Uncategorized

Matar Makaho Part 19 complete hausa novel

MATAR MAKAHO

Chapter 19

“Daga yau banason kara  gani koh jin ka kira khadija a waya yafi sau biyu a rana, na gaji da halinku kunce ba soyayya kuke va ?sannan kai bakada aiki sai kiranta karfa ka manta kai d’alibin kiwon lafiya ne, bai kamata kana wasa da karatu ba”?

Insha Allah Aunty za’a kiyaye.

“Sannan ke kuma khadija kinga dai kokarin shiga ss 2 kike, kuma niyata in kika dage saina miki registration in waec next year,  amma tunda wasa zaki saka a ranki bismillah zakiyita zama har 21 years a secondary”

Shap wayaga maman aji, kalamu yace yana dariya.

“Kaga banason shashanci kalamu, ina muku fad’a kana sako wasa”

Sorry Aunty zamu kiyaye yace yana kallon khadija, ke akwai sauran shinkafa ki zubamin yau nanne na tuwo ta dafa?

Babu kawai khadija tace tana mikewa  ta shiga daki.

“Kaga kalamu tashi akwai macaroni data dafa a tukunya kaje ka iba tunda kitchen in ba bakon ka bane, karku dameni da surutu kaina ciwo yake”.

Mikewa yayi ya shiga kitchen in ya ibo makaroni da miyar kifin gesha, yana ci yana latsa wayarsa don yanzun sumayya bata surutu kamar da.

*************

Muhammad basu farka ba kuma ba’a tadasu ba sai kusan 10 na safe suka farka don kansu, wanka sarki yayi sosai yaji sauki jikinsa yayi karfi, kaya ya saka muhammad ma wanka yayi yasha jumfa da aka kawo masa mai masifar kyau da tsada, abincin karyawa aka jera musu a daining tare suka karya su biyu suna hira gwanin sha’awa, a hankali sarki yace muhammad wai nikam ban tambaye ka kaninku ba?

Wanne kenan Abbajo?

Kanin salim mana.

Ai macece khadija tananan.

Allah sarki yanzun fa shekarun ta 18 da wata 9 ta kusa 19?nasan itama yanzun ta kusa nabila koh?

Eh Abbajo ta girma abinta.

Allah ya raya mini ku ta farkin islama?

Ameeen, haka suna ci suna hira har suka gama yusuf ya gyara rawanin sa yana rike da hannun muhammad sukayi fada.

Ana bude musu kofa suna shiga saida gaban muhammad ya fad’i, ganin wasu jajayen buzaye, cikin su harda baba da gidado da badaru a zazzaune, sosai fadar ta cika makil da manya da yara alamu dai yusuf yasan da taron, sake hannun muhammad yayi ya zauna a kujeransa  yama muhammad nuni da kasan cafen.

Ba musu muhammad ya zauna a hankali, yayinda mutane kibinsa da kallo na mamaki sosai.

 a hankali yusuf yasa hannu ya ja rawanin fuskar sa, take fuskar nan mai kamala da dattako ya bayyana koh yaransa basu samun ganinta a araha irin na yau, kowa na kasa yusuf ne kawai a kujera.

Gyaran murya yusuf yayi, Asslamu Alaikum warahamatullahi wabarkatuhu.

Gabaki d’aya jama’an dake falon suka amsa masa sallamar.

Na gode Allah daya nuna mini wannan rana,  wanda ban taba tsammanin ganinsa nan kusa ba, koh ince ban taba sa ran ganinsa ba,Ayau xan sanar daku yan uwana don duk fadar nan yan uwana ne  in aka cire mutane uku,ayau xan sanar daku abinda nasan dayawan cikin ku zasuyi mamaki,   muhammad Al’ameen, d’aya daga cikin masu aikin gidan nan D’anane, kuma shine a gabana.

Gabaki d’aya falon ya d’auki surutan mutane, daker aka samu ya lafa, yaci gaba da magana, nasan dole jama’a zasuyi mamaki Amma banda mahmah mahaifiyata, don ita tana d’aya daga cikin mutanen da suka san da wannan magana,mahmah ya kira sunan mahaifiyar sa dake xaune a gefe.

Na’am .

A taushashe yace, Mahmah ina son ki sanar dasu Asalin abinda ya faru shekarun baya da suka wuce, bani da koshin lafiya sosai kuma inbabu damuwa ina son kiyi da hausa wa’inda basa ji, Ramadan yana fassara musu.

Gyara zama mahmah tayi ta fara magana kamar haka.

*SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE* 

 Masarautar karfe shine cikekken sunan masarautar gidan nan, wanda ke d’auke da tambarin zaki ya samo asaline tun bayan shekaru da suka shude, ka’idar masarautar  ne duk yarima mai jiran gaso za’a makala masa sarka na magajin masarauta, sarkane daya samo asali daga makafan masarauta,  duk wanda ya d’aura sarkan badai tsafi jifa koh tsibbo ya kamasa ba saida ikon Allah.

mutallaf shine cikekken sunan mahaifin yusuf, a lokacin sarki ne yana da matarsa ta farko mai suna Hauwa-kulu sai dai Allah bai basu haihuwa ba har girma ya soma kama mutallaf don a lokacin harya haura shekara 50, hakan yasa kasa kara aure ya auro Hajara cikin ikon Allah shekara na zagayo wa hajara ta haifa masa yarinya mace, duk da yaso d’a namiji Amma hakan bai hanasa murnan samun mace ba, aka saka mata sunan hauwa-kulu yama uwar gidan sa takwara, haka hajara tayi ta haihuwar mata har hudu rus, sosai tsoro ya shiga zuciyar mutallaf, koh baida rabon d’a namjine kasancewar su a zuriyarsu ana yawan haihuwar mata, sama da maza gashi yana son magaji ga girma ya kamasa, Amma daga baya saiya maida lamuransa ga Allah, yaran nan kaf a wajen hauwa suke ita ke kula dasu kasancewar ta bata taba haihuwa ba kuma zaman lafiya suke da hajara.

Hajara ta sake samun ciki sam wannan karon mutallaf bai kwallafawa ransa namiji zai haifa ba sam, cikin ikon Allah hajara ta haifi d’a namiji yaro yaci suna yusuf, tunda aka haifi yusuf mutallaf ya d’auki son duniya ya d’aura masa bama shi kad’ai ba duk wani masoyinsa nason yusuf, kuma aka d’aura masa sarkan magajin masarauta, saida hajara ta haifi yusuf daga shi bata kara haihuwa ba.

Yar kaninta hauwa ta d’auko tana riko mai suna zahra, lokacin yusuf nada shekara goma sha biyar, sosai zarah keson yusuf ganin saukin kansa babu izzah koh nuna isa mutum ne na mutane, bai d’auki son mulki ya sakawa ransa ba wannan yasa zahra keson maganar sa.

A lokacin da yusuf ya cika shekara 20 yayi haddan Alkur’ani mai girma da haddisai,  yana cigaba da karatunsa na gaba da secondary, hauwa ta kwanta ciwo wanda kafun ta mutu saida ta nemi Alfarman mutallaf daya had’a aure tsakanin yar d’an uwanta zahra da yusuf, koh bayan ranta za’a tuna da ita a masarautan karfe, kuma zuriya vai kare tsakanin ta da mutallaf ba, babu wani shamaki mutallaf ya Amince mata.

Bayan mutuwar hauwa mutallaf ya tada maganar auren yusuf da zahra, daman zahra nason yusuf wanda kowa ya sani sai dai shi yusuf inne bayayinta a lokacin, yaso gardama da nuna shifa Aure ba yanzun ba sai ya girma,  Amma mahaifinsa ya murza ido akan lalle lalle auren Addanayen sa da za’ayi guda biyu Kafshatu da maisara tare za’a had’a da nasa, yusuf yayi iyya yinsa akan bayason zahra,  abasa dama ya nemo wance zai aura Amma ina mutallaf yace bazai Aminta ba.

Rana bata karya Saidai uwar deya taji kunya, a ranan da aka zartar amatsayin ranan d’auren auren yusuf da yan uwansa ya cika, Amma abin takaici an waye gari babu yusuf a gidan Sarauta.

Sarki ya shiga tashin hankali Amma daga baya saiyayi zuciya akan duk inda yusuf yaje wata rana zai juyo gida, in ma bai dawo ba yama kansa, haka aka d’aura auren zahra da wani d’an uwanta.

Tunda sarki ya rasa yusuf ya shiga wani irin matsanancin damuwa, ganin an share shekara goma babu yusuf babu a lamansa a lokacin hajara ta sake haihuwar na miji zulkiflu, sosai sarki yayi murna ya samu wani d’a na miji,  sai dai ganin girma ya fara kamasa gashi shekaru naja yana sonyin murabas Amma babu magajiiiii.

Shekaru sunja Amma shuru babu yusuf babu labarin sa, har hajara ta sake haihuwar wani d’a na mijin (Ramadan)dayake daman ita akwai kuruciya a tare da ita, Yusuf kam bai dawo ba shekaru sai tafiya suke har mahaifin sa ya kwanta ciwon ajali mai tsanani, a lokacin zulkiflu ya girma yakai saurayi, ga yan uwansa mata duk sunyi aure su hudu gashi mazajen su manya ne a kasa wasu kuma sarakuna.

