Hausa novels

Halysaah Page 194 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 194….Tun bayan da Hajja ta baro Parlon sarki take zaune bedroom dinta cikin damuwa sosai don har sai da hakan ya kusa saukar mata da zazzabi, sai ma da tayi kuka ne ta ɗan samu sukuni a ranta, wajen karfe biyu ne na rana amma ta kasa lunch har yanxu, ba kadan incident din da ya faru parlon Mai martaba ya girgiza ta ba, bata san rashin imanin Aunty ya kai har haka ba, da ba don daga bakin Walid duk maganganun nan suka fito ba da bazata yarda ba, cewa zata yi sharri aka ma Hafsat muguntar ta bai kai haka ba, ba ma Hajja kadai ba kowa na gidan komawa sashin sa yayi cikin shock din abinda ya faru barin Mami don sai da tayi kuka sosai da ta koma bangarenta, a haka Mai martaba ya shigo har dakin Hajja bayan tayi kiransa a waya, don sai yanxu taji zata iya magana da shi, a daxu kam ko maganar bata son yi, bayan Sarki ya zauna a dakin Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace “Ya muka ji da wannan abu na tashin hankali Yusuf…” Mai martaba dai yayi shiru kansa a kasa, after some seconds ya dago kansa yace “Dama a sanda Walid ke asibiti a garin nan, akwai maganar da wani likita ya gaya min few days bayan anyi admitting dinsa, but i just had to let it slide….” Hajja dake ta kallonsa tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, me likitan ya gaya maka?” Mai martaba yace “Likitan ya shiga ne zai masa allura ya samesa yana canza sim card a wayarsa, sai yace ma likitan zai yi amfani da bandaki, likitan ya fita ya kira Nurses maza suka dorasa kan Wheel chair aka kai sa bandaki, shi kuma ya zauna a ward din yana jiransa sai yaji yana waya kasa kasa a cikin bandakin, wannan ne yasa yayi eavesdropping and he overheard all his conversation, suna sa’insa ne da wa enda yake wayar akan cewar ai ya riga ya biya su kudin aikinsu miliyan uku, daga karshe kuma yace zai kara masu sauran miliyan biyun da suka bukata, kar kuma su sake kiransa kafin a fara suspecting dinsa don yanxu ma a cikin zargi yake, sai kuma daga haka ya kira uwarsa ya sanar mata ya tura mata account number din mutanen nan ta tura masu miliyan biyu, don sun ce idan bai kara kudin ba za su tona masa asiri” Salati kawai Hajja take cikin gigicewa tana kallon Mai martaba, Ya sauke wani ajiyar zuciya yace “Tun daga sanda likitan nan ya gaya min wannan maganar damuwar da nake ciki ya ninku akan na da Hajja, i couldn’t bear it a lokacin, i was so down, amma na nemi alfarman likitan ya bar maganar nan tsakanin mu, Walid ɗan cikina ne bazan yi shari’a da shi ba, and the Dr reason with me ya kuma yi alkawarin bazai gaya ma kowa ba, ban taɓa gaya ma kowa wannan maganar ba sai yanxu da nake sanar maki, so i wasn’t taken unaware abinda Walid yayi daxu a parlona, in kin kula tunda aka fita da shi kasar waje for surgery sai karshen wata nake zuwa dubasa a asibitin, shi ma bana wuce kwana daya zuwa biyu zan dawo Nigeria, har kema sai da kika min korafin haka, amma zuciyata nake kai wa nesa nake zuwa dubasa gudun maganar mutane, ita kuwa Hafsat tun daga lokacin har zuwa yau na sauya mata, ina kuma jiran su dawo ne in dau matakin da naga ya dace a kanta, sai gashi ya fallasata a gaban kowa” Hajja na goge hawayen dake zuba idonta tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, wannan tashin hankali da me yayi kama, me Junaid da Jawwad suka yi ma Hafsat da take son ganin bayansu ita da ɗan ta? Lallai Hafsat ta zame mana annoba a gidan nan, Yusuf ka dau duk hukuncin da kaga ya dace a kanta babu me hanaka, sai dai kuma kasan ba a saki a irin wannan gida me daraja, ban san yanda za ayi wannan al’amarin ba” Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “Wannan al’adar za a denasa daga kai na, don jinginesa zan yi gaskiya, bazan yi la’akari