Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 2 Chapter 1

ZUCIYA DA KWANJI 

BOOK 2___1

Na Maimuna Idris Sani Beli

Abdullahi ya mike ya fara ja da baya ba tare da fuskarsa ta bayyana tsoro ko shakka ba, sai da ya dangane da bango sannan ya daga mata hannu alamar sallamawa, yana kuma dariya ya ce “Wai dukana zaki yi ne?”

 Kawai sai ta ci kwalarsa cikin yanayi na fita hayyacin ta, ta fara magana da sarkewar murya. “Ai wallahi ba ka isa ba… Na rantse ka yi kadan ka tozarta rayuwata…. In aure ka in ci me da kai….? Ni ba na sonka…. Na rantse yau sai ka sallame ni na bar gidan nan, in ba haka ba sai dai mu kashe juna ni da kai”.

 Sun fi minti biyar a haka tana sakin maganar da ranta ya raya mata tana kuka, sannan tana faman jijjiga shi har da duka. Ya tsaya kawai ya zuba mata ido, tun yana dariya har dariyar ta gagara….. Sai da ya tabbatar ba ta da niyyar ta hakura, sannan ya yi maganinta. Ya riko gashinta da karfi, wanda ya karya lagonta ta fara kara, ta dago kanta tana surutai na cin fuska gare shi, kawai sai ya manna bakinta da nasa. Ya kuma nuna mata shi jarumi namiji ne, inda ya saki gashinta ya matse ta sosai cikin gwaninta ya fara juya harshenta da nasa. Ya rufe bakin masifa kenan, duk kokarinta ta kasa kwatar kanta ita da kanta sai da ta ji a ranta akwai inda mazan suke. Numfashinsu ya sarke da na juna, ya dinga aikawa kwakwalwarsu wani sako mai wuyar fasarawa. Ya dai yi nasarar motsa duk wata halittar soyayyarta da ke zuciyarsa, ya gadar masa da doki da fatan kasancewar su tare matsawar numfashi shaukin da ke shake numfashinsa bai taba jin rabinsa daga wata ba……. Akwai bambanci tsakaninta da shi, ita halin da ta sami kanta bai wuce kwarkwarewar komai a kwakwalwarta ba. Ma’ana ya sauke farashin masifarta da ya cushe mata zuciya kuma ya sassauta mata zafinsa da kiyayyarsa da ta ke ji a makogwaronta, sai ya sanya mata raunin jiki da na zuciya, yayin da kwakwalwarta ta dauki wani aikin daban. Sai da Abdullahi ya fahimci hakan sannan ya kyaleta, ya rungume ta tsan tsam a jikinta, ta saki raunannen kuka mai tsuma rai. Ya dago kanta da rikitacciyar murya ya kira  Sunanta, ya fara girgiza mata kai… Bai jira ta ce wani ba, abu ya fara lasar hawayenta da harshensa. Ya ja ta kujera ya zaunar sannan ya zauna gabanta a kasa da nasa kwallar ya fara magana a tausashe.

 “Fatima kar ki wahalar da numfashinmu, ba zamu iya rabuwa ba. Ban aure ki don na sake ki ba, tun kafin na dora idona a kanki…. Ya ya kike tsammanin zan iya sakinki bayan na ganki kuma soyayyarki ta shige ni da zafi? Ban taba dandanar so mai zakin naki ba Fatima, ban taba jin a raina zan iya mutuwa a kan mace ba, sai akan ki. Na kuma ji a raina ni ne zan da ce da mijinki, ni dai ana aure domin bauta….. Aurenmu ne zai samar da riba biyu, wato rayuwa mai dadi, wadda kuma zata samar da lada, ki ba ni dama mu gwada wannan sa’ar Fatima, sai kin samu kanki a aljannar da ta zarce ta gidan Alhaji don ba kudi ne kawai jin dadin rayuwa ba, sannan ki sani dole kiyi wa Allah biyayya kibi umarnisa, amma me ki ka tanada ranar tsayawa gaban Ubangiji idan har kika yi zaman haramci da Alhaji?

  A Da tana ta shesshekar kuka, sai a wannan gabar ta tare shi, “Ina ruwanka? Ko kana da kaso a cikin hisabina? Idan haka ne ka fada min?”

