Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 43 Complete Novel

.*ASM Bk2043*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

…….. Lokacin da suka iso harabar Event Center d’in shak’e take da jigunannun motoci masu numfashi kai ko ba’a fad’a ba kasan wani wanda ya kai ne zai yi aure, bayan ya parker Motar ya kai hannu ya d’auki phone d’in shi dake ajiye gefe bayan ya bud’e ya shiga call log ya fara kokarin kiran Abbas ringing biyu ya d’aga kafin yace wani abu Abbas ya riga shi tambayar sun isa wurin ne yace mashi eh yace Ok shima gashi nan ya kusa shigowa jin haka yasa yay cutting kiran ya maida wayar inda ya d’auke ta ya d’ago ya kalli Fatuu suka had’a ido da yake wurin fayau yake kai kace da rana ne don ba abunda ba’a gani hakan yasa har cikin Motar akwae d’an haske da za’a iya ganin mutum duk da glass d’in blacktinted ne amman widescreen d’in gaban bai da duhu sosae kamar na k’opopin, maida kan shi yay jikin headrest itama ta juya tana kallon abubuwan dake faruwa a wajen cikin ranta tana jinjina irin Motocin Alfarmar da aka tara ga Mutane ne sai kai da kawowa suke, bada jimawa ba Abbas ya shigo akan idon Haisam bayan ya parker Motar ya bud’e ya fito yana lallatsa wayar shi ganin hakan yasa Haisam ce ma Fatuu yana zuwa ta d’aga mashi kai ya d’auki wayar shi ya bud’e ya fita, tunkarar Abbas dake k’ok’arin kiran wayarshi yay yana ganinshi yay dariya suka ba juna hannu ya d’an kalli gefen shi ganin bai ga Fatuu ba yace “ina Zarah badai kai kad’ai d’in ka taho ba?” Fuskar shi a sake yai mashi nuni da tana cikin Mota ya jinjina kai shima ya tambaye shi ina Feenah bai bashi amsa ba sai dariya kawae yake can ya juya ya bud’e Motar ya d’an duk’ar da kan shi da alama Magana yay ya fiddo ya rufe aka bud’e front door d’in d’ayan side d’in ta fito tana sanye da irin rigar Fatuu tunda ta fito Haisam ya tsuke fuska yana mata wani kallo ganin ba Feenah bace wata ce daban yar doguwa ce don zata fi Fatuu tsawo saidae bata da jiki amman ba za’a kirata siririya ba kuma fara ce duk da da gani an k’ara dana kanti ko daga yanayin hasken fuskarta zaka gane, rigar ta amshe ta da yake roba ce amman fa da gani wurin hips d’in anyi ciko don bai tafi sosae ba kamar na gaske, tana k’arasowa Haisam ya kauda idon shi ba kamar ganin yadda ta kafe shi da ido Abbas ne yace mata ga Aminin shi Haisam su gaisa cike da kwanare da kisisina cikin mak’e murya ta gaishe dashi k’asa k’asa ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba suna haka Motar ango ta iso wata rantsattsar jeep mai bugun zuciya tasha adon su balloons ga security gefe da gefe Motocin suka ja layi suka tsaya ba tare da wani ya fito ba Abbas ne yace ma Haisam ya kamata Zarah ta fito tunda sun iso yanzu za’a shiga ya d’aga mashi kai kawae dama wayar shi na ruk’e a hannun shi ya kira ta bayan tayi picking yace ta fito da yake yasan tana ganin su tunda Motar a saitin su take, saida ta cire jallabiyar ta aje anan cikin Motar ta gyara rolling d’in gyalen ta yadda daga bayan kan ta ya d’aga sosae Saboda gashin ta dake a fake ta kai hannu ta bud’e Motar ta fito bayan ta rufe ta tunkare su tana tafiya slowly hips d’inta na wani sama da kasa sakamakon takalmanta dake da tsini sosae kai kace da gayya take yin tafiyar saidae ita tsakaninta da Allah lafiya lou take yin tafiyarta tunda ta fito Abbas ya kafeta da ido bako k’yaftawa haka budurwar tashi, kallon Abbas Haisam yay da niyyar yi mashi magana ganin gaba d’aya attention d’in shi ya tafi kan wani abu yasa