Halysaah Page 153 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 153…Da yamma wajen karfe shidda Khaleesat na zaune ita kadai daki bayan Ajay ya je dropping din Noor a gidan Aunty Murja, tasan kilan ya ma dawo ya tafi part dinsa don tun la’asar ya fita da Noor, she is so bored and tired of staying in Hajja’s part, dan parlon da take fita ta zauna wani lokacin ma ta dena fita yanxu saboda bata son issue da Hadiyah, Allah ma ya sani ta gaji da bangaren nan amma bata san yanda zata yi ba, bata san wa zata gaya ma haka ba, mai aikin Hajja ce tayi sallama bakin kofar dakin, ta amsa mata sallaman, matar ta shigo cikin ladabi tace “Ranki shi dade kin yi bakuwa tana nan parlor tana jiran ki” Khaleesat tayi shiru tana tunanin wace bakuwa tayi ita kuwa, wa ta sani a Bauchi da har za a zo wajenta, a hankali ta sauka daga kan gadon ta dau veil dinta ta fita daga dakin Mai aikin ta kullo kofar sannan ta bi bayanta, tana shigowa parlon Hajja ta dinga kallon Safiyyah da mamaki don ko daxu sun yi chatting kuma bata ce mata tana hanya ba, Hajja na zaune parlon sai Hadiyah dake kwance kan 3 sitter ta wani murtuke fuska tunda Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta karaso tana murmushi ta zauna a kan Carpet tace “Sophie” Safiyyah dai sai murmushi kawal take tana sinne kai saboda Hajja dake parion, ta kalli Khaleesat tace “Tashi ki zauna an kujera Jiddah” Khaleesat ta sauke idonta ta mike a hankali ta koma saman kujera ta zauna, Hadivah ta wani kalli Haiia iin tace KhaleesatHadiyah ta wani kalli Hajja jin tace Khaleesat ta koma kan kujera, Hajja tace “Kawarki ce wannan kenan Khaleesat ta gyada kai tace “Eh kawata ce Hajja ta kalli Safiyyah sai kuma ta kalli Khaleesat ta sake kallon Safiyyah tace “Maa sha Allah, er baka da ita kuwa kyakkyawa….” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tana kallon Sophie, Safiyyah dal sinne kai kawai take tana murmushi, Hajja tace “To bara Yakumbo ta shigo sai ta raka ki can bangaren mijin naki tun da kin ji sauki yanxu” Khaleesat taji dadin hakan sosai a ranta amma bata dago kanta ba, nan ta fara addu’an Allah ya sa Yakumbo ta shigo da wuri su yi su bar bangaren ita da Sophie, Masu aikin part din Hajja suka kawo ma Safiyyah fruits, Hajja ta mike ta koma second parlor dinta ta bar masu wannan parion, sai a sannan Hadiyah ta ja wani dogon tsaki tace “Aikin banza kiyi ta mana kwashen kwashen mutanen da bai kamata su shigo gidan nan ba, ko da yake kema by mistake kika shigo gidan ai” Ko kallonta Khaleesat bata yi ba, haka Safiyyah da ta maida dubanta kan Khaleesat tace “Kawata Yarima ne fa ya aika mota aka dauko ni tun daga Gombe” Khaleesat tace “Haba? Ai kam bai gaya min ba” Safiyyah na murmushi toce “Wallahi kuwa, da uncle dina ne zai yi drop dina sai ga mota an aiko daga gidan nan, bayan mun iso can bangarenki fa na tafi ban san kina nan ba, da naga ba kowa a can zansan kina nan ba, da naga ba kowa a can zan tafi part din Mami muka hadu da Jay a hanya shi ne ya rakoni har nan muna hira wallahi….” Khaleesat tace “Ayya ai Mami tana Gombe Safiyyah tace “Haka yace min shi ma, har na amshi numberta ma a wajensa nace zan kirata in gaisheta, da nasan tana Gombe al da na je har inda take” Mikewa Hadiyah tayi tana huci tace “Wallahi Jawwad ya fi karfin ya tsaya hira da ke har ya baki number Mami, makaryaciyar banza kawai, ke a wa har zai tsaya dogon magana