Hade Hannu sukayi aka bazama neman yusuf kasa da kasa Amma ina ba’aga yusuf ba gashi jikin mutallaf sai kara tsanani yake,  baida magana saina d’ansa yusuf yana son ganin d’ansa kafun numfashinsa na karshe.

Rana tsaka saiga shi an gano yusuf yana NIGERIA Kuma a ranan aka samu labarin An kaisa prison, bai kwana ba aka cirosa washe gari sai gasu a NIGER Har gaban mahafinsa dake kwance aka dukar dashi.

Ganin halinda yusuf yaga mahaifinsa a take kuka ya kamasa tare da neman yafiyar mahaifinsa, sai a lokacin nadama tazo masa ganin yanda uban ya tsufa matuka, shekaru sunja, da ba’a d’aukosa ba da shikenan daker ya sake ganinsa sai wani ikon Allah.

Mutallaf dake kwance cikin ciwo yace bazai taba yafe masa ba har sai ya masa Alkawari?

Ba musu Yusuf yace ya Amince a take mutallaf yace koh bayan ransa bai yarda ya sake taka nigeria ba, koma menene zai kaisa baiyarda ba sannan ya masa Alkawarin zai auri lawiza(kanwar zahra) don cikawa hauwa burinta na had’a jini da zuriyar su.

A take yusuf yasa kuka yana sanar da mahaifinsa cewa yana da mata da yara a nageria, a basa dama ya d’auko su kuma ya Amince da auren lawiza.

Kin Yarda mutallaf yayi ganin haka yasa yusuf D’aukar wannan Alkawari, shi kuma mutallf ya yafe masa duniya da lahira tare da sakamasa Albarka, anyi haka washe gari aka d’aura auren yusuf da lawiza sati mai zuwa aka nad’a yusuf a matsayin sarkin masarautar karfe, a wannan rana mutallaf yabar duniya.

Tunda yusuf ya zama sarki shikenan Rayuwar sa ta sauya bashida aiki sai tunani gabaki d’aya ya kwallafa ransa akan nigeria, yaso tura mutane aje a duba rayuwar da iyalansa keyi Amma hajara ta gargadesa akan rashin biyayya ga mahaifinsa da karya Alkawari, sannan tace bata son kowa yasan da maganar.

Yusuf  rayuwa suke da matar sa lawiza za’ace sai a hankali, batasan wan abu wai dadin aure ba, asalima yusuf ya samu ciwon zuciya wanda kullum gaba gaba yake duk wani abinda za’ayi don ganin yusuf ya dawo da walwalarsa anyi Amma abin yaci tura.

Hatta yan uwansa da dangi ya shanja musu ba kamar yusuf da aka sani daba.

Bayan wasu shekaru lawiza ta haifi yara biyu mata muwaddat da muhibbat, sai nabila yar kafshatu ce wance hajara ke riko a gidan sarauta.

An dawo labari……….

Tabbas yusuf nada yara ni shaidace mahmah tace tana hawaye.

Jama’a da dama dake fadan sunsha mamakin abinda ya faru wai yusuf nada iyali, Amma ba’a sanar da kowa ba acikin zuriyar su, sannan wasu suna ganin rashin kyautawar abinda aka ma yusuf, lawiza kam kuka ta sake yanzun daman yusuf nada wasu yaran kamar muhammad, amma tana matsayin matarsa a kasa sanar da ita, mikewa tayi zata bar falon, alamu yusuf ya mata data koma ta zauna, ba musu ta koma ta zauna.

Al’ameen ne ya dubi mahmah yanzun kina nufin kice mini kece mahaifiyar abbajo?

Kwarai nice hajara kakar ka uwar yusuf…

Yanzun kun kyauta kenan abinda kuka ma mahaifina ace mutum an yanke masa alaka da yaransa duk wani hakkin su daya rataya a wuyansa ? kai koh ashariya wannan ba daidai bane,  mijinki bai kyauta wa mahaifina ba.

Ya kyauta masa muhammad, nine ban kyauta ma mahaifinka ba,  a Ranar da aka nad’a  yusuf kafun mutallaf ya bar duniya munyi wani magana dashi akan yusuf..

A ranan da aka nad’a yusuf a ranan mahaifinsa yake sanar dani, akan na fad’awa yusuf ya d’auko iyalansa, ya masa hakan ne don yaga zai masa biyayya koh zai bijire masa, Amma tunda ya yarda da auren lawiza kuma ya hau karagan mulki ya yafe masa duniya da lahira.

A hankali yusuf ya kalli mahaifiyarsa, mahmah meyasa kika hanani?

Kayi hakuri yusuf nayi hakan ne don banason kayi nisa dani, nayi tunanin koh inna sanar dakai hakan zaka iyya bijire wa mulki.