shi d’an juyawa ya kalli direction d’in da idanun Abbas d’in suke idanun shi suka sauka akan Fatuu da take nufo su har bai san ya hadiyi abu ba lips d’in shi suka d’an motsa kad’an wani iri yaji ganinta haka sam bai yi tunanin zata cire jallabiyar bane ganin ta hau da dressing d’in sosae yama kasa gane dad’in ganinta haka yaji ko kuwa akasin hakan kawai dae abunda ya sani shine sam bai dace a ganta a haka ba, tana murmushi ta k’araso ta tsaya gefen Haisam tana kallon Abbas da shima yake d’an murmushi shi kan shi bai so ganin ta haka ba har saida yay mamakin yadda akai Haisam ya fito da ita a haka, rigar ta kamata sosae shape d’inta ya fita over ita kanta budurwar Abbas d’in duk sai ta raina kanta sai faman kikkafta ido take tana had’iyar abu bakinta na d’an motsawa ta kafe Fatuu da ido tana mata kallon k’urulla Abbas ne ya katse shirun da fad’in “Mom Zarah an yo rakiya kenan” tana murmushi ta d’aga mashi kai kafin ta gaishe dashi ya amsa ta kalli budurwar Abbas d’in suka had’a ido ganinta da irin kayan jikinta yasa tay tunanin tare take da Abbas tana murmushi tace mata sannu ta d’an yi murmushin itama amman na yak’e tace yauwa had’i da d’an juyar da kai, d’aga kai Fatuu tayi ta kalli Haisam da shima kallonta kawai yake bazaka gane yanayin fuskar shi ba d’an murmushi tay mashi bai ce komai ba kuma bai maida mata martanin murmushin ba suna haka aka sanar amarya da ango zasu fito a shirya entrance Abbas yace su je kaman Haisam d’in bazai je ba saida Abbas ya k’ara cewa su tafi sannan slowly ya kalli Fatuu yay mata alamar suje tana a gefen shi suka tunkari wurin, cikin shiga ta Alfarma da ni kaina bazan iya k’iyasta adadin dukiyar dake a jikinsu ba Bride and Groom suka fito suna ruk’e da hannun juna Amaryar na sanye da rantsattsiyar farar wedding gown da ke sakin wani irin k’yalli mai d’aukar ido da alama dai stones d’in da akai adon rigar kilan diamond ne dama tun daga kunnanta wuyanta har hannunta duk diamond ne sannan aka bi da kuma irin sark’ar su da suke sawa ta duwatsu mai kaman murjani har a saman kanta tayi kyau ba k’arya dama gasu jajur da su shima Ango Prince Obinna fararen suit ne a jikinshi sai bak’in tie da bak’ak’en takalma shima kunnuwan shi na manne da barimar diamond haka agogon hannunshi ma, bayan duk an fito an jera layi abun gwanin burgewa ashe ba iya shigar su Fatuu bace wasu bak’ak’e suka sa Matan na sanye da fararen gown wasu marron suit Matan na sanye da gown golden brown da sauran shiga kala kala sosae suka tsaru duk masu shiga iri d’aya sun jera wuri guda ga makad’an su na gargajiya sunyi shigar su suna irin kid’an su suna ma ango da Amaryar shi kirari bayan komae ya tsaru yadda ake so aka nufi cikin Hall d’in, Wow wow just wow don bansan ma ta ya zan fara bayyana tsaruwar wurin ba don duk iya hasashen mai hasashe ba zai iya k’iyasta ainihin nawa aka kashe ba wurin tsara wurin don wurin ya fitinu abun ba’a Magana suna shiga duk na ciki aka mik’e tsaye police bands suka d’auka busar sarewa kake ji ta ko ina ga kid’an su da ke sa mutum ya tausaya ba tare da yama sani ba wuri fa ya kacame da kid’e kid’e ga yan rawar gargajiya ma na nasu jikin Fatuu har tsuma yake sai faman sakin murmushi take ji take ina ma anzo da Fauzy tazo taga sha’ani da ya amsa sunan sha’ani, saida suka je suka zauna a high table sannan sauran Mutane duk aka zazzauna aka dakatar da kide kiden don fara gabatar da abunda aka zo yi, bayan MC yay welcoming kowa wani abokin ango ma yazo tare da budurwar shi ce ko