  Ya kara zagewa da rarrashi, “Wannan hisabin mu uku ya shafa, da Alama kuma zan fi kowa tabewa tunda ban mori komai ba a duniyar….. Koda yake ku ma din ba zaku mora ba, shaidan ne kawai yake rudarku, ko ba ki tuna yadda kike kin Alhaji a da? Sai bayan ya sake ki shaidan ya kawata miki shi, shi ma shaidan ya kara haska masa ke har kuka sami damar ture komai kuka halatta haram.

   Hawaye ya bushe a idonta ta fara magana a sanyaye, sai dai kalaman nata da zafi. “Ko ina son Alhaji, ko bana sonsa binciko wannan ba zai amfane ka da komai ba, don kai dai bana sonka, kuma ba zan taba iya zama da kai ba…. Kuma dole ne ka sake ni idan ba haka ba sai dai cikinmu wani ya bar wa wani duniyar. 

  “Ko a jikina, ya ce mata. “Ai na shirya, ina fatan ke ma haka…. Na yi mutuwar so ke ƙi yi taki, zan yi farin ciki idan za mu bar duniyar tare sai mu tashi da juna”.

 “Allah ya kiyaye”. Ta fada da karaji. Ya tashi da sauri tare da dora yatsa a lebe, sannan ya fara yi mata inkiya da window da kofa alamar kar makota su jiyo ta ya ce,

 “Na riga ki a wajen Allah, ga shi kuma alhairin na je masa da shi ba sharri ba, Fatima kar ki batawa kanki lokaci na fada miki ban aure ki don na saki ba…”

 Sai ta yi zuru tana kallonsa lokacin da zuciyarta ta kai matukar kuntata. Ya rabu da ita ya sa kai ya shige dakin baccinta ya yi kwanciyarsa. Ta yi kukan, ta yi rurin har ta hakurkuratar da kanta ta nufi bandaki ta dinga wankin bakinta, sannan ta zo ta dau hijabinta ta nufi kofa, yana jinta ta bude kofar dakin ta fita tana faman kuka, ya yi dif yana sauraronta don yasan babu inda zata iya zuwa. illai kuwa sai gata a guje ta dawo ta shigo falon ta rufe. Ya koma ya kwanta yana dariya.

  Ta gota karfe biyu da rabi a falo tana kuka, ta rasa ta inda zata fara wannan rayuwar bakin cikin da kuma tunanin makomar lafiyar Alhaji da ya kwallafa ransa a kanta, to ga jarrabar da Allah ya aiko musu. Babu dama ta kwashi kafa ta tafi gidan su wanda tafiyar ce zata tona asirin abin da suka binne. Bari kawai ta zauna su gurji juna duk wanda ya ji jiki sai ya sallama, wani daga ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata haka.

   Sai da karfe uku ta gota sannan ya daina jin shesshekar kukunta, sannu a hankali ya lallabo ya leko sai ya ganta kife kan kujera bacci ya kwashe ta. Ya fito da bargo a hannunsa, sai dai neman yadda zai gyara mata kwanciyar ya zama jidali, dole sai bargon ya sa ya rufe

mata ya wuce bandaki ya dauro alwala ya zo ya gurfana gaban mai share hawaye. Sai hudu da rabi ya dan kwanta ya runtsa baccin rabin awa, sannan ya farka domin sallatar sallar asuba.

  Bayan ya dauro alwala ya zo ya bude fuskarta yana yarfa mata ruwan hannunsa. Firgigit ta bude idanunta da suka kaɗa suka yi jawur, ya ce mata

  “To sarkin kuka tashi ki yi sallah, in yaso sai ki kai wa

ubangiji kara ta, ki dinga addu’a sai ki ga Allah ya warware miki duk wani kulli da ke cikin zuciyarki, yanzu ina amfanin kukan da kika kwana kina yi jiya, me ya samar miki? Da kin yi dabara sai ki yi alwalarki ki kai wa ubangiji kara ta. Idan babu alkhairi a tare da ni ya canja miki ni”.

  Ta yunkura ta tashi tana janye jiki ya bita da kallo da yanayi na nuna kulawa. “Me yasa ba ki shiga wancan dakin kin kwanta ba, idan ba za ki hada daki da ni ba? Sai ki takura kanki a nan Fatima?”.

 Ta gyara zama tana zabga masa harara ta ce. “Ai ni na gama jin dadin rayuwa, in dai da kai zan yi ta.