Ramadan ne ya kalleta Amma wallahi mama baki kyauta ba, duk irin ciwon da yaya yake Amma mahmah baki tausaya ma d’anki ba?kowa yasan dalilin ciwon yaya yusuf Amma ga magani a hannunki mahmah kika kasa basa habba mama mulki yafi lafiya ne?

Kuka mahmah ta sake tana nuna Alhininta.

Kaga ramadan ya isa haka mahmah uwatace har abada babu wanda yakai uwa son d’anta don haka ni mama bata mini kome ba.

Jin abinda yusuf yace sosai jikin wasu yayi sanyi, Al’ameen hannu yasa a wuyansa ya zaro sarkan tare da mikawa mahaifinsa, Abbajo ga sarkanku a sawa wanda ya dace?

Kallonsa zulkiflu yayi, akan me zaka cire,  wayace maka baka dace da magaji ba?

Ah ah uncle kai ya dace kasa koh uncle Ramadan nikam banida sha’awar sarauta so nake nayi karatu mai zurfi na zama soja mai mukami.

Kowa dake wajen da kallo yabi muhammad jin abinda ya fad’a, murmushi sarki yayi hade da cewa yan uwansa, bazan tilasta muhammad ba daman na basa sarkane badon na shaida shine magaji ba, na basane don na gane sa aduk shekaru da zai gabato duk da Akwai kamar jini, Amma zan aje shaida don haka Za’a d’aurawa zulkiflu.

Da sauri zulkiflu yace Ah ah wallahi yaya nikam banaso gaskiya, amini afuwa adai bawa Ramadan.

Ba musu aka d’aura wa Ramadan sarkan magajin masarauta, sannan a mana booking in fly next week zamu shige nageria.

Jin Abinda sarki yace yasa zuciyar muhamamd rawa, ganin wani rawan jiki da mahaifinsa keyi zashi nageria duk zatonsa matarsa na raye, Abbajo nace dukan mu zamu wuce ne?

Ah ah muhamamd bazamu wuce mu biyar ba,  tunda in muka d’auko su dawowa zamuyi nan?

Shuru muhammad yayi yana kallon Mahaifinsa, ya sake juyawa ya kalli mama kamar hadin baki suka had’a ido da nabila kauda fuskar sa yayi.

Waini muhammad baka bamu labarin abubuwan da suka shafeka ba, da Alakar ka da sarkin shayi da yaran nan?, zulkiflu yace yana nuna su gidado.

Da sauri muwaddat tace eh hakane Akki.

Kasa magana yayi yana kallon yusuf, gyad’a masa kai yusuf yayi Alamun yayi maganar sa,  A hankali ya fara basu labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar yusuf da wahalar da suka sha da abubuwan da suka faru da ubangari da zainab, da mutuwar Maminsa da kaninsa harda Aurensa da sumayya, sai dai bai fad’a musu dalilin da yasa aka aura masa ita ba, don baidace yace dangin ta sunyi mata kazafi ba, har kawo zuwansa cameroon.

Muhammad na bayani mutane wasu na kuka wasu na salati wasu najin haushin zainab da mahmah data hana a d’auko yaran yusuf, kuka itama mahmah ta sake tana cewa su muhammad su yafeta ta cutar dasu.

Yusuf kam zaune yake akan karagan mulkinsa sosai fuska tayi zahur, jijiyoyin fuskarsa ya mike alamu dai ran maza ya baci, gashi a fada yake dole ya matse irin na sarakun, abin tsoro koh bacin rai da tausayi baya bayyana a fuskarsu mundin suma gaban jama’arsu.

A take aka matso da tafiya zuwa jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai NIGERIA!!!!!!

Mikewa yusuf yayi ya koma falonsa kafun kowa ya mike ya fita, nabila kam jiki yayi sanyi saibin mahmah take a baya, yayinda muwaddat da muhibbat suka likewa d’an uwansu sai hira suke masa da tambayarsa labarin khadija, sosai yaji wani irin farin ciki ganin yan kannensa, lawiza ma tashi tayi batama kowa magana ba tayi flat nata, da fari tad’au abin da zafi Amma jin irin wahalar da su muhamamd sukasha da mutuwar Aisha sai taji jikinta yayi sanyi.

***************

Sumayya ce zaune a kitchen tana girka pepper chicken zallah, don ita yanzun nama kawai takeci sai shayi, yanzun ma khdija taje islamiyya ne shiyasa ta shiga kitchen da rarrafe zata girka abinci.

Sai karfe 5:21 khadija ta shigo falon da sallama, sanye take da riga da wando sai hijab babba na islamiyya, hannunta d’auke da jaka.

Amsa mata sumayya tayi tana binta da kallo ta rasa meke damun khadija a kwana biyun nan, gabaki d’aya ta shanja bata da nutsuwa sam, kullum ta zauna shuru koh aiki ta sata bata gamawa akan lokaci, shiyasa wasu aikin take lallabawa tayi duk da nauyin cikinta, don yanzun saidai ta ja ta shiga d’aki indai khadija bata nan”khadija zonan”?

