Halysaah Page 199 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 199…Khaleesat ta marairaice tana komawa baya a laundry room din tana kallonsa, da sauri ta makale jikin washing machine ganin ya nufota ta hade hannunta cikin rawan murya tace “Plss Noo, aiki fa Mami ta saka ni, don girman Allah kayi hakuri ka bari in kai mata Coffee dinta” Bai tanka ta ba har ya isa inda ta makale, ya jawota jikinsa yana kallonta yayi kasa da murya yace “Me ya sa kike gudu na tun jiya….” Da sauri ta girgiza masa kai zuciyarta na bugawa tace “A’a ni ba gudu nake ba wallahi, kaga yanxu aikena Mami tayi kar ta ji ni shiru” kallonta ya dinga yi, ya kai finger dinsa a hankali kan eyebrow dinta yana shafawa gently yace “Baki son ana yin abun ne?” Ta daga idanuwanta ta kallesa har sannan gabanta bai dena faduwa ba, but seeing how gently he was speaking, ta gyada masa kai kamar zata yi kuka, yace “To me kike son a dinga yi kenan? Gaya min” Sauke idonta tayi bata ce komai ba, a hankali yace “Jeeddah” Ta kasa kallonsa, yayi kasa da murya yace “Toh tunda baki so baza a sake yi ba kin ji, amma idan kin kai ma Mami shayin come to my part kin ji?” Don dai ta samu ya kyaleta ta gyada masa kai kawai, yana rike da hannunta suka fito daga room din, ta zame hannunta a hankali daga nasa ta nufi kitchen ya bi ta da kallo, Khaleesat na shiga kitchen ta sauke wani ajiyar zuciya, ta dau Coffee din don har sannan da zafinsa ta fito daga kitchen din ta tafi ta kai ma Mami. Har karfe tara saura Khaleesat tana daki tare da Mami da Hadiyah taki zuwa bangaren Ajay, cause ko kadan bata yarda da shi ba, tasan kawai ya lallabata ne taje part dinsa daga nan labari ya canza shi yasa ko attempting zuwa bata yi ba, karfe tara na yi Khaleesat ta kalli Hadiyah tace “Hadiyah mu je ki tayani let’s make breakfast” Hadiyah tace “Ohk” Mikewa tayi suka fita daga dakin tare suka sauka downstairs, before 10 am suka gama komai suka kai ma Mami breakfast daki, sauran breakfast din suka bari a dinning table, Mami na shiga bandaki Khaleesat ta kalli Hadiyah dake danna wayarta, a hankali tace “Plss let’s go to my bedroom, Ina son inyi wanka” Hadiyah ta kalleta, sai kuma tace “Tell me what u are running away from Halysaah” Khaleesat tayi dariyar yake tace “Ni fa haka nake, bana son zama ni kadai a daki, cause I am always afraid” Hadiyah tace “Afraid of what?” Khaleesat ta bude ido sosai tace “Kawai dai ina da tsoro ne, ban iya zama ni kadai ba sai inji kamar zan bude ido in ga wani abun tsoro” Hadiyah tayi murmushi, ita dai tasan a Emirate tsaf Khaleesat ke zama ita daya a part din Ajay, yanxu kuma ta kirkiri cewar ai tana da tsoron zama ita kadai, Hadiyah tace “Ke dai zaki fadi gaskiya, gudun Ya Junaid kike ko? To saboda me?” Khaleesat ta daburce ta rasa abun cewa, amma ta wayance tace “Gudun sa na me kuma?” Hadiyah na murmushi tace “To in dai tsoron kasancewa ke kadai a daki kike, ki tafi part dinsa mana ai yana can shi kadai, kinga baza ki ji tsoro ba” Khaleesat ta mata wani kallo, sai kuma tace “Ni dai don Allah ki tashi mu je ki rakani” Hadiyah bata fasa murmushin da take ba ta mike tace “To mu je” Khaleesat ta mike ta bi bayanta suka fita daga dakin suka kullo ma Mami kofa, suna shiga bedroom din