugun so na take,Suka leka wayar,Wanda ke driving garin kallon pics Saura kadan ya make wata budurwa a gefen titi tana tafiya dauke da katon botikin markade, Auta yace ya zaka tafi Nura zaka kade Yarinyar mutane mutum ce fa a tsaya kaje ka bata hakuri gaskiya ai bai dace ba,Parking yayi Nura ya fita yace malama,ta juyo da sauri yace dan Allah kiyi hakuri,Murmushi tayi tace kaci sa’a yau birthday Dina wlh da sai ka Sha Mari yanzu,Nura ya saki baki Yana kallonta Omaira ce ta tafi da imaninsa Yara basu tafasa ba za
su kone,Auta yana mota ya dago ya ganta Ido ya zaro yace Aunty Rabi sak wallahi Kawai Rabi tafita fari da yawa ne,Auta mota ya bude ya fito yace ke kin San wata Rabi? tace wace Kuma haka,mu duk gidanmu ba rabi dama cewa kayi Rufaida sai nace tana makkah,Yace akwai wata wallahi irinku daya,Baki ta tabe ta juya zata tafi Auta yace ke ya ina Miki magana kina Raina min hankali bafa cewa nayi Ina sonki ba ya kamo pic din Rabi na biki yace kin ganta,dariya Omaira tayi tace wannan ai Cele ce,to ita Cele yaushe tayi aure ne wai, yace wace Cele Kuma ke wanne sunanta Rabi ana ce mata Miracle,Omaira tace Kama min na sauke markaden nan abin nan nayi ne,Auta ya Kama Mata Suka sauke tasa Hannu a cikin bra dinta ta dakko wayarta Vivo karama,Nawaf dariya ta kamashi yace maza cancer ta kamaki kyayi bayani ai waya a wajen abubuwa haka Allah ya kyauta,Omaira tace kaji mutum Ina ruwanka,tura min pics din kawai,ya tura Mata pics din Rabi,ta tura Masa pics din kaf Yan gidansu tace gashi nan ka nuna mata akwai wacce aka sace tun tana jaririya a cikin jini idan itace to ta neme mu,ga Number ta,Auta ya saka number,Omaira tace Dan Allah masifaffiya ce? Auta yace tab ai Yar kunama kenan Aunty Rabi wa ta kyale,sai yaga Omaira ta washe baki tace yawwa Kar ta bar ko ta kwana kowa ya mata ta Masa haka ake so amma wani salihancin nan ba cinyewa bane,Nawaf yace ke kin ganki karama dake to anfi son mutum me hakuri,Allah Yana tare da masu hakuri ba ko Baki sani ba,ai nima bance tayi tsokana ko taci zali ba Kawai nace idan an Mata ta rama Kai nawa kake da zaka ce min yarinya,Auta ya juya abinsa mota Suka shiga Suka wuce sun manta ma suna ta labarin Yan matansu.
Karanta>>>Â Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
Ranar da Mami zata tare walima Baffa ya hada da abokansa da Kawayen Mami da Yan Uwa na kusa aka ci nama aka more amma ba kida ba komai daga wajen Walimar ya dauke matarsa sai gidansu Wanda yaji gyara an canja abubuwa da komai gida ya dauki gyara,Iyamami ko leke bata leko ba ko a jikinta.
Amarya da angonta kayan makulashe Suka ci sannan Mami wanka tayi ta fito suka yi Nafeela tayi shirinta cikin rigar baccinta me Jan hankali,Baffa ko da yayi wankan ma kasa shiri yayi sabo da zumudi Kamar yau ne ya santa,Mami Kuma sai yanga ake ana Jan aji,Baffa inda take zaune a gefen bed ya dawo a kunne ya rada mata Babyna haba Sahiba,kiji tausayina Ni rayuwata sai da ke,Ki duba Allah ki duba manzo ki tausaya min,ki agaza min,Ki bani dama please,ni rayuwarki ma kadai tare dani na godewa Allah,Dan Allah ki bani ta biyu ki saki ranki,Mami tana Jin dadi a ranta tayi kasa da kanta tace da Kai na saba in babu Kai zuciyata baza ta zauna kalau ka daina rokona,Kawai ka rike ni Amana,da sauri Baffa yace yace nayi Alkawari ga zuciyata ma karbi idan yaso ki sata a cikin kwalaba ko keji,dariya Mami tayi yanda Baffa ke zuba abin kunya matuka Kamar yaro,ko yaran ma wasu baza su iya wannan magiya da kalamai haka ba,Kumatun Mami ya sumbata yace gaki Yar farata,yau Ina cikin murna za nayi kwanan farin ciki,Mami tace nima haka, ni ai Dadi ma ya isheni ko rungumeni kayi to ya isheni nishadi ma,Baffa yace Shedan sai dai ya mutu yau sabo da bakin ciki suka Yi dariya Mami ta mike Baffa ya jawo ta jikinsa yace Ina kuma Zaki je yau Ina ango na, jikinsa ya jawota Yana bin jikin Mami da shinshina yana kissing wuyanta,Light Mami ta kashe Suka koma tsakiyar bed.
