Hausa novels

Halysaah Page 94 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 94…Ajay ya bude kofar dakin Jay a hankali yana kallonsa, zaune ya samesa kan kujera yana danna wayarsa, karasawa cikin dakin yayi ya zauna still looking at him, shi dai Jay bai kallesa ba he was just pressing his phone, wani lokacin har mamakin karfin hali irin nasa Ajay yake yi ga dakiya da basar da duk wani situation that is a threat to him in anyway, bayan kusan minti daya Ajay yace “I think this shouldn’t be something to be worried about Bruh, I guess you weren’t expecting less duba da cewar baka sanar masu wacece yarinyar da kake son aure ba, sannan baka gaya masu matsayinta ba so their reaction is nothing to be surprised or worry about, even our dad was a bit disappointed at first after finding out truth, so sauran ma duk za su yi give up su hakura daga karshe, just that you have to turn deaf ear since the king is fully in support of you” Shi dai Jay bai ce komai ba kuma bai ɗago kansa ba, mikewa Ajay yayi yace “Abba yace kaje yana jiran ka…” Daga haka ya juya zai fita daga dakin sai kuma ya karasa gaban mirror dake dakin ya dau turarensa biyu da Jay ya ajiye wajen, ta madubi yaga Jay na kallonsa, Ajay ya bude turarurrukan yana perceiving kamshinsu yace “Why will you hijack my birthday gift…” Shi dai Jay bai ce masa komai ba, Ajay ya dau wanda kamshinsa yayi masa ya bar masa dayan sannan ya fita daga dakin. Jay na zaune gaban Mai martaba idonsa a kasa yana sauraronsa, Mai martaba yace “Don haka ka kwantar da hankalin ka Ahmad, babu me hanaka auren yarinyar nan as far as I am concern don baza a maida ni karamin mutum ba, Fulani kuma ka kyaleni da ita ni nasan yanda zan yi da ita, kaje ka ci gaba da shirye shiryen ka tunda kaga ba lokaci me tsawo aka tsayar ba don nasan ire iren issue din nan dole zai yi arising daga ɓangaren iyayenka mata dama, daxu mun yi magana da Shafa’atu akan kayan da ake hadawa na aure, so ita zata hada na ita wancan yarinyar, su kuma nan su hada na Hadiyah ina ga zai fi” A hankali Jay yace “Nagode Abba, Allah ya kara girma” Mai martaba yace “Za ka iya tafiya Ahmad” Mikewa yayi Mai martaba ya bi sa da kallo har ya fita. Jay na fita parlon Mai martaba babu dadewa sai ga Aunty ta shigo parlon, ta ajiye masa fruit din da ta kawo masa ta zauna tayi masa sannu da hutawa sai kuma tayi shiru, bayan wani ɗan lokaci cikin kwantar da murya tace “Ranka shi dade dama wata er shawara ko ince suggestion nake son badawa idan ka bani dama” Sarki na kallonta calmly yace “Ina jin ki Fulani” Ta gyara zama cikin nutsuwa ta fara magana tace “Ranka shi dade akan zaman Meeting din daxu ne da aka karesa babu dadi a zukatan mu gaba daya, sam ban ji dadin irin maganganun da Fulani Asiya tayi maka akan ɗan ta ba a gaban kowa da kowa, kuma ba yau ta saba maka irin wannan ba, amma na yau yayi min ciwo matuka, tun safe har yanzu bani da sukuni, ni kuma bana son biyeta mu yi batattciya a gidan nan, shi ne ni a nawa tunanin nake ganin for peace to reign da an hakura da batun auren ita bazawaran nan tunda har Asiya ta nuna bata so, yanxu zancen da nake maka maganar nan duk ya zagaye masarautar nan kan kace me kuma har cikin gari