Khaleesat Hadiyah tace “Wai don Allah ki gaya min gudun menene kike yi, har da wani cewa in kwana dakin ki jiya” Khaleesat tace “Ohh baki yarda ina jin tsoro ba?” Hadiyah tace “Na yarda kina tsoron mijin ki mana” Khaleesat tayi murmushi ta zauna gefen gado, kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace “He is stressing me so much Hadiyah” Hadiyah ta karasa ta zauna gefenta tace “Wani irin stress?” Khaleesat ta sauke idonta ta kasa cewa komai, after few seconds cikin sanyin murya tace “Baya bani breathing space kwata kwata, ina shan wahala sosai, and he is always not tired” Hadiyah ta sauke idonta tace “Na gane, but kinsan me, i passed through this phase too while married to Ya Jawwad, sai nake ganin ma naki nafila ne akan what i went through, and I had nobody to talk to sai nayi ma cousin sis dita magana cause I was always in pain a lokacin” Khaleesat ta kalleta a sanyaye tace “I am in so much pain too, I can’t endure anymore….” Hadiyah tace “You will endure, since I also endured too, har ya kai ya kawo na dena jin pain din, although it’s exhausting but no pain, ba tonan asiri ba Halysaah ina ga ke wani lokacin mijinki na ɗaga maki kafa, Ni fa kwata kwata babu wannan zancen a lokacin, i really suffered, and you know one thing about men, idan kika zama me korafi always akan bangaren nan da nuna rashin juriya to haushin ka za su fara ji, su dinga ganin kamar raki ne, whereas da gaske kai kadai kasan abinda kake ji, but i will tell you the scope I used da har na fara sabawa na zama me juriya” Khaleesat dai bata yarda sun hada ido da ita ba, a hankali tace “Ko za ki rubuta min kawai?” Hadiyah na murmushi tace “Ohk, get me a pen and paper” Mikewa Khaleesat tayi ta dubo mata takarda da Biro ta mika mata, Khaleesat tace “Pls har in fito wanka kar ki je ko ina don Allah ki jira ni” Hadiyah tayi er dariya tace “To zan jira ki” Daga haka Khaleesat ta mike ta shiga wanka, Hadiyah ta fara rubutu a takardan hannunta, babu abinda ta boye akan irin styles na kwanciya dake saka mace kar taji wani discomfort ko pain a yayin mu’amala, tayi rubutu har kusan rabin takardan taji an bude kofar dakin, ɗaga kai tayi suna hada ido da shi ta mike ta bar kusa da gadon pouting her mouth, ya karasa cikin dakin yana kallon takardan da ta bari kan gado ya dauka zai duba abinda take rubutawa, tana ganin haka ta nufesa da sauri zata fixge, yaki barinta tayi hakan ya saka takardan a aljihunsa yana kallonta, kamar zata yi kuka tace “Stop pls, don Allah ka bani abu na” Hakan yasa yaji yana son karanta abinda take rubutawa, ya nufi kofa ta zaro ido ta bi bayansa da sauri tace “Noo pls, don Allah ka bani” Ko kadan bata son ya ga abinda ta rubuta don har taji kunya ya rufeta, tuni ya fice daga dakin kuma bata fasa bin sa ba, dai dai sanda Ajay ya nufo corridor din, kallonsu kawai yake, Jay dai tunda ya kalli Ajay sau daya ya wuce dakinsa ya shige, Hadiyah ta kasa bin sa, ta jira Ajay ya karaso inda take tace “Yaya ka yi breakfast, mun ajiye maku a dinning table” Ajay yace “Ohk….” Downstairs ta sauka, ya bi ta da kallo sannan ya bude kofar dakin Khaleesat ya shiga, Yana tsaye dakin har Khaleesat ta bude kofar bathroom din ta fito tana daure da towel, zaro ido tayi