Bayan sati uku Cele ta dage tana ta faman koyon larabci idan Hajiya Hauwa tazo har Ahsan ake koyawa Hausa sosai yanzu Cele tana tsintar abubuwa da dama dama ba wuyar iyawa idan kana zaune da masu ji, Maheera tunta ta bar gidan bata dawo ba tana can tana cin duniyarta da tsinke ita da Kwartonta, tunda Cele ta tsaga Masa Duwawu ko unguwar Ahsan Bai sake bi ta wajen ba a hakan ma Maheera ce mayyarsa da kyar ta shawo Kansa itace take Kama musu hotel a zuwan mijinta ne Watarana kuma idan matarsa bata nan sai ya kirata taje gidansa a boye, wani bangare na zuciyarta Kuma tana son Ahsan dinta,taga kwartancin bazai Kai ta ba gwara idan tana gidan mijinta yafi safe,Iyayenta ta dinga yiwa kuka tana fadar karya da gaskiya suzo suyiwa Ahsan magana ya daina kula Cele,Kuma sun yarda zasu je.
Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document
Ahsan ganin Cele yanzu tana dan tsintar abubuwa sai yace yanzu cikinta ya Kai wata hudu,baki Cele ta bude tace ciki a Ina na samu ta tambaya da larabci,yace bata San anyi dashen ba? to bata Yi nisa da larabcin ba bata fahimtar wani wani Abu,Kawai sai ta karbi wayarsa ta Kira Hajiya Hauwa ta roketa dan Allah tazo, ai Kuwa tazo yace tayiwa Cele Maganar cikin ya bawa Hajiya Hauwa labarin Kan zancen da komai,Hajiya Hauwa ta dinga salati tace da Ahsan ai Cele budurwa ce bata San namiji ba Sam Kuma bata San ma tana da ciki ba ko sisi ba a bata ba bata San ma an Mata dashen ciki ba sato ta akayi shigowart Saudiya,Nan take fuskar Ahsan ta canja ya shiga matsanancin damuwa,wani tausayin cele ya kamashi abinka da Balarabe harda hawaye Yana kallon Cele Yana tausayinta,Yace dan Allah Hauwa ta fadawa Cele komai ta bata hakuri,Cele taga Ahsan yana hawaye tace mene Kuma lafiya ko solobiyoncin ne ya motsa,Hajiya Hauwa tace ke dalla ki tsaya kiji Maganar gaskiya Cele ciki ne fa dake wallahi dama na fada miki ta kwashe zancen komai ta fadawa Cele,Cele mikewa tayi tsaye tace na tuna ohhhh shine ta kaini asibiti nayi kwananki a can ya min Allura hankalina ya gushe,Cele ta taba local government dinta tace shi yasa na tashi naji Nan ya canja ashe abinda aka zuba min kenan, Hajiya Hauwa tace kinji shi Ahsan baida laifi, Kara Cele ta kwalla ta dafa kai ta sake kwala ihu sai da tayi sau uku sannan tace bazan Yi kuka ba tana Kuma share hawayenta tana cewa karki kuka bazan Yi kuka tana goge hawayen dake sintiri a kumatunta,tace na yarda da kaddara,Kaddarata ce Allah ya rubuta ba komai Zan zauna na haihu ba damuwa,Ni yanzu ta Kaka nake yi burina na hadu da kaka wannan ya Riga da ya afku amma tabbas Maheerah sai Allah ya saka min ko ban Mata komai ba,to me ma Zan mata ni Wanda zai huce min zuciyata babu shi a duniya ko me nayi Mata ban rama ba batawa kaina lokaci ma zanyi, cuta ce ta rigada ta cuceni Allah ya Isa wallahi Allah ka isar min na kai file Dina gaban Allah Kara ta na daukaka ta wajen Allah tana kotun Allah, Allah Kuma yasan yanda zaiyi dani wani bala’i ya Kare me zan ce,Ina budurwa ban San Namiji ba tasa aka sa min ciki a jikina Allah ya Isa wallahi tana kuka wiwi Cele abinda bata taba yi ba,tace yanzu mutane idan zan kwana Ina cewa ban namiji ba waye zai yarda,ya zanyi da kunyar mutane me zance, Ni tuni nasan wannan Dan iskan shi na kirki ne Dan banza ta daki Ahsan a kafada tace kai karamin alhaki ne a wajena bare ma ba Kaine da laifin ba tana goge hawaye,Ahsan Yana kallonta shima sai hawaye yake.