da wannan al’adar ba a situation din da ake ciki yanxu, don Hafsat bata cancanci ci gaba da zama a masarautar nan ba, duk wanda zai iya sakawa ayi kissan kai to babu abinda bazai iya aikatawa a rayuwa ba har shirka kuwa, ni na fara tunanin ita ce ta kashe mahaifiyar Junaid don a ranan da take nakuda ai ita ce a tare da ita a daki da daddare, ta kuma hana a je a sanar min, ta kori Jakadiyarta wai ta basu waje, ita Hafsat nawa take a lokacin da zata amshi haihuwa ita da ba karatun lafiya tayi ba? Duk sai bayan da likitan ya gaya min conversation din Walid da yaji sannan tunanin nan ya zo min, Yaya Ahmad ma a ranan da ya rasu ita ce ta shiga dubasa na karshe kafin ni in shiga in tarar da gawarsa, kuma kar ki manta a sannan jikinsa da sauki sosai, har yace ki yi masa dambu yana son ci….” Hajja ta dinga kallon Mai martaba bata ko kiftawa alamar ita ma komai ya fara dawo mata gradually a kai, kuma dai dai da rana daya basu taɓa zargin Aunty ba, Cike da takaici Mai martaba ya girgiza kai yace “Don haka zan datse duk igiyoyin aurena da ke kanta a yau ba sai gobe ba, sannan zan nisanta ‘ya yana daga gareta, tunda har ta iya saka Walid ya aikata kisan kai to sauran matan ma babu abinda bazata iya cewa su yi ba kuma su yi, babu su babu ita as far as they are in this palace, idan sun yi aure suna gidan mazajensu sa iya mu’amala da uwarsu, but for now I am going to cut all communications with her” Kukan bakin ciki kawai Hajja take, da kyar tace “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi Yusuf, bazan hanaka duk abinda kayi niyya ba, Allah yayi mana hisabi da Hafsat, in dai ita tayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyar Junaid, da ɗa na Ahmadu to Allah kadai yasan yanda zai yi da ita tun a duniya, wallahi bamu yafe ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita….” Gimbiya Firdausi da Hajiya Shafa’atu na zaune parlon Aunty bayan sarki ya umarcesa da su je can, basu dai san dalilinsa na cewa su je parlon ba amma tun da suka shigo Aunty taki fitowa daga daki ta kulle dakinta don duk tunaninta sun zo ne su jajanta abinda ya faru a parlon sarki, ta yanda Gimbiya Firdausi zata ji dadin yamadidi da ita don kowa ya san ta da yamadidi da zance duk da shekarunta, duk inda ta zauna sai ta fadi abinda ya faru ko kuma abinda Auntyn ta ce, wannan ne yasa Aunty ta ki fitowa, Ita Hajiya Shafa’atu dama babu ruwanta da sabgar gidan sarauta, bata ma zaman Nigeria sai dai ta zo ta koma Canada don can Family dinta suke, suna ta zaune parlon Aunty bata fito ba sai ga Hajja ta shigo, Mikewa suka yi suna mata barka da shigowa, Hajja ta zauna cikin sanyin murya tace “Ina Aseeyah ko bata karaso ba?” Gimbiya Firdausi da Hajiya Shafa’atu suka zauna suka ce “Bata karaso ba kuwa Hajja….” Ko rufe baki basu yi ba sai ga Mami ta shigo tare da Ummi, duk suka zauna parlon, Hajja dai kallon Mami kawai take don kana kallon idonta zaka san tayi kuka sosai, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, bayan kusan minti biyar sai ga Mai martaba ya shigo parlon, duk suka mike suna masa barka da shigowa, Hajja dai bin sa kawai take da kallo har ya nemi kujera ya zauna, su Ummi kuma suka zauna kasan babban carpet din dake parlon, After some seconds ya kalli Ummi yace “Yi sallama da Hafsah, ko bata nan ne?” Gimbiya Firdausi tace “Ina jin tana ciki ranka shi dade” Ummi ta mike ta nufi hanyar da zai sadata da dakin Aunty, knocking kofar dakin tayi, amma taji shiru, sai da ta kwankwasa kofar sau uku sannan aka bude kofar, Baby ce tsaye bakin kofar, Ummi tace “Ina Fulanin?” Baby tace “Sallah take” Ummi tace “To idan ta idar ki ce mata Mai martaba na bukatar ta a parlor” Baby ta gyada mata kai, Ummi ta juya ta koma parlor, har bayan wasu mintuna goma Aunty bata fito ba, wannan yasa Sarki ya