Fentin Zina Page 30 Hausa Novel
*****Juyawa yayi zuwa bakin kofa ya samu maryam yace mata kije dakin naki zanzo yanzu! Ta girgiza kai cikin rashin gamsuwa tace ai naji duk abunda tace nasan baza ka zo ba.Ki yadda dani maryam zanzo ki tafi kawai. Toh tace ta juya ba don ranta naso ba ta koma dakin ta. Shima zuwa yayi ya kwanta bai kula ta ba sai da yaji saukar numfashinta ya sauya ya tabbatar tayi bacci ya zari jiki a hankali ya fice daga dakin ya tura kofar dakin maryam ya shiga. A tsakiyar gadon ya tadda tana zaune ta hade kanta da gwiwarta tana kuka, da hanzarinsa ya isa gareta yana tambayarta lafiya meke damunki? Wani abu na miki ciwo ne?. Duk a jere yayi mata wadannan tambayoyin.Dago kanta tayi da idanunta da suka jika da ruwan hawaye ta kalleshi bata ce komai ba ta sunkuyar da kai. Hakan ba karamin kara tada mai hankali yayi ba yace ki fada mun dan Allah kada ki bar zuciyata cikin wasiwasin na cutar dake ko akwai laifin dana miki.A Karo na biyu ta kara dago idonta wannan karon babu hawayen sun dakata da zubowa tace dama da naji shiru ne baka zo ba kuma ina jin tsoro sosai na kasa bacci shine na zauna ina jiranka. Ta karashe da dan jan numfashi.Dafe goshi yayi yace my God! Maryam ai tunda nace miki zanzo zanzo din kuma kinsan ba kwanan ki bane shiyasa dole insan dabarar da zanyi in fito kada ta ji ta farka amma kiyi hakuri bisa ga rashin zuwa da wuri da banyi ba har hakan ya fitar mun da hawaye daga wannan kyakkyawar fuskar. Ya fada yana shafo gefen kumatunta.Murmushi tayi na jin dadi tace kada ka damu ai baka laifi yanzu dai mu kwanta bacci nake ji sosai. Ta fada tana kiciniyar kwanciya.Toh kice dai dama dumina kike son ji kawai kika wayance da tsoro kike ji.Da gaske ina jin tsoro kamar yadda da gaske ne ina jin begenka, nidai kazo mu kwanta.Jinjina kai yayi kawai don ya gane nufinta sarai kuma abunda take so din bazai faru ba sakamakon baida kuzari ko kadan kuma da alama wannan tafi Ameena jarabar tsiya saidai ya barwa kanshi kila don sabuwar budurwa ce shiyasa.A daren dai maryam bata samu abunda take so ba domin kusancin da ta kulla hanawa bata san ya dade da kusantuwa ba, hakan ba karamin kara bata ranta yayi ba har yasa ta dau alwashi masu yawa a zuciyarta wanda kuma yasa tayi kwanan bakin ciki.*****Ameena cikin dare fitsari ya tashe ta tun tana kiwyan tashi hardai ta tashi zaune ta laluba makunnin haske mara karfi na dakin nasu ta kunna, idontane yakai inda Abdul ke kwance taga wayam babu shi, sai tayi jim tayi tsammanin koya shigabayi ne, saidai mintuna kusan biyar sun wuce bata ji motsin shi a ban dakin ba, nan take zuciyarta ta hasko mata abunda ya faru dazun da daren nan take idonta yakai kan kofa tana nan dai a kulle, sai taji zuciyarta bata aminta ba ta mike ta is a gun kofarta murda handle din taji ya budu mamaki matuka ne ya kamata tana kara girmama lamarin rainin Abdul gareta, ashe har zai iya barinta kwance a ranar kwananta ya tafi gurin wancar mai kamar matan barikin? Itafa bata yadda wai tsoro take ji ba kamar yadda ta fada ba ta daifi karkata akan makirci ne kawai ba wani abu ba.Haka ta karaci tsayuwarta a bakin kofar kana daga bisani ta gaji ta komo ta shiga