sai maganar nan ta fita, kaga nan jama’a za su dinga ganin don ba ɗan cikin ka bane shi yasa ka amince da bukatarsa na auren Bazawara, don guje ma wannan zargi ina ga zai fi kyau a ajiye batun auren yarinyar kawai mu yi facing na Hadiyah ranka shi dade, ba wannan karon bane na farko da mutane ke ganin kamar kana nuna bambanci tsakanin Jawwad da Junaid, ita dama Asiya kullum tunaninta a haka yake tana ganin baka yi ma ɗan ta adalci don kawai ƙasa ya rufe ma ubansa ido, to ina amfanin wannan ranka shi dade ana ɓata maka suna a gari? Tun asali bai kamata ka biye Jawwad da maganar nan ba duba da irin zaman da uwarsa ke yi da mu da wasu abubuwa marasa amfani da ta dauka ta saka a ranta taki a zauna lafiya, don haka ni a nawa karamin tunanin ya kamata kayi watsi da maganar bazawaran nan don a samu zaman lafiya a gidan nan ka kuma guje ma kanka zargin da jama’a za su fara yi maka, tunda ga ɗan cikin ka Junaid har yanxu ko buduwar auren ma bai da ita kuma baka ce lallai sai yayi ba, yanxu fa kamar ace Walid ya kawo maka bazawara mara asali yace zai aura ne, zaka fara sauraronsa? Amma fa ni a karamin tunanina nake magana ranka shi dade tunda ban fi ka hangen nesa ba, kuma ina fatan ban ɓata maka rai ba Ur Highness” Mai Martaba dake ta sauraronta ya ɗan yi murmushi yace “Kina zaune da ni shekara da shekaru kin taɓa ganin maganganun mutane ya girgiza ni ko ya hanani abinda nayi niyya Fulani?” Aunty tayi shiru, yace “Don haka in this case i don’t think there is anything that will move me, as far as Ahmad is okay with marrying the lady, I am also okay with that, kawai dai Hadiyah ce zata zama matarsa ta farko kafin ita yarinyar wanda na riga na sanar da hakan tun farko, Walid kuma da kika ce in yau ya kawo min bazawa yace yana so zan basa shawara ya hada da budurwa duk a aura masa, hakan ma gata ne ai” Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya ganin babu nasara a plan din nan ma, shiru tayi bata sake cewa komai ba. Har washegari Jay bai yarda ya hadu da Maminsa ba cause deep down he was really disappointed, tun jiya har yau bai dawo dai dai daga shock din da ya shiga ba, it was something he never saw coming, ko da ya dawo masallaci ko zuwa gaisheta kamar yanda ya saba bai yi ba ya koma bangarensa ya kulle, bai san ita ma ana idar da asuba ta bar masarautan ba da traveling luggage dinta…. Wajen karfe shidda na yamma Malam Ali na tsakar gida bakin pampo yana alwala, Nenne na zaune kan farin kujeran roba tana kara jaddada masa abubuwan da za ayi ma Khaleesat na fita kunya tunda ba karamin gida za a kai ta ba, Tace “Wallahi Ali sai kaga setin kayan gadon aka ce mana miliyan uku babu ragin ko biyar, setin kujeru kuma Miliyan biyu cif cif, in ba ‘ya yan sarakunan ba ma ni bana jin akwai er da za ayi ma wannan setin kayan dakin, ko iya su muka kai mata babu me renamu wallahi, akan dai ace mu cakalkala kudi mu siya mata tarkacen banza masu arha da baza a ga darajarsu ba, don haka ni dai ga dubu dari biyar ina da shi a ajiye, Parida zata kawo Miliyan daya tace, ita Zahra’u dama babu ita a lissafi in ba dogon hancinta zata kai kasuwa ta siyar ba, don haka nake baka shawara wannan gidan nan naka na Mariri da nawa ka