Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 5 Hausa Novel

‘Kada ka damu ina jinsu.’ Ta fada sannan ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya ta rufe ido. Haka kawai zai ce taje ta kwana a cikin yara; to ai ko ‘yar da ta haifa ce shekara uku ai raba wajen kwana zasu yi. Ba zama ta fara wannan aikin ba balle ya sallamawa yaran ita. Har barci ya fara daukanta suka ji an murda kofar, ya riga ya murda mukullin da ya shiga don haka sai kofar bata bude ba. Aka kwankwasa a hankali, suka tashi zaune tare shi da Khadeejan. Kafin suce wani abu Nasreen tace ‘Abba Shukra ce ta tashi zata sha shayi.’Ya kalli Khadeeja yace ‘Oh, na manta ban gaya miki ba tana farkawa shan tea da daddare, tunda aka yaye ta ta saba. Kije ki hada mata shayi, da ga ta sha zata koma bacci.’ ‘Shayi? A wannan daren? Ko fa 4 hours basu yi ba da cin tuwo, ikon Allah.’ ‘Idan baki bata ba haka zata yi ta yiwa mutane kuka har sai an bata, kije ki hado mata gobe sai ki hada ki sa a flask kafin ta kwanta.’ Ya fada yana sake bata rai.Ta daura zaninta a kirji ta sauka daga kan gadon ta fice daga dakin cike da takaici.A tsakiyar gadon ta sami Shukra tana kuka, duk yanda zuciyarta ta kai ga kuna a wannan lokacin dole ta danne fushinta. Ta mika mata hannu tana dan murmushi tana cewa ‘Ahh! Sorry Shukra, ya aka yi? Kukan me kike yi?’ Cikin shesshekar kuka da gwarancinta tace ‘Tea.’ Ta zauna a gefen gadon ta rungumeta tana shafa bayanta tana mata magana cikin lallashi ‘Ya Isa, ya isa. Da safe ke zan fara hadawa shayi kinji Baby Shukra, kinga dare yayi ko? Muyi bacci da safe sai mu sha tea ko, harda bread ma da kwai ko?’ Ta gyada kai alamar eh, amma fa hawayenta ya ki daina zuba harda shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallabata yayinda Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara daukanta. Abbansu ya ya turo kofa ya shigo dakin, Shukra ta leko ta kafaradar Khadija cikin shessheka tace ‘Abba tea zan sha.’Ta kwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya dauketa ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti bata baki shayin ba?’’Tace sai da safe.’ ta fada tana shessheka.Ta mike ta rungume hannuwanta a kirjinta ta kalleshi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka barni da ita zata koma bacci kuma a hankali zaka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallabata idan tayi bacci zan taho.’Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka zata kwana da yunwa. She’s only 3, idan ta girma da kanta zata daina duk yayyenta ma haka barsu take raininsu.’Cikin kosawa tace ‘Kai dai ka barni da ita mana, I promise you she will be just fine.’Ta karaso kusa da shi, ta mika hannu ya dafa kafadarta yana cewa ‘Kin ga, ki yi hakuri ki hado mata shayi kada ki sakata kwana da yunwa tunda bata saba ba. A hankali zaki ga da kanta zata daina.’Murya kasa-kasa tace ‘Ohkk!’Ta wuce ta barshi a nan ta nufi kitchen; tea at 1pm, wannan wane irin tashin hankali ne? Idan da ya kyalesu ta san tabbas zata rabata da wannan shan tea din amma har wani cewa yakeyi kada ta barta da yunwa. Ta karasa kitchen din ta hado mata tea a kofi ta daukonta fito.Tana zuwa ta sameshi zaune a gefen gadon ragowar yaran duk suna ta baccinsu yayin da yake zaune rungume da Shukra; har bacci ya fara dibanta amma tana shiga ya dagata yace ‘Yauwa Baby tashi ga shayinki.’Ta tashi tana muttsike ido, ya mike tsaye ya nunawa Khadijan wajen ta yana cewa ‘Zauna sai na ajiye miki ita idan kin gama bata tayi bacci kya taho.’Ya ajiye mata ita a kan cinyarta ta fara bata shayin sannan ya fice ya barsu.Bayan ta gama bata shayin ta sakata tayi fitsari sannan ta kwantar da ita ta dan jijjigata bacci ya fara kwasarta sannan ta wuce dakin. Ko da ta shiga dakin ya riga yayi bacci, don haka ba tare da ta kunna fitila ba ta lalubi waje ta kwanta a gefen gadon. Motsin kwanciyarta ne ya farkar da shi, ya dan matso ya rungumota ta baya yana sumbatar bayan wuyanta. Ta dan motsa tace ‘Mmmm!’Yace ‘Kin San gobe yara zasu school ko? Sai ki tashi da wuri don ki shirya