 Ya yi murmushi, tukunna tawa taƙare, tunda ni ba ni da rayuwa mai dadi, sai kuma kika yi sa’a muka yi haduwar da babu rabuwa”.

  Cikin girgiza kan girmmar bacin rai, ta ce “Allah ba zai cika wa maci amana irinka burin ba Abdullahi….”

  Ya tare ta yana kallon kwayar idonta. “Da na ci amanar wa? Ke ba ki san an ce mafi sharrin mutane shi ne wanda yake salwantar da addininsa domin duniyar waninsa ba? Matsayina ke nan idan kuka yi tsani da ni kuka kulla zaman haram…… Kuma da kike maganar Allah ba zai cika min buri ba, ai ni Allah ya cika min buri a kanki Fatima, ya aura min soyayyarki wanda ina cike da fatan hakan. Tunda har Alhaji da kika aura bisa kaddara kika yi zaman dole da shi, kuma ya sami gurbin son da kike jin za ki iya zaman haram da shi, balle ni da kika zaba a matsayin jaruminki Fatima…. Karkari ki yi boren ba ni da kudi, to ni

zan tabbatar miki kudi ba su kadai ne nasarar a rayuwa ba”.

  Ta yi kasake kawai tana kallonsa, ya ya aka yi ne yasan tsakaninta da Alhaji haka?

  “Tashi ki yi sallah” Ya fada lokacin da ya daidaita kan sallayar, sannan ya tayar da kabbarar raka’atainil fijir. Bayan ya idar ya sa kai ya fice masallaci.

   Cikin sanyin jiki ta tashi wasu abubuwa na yawo a ranta, dole ta yi taka tsan tsan da Abdullahi tunda ya san abubuwa da dama a kanta.

 Ta dauki shawararsa wajen kai kukanta wajen mai duka sannan ta takure akan sallayar har ya dawo masallaci ya same ta. Kai tsaye wardrobe ya wuce ya bude yana nazarin ciki, sannan ya fara yo waje da kayan wankinta. Kayan da ta shafe kwanakin ta a gidan tana sawa ba tare da ta nemi mai wanki ba. Ya ware wadanda suka kamata akai wanki ya kulle, sannan ya kwashi kananan kaya irin su vest da underware da su rigunan bacci zai fita da su. Fatima da ke satar kallonsa tun dazu sai ga ta tsaye.

  A kufule ta ce, “Ina zaka kai min kaya?”

  Ya tsaya yana dubanta ya ce, “Wai gaisuwar ke nan?” 

  A tsiwace ta ce masa. “A matsayinka na wa zan gaishe ka?” 

  Ya yi mata kallo da gefen ido, sannan ya ajiye kayan a gefe yana cewa. “To ko in zo in nuna miki matsayina?” Ta yi saurin komawa ta zauna tana kunkuni. “Abin da ka iya ke nan”.

  Ya tuntsure da dariya ya dauki kayan ya fice. Yana cewa. “Ashe har kin fahimce ni?” Can baya ya zagaya ya wanke kayan tsab ya shanya sannan ya dawo ya yi musu sassaukan karin kumallo, ya shirya ba tare da ya tsumaye ta ba ya yi nasa.

  Takwas daidai ya same ta a dakin bacci tana zaune bakin gado tana faman kuka, kafin ma ya yi magana ta riga shi. “Abdul ka cuce ni wallahi, sannan ka cuce Alhaji wanda na tabbatar zai yi wahala wannan bai zama sanadin tashin hawan jininsa ba. Idan ya rasa ransa ta wannan hanyar ka shirya zaka dauki alhakin mutuwarsa?”

  Babu wata shakka ya amsa mata….. “Idan ke da kika yi sanadiyar jaza masa ciwon zuciyar ba ki dauki hakkin mutuwarsa ba, ya ya kike tsammanin ni zan dauka? Ai ni masoyinsa ne mai son saukaka masa hisabi, idan mutuwar ce ta zo ina masa fatan samun sauƙin kwanciyar kabari”. 

  Sai da ta yi nazari sannan ta amsa. “Sai ka bi a hankali don kai ma dab nake da jona maka ciwon zuciyar idan kuma ya kashe ka bai min asara ba, sai dai ya yi wa wadancan akuyoyin da ka ajiye”.