siyar kawai mu fita kunya, ko miliyan hudu aka samu aka siyar da gidajen kaga ai sai mu fitar da er mu kunyar gidan sarauta Ali, wallahi hankalina a tashe yake ga lokaci da aka sa ba mai tsawo ba, kan kace me zaka ga kamar gobe ne” Malam Ali dake ta sauraronta ya idar da alwalan da yake sannan yace “Allah ya rufa asiri ya nuna yanda za ayi amma siyar da gida kam bai taso ba Nenne, shikenan fa gare mu….” A fusace Nenne tace “Baza ka raba kanka da kalman nan na shikenan gare ka ba, shi kuma wannan da muke ciki na gwamnati ne?” Malam Ali dai bai ce mata komai ba, don su ne suke ma gidan nan kallon gidan zamansu amma banda shi, har cikin ransa ya riga ya sa cewar gida ne aka basa ya zauna na ɗan wani lokaci ya tashi, Tsayuwar mota suka ji a kusa da gate, Nenne ta kalli gate din, can tace “Kaddai tsinannun iyayen Awdul din ne suka sake biyo ka…” Mikewa tayi ta nufi gate din fuskarta babu rahama, wasu manyan mata ta gani har su hudu cikin shiga ta alfarma, suna kallonta suka ce sannu, Nenne ta koma gefe tace “Yauwa sannun ku, ko batan hanya ku ka yi ne” Daya daga matan tace “Ba nan ne gidan su Halysaah ba?” Nenne tace “Eh nan ne, Khaleesat ba, Malaman makarantar su ne halan?” Matar tace “To mu dai shiga daga ciki ko?” Nenne ta juya ta koma ciki da sauri tana cewa “Bisimillan ku, sannun ku da zuwa, ai Khaleesar ma ta ɗan yi tafiya bata nan, amma ku shigo ciki” Suna biye da ita har zuwa parlon gidan, shi dai Malam Ali bai ce masu komai ba kamar yanda babu wanda ya ce masa komai balle su gaishesa, Nenne na shiga parlor ta kora yaran Mama Shatu dake zaune suna kallo, duk suka fita daga parlon, ko wacce a cikin matan ta samu kujera ta zauna a parlon, Nenne na murmushi tace “Halan kun samu labarin an sa mata rana ne, bari in kira maku uwarta tana ciki” Da sauri Nenne ta tafi dakin Umma ta sanar mata Khaleesat tayi baki kamar Malaman makarantar su a Amurka don ko wacce shiga tayi ta alfarma ga gwala-gwalai, a tare Umma da Aunty Farida suka fito parlor, haka kawai Umma taji gabanta ya fadi, ta dai karaso parlon ta zauna ta gaishesu duk suka amsa, Aunty Farida ma ta gaishesu tana kallonsu, ledan pure wata guda Nenne ta kinkimo ta kawo masu tsakar parlon ta ajiye tana cewa “Wallahi yaran duk sun shanye wanda ke prij me sanyi” Matar dake tanka Nenne tun daxu tace “Mun san duk baku san mu ba, baku kuma san daga inda muke ba” Nenne ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace “Ba Malaman makarantar su Khaleesah bane a Amurka?” Matar tace “Ko daya, ni sunana Hajiya Fatima, kuma ni din kanwata ce ga Mai martaba Sarkin Bauchi…” Ƙabbara Nenne ta saki ta mike tsaye tana tafe hannu tace “Lale lale, lale marhaba, sannun ku da zuwa, ashe manyan baƙi muka yi bamu sani ba, wallahi ba a sanar mana kuna hanya ba” Hajiya Fatima tace “Yana da kyau dai ki fara sauraronmu ki ji me ke tafe da mu tsohuwa” Nenne ta zauna kan Carpet tana kara masu sannu da zuwa baki har kunne, Hajiya Fatima ta nuna warce ke zaune gefenta tace “Fulani Asiya kenan, matar yayanmu Marigayi sarki Ahmadu Yusuf, mahaifiya ga Ahmad Jawwad….” Nenne tayi shiru tana kallon Mami da idanuwanta kamar za su fito, haka ma Umma da Aunty Farida da duk jikinsu yayi sanyi