Uncategorized

Rikici ya barke tsakanin Jamila Makira da mashiryin shirin

 

Wani Abu da ya ke neman zama ruwan dare a masana’antar Kannywood shine yadda masu shirya shiri mai dogon zango ke yawan samun saɓani da jarumai musamman mata kuma masu jagorantar shirin wanda irin haka ya faru a finafinai da dama mafiya shara sune Bugu zuciyar masoya inda a dalilin cire jaruma Hannatu Usman takai ta zagi darakta har Lawan Ahmad ya tsinke ta da mari a gurin daukar shirin. Kwanannan kuma muka ji yadda yadda aka cire Ummi Rahab daga Farin wata sha kallo aka dinga sa toka sa katsi tsakanin ta da Adam A Zango.

To, anan ma irin haka ce ta faru tsakanin Jaruma Rahama Kumo wacce aka fi sani da Jamila Makira da darakta da producern shirin jamila makira inda labari yafara yawo cewa an cire jarumar daga shirin har tayiwa mashiryan shirin zagin tsamar nama. Rahama Kumo dai in bazaku manta a ita ce jarumar da kwanakin baya muka kawo muku labarin ta musulunta sanadiyyar film ta kuma sha gwagwarmaya kafin ta samu fitowa a shirin Jamila makira na kamfanin brothers point multimedia da ke zuwa a YouTube channel mai suna makira tv.

Domin jin yadda lamarin ya ya faru mun tuntubi Rahama kan wannan batu inda ta bayyana mana ita ma yadda ake jita jita haka taji cewa an cire ta a shirin bata da masaniya kawai dai taga an fita location ba tare da an sanar da ita ba, kuma alaka ta dan yi sanyi tsakanin ta da masu shirin domin takan yi musu magana basa amsawa dan haka da taji jita jitar an cireta ta yadda cewa abincin ta ya kare a shirin.

Mun sake komawa ga Rahama domin jin ko me zata ce kan wancen zancen zagi da akace tayiwa masu shirin Jamila Makira Rahama ta amsa tabbas sautin muryar ta ne amma bawai tayi da niyyar sakon yaje gare su bane magana suke da wata kawarta Fatima wacce a cewar ta ita ta kai musu sautin kuma sun yi magana ne a matsayin sirri yadda da ita shi yasa har ta saki jiki tayi maganganun da tayi har da zagi inda ita kuma Fatiman bata sa musu abin da ita tace ba sai ta yanke ta sa iya muryar ta dan wata manufa ta ta.

Back to top button