mike da kansa ya nufi dakin, ya bude kofar dakin ya ga Aunty zaune kan kujera idonta ya kumbura don kuka, Calmly yace “Fito mu yi magana Fulani” Aunty ta mike ta marairaice tace “Ranka shi dade ka shigo mu yi maganar a cikin nan mana” Sarki yace “A’a, ki fito parlon mu tattauna” Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Aunty ta ji ta ɗan samu courage da taga yanda Sarki is calm, ta dau gyalenta ta yafa sannan ta fito parlor, kallon su Hajja da Mami ta dinga yi har ta karaso cikin parlon ta zauna, da kyar ta bude baki ta gaida Hajja, Hajja ta amsa gaisuwarta ba tare da ta kalleta ba, Mai martaba na kallon su Gimbiya Firdausi yace “Na kira ku nan ne gaba daya domin ku shaida abinda zai faru yanxu….” Yana fadin haka ya ciro farin envelope karami daga babban rigar jikinsa, ya mike ya isa har gaban Aunty da ta rude ta fara Salati, ya ajiye mata takardan sannan ya juya yana kallon su Gimbiya Firdausi yace “Daga wannan rana na datse duk igiyoyin aurena da Hafsat, babu wani sauran aure tsakanina da ita….” Duk suka zaro ido suna kallon Mai martaba, Aunty ta dinga kururuwa a Parlon tana cewa “Ka sakeni fa kace? Me nayi maka ranka shi dade da zaka sakeni, in dai akan maganganun Walid ne wallahi kwakwalwarsa ce ta taɓu, komai ya zo masa baki fada yake yanxu, ka kai sa asibitin mahaukata ina me tabbatar maka za su ce maka ya samu matsala a kwakwalwarsa tun faruwar abun nan, wallahi ya haukace ne shi yasa yake sumbatu” Mai martaba ya nufi kofa ya bar parlon without saying a word, Hajja ta mike tana kallon Aunty tace “Allah ya isa tsakanin mu dake Hafsat, kin sa Sarki yayi abinda ba a so a masarauta wato saki, amma idan aka duba za a ga kin cancanci sakin don zama dake bala’i ne a duniya….” Tana kai wa nan ita ma ta fita daga parlon ta bar Aunty da ta dawo kamar mahaukaciya a parlon tana kuka, Tsam Gimbiya Firdausi ta mike zata tafi ta idar ma yan cikin gida abinda ya faru, wato sarki ya saki Fulani Hafsah, Hajiya Shafa’atu dai ta kasa dago kanta a inda take zaune, daga karshe cike da karfin hali ta mike ta nufi kofa, a tare Mami da Ummi suka mike duk suka bi bayan Hajiya Shafa’atu suka bar Aunty na ihu da koke koke a parlon, kan kace me labarin sakin Aunty ya karade kunnuwan duk jama’an gidan sarauta…. Karfe hudu saura na yamma Khaleesat na zaune parlon Mami da Ajay sun je yi mata sallama, basu sameta a parlon ba shi ne suke zaman jiranta, tun incident din da ya faru parlon Mai martaba da safe coupled with sakin da aka yi ma Aunty daxu yasa Khaleesat wasn’t just herself, sosai ta shiga damuwa da tashin hankali, duk jikinta yayi sanyi, she can’t just fathom all what happened, ta dade tana tunanin me Ajay yayi ma Walid da ya so kashesa, idan ma dukan da yayi masa ne ai shi ya ja abinda aka masa dukan, Ajay dai kallonta kawai yake duk motsin da zata yi, shi dama har a yanxu abinda ya faru da shi yasan kawai plot ne da aka shirya, from the beginning he suspected Walid amma Jay yaki gane abinda yake nufi, so he wasn’t even shock at all what Walid said in the morning, it was something he already knew, ko brake din motarsa da aka yi tampering with back then yasan duk aikin Walid ne, but he is glad yanxu sai ya ci gaba da muguntarsa akan Wheel chair don ko tausayi bai basa ba, Mami ce ta shigo parlon da sallama, ta zauna tana kallonsu tace “Kar dai yanzu za ku tafi Junaid?” Ajay yace “In sha Allah Mami…” Mami tace “To Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, Allah ya sa ayi aikin a sa’a, ya baka lafiya son” Ya sauke idonsa a hankali yace “Ameen Mami” Mami ta kalli Khaleesat tace “Take care of him kin ji Halysaah” Khaleesat ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “I will in sha Allah Mami” Mami na murmushi tace “I trust you dear, Kun samu Hajja a bangarenta?