Ba musu ta kwabe hijab nata tazo ta zauna kusa da sumayya, Aunty gani.

“Khadija meke damunki”?

Babu Aunty

“Wani irin babu kome, ki dubi halinda kike ciki duk kinsa rayuwar ki a garari, sai kinzo kin samu ciwone a koma ana sayan magani koh yaya”?

Babu kome fa Aunty

“Bankai ki fad’amin damuwarki ba koh”?

Sunkuyar da kai khadina tayi bata iyya cewa sumayya kome ba, tana wasa da yatsarta.

“kunyi fad’a da kalamu ne kwana uku yau baizo ba”

Wallahi Aunty bansan meke faruwa ba yau kwana uku bai kirani ba, inna kirasa wayar sa a kashe.

“Ok abinda ke damunki kenan?amma meyasa baki tambaye kannensa ba tunda islamiyyar ku d’aya kuma boko ma d’aya”

Wallahi Aunty kunya nake ji, karsuce da wani abu.

“Kunya?lallai khadija bakisan inda ke miki ciwo ba, yaro kullum sai yazo wajen ki kwana uku bakisa sa a idanunki ba, bazaki iyya shigiyarsa  ba?

Sai gobe innaje school saina tambaye falmata(kanwarsa)

” ohon miki”

Tashi khadija tayi jin amsar da Auntin ta ta bata.

Washe gari bayan khadija ta dawo gida take sanar da sumayya ai kalamu ba lafiya yana hospital, kasancewar sumayya tayi nauyi, khadija ce tayi girki mai rai da lafiya, kawarta ta rakata suka je asibiti wajen kalamu, sosai suka samu jikin nasa yad’anyi sauki, kuma taji dadin tarbar da aka mata maman sa nada kirki sosai, haka ma babansa, wanda ke d’auke da zanen kanuri a fuska, amma mamansa bata dashi, haka kannensa sukayita tsokanarta wai budurwan kalamu ne,  sosai tayita jin kunya.

************

Kwana biyu da muhammad yayi a gidan sarauta, da ace zasu hadu da wanda yasansa a baya indai ba farin sani ba,  bazai ganesa ba, ya samu gata kota ina bana wasa ba yayi kyau ya kara fresh yana cin mai kyau yana shan mai kyau, ya kwanta a maikyau baida buri daya wuce yadawo yaga matarsa abar sonsa, sannan yana iyya bakin kokarinsa wajen ganin mahaifinsa bai saka damuwar rashin Aisha da salim ba, sosai yake kula dashi baya barinsa shi kad’ai mundin yabar fada, toh zasu kasance tare haka yan uwan babansa na sonsa, kannensa ma duk ya shaku dasu, nabila ce kawai bata samu fuska a wajen saba duk da mahmah tasata ta basa hakuri kome ya wuce, kuma ya nuna ya hakura Amma bata ganin fuska koh hira yake tazo wajen sai yayi shuru abinsa koh ya tashi.

Su gidado da sarkin shayi duk sun dawo gidan da zama.

Waya mai tsada zulkiflu ya saya masa da kayayyakin sawa masu yawa, wanda zaina sawa.

Kamar yanda Aka saka rana yaune za’a diro nigeria, maimartaba ne da mahmah sai muhamamd da zulkiflu Adda maisara, dayake su muwaddat na jarabawa an barsu da lawiza a gida, karfe 2 na rana jirginsu ya d’aga zuwa Kasarmu ta gado!!!!!

Sun sauka lafiya, suna fita a jirgi dayake sarki  yasan da zuwansu yasa suka samu tarba na musamman direct gidan sarki suka nufa, duk da muhammad yaso ya fara zarcewa sintali sai dai ba dama.

Bayan sunyi wanka sunci abinci,kasa hakuri yayi ya ce zaije sintali ramadan ya rakasa a mota tare da driver.

Tunda suka shigo sintali yake bin koh ina da kallo  yana tuna abubuwan da suka shude watan nin baya, har kofar gidan Adara akayi packing in motar,jikinsa har rawa yake  yana Allah Allah ya fitoh, saura kad’an ya buge kafarsa saban sauri ya bude motar ya fita,  gashi daman yammane ana shirye shiryen kiran mangariba, abin mamaki yana fita babu wanda ma ya zaci shine, harya ratsa mutane sai binsa ake da kallo ganin babbar motar da ya sauka a ciki.