matar shi oho yay ma kowa sannu da zuwa da gabatar da abunda aka taru yi bayan ya gama babban Abokin Ango da Amarya inyamurai suka fito suka bada tarihin Ango da Amarya bayan suma sun gama aka buk’aci Bride and Groom suka fito don taka rawa zo kaga yadda suke cashewa abunsu cike da nuna ma juna kauna abun sai yama ba Fatuu kunya sai faman sunnar da kai take yayin da ake ta masu ruwan lik’i masu lik’a dollars nayi masu lik’a Naira nayi manyan mutane masu sanye da shigar su ta gargajiya ta ko ina sai tasowa suke suna lik’i daga baya aka bukaci kowa ya koma Abokan Ango da Amarya inyamurai suka fito aka fara casu mai sunan casu Fatuu sai dariya take haka ma su Abbas ji take kaman tay tsuntsuwa ta ganta a cikin filin itama tayi rawar saidae ba dama, bayan duk an gama abubuwan da ya dangance su aka dawo kan hausawa shi Angon da kanshi ya fara bayanin irin alak’ar shi da mutanen Katsina da irin karar da suka yi masu tun bayan da suka tsinci kan su a cikin garin ba tare da nuna k’yama ko tsangwama ba Saboda bambancin Addini ya tabbatar ma Mutane da musulunci addinin zaman lafiya ne sa6anin wasun su da suke masu kallon yan ta’adda yace shi shaida ne game da Mutuncin hausawa don sun nuna masu k’auna ta yadda har sun zama daga cikin Family d’in shi a k’arshe yay godiya ga musulman da suka zo wurin ya nuna hakan ba k’aramin abu ne a wurin shi ba yay fatan Allah ya k’ara had’a kan su suci gaba da zama da juna da Amana yay Addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata ga K’asar mu Nigeria sannan yay godiya ga Governor d’in Katsina da Sarakunan D’aura da Katsina da sauran manyan mutane Mutane nata amsawa da Ameen bayan ya gama itama Amaryar aka bata tayi godiyar bayan duk sun gama aka buk’aci babban Abokin Ango bahaushe da ya fito ya bada tarihin Ango na nan garin irin alak’ar shi da mutane da sauran su MC ya tambayi angon waye zai fito ya nuna mashi Haisam duk ido ya dawo kan shi a nutse ya mik’e ganin zai fito shi kadae MC yace the equation isn’t balanced nan take duk aka gane abunda yake nufi da yake d’an barkwanci ne duk aka sa dariya dakatawa Haisam yay ba wai fita da Fatun ne bazai yi ba sam shigar ta bata dace da wurin ba a matsayinta na Musulma Abbas ne ya kalli Fatuu yace ta tashi suje ganin Haisam d’in bai ce komae ba yasa ta mik’e ta fito suka jera wohoho all eyes on them ita kanta Fatuu duk sai ta ji ta takura, tunda suka fara saukkowa daga kan steps d’in MC ya saki baki galala kamar rainon sakarai yana bin su da kallo tun daga sama har k’asa, lokacin da suka k’araso gaban shi suka tsaya fuskar Haisam dai ba wata walwala don duk ji yake wurin ya fice mashi a rai maimakon MC d’in ya bashi loudspeaker d’in sai yace mashi wait ya juya kan Mutanen wurin yace “People are u seeing what am seeing???” gaba d’aya aka sa dariya ya sake juyawa kan angon harda d’an rankwafawa alamar girmamawa cikin harshen turanci da yake dashi ake Magana a wurin yace ya gafarce shi amman abokin shi bahaushe ya tambaya ba Arab ba ko Indian gaba d’aya wurin aka kwashe da wata irin dariya har dai shi Haisam d’in saida ya d’an dara Fatuu ma haka daga inda Angon yake zaune yace ma MC ya ba Haisam d’in speaker ya tambaye shi tarihin shi da Hausa anan zai gane wanene shi ya juyo kan Haisam yace suna rok’on Alfarmar jin tarihinshi da hausa farko kafin ya fad’i abunda aka bukace shi ya fito yi, shiru ya d’anyi MC d’in nata fad’in please can ya kai hannu ya amshi speaker d’in cikin cool voice d’in shi ya fara bada tarihinshi