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Eh mun sameta” Mami tace “Amma za ku je bangaren Auntyn ku ai, daga can nake ma yanxu?” Ajay yace “Can za mu je yanxu” Mami tace “Toh har su Kilishi duk kaje ku yi masu sallama don Allah ka ji” Kai kawai ya gyada ma Mami, Mami tace “Ina Jawwad din?” Ajay yace “Mun bar sa a wajen Hajja” Basu kara minti daya ba a parlon Mami suka fita, Bangaren Aunty Faridah suka nufa, nan suka sameta zaune a parlor tare da su Kilishi da shigowarsu part din kenan, zaunawa suka yi a parlon suka gaida Aunty Farida da su Kilishi da Hajiya A’isha, Aunty Farida tace “Ya jikin Junaid?” Ajay na kallonta yace “Alhamdulillah Aunty, mun zo yi maki sallama ne” Kilishi tace “Ba dai tafiyan za ku yi yau ba?” Ajay yace “Yau za mu tafi” Hajiya A’isha tace “Har da Jawwad din?” Ajay yace “Eh, in sha Allah” Kilishi tace “Ikon Allah, to Allah Ubangiji ya kai ku lafiya ya tsare hanya” Khaleesat dai kallon kanwar Ummanta kawai take with admiration, cause she was just glowing, Kilishi na kallon Ajay tace “Ka ga wannan matar taka Halysaah, wallahi tallahi ka rike ta da hannu bibbiyu don samun mace irinta da zata so ka tsakani da Allah sai an tona, mu za mu bada labarin halin da ta shiga bayan bacewar ka, zaman shekara biyu tayi a gidan nan ko nan da kofar gida bata son fita duk tana zaman jiran ka, muka dinga mata kallon mahaukaciya, babu asibitin mahaukatan da sarki bai sa an kai ta ba amma kullum jiya e yau, ashe ita tana ji a jikinta kana nan a raye shi yasa taki hakura, tayi abinda ba ko wace mace zata iya yi ba har na tsawon shekara biyu, duk ta zama abar tausayi a gidan nan, kuka ba dare ba rana, wallahi ko wataran kace zaka mata kishiya sai mun tsine maka mu dai, don irin ta ba matar da ake hadawa da kishiya bace, ko shi Jawwad din har yanxu bai zaunar da kai ya karanto maka halin da matar ka ta shiga bane shekaru biyu da suka wuce? Daga ita har shi komawa suka yi kamar taɓabbu a gidan nan, suka dawo majinyata har likitoci aka dauko musamman saboda su” Ajay dai kallon Kilishi kawai yake, Hajiya Habibah ta sauke ajiyar zuciya tace “Ai kin gama magana Kilishi, wannan yarinya dai in dai da ranmu da lafiya baza mu bari ya ce zai mata kishiya wataran ba, balle shi dama ba me kule kulen mata bane, tayi masa halaccin da ba ko wace mace bace zata iya yi masa wallahi, muna cewa ya mutu tana cewa bai mutu ba, ta zauna tayi zaman jiransa taki komawa gaban iyayenta, mu duk mun dauka hauka tayi, ashe sarai tasan abinda take yi, jikinta bai bata mijinta ya mutu ba, dama tsakanin mata da miji sai Allah, kawai muna fatan Allah ya basu zuri’a ta gari amma zancen kishiya kam babu ita” Hajiya A’isha dai tayi shiru bata ce komai ba a parlon, don da Ajay zai ce zai kara da er ta Iklima ita ai so zata yi, Ajay dai ya kasa cewa komai a parlon kansa a sunkuye, Kilishi ta mike tace “To bara mu fita, su gana da Baabar tasu, yau dai karshen zaman annoba ya zo a gidan nan, ana can ana hada kaya….” Daga haka ta fita daga parlon sauran ma duk suka fita, Ajay na kallon Aunty Faridah a hankali yace “Aunty ya bakunta?” Ta ɗan yi murmushi tace “Lallai kam, yanxu idan ku ka tafi sai kuma yaushe?” Yace “Aunty za mu ɗan zauna a can na wani lokaci kafin mu dawo” Khaleesat ta juya ta kallesa, har taji dadi a ranta don she even prefer staying in America daga ita sai shi, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace “Sai dai mu yi ta magana ta waya kenan” Yana murmushi yace “Amma ai za mu dawo Aunty, just that za mu dade” Aunty Farida ta sauke kanta tace “To Allah ya tabbatar da alkhairi Junaid, Allah ya baka lafiya, yasa ayi aikin a sa’a” Yace “Ameen Aunty” Kallon Khaleesat yayi yace “I will wait for you outside” Daga haka ya mike ya kara yi ma Aunty Farida sallama ya fita daga parlon, mikewa Khaleesat