su.’A take jikinta yayi sanyi; gaba daya ma ta manta da wannan tunda ita ta riga ta sanar da kawarta su yi mata attendance ba zata koma ba sai tayi sati.Ya cigaba da lalubenta tana kokarin zamewa, saboda ita gaba daya ma komai ya fita daga ranta; a halin yanzu ma kuka take son yi. Sai dai haka ta hakura ta barshi yayi yanda ya so sannan ta kwanta tana fargabar yanda zata tashi nan da awowi kadan ta cigaba da hidima.Ana fara kiran assalatu ya tasheta daga bacci, sai da tayi da gaske sannan ta iya saukowa daga kan gadon. Tayi alwala ta wuce kitchen tunda da dan sauran lokaci kafin a tada Sallah. Ta tsaya a tsakiyar kitchen din tana tunanin inda zata fara; a hankali dabara ta fado mata; macaroni da sauce zata dafa musu in ya so sai ta dafa indomie da kwai suyi breakfast. Nan da nan ta dora sannan ta debo tsofaffin flasks dinsu da ta gani a store ta wanke sannan taje tayi Sallah.Ta zata idan ya dawo daga masallaci zai tsaya ya tayata shiryasu amma ga mamakinta sai ya wucesu a parlor ya koma daki ya kwanta ya cigaba da baccinsa. 7:15 am ta gama komai duk ta yi musu wanka sun shirya, suka zauna a dining table ta kawo musu abinci ta zubawa kowa Indomie da dafaffen kwai guda daya. Daga fuskokinsu ta san ba indomie suka so ci ba, suna cikin cin abincin yayinda ita kuma take zaune a table din tana bawa Shukra a baki Nasreen ta kalleta tace ‘Anti da ma dankali da kwai kika soya mana.’Ta kalleta tana murmushi tace ‘Saboda kar ku makara shi yasa nayi sauri na dafa Indomie, but in sha Allah weekend idan babu makaranta sai a soya muku dankali kin ji. Yanzu maza ki cinye kafin Abba ya fito ya kai ku school.’Suka cigaba da cin abincinsu. Jimawa kadan Abbansu ya fito yana rike da mukullin mota, suka hada baki gaba daya suka gaisheshi. Bayan ya amsa yace ‘Maza ku gama mu wuce a school kada ku makara.’ Ya kula da ragowar kwai a plate din kowa banda Habib, ya dubeshi yace ‘Kai ina naka kwan.’Yace ‘Shi na fara cinyewa Abba.’ Nasreen tace ‘Abba ni ina son dankali, Anti tace ba za a dinga soya dankali ba sai weekend.’ Ta langabe kai kamar abun tausayi. Ba tare da ya kalli Khadeejan ba yace ‘No, za a dinga soyawa kada ki damu, maza ki ci abinci mu tafi.’ Tana jinsu ta kawar da kanta, don sai dai idan shi zai dinga tashi ya soya ita bazata iya soya dankali da sassafe ba. Nan da nan suka gama; Habib ne ya fara mikewa har ya juya tace ‘Dauke plate dinka da cup din ka kai kitchen.’Ya dauke plate din ya tafi da shi, suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi.Suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi. Suka karasa shiryawa suka fice tare da Abbansu. Kafin ya dawo ta soya dankali da kwai ta jera a dining table sannan ta wuce daki; wanka zata shiga sai kuma ta tuna ko da ta yi wankan dai kitchen zata shiga tayi wanke-wanke ga shara, don haka taga gara ta bari idan ta gama aikin ta yi wankan. Sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito a shirye, kai tsaye ta riga ta shirya abincin a dining table don haka suka zauna. Yana bude kwanon yace ‘Sai da suka tafi kuma kika soya dankali? Sun fi son soyayyen abinci idan zasu tafi school.’Ta dan langabe kai ‘To ai Babe ba zan iya soya wani abu before 7am ba, da ace ma dai ina da mai aiki ne. Amma hakan ma weekend zan soya musu in sha Allah.’‘To ai da kin bari sai weekend din ma ci gaba daya, yanzu idan sun dawo ai zasu ga bawon ba dadi ai kuma ma Shukra zata gaya musu tunda ita taci. Mai aikin ma kuma za a dauka.’’Uhm.’Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba. Gaba daya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba zata bawa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta. Ya gama cin abincin ya fice ya barsu ita da Shukra.Sai wajen 10am ya kirawota a waya, bayan ta dauka yace ‘Mantawa nayi ban gaya miki ba idan 1pm tayi sai ki je ki dauko yara daga school.’Ta dan yi shiru don ta zata shi zai daukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a kasa?’’No, kin san school din ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’’Ok.’

Back to top button