  Ya yi murmushi har kumatunsa suka lotsa ya ce, “Allah ya asuttura min nayi ciwon zuciya a kanki, shi ma Alhaji kaucewa umarnin manzo Allah (S . A. W) ya yi yasa hanunsa a turbaya, amma ni tsaye nake da kafafauna. Sannan a Jajirce nake ba zan salwantar da addinina da lafiyata dalilinki ba, tunda a lahira ba za ki amafane ni da komai ba. Sannan idan na mutu na barki wani na za ki aura. Zata yi magana ya tare ta, “Kinga da Allah ya isa, ni zan fita akwai abin da kike bukata?”

   Ta yi banza da shi, don haka ya iso gabanta yana cewa.

   “Bari na sami ladanki na rage miki wadananan hawayen”. Tuna yadda suka yi jiya ya sanya ta zabura ta mike, sai ga ta a hanunsa. Ba ta yi wani yunkurin kwatar kai ba don ta san ba ta da tsiri, kawai sai ta kwantar da kai a kirjinsa tana kuka a hankali. Ya rungume ta da sassauci alamar rarrashi yana fada mata kalamai masu sanyaya rai. 

  “Haba fadima hawayenki fa ba abin banza ba ne da za ki dinga salwantar da su a wofi, kar ki ga ina sharewa kukanki na min ciwo wallahi, ki ba ni lokaci na nuna miki irin kaunar da nake miki na rantse ba irin wadda za ki zuba a kwandon shara ba ce”

  Haba sadiya ta yi masifar zuwa wuya, cikin bala’i ta ce, “Wai duk aikin dubu biyu da dari biyar din ne wannan kike….?”

  Hindatu tari.numfashinta ta ce, “Kwarai da gaske, tunda

wani bai taba zuwa a gidanku ya bani kobon shi ba, kuma har wajen Allah ban zama kaza ci ki goge baki ba. Na hadiye alkhairi kuma na yi girgiza in yi hamayya da wanda aka yi min ta silarsa”. Fuuu…. Sadiya ta ajiye kayan ta fice daga wajen. Da sauri Fatima ta tattare kayanta ta gudu daki don ba ta saba da masifa da hayaninya irin.wannan ba, ta kuma sha jin labarin fadan kishiyoyi, yanzu idan sadiya ta fito da tabarya da me zata kwaci kanta? Hindatu ta ci gaba da karatunta, sai ga sadiya da kudi 2500 ta watsa mata, wadda ba ta yi ko gezau ba don tuni ta saba da wannan bala’in na sadiya. 

   Sadiya na huci ta ce, “Sai ki hada ki kara kwazon aiki, don ni a kansu ba zan sarayar da ‘yancina ba”.

   Hindatu ta kwashe kudi ta bude tsakiyar littafinta ta zuba tana cewa, “To yanzu da ba ki sarayar da yanzcin naki ba fada min ribar da kika samu, don kin ƙi yarda ne, amma shi Allah babu ruwan sa, ba a yi masa dole, kuma dole ki san sarki goma ne zamani goma, Abu Turab ya gama yayinki, sai dai ki rungumi sorry ki adana tsufarki…..”

   Ba ta jira cewar sadiya ba ta ture kujera ta yi tafiyarta ta bar sadiya a nan tsaye.

   Fatima ta zube kaya kan kujera cikin hawaye, da me zata ji, da ganin duhun gidan nan da ma’abotansa, ko kuma bala’in wannan matar?

  Kamar hindatu ta san yadda za a yi, karfe biyar saura minti goma Abdullahi ya dawo gida, ko kallon dakinsa bai yi ba ya sauke gajiyarsa a dakin Fatima, wadda jin dirar motarsa ya sanya ta rarumo hijab ta saka, sannan ta nemi guri ta zauna ta bata rai. Ko ƙala bai ce mata ba, bayan sallama bai kuma matsawa kansa kallonta ba, ya shiga da jakar lap top dinsa dakinta, sannan ya fito ya wuce kicin ya dauko lemo ya dawo ya zauna a gajiye. Don neman ta kula shi, sai ya dauki remote ya sauya tashar da ta ke kallo zuwa kwallon kafa. Nan ma sai ta share ta kwantar da kai jikin kujera kawaima sai ta lafe jikin kujerar tana kallon rufin dakin da fanka na juyawa wadda kamar tana hadawa da numfashinta, shi yasa ya sami damar hakura da kallon kwallon yana kare mata kallo. Can ya ankara da kayan wankin, ya dan tara gira ya ce,

   “Ba ki debo kayan nan da wuri ba ko?” 