Shiga gidan adara yayi kamar yanda ya tsammani hakan ce ta faru, wato jama’ar gidan na tsakar gida, duk juyawa sukayi suna kallonsa harya karaso tsakar gidan, gaidasu yayi da sauri gabaki d’ayansu suka Amsa hade da shiga shock, indai ba gizau ba Al’ameen ne, duk gatan da ya samu bazai hana su kasa gane saba.

Da sauri iro ya mike bura uba wanake ganin nan kamar muhammad ina ka shiga?

Bai samu daman basu amsa ba, kofar su kawai ya nufa cikin sauri ya bude kofar shashen, da mamaki yakebin kofar ganin duk datti, Alamu dai an dade ba’a share ba da sauri ya karaso kofar, yana bin koh ina da kallo,da sauri ya shiga kitchen insu ga mamakinsa kome a zaune yayi kura, da sauri ya fitoh a kofar, daidai lokacin Ramadan ya shigo gidan, da sauri muhammad ke tambayar yan gidan da har yanzun suke a tsaye sun maidashi madubi,tambayar su yayi ya yaga kofar sumayya a kulle?

Inna asabe ce take sanar dashi ai ba’aga sumayya ba, kama kai kawai yayi yana salati, da sauri ya fita a gidan da kafa ya taka har gidan goggo, yayinda su iro ke mara masa baya, duk inda suka wuce saisu cewa mutane ga MAKAHO ya dawo ga makaho, har gidan goggo va tare da wani neman izini ba ya shiga gidan.

Goggo dake zaune a gindin bishiya, gabaki d’aya ta rame ta zama abin tausayi zaune take tayi tagumi, jin sallamar muhammad yasa ta mike da sauri, wanake ganin nan kaman muhamamd?Allahu Akbar Allah mungode maka sai kuma ta fashe da kuka tana rungumar Al’ameen.

Saida tayi kukanta mai isarta kafun Suka gaisa na yaushe rabo, hade da karama mujammad karin bayani akan batan su sumayya, wanda shagari ya sanar dasu guduwa sukayi bawai sacesu akayi ba, sosai muhammad yaji wani irin ciwo na abinda dangin sumayya sukayi bayan rabuwar su,  taya zasuce ya rabu da matarsa akan wani dalili, anan yake sanar da goggo abubuwan da suka faru sannan yace mata yana son zuwa gidan su sumayya don ganawa da iyayenta, koh Allah yasa sunsan inda sumayya zata iyya zuwa.

Ba karamin mamaki Goggo tasha ba jin wai yusuf sarkine yanzun, Allah sarki duniya, mikewa gogho tayi tad’au hijabinta suka fita gidan da Al’ameen, ai suna fita kofar gida, me zasu gani mutane ne makil a kofar gidan, sunzo kallon Al’ameen don lokaci d’aya labari ya samesu makaho ya dawo yayi kudi, goggo ma a take ta kara musu da wani ai yanzun d’an sarki ne babansa yana mulkin wani gari, a nijar, muhamamd in ma kudi ya ciro a Aljuhunsa ya rarraba musu dubu bibbiyu.

Yana gama raba musu kowa ya watse yana saka masa Albarka, harya juya zasu shiga mota,don driver yajawo ramadan dake ciki har kofar gidan goggo, yana shiga tun daga nesa ya fara jin ana kwala masa kira oga oga oga!!!!

Shagari ne ya iso wajen da gudu, da ido muhammad ke binsa koh ba’a fad’a ba yasan shagari ne daga muryarsa ya gane sa.

Oga sannu da dawowa ka dawo lafiya, yanzun Abdu ra’uf kece mini wai ka dawo.

Murmushi muhammad yayi, lafiya Alhamdulilah shagari.

Da sauri shagari yace munyi kewarka oga shagon mu ya bunkasa nima, yanzun ina makaranta bara na kira Ammar na sanar dashi daman ina da number sa?

Ah ah basai ka kiraba ka bani number sa zan kirasa.

Kallon ramadan da goggo dake mota shagari yayi sai kuma ahankali yace oga tafiya zakayi ne?

Ah ah shagari ina Taraba har sai anga sumayya.

Number Ammar ya basa sukayi sallama suka tafi, dayake shugaba family house sanannen gidane kuma driven dan garine, yasa da kwatance suka gane gidan, goggo ramadan da muhamamd suka shiga gidan,ganin zubinsu yasa mai gadin basu hanya suka wuce cikin compound, ya shiga gidan don musu sallama da mai gidan, ba’a jima ba saiga Uncle Abubakar ya fitoh suka gaisawa, sannan suka gabatar masa da kansu, kuma suna son magana da mahaifin sumayya, da rawan jiki Abubakar ya musu iso zuwa cikin gidan, da gaggawa ya hado kan mutanen gidan a falo, kowa na zazzaune don su daman ba farin sani sukayiwa muhammad sosai ba, a d’auren aure suka fara ganinsa hakan yasa basu wani ganesa ba, gashi ba’a makaho yake ba yau.