dake Sai a sannan Safiyyah ta kalli Hadiyah, sai kuma ta kalli Khaleesat tace “Wai wacece wannan ne kawata? Ni fa duka nake idan mutum yace zai kawo min iskanci kema kin sani, kar in doki yarinya ace min don me a gidan nan Hadiyah ta mike tsaye a fusaçe tace “Kan bala’i, ni zaki duka?? To idan baki dokeni ba baki haifu ba, ki taso ki dokeni in kin isa, a cikin masarautar mu zaki dokeni saboda kinyi hauka? Ai ko da sai kin yi life imprisonment kuma babu uban da ya isa ya fito dake wallahi” Safiyyah ta bude baki tana kallonta, can tace “To naga kawata ma da ta doke ki ba ayi komal ba a gidan, ko dai ba ita kika ma duka wancan ranan ba Khaleesat?” Hadiyah tayi wani kukan kura ta finciko Safiyyah tana cewa “In baki dokeni ba baki haifu cikin uwarki da u ba, don Allah ki dokeni ki ga abinda zai laru yau a gidan nan, daga ke har kawar taki sai kun yi life imprisonment wallahi” Murmushi kawal Khaleesat tavi iin abinda Hadivah ke take ba tana kallonta, Safiyyah ta wani yatsine fuska tace “Kwana biyu fa kawai zan yi a nan, kai baka san abinda zaka ce ma Daddy ba….” Katse wayar tayi ta mayar cikin jaka tana cewa *Since he covered up for me all through my stay in Gombe wannan ma ai zai iya, don dai karin kwana biyu” Yakumbo ta fito parlon bayan ta gama gyara ma Safiyyah Bedroom, tana kallon Khaleesat tace “To Gimbiya bari inje a taho da abinci kafin a kira Magariba” Khaleesat ta gyada mata kai, tana son tambayarta ko Ajay na part din amma ta kasa har Yakumbo ta fita daga parlon, Safiyyah ta mike tace “Ni dai bara in shiga ciki inyi wanka in canza kaya, wani dakin aka gyara min a dakunan?” Mikewa Khaleesat tayi Safiyyah ta bi bayanta zuwa dakin da aka gyara mata, Khaleesat taga ba dakin da boxes dinta ke ciki ba Yakumbo ta gyara ma Safiyyah, instead daya dakin dake kusa da shi ta gyara mata, Safiyyah na shiga dakin ta cire kaya ta shiga bandaki har sannan tana bakin cikin abinda Khaleesat tace mata akan Ya Musty, Khaleesat ta fita daga dakin ta nufi parlon Ajay, bude kofar parlon tayi gently ta shiga ciki tana kallon bakin kofar parlon ko zata ga indoor slippers dinsa, nan ta gansu a bakin kofa alamar baya nan, tana taeva a hankali ta karasa bedroom dinsa ta kofar a hankali tana leka ciki, it was extremely neat as usual ga wani daddaden kamshi dake tashi, littafin da ta gani kan gado ta karasa ta tashi, littafin da ta gani kan gado ta karasa ta dauka tana kallon title din kamar haka “The 5 love languages” tana ta kallon book din sai kuma ta juya ta koma parlonsa ta zauna still holding the book…. Bayan magrib Yakumbo tayi sallama bakin kofar parlon, Khaleesat ta mike daga kan darduman da take zaune ta tafi ta bude kofar Yakumbo tace “Ranki shi dade ga abinci an ajiye a parlor….” Khaleesat tace “Ohk, dama bai dawo ba?” Yakumbo tace “Eh bal dawo ba ranki shi dade” Khaleesat tace “Ohk” Yakumbo tace “A hada maki ruwan dumi a bandaki yanxu ko Gimbiya?” Khaleesat tace “To Mama” Daga haka ta juya ta koma parlon Yakumbo ta bi bayanta sannan ta nufi hanyar bandakin dake parlon ta bude ta shiga, da farko Mami ce ta dinga hada mata ruwan dumin da take seat bath, tayi mata haka for 3 days sannan Yakumbo ta ci gaba da yin hakan, kullum sai Yakumbo ta hada mata ruwan dumi sau biyu a rana, bayan wani lokaci Yakumbo ta fito tace Zaki iya shiga Gimbiya” Mikewa Khaleesat tayi ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye sannan ta dau littafin da ta dauko al dakinsa ta shiga bandakin da shi, ta fi minti sha biyar zaune cikin bath tub din da Yakumbo ta tara mata ruwan dumi a ciki, duk hankalin kan littafin hannunta tana duba content c bude kofar bandakin aka yi ta daga kai don yakumbo sai ta fara knocking ko da zata shigo balle tunda ta samu lafiya Yakumbo ta dena balle tunda ta samu lafiya Yakumbo ta dena tsare ta a bandaki, ta zaro ido tana kallonsa with shock har sai da book din hannunta ya fada cikin ruwan ta cire da sauri ta ajiye tace “Meye haka? don girman Allah kayi hakuri ka fita sosai ta tsorata ganinsa a bandakin, Nannade long sleeve din shirt dinsa ya fara yi yana kallonta, tayi saurin jawo Shower gel da Yakumbo ta ajiye mata ta tsiyaya kusan rabi a tub din tana kadasa a ruwan don yayi kumfa ta yanda bazai ga jikinta ba, babu abinda ya dawo memory dinta sai daren da yayi disvirgin dinta and the pain and everything came back fresh in her brain taji hawaye sun kawo idonta zuciyarta na wani irin bugawa, ya karasa har gaban Bath tub din ya durkusa yana kallonta a hankali kamar me rada yace “Jeeddah” ta fashe masa da kuka har sannan bata fasa motsa ruwan tub din da hannunta ba duk da yayi kumfa sosai, hannu taga ya kai yana laluban Bath plug din ya cire, ta fara kokarin mayarwa muryarta na rawa tace “Nooo, don Allah ka bari piss kayi hakuri tuni ruwan ya fara raguwa don sai da ya cire plug din, ya rage sai Sud din bathtub din dake covering din naked skin dinta, taga ya zame shower cap dinta sannan ya bude shower ruwan dumi ya fara sauka jikinta, ka take masa sosai tace “Don Allah kayi haku fita pls ina rokon ka, wallahi bana so” Kallon naked skin dinta kawai yake yi bayan ruwan shower din ya wanke duk Sud din jikin nata, shower din ya wanke duk Sud din jikin nata, bal taba ganinta cikin haske a haka ba, sai dai cikin duhu ko dim light, and he couldn’t stop staring at her beautiful body, every part of her body is breathtaking, ganin da gaske ta tsorata ga kukan da take yi sosai, ya kwantar da murya yana gyara mata dogon gashinta yace “Ba abinda zan maki Jeeddah, I just want to help….” Cikin kuka tace “Bana so, kawai ka fita pisss” a hankali yace “Ohk” Mikewa yayi ya nufi kofa yana jan kafa ya fita daga bandakin, da sauri ta karasa dauraye jikinta ta fito daga bath tub din jikinta na rawa ta dau towel ta daura ko bin ta kan littafin nasa bata yi ba ta fice daga bandakin, hijab dinta ta saka a parlor ta maza ta fita zuwa Bedroom dinta zuciyarta na bugawa har lokacin. Bayan Khaleesat tayi sallan asuba tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba sannan ta koma bacci, wajen karfe bakwai saura taji ana shafa gashinta a hankali ga kamshin turare duk ya cika hancinta, ta bude ido a hankali, fuskarsa ta gani kusa da nata yayi kasa da murya yana kallon eye balls dinta yace “Take care of ur self Jeeddah, we are leaving for Abuja now…” Shiru tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, a hankali tace “Kai da wa?” Ya sauke idonsa daga nata yace “Jawwad” Ta c masa kai tace “Are you driving?” Murya can kasa yace “No Jeddah, Flight za mu bi cikin sanyin murya tace “Yaushe zaka dawo?” Ya hade forehead dinsa da nata ya saka hannunsa cikin nata hannun yana magana kamar me rada yace “Gobe in sha Allah, Sophie will keep you company har in dawo….” Nan ma ta gyada masa kai tana kallonsa, lumshe