tun Hajiya Fatima bata fara introduction ba, suna ganinsu sun san babu alkhairi a tattare da zuwan su dama, Hajiya Fatima ta ci gaba da magana cike da isa da gadara tana nuna warce ke zaune 2 seater tace “Wancan Hajiya A’isha kenan kanwar Fulani Asiya, ta kusa da ita kuma Hajiya Nafisah kanwar matan Mai martaba Sarkin yanxu….” Nenne tayi karfin halin cewa “To Allah Ubangiji dai yasa lafiya, don ni ban gane kan wannan zuwan naku ba kuma” Hajiya Fatima tace “Gaskiya ba lafiya ya kawo mu ba tsohuwa, duk da zuwa muka yi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba” Nenne ta ɗaga kai ta kalleta baki bude, cikin nutsuwa Mami ta fara magana tace “Ni ce Mahaifiyar Jawwad, kuma Jawwad shi kadai Allah ya bani a duniya, a burikan da nake da shi kan Jawwad a duniya babu auren bazawara ciki, ko kuma auren wata kabila can baya ga cikakkiyar Hausa Fulani, tun daga neman auren da aka zo aka yi na ɗa na har saka rana bani da masaniya akan ko daya, sannan duk wani bautatawa da kashe uban dukiya da Jawwad ya dinga yi akan er ku da ma ku kanku babu wanda ban sani ba, amma duk ba wannan ne damuwata ba, kuma bazan ce zan amshi duk wani abu na alkhairi da yayi maku ba, kamar yanda nace maku mun zo cikin aminci ne babu tashin tashina, don haka tun da girma da arziki ku cire ran auren er ku da ɗa na Jawwad idan ba haka ba wallahi duk wani mummunan matakin da na dauka a kanku ku kuka siya, er ku ba sa’ar auren Jawwad bace don shi din ɗan gidan sarauta ne, ɗan sarki jikan sarki babu abinda zai yi da er ku bazawara, kai ko da ba bazawara bace wallahi babu abinda zai yi da wata kabila warce ba ma na kasar nan ba, ina sake jaddada maku tun da girma da arziki ku janye batun auren er ku da ɗa na….” Cousin sister din Aunty me suna Aunty Nafisa tace “Iya tatsarsa da ku ka dinga yi ma ya isa haka, don hidimar da yayi maku in muka ce yafi na miliyan dari biyu tsaf bamu yi karya ba, da ace tsiya ya kawo mu hatta gidan nan wallahi sai mun kwace amma mun zo maku cikin lumana don mu din ba kananun mutane bane kuma mun fi karfin dukiyar da Jawwad ya kashe maku, kawai abinda za ku yi a zauna lafiya shi ne ku janye batun auren nan cikin ruwan sanyi tun kan tijara ya biyo baya” Har sannan Nenne ta kasa rufe bakin da ta hangame zaune kan Carpet with shock, Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallonsu daya bayan daya tace “Mu janye batun aure sai kace mu muka je neman auren Jawwad din? Ina ce wa enda suka zo neman aure su za su dawo su janye sannan su amshi kudin da suka kawo, kuma ni a iya sanina ba mata bane suka zo neman auren Khaleesat, mazan nan dai da suka zo neman auren su nake tunanin za su sake dawowa su ce sun janye a maido masu da kudin ɗan su, ko kuma mafi sauki in kin isa da ɗan ki ai tun daga gida zaki masa umarnin ya janye ba sai kin zo mana nan ba, a yanxu mu dai bamu da sauran magana da ku sai dai iyayenmu maza su saurari wakilan Mai martaba, duk da dai ban san ko gidan sarautar taku har dankwali da dankwali na zama batun neman aure ba” A tare Hajiya Fatima da Hajiya Nafisah suka mike suka daka mata wani tsawa suna nunata da ɗan yatsa, Hajiya Nafisah tace “Ke karamar er iska mu kike gaya ma magana? Kin san su