ganinsa, tun kan ta koma bathroom din ta rufe kofa ya bi ta ciki, tayi narai narai da ido tace “Na shiga uku” Ya kulle kofar yace “Ya muka yi da ke?” Rikicewa tayi tace “Yanxu fa nake son zan je, Mami ce ta sa ni aiki ban gama da wuri ba, shi ne bayan na gama na shigo inyi wanka sannan sai inje part din ka” Yace “Ba sai kin je ba, na riga na zo ai” Kuka ta sakar masa amma babu hawaye tana rike da hannunsa cause he is standing very close to her tace “To don Allah kaje daki ka jira in fito” Jawota yayi yace “Wai ke me wayo ko?” Ta marairaice fuska tace “Ni dai ka fita pls” Bata rufe baki ba ya kwance towel din jikinta, tayi saurin rikewa with shock amma tuni ya fixge towel din ya ajiye yana kallon jikinta from head to toes da lumsassun idonsa, rungumosa tayi don kar ma ya ci gaba da kallonta tana boye jikinta a nasa, Ajay bai bar bandakin nan ba sai da ya tabbatar yasa ta tayi abinda ta dade bata yi ba, he explored every part of her body in different angle of the bathroom, ta sakar masa jiki gaba daya ta mance da wani tsoronsa, da yayi niyyar having dinta tsaf zata bada hadin kai tsabar yanda ya gama tsuma ta a wannan lokacin, sai da ya tabbatar yayi satisfying dinta and she became very weak sannan ya zame bakinsa daga nata yana kallonta, ta kasa bude ido ta kallesa saboda kunya tana sauke numfashi a hankali, ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace “Idan kin fito plss i need Irish and egg wife….” Bata bude ido ba cikin sanyin murya tace “Ohk” Ya mike ya fita daga banɗakin, sai da taji ya rufo kofar sannan ta bude ido a hankali, sai a sannan ne tayi realizing she was inside the bathtub, bata ma san ya aka yi har ta dawo cikin tub din ba…. Hadiyah na ta zaune dakin da ta shiga bayan ta koma upstairs, gashi tana son fita ta dauko wayarta a dakin da Mami take amma ta kasa fita don gudun haduwa da Jay, after almost an hour ta gaji da zama ta mike ta nufi kofa, gently ta bude kofar ta fita ta jawo kofar a hankali ta kulle, sai ga Jay shi ma ya fito kamar hadin baki, zata gudu ta koma dakin yayi saurin bin ta ya janyota, kamar zata yi kuka tace “Innalillahi, wai don Allah menene haka” Manne ta yayi da bango ya matsa dab da ita, ta zaro ido tana kalle kallen wajen tace “Na shiga uku, yaya in wani ya fito fa…” Tun da ya fara bibiyanta sai a rannan ya bude baki yayi mata magana, yana kallonta kasa kasa kamar an tilasta sa yin maganar yace “Intimacy teacher kika dawo yanxu da har kika san such bad styles?” Ta kasa kallonsa tana turasa tace “I don’t know what you are talking about plss, ni ka kyaleni” Kallonta yake babu ko kiftawa, bata fasa turasa ba tace “Don Allah yaya ka rufa min asiri ka kyaleni kar wani ya fito, wai meye haka kake yi ne” Kauda kanta tayi da sauri ganin abinda yake kokarin yi, dai dai sanda aka bude kofa sai ga Mami ta fito daga dakin da take, Jay ya sake Hadiyah bai yarda ya juya ba ya nufi stairs ya sauka downstairs, Hadiyah taji kamar ƙasa ya bude ta shige ciki don kunya, she was so very ashamed, ita ma ta kasa kallon Mami, har sai da taji alamar Mami ta koma daki ta rufe kofa, da kyar ta daga kafarta ta bar gun ta koma dakin da ta fito don bata san ko Ajay na bedroom din Khaleesat ba, zaunawa gefen gado