ido yayi ya hade bakinsu ya fara kissing dinta deeply, tayi wrapping hannunta a wuyansa duk da yanda zuciyarta ke bugawa amma bata yi resisting ba, he kissed her passionately for a minute kafin ya zame bakinsa a nata ya kai thumb dinsa yana shafa girarta slowly don girar nata kamar an zana mata shi tsabar yanda yake daukar hankali, yayi kissing dogon hancinta murya can kasa yace “Take care of ur self pls Mermie, zan hada ki da Ammi ki mata gaisuwa idan mun isa, tasan baki da lafiya i can’t go with you” ta sauke idonta a hankali, ta gyada masa kai, ya zame hannunsa dake cikin nata sannan ya tashi daga kanta ya nufi kofa ta bi sa da kallo babu ko kiftawa har ya fita, a hankali ta mike zaune ta jingina da gadon dakin har lokacin tana jin kamar bakinsa na cikin nata ga kamshinsa da ya cika hancinta. Throughout ranan haka Khaleesat ta wuni babu wani walwala duk da tun karfe goma na safiyan yayi mata message yace sun sauka Abuja, karfe sha biyu saura kuma ya hadata da Ammi da Umar tayi mas gaisuwa ta waya, ko da wasa bai ce ma Inteesar ba…. Bayan isha’i suna zaune dakin da Safiyyah ta sauka, Safiyyah na kallon Khaleesat dake juya fruit salad din gabanta tace “Wai ya na ganki wani iri ne duk yau Khaleesat, are you sure you are okay?” Khaleesat ta dan yi murmushi tace “Tun da nayi rashin lafiya sai kaina yayi ta min ciwo Sophie, bana son magana da yawa, baki ga yau ke kike ta ban labari ba ko magana ban son yi” Safiyyah tace “To wannan wani irin rashin lafiya ne haka? Irin wannan gidan fa mutum baya zama haka don tsaf sai a iya jefe sa ya haukace barin ke da ake jin haushinki ta ko ina, ranan mun yi waya da Nenne tace min zata je kai maki magani hope dai kina amfani da magungunan da ta kawo maki?” Khaleesat tace “Ai sai na je gidan Aunty Murja zan amshi maganin, da ta zo bata bani ba” Safiyyah tace “Kinga da ba don Ya Musty ya sako ni gaba in dawo gobe ba ai tare za mu je nima Nenne ta sam min don baki ya min yawa Khaleesat shi yasa nake kara duhu kullum dama gani baka, kowa ya bude rubabben bakinsa yace Soppie er baka” Khaleesat tayi murmushi tace “To in ta koma Kano ai sai ki je gida ki amsa” Safiyyah ta jawo wayarta dake ringing ganin ya Musty ke kiranta ta tsuke fuska tace “Kai wannan yaya Mustyn ya fiye fitina, na fa ce masa gobe zan taso ba sai ya kyaleníba, nasan cewa zai yi Daddy yana ta fada Ita dal Khaleesat bata ce mata komai ba, tana waya Khaleesat ta mike ta dau wayarta tayl mata alamar zata je ta kwanta sannan ta fita daga dakin ta kullo mata kofa, parlon Ajay ta mata alamar zata je ta kwanta sannan ta fita daga dakin ta kullo mata kofa, parlon Ajay ta shiga ta karasa har Bedroom dinsa, dim light ta kunna a dakin sannan ta kwanta kan gado ta rufa da duvet dinsa ta takure waje daya, nan da nan kamshin turarensa ya cikata ta lumshe ido, bayan few minutes bacci ya dauketa, wajen karfe sha dayan dare vibration din wayarta da ta ajiye gefenta ya tasheta, ta bude ido a hankali ta jawo wayar tana kallon screen din taga shi ke kiranta, ta daga kiran ta kai kunne ta lumshe ido tayi shiru, daga can bangaren taji yace “Jeeddah” tace “Um” Yace “Kin fara bacci ne?” Tace “Um” Yace “Alright sleep tight…” Katse wayar yayi, tun daxu ya so kiranta but saboda suna tare da Jay shi yasa bai kirata ba, gashi gobe da yamma ne tafiyarsu zuwa Tanzania ko gaya mata bai yi ba balle ta shirya kayanta…