Bayan sun zazzauna wannan zaman ma ba momy a ciki, a nitse goggo ta musu bayanin ga mijin sumayya ga kuma bappansa ta nuna Ramadan, da mamaki suke tambayarta ba’ance mijin sumayya makaho bane kuma ya bata.

Ramadan ne ya musu bayanin kome a take jikinsu yayi mugun sanyi, sannan suke sanar dashi rashin ganin sumayya anyi iyya bincike Amma shuru, duk inda ake tsammanin zataje ba’a ganta ba, abie har wani ya samu ya tura unguwan su Hafsa a maiduguri a dubo masa koh sumayya ta gane gidan kakan ninta shan taje, amma an samu tabbacin banan sumayya taje ba, Asali ma hafsa tayi aure bata maiduguri yanzun.  

Hankalin muhammad ba karamin tashi yayi ba, fiye da hankalin yan gidan duk da abie ya shiga damuwa don har rama yayi mai tsanani, suna tsaka da maida zancen sukaji an turo kofar falon koh sallama babu.

Gabaki d’aya suka juyo suna duban falon,  safina ce ta shigo Alamu dai daga unguwa take, duk suka bita da kallo itama, d’aga ido tayi ta kalli jama’an falon da karfi ta kwala kara ta zube a kasa sumammeya..

Da sauri dada tayi kanta, sabanin Abie da sauran yan gidan dako a jikinsu alamu dai ba karamin tsanarta sukayi ba, muhammad ma mikewa yayi shida ramadan suka nufi kan momy, da taimakon su aka kaita asibiti don anyita watsa ruwa bata farfado ba, gashi yan gidan koh a jikinsu, sune suka d’auketa har asibiti suka biya kudin kome suka tafi suka barta da dada, gida suka koma bayan isha’i suke sanar dasu yusuf abubuwan da ya faru da batar da sumayya tayi,sosai suka nuna Alhininsu  da damuwa sosai muhamamd ya basu tausayi yaro tun yana karami yasan wahalan duniya, har tashinsa ma yayi gwagwarmaya.

Washe gari da sassafe saiga Ammar a gidan sarauta, daya samu aka barsa ya shiga ya tura wani dogari yace ana sallama da muhamamd bakin Niger, ba’a jima ba sai ga muhammad ya fitoh, tun daga nesa yake kallon muhamamd kamar bashi ba gabaki d’aya rayuwa ta sauya, sanye yake da jallabiya yar saudi sai hula taba kaji hadisi,  sosai yayi kyau saidai fuskar sa a tamke take alamu baya cikin walwalarsa, yana karasowa da sallama a bakinsa, amsa masa Ammar yayi ai yana jim muryar Ammar da sauri ya rungume sa, cikin farin ciki suka hau hira har cikin gida muhammad ya shigar da Ammar suka gaisa da yan uwansa da mahaifinsa,  sai a lokacin yake sanar dashi ai shagarine ya kirasa yake sanar sashi muhamamd ya dawo, yana gidan sarki kuma ya basa number Amma shuru Al’ameen bai kirasa ba shiyasa yabuga sammako yazo ya gansa.

Abinci aka kawowa Ammar, suna zaune a d’akin da aka sauke muhammad ana hira da labarun abubuwan da suka faru a baya harda Ramadan, kawai saijin muryar jama’a sukayi a sashen sarki, dayake window d’akin da aka sauke muhammad yana saitin sashen.

Mikewa sukayi gabaki d’ayansu suka zagaya zuwa falon sarki,family shugaba ne, suka gaishe dasu abie, aka daura zancen batan sumayya kowa na kawo shawaran sa, karshe dai akace za’a dage da rokon Allah da sadaka sannan za’a zuba jami’an tsaro a bincike su, kafun kowa ya watse, daman yan gidan su sumayya gaida yusuf sukazo da mahaifiyar sa tare da bada hakuri akan abinda ya faru kuma ba laifi sun nuna musu bakome, kome ya wuce Allah ya kiyaye na gaba.

Satin yan nijar biyu a taraba ba’aga sumayya ba, gashi kaf gidan su an duba hotonan ta duka ba’a gani ba, hatta dakin su muhammad ya koma yayi bincike sap baiga wani hoto ba, don sumayya ta tafi da hotunan su, gashi na wayar maimuna kanwar Ammar ma, wayar ta lalace harma ta saida ta, bare su samu hotunan su, da yake yanzun zamani ya sauya ba kamar daba, mutun ya bata a gari ma  ba’a ganesa sai da rabo bare a kasa sukutum, dole tasa Yusuf komawa dasu ramadan aka bar mahmah da muhammad, kafun su tafi saida aka sai musu gida mai shegen kyau a Amazon suka koma ciki su uku harda goggo,  kasancewar mijinta ya rasu bayan tafiyar sumayya hakan yasa muhammad d’aukar ta suka koma gidan su  suna zaune tare da mahmah.