toilet tayi uzurinta ta fito ta dauki tsumman data ajiye a gefen side drawer dinta ta kade gadon sau uku bayan tayi bismillah ta hau ta kwanta ta cigaba da baccin ta.Washe gari haka ta tashi duk bacin ran da take ji bai hanata tayi duk ayyukanta kamar yanda ta sababa. Tana zaune a falon said gasu sun fito, maryam ce ta fara lura da ita don haka ta fara nanuke masa tana cewa honey naji dadin daren jiyan nan sosai kamar kada gari ya waye, juyowan da zaiyi idonshi carap akan na Ameena idanunsu suka sarke dana juna, wani irin faduwar gaba yaji ya ziyarce shi amma bai nuna ba.Daga inda take zaune tace sabon ango baka bukatar takura kyanka abar ka da amarya, kayi kyalli kayi kamshi barka da fitowa.Sosai kalamanta suka shige shi tabbas sakonta ya isa ga inda ta aike shi, murmusawa yayi cikin iya karfin halinsu na maza yace kece ran gida dole a biki a sannu takawar ki lafiya uwar gida a gurin Abdul.Kallon gefen ido tawa maryam taga yadda ta cika kamar ace kiris ta fashe, hakan kuwa ya mata dadi don haka takai dubanta ga uban gayyar ta kara fadada murmushinta tace uwargidar Abdul, Shalelen sa, abar sonsa duka ko? Ta tambaya tana dage gira daya.Abdul ba tare da wani tunani ba yace kwarai kuwa toh dai yanzu aji da cikina ina jin yunwa.Da sauri ta mike tana fadin an gama ranka shi dade, ta nufi dining suka bita a baya tayi serving dinsu dukkansu nan suka fara cin abinci abdul said santi yake bugawa ita kuwa dariya kawai take mai kuma tana sane take bite ma I don’t talk Lura da yadda maryam ke ta wani hade rai said kace ba daren jiya ta zalunceta ba. Aranta tace yanzuma kika fara gani indai zakiyi wasa da Ameena, ni ba muguwa bace amma cikin ruwan sanyi zan dafa ki har ki kone idan baki shiga taitayinki ba. Duk tana tunanin nan ne da cokali a hannunta tana cin abinci tana binsu da ido dukansu.Haka suka gama ta tattare gurin kamar ko yaushe kowa ya kama gaban shi. Abdul dakin shi ya wuce bai tsaya bata lokaci ba ya fada ban daki yayi wankan sabulu ya karasa da wankan tsarki ya fito ya shimfida darduma ya tada sallah. A daidai zaiyi sallama Ameena ta shigo da mamaki take binshi da kallo harta karaso ta zauna a gefen gado ya idar ya juyo gareta yace lafiya kike ta kallona kamar naci bashi ban biyaba?.Hum Abdul garage con bash in ma da irin rayuwar nan da kake ciki. Duban ban gane ba ya mata yace kamar ya kenan?.Tace nasan ka gane abunda nike nufi dan Allah na rokeka ka gyara, ka duba fa kusan karfe tara amma ace sai yanzu kake sallahr asuba ai ba daidai bane kaji tsoron Allah ka gyara alakarka da ubangijin ka kayi sallah a daidai lokacinta.Cikeda gajiya da mitarta a cewar shi yace naji zan gyara daga nan ya rude zance da cewa duba mun kayan da zan saka zanje gidan su mama in gaishesu.Ta mike ta is a walldrop din tana cewa nima na kwana biyu banje ba ka gaishe su.Zasu ji.Ciro mishi kayan tayi ta ajiye tace sorry minti biyu ina zuwa.Ok yace.Dakinta ta koma tana tunanin meya kamata ta bashi yau dai kam ya kaiwa mamar shi dukda bawai sonta take ba amma hakan bazai hana ta kyautata mata a matsayinta na wacce ta haifi mijin da take aure………… *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️