Cele tace kice yaushe zamu Fara zuwa awooo ta karasa da kuka ?
Karanta>>>Â Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi
Hajiya Hauwa ita dai tausayin Cele take ji ta fadawa Ahsan tace ta hakura tace babu laifinka Kuma ta karbi kaddara yaushe zaku fara zuwa awo? Ahsan yaji Dadi sai Allah yake godewa Yana Addua yace ko yaushe ta shirya,tausayi yasa Hajiya Hauwa tace Zan tabi yaushe Zan dawo karatun? Cele tace bana so bazan koya ba suje da yaren kasar su,Hajiya Hauwa tace yanzu ne ma yake da amfani,tace bana so ni na fada miki,Hajiya ta kyaleta tace idan kin huce ma Zaki neme ni tace ni dai Ina Kara Baki hakuri ta tashi ta musu sallama ta tafi tana cewa maganin Matan mu hausawa kenan da matan aure da zawara da Yan Mata burin kowa ya tafi kasar waje,gani ake kana zuwa ka Zama me kudi kawai.
Cele zaman dabaro tayi ta dinga uban kuka sosai,Ahsan ya dawo kusa da ita ya dafa Kafadarta Yana lallashinta yana bata hakuri amma Cele taki yin shuru,yayi yayi duk masifar lallaba irin ta balarabe yayi ya hakura karshe ma daki ta koma ta kulle kanta da key tayi zaman Yan bori tana rusa kuka tana cewa yanzu ya zanyi da Kaka da mutanen dunuya Maheerah ittaqillah Maheerah Ittaqillah haka Cele take fada,Ahsan Yana jinta cike da tausayawa,ta koma sai kinci kwalabar ubanki Maheerah Dan Kan uwarki me gashi Kamar Audugar Rimi wayyoooo ta Danna min kabiri Ashe ba miciji bane kasurgumin da ne a cikina da aka sa min me katon kai me suffar fatalwa….Tsit tayi Jin larabci na tashi Ahsan Yana ta masifa,ashe su Maheerah ne da iyayenta Suka Zo bada hakuri Maheerah zata dawo sunzo saji,Maheera tayi mugun girgiza ganin Ahsan ba makaho bane gashi ras dashi,Cele tashi tayi ta fito a hasale.
Kwanan Auta Uku Mami tace idan bai dawo ba wallahi sai taci mutuncinsa ba shiri Suka dawo,Ko hutawa baiyi ba ya shiga wajen Mami suna tare da Baffa Wanda sai kace sabon ango Wai ya dauki hutun angwanci na sati uku,yace Mami na dawo tace ko kaifa ni bana son yaro da yawo yaje ya hadu da abokan banza kana tarbiyya wasu suna lalata maka Yara a gefe.
Ko hutawa baiyi ba ya taho gidana Ina Shan kunun tsamiya ya shigo yace Aunty zo kiga yan gidanku,dariya nayi nace Kamar ya? yace Allah wannan Kuna da danganta yazo ya nuna min pics harda na cele a gaban kasko tana suyar awara,Nace Kai a Ina ka gansu? ya kwashe labari ya fada min, nace tab Amma wannan Kamar tayi yawa wlh muna Kama musamman me suyar awarar nan irin mu Daya,Auta yace wlh ki nunawa mayenki ku tafi tare kuji Kuma sunce wata ta bata tana jaririya,waye mayenta Nawwar ya furta Yana sakkowa daga steps,Auta yayi dariya yace Sorry,Wayar Nawwar ya karba yace mu gani ni Kuwa na kasa magana,dariya Nawwar yayi yace ah ai sai nace kece Baby,to ka kula Kar Watarana ku hadu ka rungume matar wani cewar Auta,Nawwar kunnensa ya ja yace Wai ni sa’an ka ne? nace kai hankalina ya tashi mu tafi dan Allah naji su waye,to ai kya bari dai gobe tayi ko,Auta yace ni Ina da number ma Zan Kira su bamu address din gidan,Nace shike nan Alhmdllh.
Washe gari daga ni sai Nawwar sai Auta Muka tafi can a sirri muji mene gaskiya.
Click Here To Read Book 2 Page 31-35
BA EDITING AYI HAKURI
AsmaBaffa.