tayi, taji baza ma ta iya ci gaba da zama ba kawai ta kwanta ta takure gu daya wishing this never happened, Ya jawwad ya ja mata abun kunya, yanxu da wani ido zata kalli Mami a gidan nan, sai Mami tayi tunanin sun saba haka, rufe har kanta tayi da bargo with so much shame. Khaleesat ta fito wanka har sannan jikinta was very weak, ta zauna gaban madubi ta busar da gashinta, sannan ta gyara ta daure gashin waje daya, shafe shafenta tayi bayan ta gama ta mike, walking slowly ta nufi gun kayanta ta fiddo wanda zata saka, bayan minti goma ta gama shiryawa sannan ta fita daga dakin, Bedroom din Mami ta nufa bayan ta zauna tayi ma Mami sannu da zama tace “Hadiyah fa Mami?” Mami tace “Bata nan Halysaah” Khaleesat ta mike tace “Bari in duba ta” Fita tayi daga dakin ta bude dakin da take zargin zata tarar da Hadiyah, da sauri Hadiyah ta sauke duvet din jikinta duk tunaninta Jay din ne ya shigo, ganin Khaleesat ta mike zaune, Khaleesat ta karasa ta zauna gefenta tana kallonta tace “Kin yi breakfast Hadiyah?” Hadiyah ta kasa cewa komai, ganin kamar a daburce take Khaleesat tace “Me ya faru, na gan ki wani iri” Hadiyah tayi narai narai da ido tace “Kin ga inyi ta avoiding Ya Jawwad a gidan nan amma bazai dena bi na yana wasu abubuwa ba, yanxu gashi daxun nan na fita zan je wajen Mami sai gashi ya fito dakinsa kawai ya kama ni, sai ga Mami ta fito ta same mu a haka, i am so ashame Halysaah, ban san da idon da zan kalli Mami ba yanxu” Khaleesat ta ɗan bude ido kamar tayi mamaki whereas ba haka bane, bata san sanda tayi murmushi ba, Hadiyah ta wani kalleta, Khaleesat tayi maza tayi keeping serious face tace “Kai amma abun nan bai yi dadi ba, you mean she caught you people very close to each other, was he holding you” Hadiyah tace “It’s not funny Halysaah, wallahi ji nake kamar in gudu in bar gidan nan in koma Naija” Khaleesat tace “Ba inda zaki je, muna nan da ke, iyaka kawai very soon za ki koma dakin Ya jawwad da kwana” Hadiyah ta jefa mata wani kallo, Khaleesat ta fashe da dariya tace “Eh mana, kawai a biyo ki da sauran kayan ki dake Nigeria, sai mu raba girki, kiyi girkin kwana biyu nima inyi na kwana biyu, you sleep in Ya Jawwad’s room, and I sleep in my room” Dariya Khaleesat ta dinga yi ganin irin kallon da Hadiyah ke yi mata ta fita daga dakin ta sauka zuwa kitchen zata yi ma Ajay abinda ya saka ta….. Da yamma kamar yanda Mami tace Mai martaba da Aunty Farida suka iso gidan, Khaleesat was so happy to see her Small Mom, barin yanda taga ta kara wani kyau tayi fresh, Hadiyah dai na makale a daki ta kasa fitowa tsabar tana kunyan haduwa da Mami. Slm…. Good evening fans, so sorry for not updating steady which I know is frustrating, in sha Allah we are almost there in few days, the book Halysaah wouldn’t have been possible without u guys, so the credit goes to each and everyone of you, kune ku ka yi making Halysaah, and I soo much appreciate the patronage, yau in sha Allah akwai giveaway, if you are in my WhatsApp groups fine, if you are reading from Arewa books just say Hi via 07087865788 I will save ur digit and add you to my group… Allah Ubangiji ya maku albarka, ya kara maku budi, ya raya maku zuri’a, sannan ya raba ku da iyayenku lafiya. Happy 2026……
