Zaune take ko ajikinta duk da kasancewar ce-ce kucen ake yi a harabar station din.
Tamkar ba ita aka kawo ba, domin inda aka kawo ba,domin inda sabo ta saba,hakan ba sabon al’amari bane a gareta.
Wani Kofir ne ya ƙaraso gareta da fadin, ” ke Wai ba mai zuwa belinki ne?”
Cikin isa ta kare masa kallo kafin ta ce, “Je ne sais pas (ban sani ba).
A fusace ya dago yana kokarin kai mata mari.
Ya ci gaba da magana,”Pourquoi tu te mêle dans les affaires des marié ? Même s’il va la tué quel ton problème. Tu les as vus ensemble non?
(in ban da jaraba ina ke ina shiga harkar mata da miji? Ko kasheta zai yi menene matsalar ki? Ba tare kika gan su ba?.”)
Zeeyter ta ce, “La femme n’est pas une exclave (mace ba baiwa ba ce) bai dameni ba da cewa suna son juna ko aa ba zan bari a idanuna aci jarafin ‘Ya mace ba.”
“Na ji Yanzu ki kawo kudin beli tunkan inyi ƙasa-ƙasa da ke,kuma daga yau kar in kuma gani ko ji an kawo ki station dinnan.”
Jika (dubu ɗaya) ta miƙa masa sai da ta fice can kan ta juyo ta masa gwalo kafin ta ci gaba da tafiya.
Tafiya take tana tsintar ledoji da robobi ko ajikinta har ta isa matsuguninta.
Zuwan ta ke da wuya yara suka fara taruwa kowan ne ɗauke da buhun ledoji da gorina.
Zama tai tana karɓa ɗaya bayan ɗaya tana basu naira ashirin, Hamsin, Ɗari kowani yaro na fita cikin farinciki, mutane da yawa na mamaki abubuwan da suka kasance shara ana nisanta ita kuma su take kusanta har tana iya biyan kudi ga duk yaran da suka ɗibo mata.
Sai da ta gama tattarawa tas ta sa cikin babban buhu ta kulle.
Fita tayi ta siya pure water da biredi sai da ta zauna ta cinye tas kafin ta kulle karamin ɗakin.
Domin sauke cikakken littafin sai ku danna inda aka saka Download
WRITTEN BY: AISHA SANI ABDULLAHI
NOVEL NAME: YEL COMPLETE
UPLOADER: AIHAUSANOVELS
DOCUMENT SIZE: 236KB
DOCUMENT TYPE: TXT
MODIFIED DATE: 15- JULY -2022
CATEGORY: LOVE STORY
PRICE: FREE
Proceed To Download YEL Complete Hausa Novel Document.
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More
DOWNLOAD: “HARIJI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT”
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Copyright
If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com