   Ta watsa musa harara shi da kayan, sannan ta kawar da kai a raunane ta ce, “Ɗaya ke nan daga cikin cutar da ka yi min, wadda ba zan taba fanshewa ba. Da idanuna ba zan kalli mai mata na aura ba, bare har matansa su zame min matsala a rayuwa…. Ni ba kaunar zama da mijinsu nake ba, amma haushi na suke ji”.

   Kai tsaye ya gano inda gizo ya yi sakar, ya kuma san aikin sadiya ne don ya sha jinsu da Hindatu, kwanaki sai da suka tashi hankali akan haka don haka ba shi da ta cewa, ga shi kuma dole ya nemo, sai ya yi murmushi ya ce, “Za su ji haushinki ne don kina son mijinsu ko kuma dan mijinsu yana sonki? Da zaki yi dabara sai ki toshe kofar da za su dinga sanin tsakaininki da mijinki, dan ki ba wa mara da kunya, duk sharrin mutum dai ba sai ya ga abin fada sannan zai fada ba? Idan kika ƙara bata kayan sai na kuma wankewa, mijinsu suka wahalar ba wani ba. Bai ma saureta ba ya kwashe kayan ya fita ya kuma wankewa ya shanya har da matsewa da clip, ya kwashi kayan Sadiya wadanda sun bushe ya kai mata har dakinta ya ce, “Adana kayanki sun bushe”.

  Saboda da takaici sadiya kasa magana ta yi, shi kuma ko a jikinsa ya kada kai ya fice zuwa dakin Fatima, ya yi wanka zuwa magarib ya fice masallaci. Duk da haka ba zai rasa burgewa da ya dorar a cikin zamansa da Fatima, wanda ya fahimci ya fara ne tun daga ranar da Sadiya ta taka mata kayan shanya. Wato duk bala’in da ke tsakaninsu da irin yadda ta ke wulakanta shi a dakinta agaban mutane karrama shi ta ke, yadda ko hindatu da sadiya sai dai su yi msu hasashen matsala ba wai ta hanyar gani da ido ba, sannan duk lokacin da take guri to sadiya ba ta isa ta keta idon Abdullahi ta yi masa rashin kunya ba tare da ta shigar masa ba. Ya gama fahimtar ko kadan ba sa jituwa, ko Sadiya ba ta zunguro bala’I a tsakaninsu ba sai Fatima ta zunguro yanzu sun tashi ‘yar karamar fitina. Idan sun kebe ta hau masa boren ya kawo ta cikin matansa suna nema jaza mata hawan jini.

   Ranar wata asabar Fatima ke da girki, amma har karfe goma sha daya ba ta bude dakin baccinta ba, har ya gaji da kwankwasawa ya sa mata ido, ya yi zamansa a falo yana nazarce nazarcen sa a computer. Can sai gata ta bude kofar ta fito tana ta faman atishawa da alama sabuwar mura ce ta kamata, ta wuce kicin mintuna kamar goma sai gata da ruwan citta a cup zata kuma shigewa daki.

Also Read:

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 1

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 2

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 3

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 4

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 5

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 6

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 7

 “Fatima idonsa kan computer ba tare da ya dube ta ba.

  Ta yi turus amma ta ki tankawa.

  Ya dago ya kalle ta ya ce, “Fatima wai ba ki ji ne?”

  Sai ta juyo ta nemi kujera ta zauna ba tare da ta dube shi ba, ta fara kurbar ruwan cittarta fuskarta a bace. Ya yi nazarinta a nutse sannan ya kara kyautata murya ya ce.

  “Wai komawa zaki yi ki kwanta ba zaki yi wanka ki karya ba? Ta share kamar da dutse ya yi batunsa. Bai damu ba sai ya kuma dorawa. “Kin san kuwa abin da ya jaza miki murara nan ba zai wuce kunshe kanki da kike a daki kina fama da sanyin A C da iskar fanka, kuma ba kya gaurayawa da hasken rana da sassanyar isaka ba? Ta kuma sharewa, sai kawai ya tashi ya shige toilet ya hada mata ruwan wanka, sannan ya fito ya mika mata hannu ya ce. “Ba ni wannan cittar, shiga ki yi wanka”.

