Kannywood

Tirkashi! Tijjani Asase ma ya fusata ya fito yayi maganganu masu nauyi kan Adam zango da Sinana.

Tijjani Asase ya ragargaji Adam A Zango kan kiransu da butulaye da yayi.

 

A yayin da wasu daga abokan sana’ar Adam Azango ke ta lallaba shi suna bashi hakuri gami da rarrashin sa da bayyana irin dinbin Alkhairan da yayi musu wajen gina daukakar su, shiko jarumi Tijjani Asase a nasa bangaren yayi birgimar hankaka ne wanda Hausawa ke cewa in an
ga farin ka za’a ga bakin ka, inda bayan ya fadi irin soyayyar da yake yiwa zango har kawo yanzu da kuma
irin Alkhairan da Adam a zangon ya dinga yi musu a baya,
na yadda yake musu film kyauta ya basu dan su tsaya da
kafar su a karshe ya ya bayyana laifukan Adam A zangon.

A cewar Tijjani Asase Adam A zango shi ya kori abokan nasa duka yace baya bukatar su a tare da shi saboda ya sa a ransa dole sai da shi za suyi arziki, sai kuma Allah ya barshi da wayon sa, abokan nasa suka watse kuma Allah ya rufawa kowa asiri ba tare da shi din ba, da sauran laifukan sa na rashin iya mu’ama da ya fada, kamar rashin zuwa gaisuwar mutuwar wasu da rashin daga waya da sauransu.

Tijjani ya kara da bayyana yadda su falalu da Tahir I. Tahir da baban cinedu suke son Adam A Zango kamar me, a bangaren shi kuwa ya ce yayi duka ba adadi, ya sumar, ya kuma sha dauri duk akan shigar wa Adam A zango fada, taya za’a ce baya tarewa Adam A Zango fada.

 

Kalli cikakken bidiyon a kasa 👇👇👇

 

Back to top button