Wasa wasa saida muhamamd suka share wata biyu a jalingo Ana kan bincike har yanzun shuru ba’aji duriyar sumayya ba, koh khadija sosai abin ya dame muhammad koh abinci baya iyyaci sosai, ba irin tunanin da baiyi ba don shi gani yake saceta akayi tunda makiyansa suka iyya saka a kashesa, Amma ammar na yawan kwantar masa da hankali ba kad’an ba.

Ta bangaren safina dai tunda ta farfado a gadon asibiti ta makance bata gani kwata kwata haka magana ma bata iyyawa saboda bakinta daya koma gefe, fuska ya karkace  ya murd’u ya wainu wanda likitoti sun tabbatar hawan jinine daya hau lokaci d’aya, daya bugar da ita ta fadin nan, shine ya kaushar mata da fuska, sai dai makantar ne basu gano sila ba, kuma kaf gidan babu wanda ya damu da lamuranta sai dada ita ke jinya amma hatta abie yaji ya tsaneta hakama y’an gidan wanda basu san dalili ba,  dada ma daurewa take Amma ba kaunar safinan take ba yanzun.

Ammar  ne zaune a falon gidan su shida kannen sa, abinci yake ci gabaki d’aya hankalin sa nakan TV, yayinda iyayen sa ke hiran batar sumayya da dawowar Al’ameen wanda Ammar ke kawo musu zancen, don iyayen sama sunje har gidan muhammad, suka masa jaje, kaninsa ne kawai baya falon.

Kwala masa kira yaji kaninsa yayi daga d’aki sai gasa ya fitoh da gudu hannunsa d’auke da waya yana zuwa baiyi magana ba, kawai ya mikawa Ammar wayan.

Kallon wayan yayi hotunane akayi posted nasu a instagram guda uku, Khadija ce sanye da uniform ita da wani bakin yaro wanda zaiyi sa’ar ta koh ya fita da kad’an shima da uniform in nurse suka d’auki hoto a unguwa mai kyau, sai na biyun tana sanye da uniform in islamilayya nan ma su biyu sai na ukun ita da yaron suna sanye da kayan hausa atamfa da shadda.

Jikin Ammar na rawa yake tambayar Abdul wanene yaron nan?

Aboki nane kalamu-wahid, school namu d’aya  dashi a abuja naga yayi post kuma naga kamar khadija?

Ba kama bane Abdul itace, yanzun kasan inda yaron yake takamamme a Abuja?

Eh na sani yaya don inban manta ba kafun mu dawo hutu yayi ciwo danaje asibiti dubasa na samu an sallamo sa, so yamin kwatancen gidan su naje.

Waya kawai Ammar ya fitar a Aljuhunsa yana lalubar numban muhammad gabaki d’aya yabi ya gigice. 

*******************

Kalamu yaji sauki har ya dawo da normal life nasa, a haka sukaci gaba da rayuwa abinsu cikin farin ciki duk da basa rasa kalubalen rayuwa.

Sumayya ciki ya shiga wata tara duk rashin tausayin mutun inya ganta sayya tausaya mata, cikine yayi kato matuka yayi tsayi ga nauyi don yanzun koh tafiya bata iyyawa sai dai rarrafe abin tausayi bata fita koh ina daga falo sai toilet khadija ke kome wani sa’in kalamu zaizo ya tattara wankin ta ya kai mata dana khadija, wani sa’in har girki yake zuwa ya taya khadija in ayyuka sun mata yawa, sumayya kam yanzun sai a hankali, koh riga bata iyya sawa sai wasu manya manyan vest na gwanjo da zani shine kayanta, sosai laila ke tausaya mata.

Yau laila da mijinta harda yaranta sunyi tafiya zuwa Adamawa wajen dangin mijinta, bayan isha’i kalamu yazo ya kawowa sumayya balankun nama, amma ta kasa ci saboda ciwon kanda ke damunta, suka sha hira da khadija suna cin nama, bai koma gida ba sai kusan 9 ya ma khadija sallama ya wuce, don zuwa lokacin sumayya ta dade da kwanciya.

Da misalin karfe 1 na dare sumayya ta farka jin wani irin matsetsen fitsari  daya kamata, mikewa tayi zaune a hankali jin fitsari ya cika mata mara, gashi dare ne batason shiga hakkin khadija, yasa ta rarrafawa ta shiga bedroom da rarrafe har cikin bandaki, tsungunawa tayi, tayi fitsari ai tana gamawa taji bayan ta ya kama ga wani irin c…………….

✨Ruqeenjalal✨

Back to top button