waye mu? Who the hell do u think you are?” Aunty Farida ta ja wani dogon tsaki ta juya ta bar parlon alamar bata da lokacin ci gaba da basu amsa, Cikin azama Aunty Nafisa ta bi ta a fusace, Mami tayi saurin dakatar da ita tace “Dawo Nafisah, dawo, kyaleta kawai” Umma dake hawaye ta dinga basu hakuri a rikice tana cewa “In sha Allahu duk bazai kai ga haka ba, in dai ta bangaren mu ne babu batun wannan auren da izinin Allah, mu mun janye ba wannan batun in sha Allah, don Allah ku yi hakuri” Mikewa Mami tayi tana kallon Umma cikin nutsuwa tace “Da ya fi maku, don in baku janye cikin lumana ba za ku janye saboda tashin hankali, bana hada ɗa na da kowa, kuma ba don ko wace irin mace na haifo ma ɗa na a duniya ba, in ma wani abu ku ka yi ma Jawwad irin naku na yan kabilar ku to tun wuri ku warwaresa tunda kun tatsi arziki son ranku daga jikinsa har da siya maku gida, to duk nafi karfin abinda yayi maku bazan kuma ce zan amshe ba, kawai dai ina me maku gargadi da babban murya ku raba kanku da ɗa na, ku nisanta er ku daga ɗa na” Mami na kai wa nan ta nufi kofa, sauran matan suka bi bayanta suna yatsine yatsine, rabon Nenne da shiga irin wannan shock din tun da Motar yan sanda suka zo tafiya da Malam Ali farkon case dinsa da Baban Abdul, Umma ta zauna kan kujera ta dafe kanta ta dinga kuka, Mama Shatu dake makale bakin kofar dakinta sai zazzare ido take taki karasowa cikin parlon, Sai a sannan Nenne ta samu bakin sakin salati ta rushe da matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma da mutuwa, Duk wannan abun da aka yi Malam Ali dake zaune Balcony yana ji, har su Mami suka fito basu ce masa komai ba suka nufi gate. Sai bayan Magrib Aunty Farida ta samu Ajay a waya, he was shock an speechless bayan ta sanar masa abinda ya faru don sai da ya mike tsaye daga zaunen da yake, gaba daya ya ma rasa me zai ce, after some seconds ya dake yace “Zan kira ki Aunty” Yana katse wayar ya fita zuwa bangaren Mai martaba, Sarki ya fi minti biyar bai ce komai ba bayan Ajay ya sanar masa abinda Aunty Farida ta gaya masa, kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai, after another 2 minutes ya numfasa cikin nutsuwa yace “Dau waya ka saka min Number Mahaifin yarinyar” A hankali Ajay yace “Bani da numbersa ranka shi dade” Mai martaba yace “Sa min Number Faridan” Mikewa Ajay yayi ya dau wayar Mai martaba ya saka masa number Aunty Farida sannan ya mika masa, Mai martaba ya amshi wayar yace “Wannan karan zan yi maganin Aseeyah, i have tolerated her for so long for the sake of my late brother, amma zan nuna mata na fi ta iko da Ahmad, kuma juma’an nan mai zuwa in sha Allahu za a daura auren nan” Murya can kasa Ajay ya fara basa hakuri don har ya mance rabon yaga bacin ran Abbansa haka, Mai martaba ya mike yana rike da wayarsa ya shiga dakinsa, ashe duk wannan abun Aunty na tsaye bakin kofa tun da taga Ajay ya taho parlon Abban nasa ta biyosa ta tsaya bakin kofar duk tana sauraron su, mikewa Ajay yayi zai fita yaga Aunty tsaye bakin kofar tana masa wani matsiyacin kallo, sauke idonsa yayi ya canza wata hanyar don kofa biyu ne a parlon.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* 07087865788

Back to top button