tayi ta koma kusa da Aunty Faridah tana murmushi tana kallonta tace “Aunty kin ga kyan da kika yi kuwa?” Aunty Farida ta mata wani kallo, Khaleesat ta kyalkyale da dariya ta mike ta shiga dakin Aunty Faridah, girgiza kai Aunty Faridah tayi tana murmushi ta tashi ta bi bayanta zuwa cikin dakin. Gun Mai martaba ne waje na karshe da Ajay da Khaleesat suka tafi don yi masa sallama, Sarki kallonsu kawai yake a parlon bayan Ajay ya sanar masa za su tafi, Khaleesat dai kanta na kasa tana wasa da veil dinta, Mai martaba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “Surgery din da healing duk bazai wuce wata daya ba ai ko?” Ajay ya daga kai ya kallesa yace “Haka ne ranka shi dade” Mai martaba yace “Nan da wata dayan za ku dawo kenan?” Ajay ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds a hankali yace “Ina son za mu zauna a can na wani lokaci ranka shi dade” Kallonsa Mai martaba ya dinga yi babu ko kiftawa, bayan wani ɗan lokaci calmly yace “Har na wata nawa?” Ajay bai ce komai ba, Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace “Amma kasan ba mu je can Benue wajen mutanen can ba Ahmad, kar ka zama me mance alkhairi mana” Ajay ya girgiza kai yace “Wallahi ban manta ba ranka shi dade, ko jiya mun yi maganar da Mukhtar, nayi bincike na gane local govt din wajen har da sunan garin, nace zan tura masa kudi ya kai masu kafin mu dawo, i still can’t bear journeying on water for now ur highness, I think I’ve got Aquaphobia for now, kuma dole sai an bi ta ruwa za aje garin” Mai martaba ya gyada kai a hankali yace “I understand Junaid, ko baka nan za mu je garin da Mukhtar din in sha Allah, jiya ma DSP Bilyamin ya ajiye min message ta WhatsApp zai shigo Bauchi gobe, kasan 2 days ago na siya masa motar 25M, and he appreciate it so much…” Ajay na kallon Mai martaba yace “Allah ya kara budi ranka shi dade” Mai martaba yace “Ameen, amma ina son in an gama Surgery din ka samu lafiya ku dawo Nigeria, idan ma baza ka zauna a Emirate ba you can stay outside of the Emirate bazan hana hakan ba yanxu, ka zabi duk inda kake son ka zauna da matar ka….” Ajay ya gyada masa kai a hankali yace “To in sha Allah ranka shi dade, Allah ya kara girma” Mai martaba dai kallonsa kawai yake cause he can’t bear Junaid being far away from him again, America yayi nisa kuma baya son wani abu da zai sake sa ɗan nasa yayi nisa da shi, Mai martaba ya kalli Khaleesat da kanta ke kasa har sannan, sai kuma ya kalli Ajay yana nuna masa ita yace “Ka ga Jiddah…” Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat, Calmly Mai martaba yace “Ɓacin ranta ɓacin rai na ne, a duk sanda kayi kuskuren bata mata rai, to ka sani wallahi ni ka ɓata ma Ahmad, don haka try all possible best to avoid hurting her by all means, kuma ka sani ko da ka ci amanarta wataran ko da raina ko babu raina to wallahil Azeem amanata ka ci” Khaleesat ta ji hawaye sun kawo idonta, shi dai Ajay kallon Mai martaba kawai yake a sanyaye, Mai martaba ya girgiza kai yace “Ko da wataran ka ji kana son kara aure to Ahmad ka sani ba da son raina zaka yi auren nan ba, ba kuma da goyon bayana zaka yi auren ba, kawai dai babu yanda na iya ne saboda addininmu ya yarje maka da karin auren, amma baka da goyon bayana idan har hakan ta kasance, yanda nake jin ‘ya yan da na haifa a cikina haka nake jin Jiddah, she means a lot to me, don haka ka guji duk wani abu da zai bata mata rai, yin hakan tamkar ka guji ɓacin raina ne, ita kuma na yarda da ita nasan bazata taɓa saɓa maka da gangan ba sai dai bisa kuskure, ina kuma fatan Allah Ubangiji yayi maku albarka, ya baku zaman lafiya na har abada ya baku zuri’a masu albarka, but know that Jiddah is dear to me Ahmad…” Ajay ya sauke idonsa a hankali maganganun Mai martaba na sinking cikin kansa.

Back to top button