Shugabannin Afirka da suka fi kowanne albashi a 2022: Shugaba Buhari ya shiga jerin sunayen
Afirka nahiya ce mai tasowa da ke fuskantar kalubale da dama kamar cin hanci da rashawa, rashin shugabanci, rashin zaman lafiya da kuma uwa uba rashin tsaro.
Wani abu da yakan shafi tattalin arzikin wasu kasashe a Afirka shi ne tsadar rayuwa.
Shugabancin kasa ba aiki ne mai sauki ba don haka ana sa ran kowane shugaba ya kasance jajirtacce idan tattalin arzikin kasar ya gaza, Talauci ya na karuwa. Koma bayan tattalin arziki da karbar bashi ya zama ruwan dare a ƙasashenmu na Afrika.
A Afirka, yawancin shugabanninmu suna kwasar albashi mai yawa ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikinsu ba.
A ƙasa akwai shugabanni 10 wadanda suka fi ko wane shugaba daukar albashi a Afirka;
9) Shugaba Paul Kagame
Albashinsa na shekara: $85,000
Adadin kuɗi: $ 500 miliyan
Paul Kagame shi ne shugaban kasar Rwanda; ya hau kan karagar mulki tun a shekara ta 2000. Paul Kagame tsohon ya taɓa riƙe shugaban sojoji na ƙasar Rwanda.
Kagame ya taba riƙe mukamin mataimakin shugaban kasar Rwanda, ministan tsaro na ƙasar da kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika.
Ana biyan shugaban na Gabashin Afirka dala 85,000 duk shekara.
8) Shugaba Alassane Ouattara
Adadin kuɗi: $185 Million
Albashi na shekara: $100,000
Alassane Dramane Ouattara shi ne shugaban kasar Ivory Coast.
Alassane ya dare a kujerar mulki tun 4 ga Disamba 2010.
Kafin ya zama shugaban kasar Ivory Coast, Alassane masanin tattalin arziki ne wanda ya yi aiki da babban bankin kasashen yammacin Afirka da kuma asusun lamuni na duniya.
Shi ne tsohon firaministan kasar Ivory Coast, tsohon gwamnan babban bankin kasashen yammacin Afirka, tsohon ministan tattalin arziki da kudi na Ivory Coast da kuma tsohon mataimakin darekta janar na asusun lamuni na duniya.
KARANTA: “Shugabannin Mafiya Yawan Shekaru A Afrika”
7) Shugaba Denis Nguesso
Albashi na shekara: $110,000
Denis Sassou Nguesso shi ne shugaban kasar Kongo. Tun a shekarar 1997 yake kan mulki.
Kafin Denis ya zama Shugaban ƙasa, ya yi aiki a rundunar Sojan Kongo a matsayin Kyaftin, Kwamanda, Kanar da Janar na Soja.
Ana biyan Denis Nguesso $110,000 duk shekara, wanda hakan ya sa ya zama shugaban kasa na 7 a mafi yawan albashi a Afirka.
6) Shugaba Hage Geingob
Albashi na shekara: $111,000
Hage Gottfried Geingob shi ne shugaban kasar Namibiya.
An zabe shi a shekara ta 2015 a matsayin shugaban kasar Namibiya na uku.
Kafin Geingob ya zama shugaban ƙasa, ya riƙe firaministan Namibiya a karkashin shugaba Hifikepunye Pohamba, ya kuma taɓa zama ministan kasuwanci da masana’antu da kuma shugaban jam’iyyar SWAPO.
Ana biyan sa jimillar $111,000 duk shekara.
5) Shugaba Azali Assoumani
Albashi na shekara: $115,000
Adadin kuɗin: $5 Million
Azali Assoumani fitaccen ɗan siyasan ƙasar Comoriya ne kuma shugaban ƙasar Comoros tun daga 2016.
Ya yi aiki a matsayin Babban Hafsa a Rundunar Tsaro ta Comorian da kuma Kanar da Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasa (NAD).
4) Shugaba Uhuru Kenyatta
Albashi na shekara: $132,000
Adadin kuɗin: $500 Million
Uhuru Muigai Kenyatta dai shugaban kasar Kenya ne.
Dan shugaban Kenya ne na farko wato Jomo Kenyatta.
Uhuru Kenyatta shi ne tsohon mataimakin firaministan kasar Kenya kuma tsohon ministan kudi. Ana biyan shi $132,000 duk shekara.
3) Shugaba Cyril Ramaphosa
Albashi na Shekara: $272,000
Adadin kuɗin: $450 Million
Matamela Cyril Ramaphosa ɗan kasuwa ne kuma shugaban Afirka ta Kudu. Ya zama shugaban kasa a 2018.
Yana daya daga cikin masu kudi a Afirka ta Kudu. Kafin Cyril ya zama shugaban kasa, ya taɓa zama shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, babban sakataren jam’iyyar National Congress na Afirka da mataimakin shugaban majalisar dokokin Afirka.
Shi ne kuma shugaban jam’iyyar ANC mai mulkin kasar Afirka ta Kudu.
Yana daukar $272,000 a shekara.
2) Sarki Mohammed VI
Albashi na Shekara: $460,000
Adadin kuɗin: Tsakanin dala biliyan 2.1 da dala biliyan 5
Mohammed VI shine sarkin Morocco. Ya zama Sarkin Maroko lokacin da mahaifinsa ya rasu a shekara ta 1999.
Shi ne sarki mafi arziki a Afirka kuma sarki na 5 a mafiya arziki a duniya a cewar Forbes.
1) Shugaba Paul Biya
Albashi na Shekara: $610,000
Adadin kuɗin: $200 miliyan
Paul Biya shi ne shugaban kasar Kamaru.
Kafin ya zama shugaban ƙasa sai da ya fara zama firaministan kasar Kamaru daga shekarar 1975 zuwa 1982 sannan kuma ya dare kujerar shugaban kasar Kamaru tun a shekarar 1982.
Ana biyan sa dala 610,000 duk shekara wanda hakan ya sa ya zama shugaban kasa wanda ya fi ko wanne shugaba daukar albashii a Afirka.
10) Abdelmadjid Tebboune, Shugaban Aljeriya – $168,000
11) Emmerson Mnangagwa shugaban Zimbabwe – $146,590
12) Denis Sassou, Shugaban Jamhuriyar Kongo – $108,400
13) George Weah, Shugaban Laberiya- $90,000
14) Nana Akufo-Addo, Shugaban Ghana – $76,000
15) Muhammadu Buhari, Shugaban Najeriya Yana Samun Dala 69,000 wanda hakan ya sa ya zama dan kadan a jerinmu.
Za ku iya ajiye mana comments ɗinku domin miji ra’ayin ku game da wannan rahoton da muka kawo maku.