   Ba ta musa masa ba ta dire cup ɗin, ta mike ta shige wankan. Kafin ta fito ya tanadar mata shayin tafarnunwa da zuma ya kai mata har daki sannan ya koma mata da madara peak wadda zata dusashe waurin tafarnuwar. Bayan ta shirya da kansa ya shasshafa Robb a makogwaronta zuwa kirjinta, sannan ya rike hannunta ya yi kokarin kallon kwayar idonta ya ce. “Don Allah ki zo mu je ki sha hantsi kinji? Kar ki daka ta ni ki duba lafiyarki kinji?”

  Ta kawar da kai tana shakar hancin, da sauri ya saki hannunta ya yago tissue ya mika mata. Wannan dawainiyar da yake mata ce ta hanata yi masa musu wanda ta ke ji kamar yana mata ne domin saihiyar kaunar da yake mata tunda babu abin da yake amfana daga gare ta. Ya daukar musu darduma da ruwa da filo ya bata rikon ruwan da tambulan, shi kuma ya dauko mata lemon citta guda biyu suka tafi. Sun sami Sadiya zaune a daya daga cikin kujerun da ke rumfar tana danne-danne a waya, Abdullahi ya yi mata sallama tare da dan zolayarta amma ta yi fuska.

   Ya shimfida dardumar ya sanya filon sannan ya karbi ruwan hannun Fatima yana cewa. “Sannu da kokari, zama ban da kwanciya”.

   Ta yi murmushi a kasalance ta kwanta, ba tare da ta tayar da kanta akan filon ba. Ya bita da kallo kafin ya yi magana ta riga shi da taushin murya. “Ka yi hakuri don Allah.

   Ya ji sanyin maganar har cikin ransa, ina ma tare da Sadiya ko Hindatu suke wuni su kwana? Ya zauna yana mika mata filon yana cewa. “To na hakura sa filon”.

   Ta girgiza kai ta ce, “Zauna akai ka karanta min magazine. Kafin ya yi magana sai ga Hindatu cikin shirin fita. Ta yi musu sallama tare da gaishe da Abdullahi, ita kuma Fatima ta

gaisheta,

   Abdullahi ya ce, “Kin ga kuwa Hindatu gaba dayanku ya kamata ace kun je ganin jariri, Fatima Matar yaya ce ta haihu na manta ne ban sanar da ke ba, kuma ya kamata ki je barka, ko bari zamu yi da dare na kai ku gaba daya? Kamar gaske ta ce. 

   “Ai tunda ba ka sanar da ni akan kari ba ka

makara, Allah ya kai mu suna, Hindatu ki shafo

min kan baby…… Ya tare ta. “Idan na ce sai kun

je sai a yi yaya? “Sai ka aikata abin da bai kamata ba, ka ɗebe ni da mura na je na shafawa mutane”. 

   Hindatu ta ce, “Ni fa Abu Turab ko me ka tsara ba zan fasa fitar nan ba tunda na shirya, sati biyar fa ban ga waje ba….. Haba kai har yanzu ba ka tsufa da kulle ba”. Ta karasa da dariyar zolaya.

    Shi kuma ya saci kallon Fatima ya ce, “Kina korafi akan wata daya, me wata uku ta ce me?” 

Fatima ta juya baya tana shakar hanci ta ce, “Kai za a tambaya tunda kake jin zaka iya

maye min gurbin duk wani hali da aboki”

    “Dan ma yana kwatantawa”. Inji hindatu cikin raha Fatima ta dan yi dariya kawai, shi ma Abdullahi haka yana kallon Fatima da ta juya musu baya ya ce, 

“Ita ma dan ba ta sai da turaren wuta a gidan biki ne shi yasa ba ta matsa min sai ta fita ba”

     Ba ta damu da juyowa ba ta ce, “Ka dai samu dama a kaina kawai, amma nawa uzurin ai ya zarce na turaren wuta, na kuma zuba maka ido nan da wata uku masu zuwa in sabuwar amaryaka zata shigo ka barni na fita”.

      Ya jima kafin ya samo inda wannan maganar ta samu, sai can ya tuna ganinta, dan haka da kyar ya samo abin cewa. “Ni ban san wata amaraya ba ban da ke shekaru talatin nan gana ba watanin uku ba”

      “Allah ya nuna mana”. Inji Hindatu da ta so katse hirar bayan kishi ya sosa ranta, ta nufi Sadiya tana cewa.

       “Kin ga sadiya dan Allah Rabi kanwata zata zo yau mun yi waya da ita yanzu suna bisa hanya, ni kuma na riga na shirya ban son fasa fita, kuma da yake dama hutu zasu zo min sai kawai na ce su sauka a wajenki. Dama Sadiya a wuya ta ke, neman me taba ta take ta fanshe a kansaa. A wulakance ta ce, “Ni ma fita zan yi”.

     Abdullahi ya dan kalli Sadiya amma bai tanka ba, sai Fatima da ke jinsu ta ce, “Idan babu damuwa ba sai ta zo wajena ba, Allah ya sa matar aure ce mu samu mai gidan nan ya barni mu sarara”.

      “To addu’arki ba ta ci ba”. Suka hada baki shi da Hindatu suna yi mata dariya, Hindatu ta yi mata godiya, shi kuma ya dubi fatima da muryar rarrashi ya ce, “Bari na kaita titi na samar mata taxi”. Ta amsa masa. Suka fice aka barta da Sadiya wajen ya yi dif! Kamar babu masu rai a wajen, wannan ya ba wa Fatima damar bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita saboda kasalar da murar dake damunta ta sakar mata. Can hayaniyar Abdullahi da Sadiya ta farkar da ita, Abdullahi nace wa “Sadiya dama ana tambayata unguwa ranar da za a yi ta ne da kike neman ki zage ni dan na hanaki fita?” 

       A tsiwace ta ce masa, “To da wanne KWANJIN zaka ce sai na yi abin da kake so alhalin kai ka take dukkan adalcin da ya kamata ace ka yi min? Ai babu wani dalilin da zai sa ka ce sai na bi dokarka” 

     Cikin alamar sikewa ya ce, “Ai dama ke batunki ba ya wuce nan, kullum ke an bata miki. A’a ba a yi miki adalci ba, komai aka yi miki ba a burge ki alhalin ke kin gaza da taki biyayyar. Ni na rasa wannan mugun son mulkin naki wallahi…..”

      A kufule ta katse shi da cewa, “To idan an yi min makauniya ce da ba zan gani ba, ko kana tsammanin gara ce ni irin Hindatu wadda za a mayar borar gida ta kasa damuwa? Kaga tun da abin ya fara kawo mun irin wannan

bakaken maganar kafin ka kai ga sa hannun ka dake ni….. Sallame ni, tunda ba kwai na ajiye a gidan ba, sai ma na baiwa wasu sarari su shigo idan sun ga zasu iya su zauna su haifi kashi, idan ba zasu iya ba su ma su ci taya”.

     Fatima ta gaji da sauraron wannan hayaninyar sai ga ta zaune tana mutsuke ido, sannan ta dubi Sadiya ta ce

“To ke baiwar Allah akwai wanda ya yiwa Ubangiji rawa ya ba shi tsatso ne? Na tabbatar kin san inda gadar haihuwa ake da yanzu kun cika gidan nan da ‘ya’ya mts! Ina mamakinki wallahi, ke babu wani mutum mai mutunci a idonki da ya fi karfin ki dagawa harshe. To tsoronki za a ji ayi miki abin da kike so? Ai duk mutumin da yake jin kowa ya tsane shi, to ya binciki kansa halinsa ne ba shi da kyau”.

      Kawai sai Abdullahi ya nemi guri ya zauna, ransa na yi masa dadi. Fadima ta karbe shi faɗa, ya san kuma yanzu zai mutu, don tana ƙule Sadiya da takaici zata tafi ta ba shi guri. 

     Sadiya ta kara bala’i kamar zata cinye Fatima danya, “Wai ke ina ruwanki? Ban yi miki kashedin kar ki kara shiga

sabgata ba? Ni iskar da ki ka kwasoma idan ina kaunar shakarta Allah ya tsine min….”

     Fatima ta yi saurin tare ta da rashin nuna damuwa. “Me yasa za ki ce babu ruwana? Ki saka min miji a gaba kina faman ci masa fuska ki ce babu ruwana. To me ye amfanina? Idan ke ba kya so ni ina so, saboda haka a kansa sai in da karfin ya ƙare, kenan kina da bukatar canza tunanin, da ruwana har da komai nawa”. Da sadiya ta rasa abin cewa, sai ta harde hannu cikin rawar murya ta ce.

   “To daga nan ki sa shi ya sallame ni mana tunda da alama kamar ke ce mijin shi ne matar”.

Back to top button