a tak’aice cikin harshen hausa aikuwa masu jin hausa a wurin aka hau tafi da sowa Haisam d’in na d’an murmushi MC sai faman jinjina kai yake baki bud’e alamar mamaki bayan ya gama ya canza harshe zuwa turanci ya fara bada tarihin Ango da mu’amalar shi da mutane anan sai ka rantse ba shine ya gama Magana da Hausa ba gaba d’aya ya gama tafiya da mutane sai faman sakin murmushi ake bayan ya gama ya mik’a ma MC d’in speaker d’in amman sai yak’i amsa yace yana son yay mashi few questions ba yadda Haisam d’in ya iya dole yace mashi yana jin shi farko tambayar shi yay miye alak’ar shi da Fatuu har saida gabanta ya fad’i Haisam d’in yay d’an shiru kamar mai nazari Abbas kuwa mi zaiyi in ba Dariyar mugunta ba can ya nisa yace mashi girlfriend d’in ce da sauri Fatuu ta kalle shi sai kuma ta kauda kanta gudun kada a gane ba gaskiya ya fad’a ba saidae bata yin zaton zai boye gaskiya ba, tambayar shi yadda akai suka had’u ya k’ara yi anan bai 6oye ba yace mashi Neighbor d’in shi ce daga baya ya koma kan Fatuu itama ya tambayeta tsakanin su waya fara cewa yana son wani shiru tay ta rasa amsar da zata bashi kawae sai ji tay Haisam d’in yace mashi shi ya fara MC d’in ya k’ara tambayarta ya taji da ya furta yana sonta tace taji dad’i sosae har bata san yadda zata bayyana ba tana fad’in hakan ta sunnar da kai, haka dae yaci gaba da yi mata tambayoyi daga baya Haisam yace ya d’an yi excusing nasu yay ma Fatuu alamar su je suka juya MC nata kod’a su yana fad’in “What a match, What a perfect Match…….” Maimakon su koma high table d’in sai gani tay ya nufi hanyar fita daga hall d’in hakan yasa ta bi bayan shi suka fice, inda Motar su take ya nufa tay tsaye tana kallon shi ya bud’e ya kalleta yace ta shiga cikin rashin fahimtar dalilin fitowar su ta kai hannu ta bud’e ta shiga tana ta kallon shi har yay ma Motar Key ya fara yin reverse tana dae ta kallon shi da alamun mamaki har ya juya Motar suka tunkari gate d’in fita, suna hawa hanya sai ga kiran Abbas yana yin picking tun kafin Abbas yace wani abu yace mashi yaba Prince hak’uri he has an urgent call ya tafi daga haka yay cutting call d’in yaci gaba da driving baki bud’e Fatuu ke kallon shi sam bata yarda da Maganar da yay ba a yaushe aka kira shin, d’an juyawa yay ya kalleta yace mata lafiya fuska a tur6une tace mashi ya akai suka baro wurin daga farawa shiru yay kaman ba zai ce komai ba sai kuma yace mata gida zai maida ta kamar zatai kuka murya na rawa tace “to Saboda me, duka fa bamu wani dad’e da zuwa ba” nan ma shirun yay tana ta k’unk’uni sai da ya d’an d’auki lokaci sannan yace “ban ce in akwae wani problem da kayan ba u shall inform me a canzo?” tura baki tay yanzu ta gano dalilin kaman zatay kuka tace “to ai naga ta shige ni ne” banza ya mata taci gaba da k’una k’uni da jan majina alamar zatai kuka can ya juya ya kalleta sai kuma ya maida idon kan hanya calmly yace “ai mun je ko miye na damuwar?” kallon shi tay kaman bazata tanka ba ta d’aure fuska a shagwa6e tace “to wannan zuwa ne, kofa Abinci bamu ci ba gashi serve ur self za’ai harda bank’ararrun raguna mutum yaci iya cin shi ga wannan yar giyar ma da aka aje mana saman table ko sha bamu yi ba” Haisam baisan lokacin da yay dariyar da har hak’oran sa suka bayyana ba jin wani shirmen ta wai giya d’an juyawa yay still yana dariyar yace “Har yanzu baki daina ganin lemu kice giya ba ko” tana tura baki tace “to ai giyar ce wannan ko ga kwalaben nan manya manya masu duhu kuma dama ai su suna shan ta” d’an shaking kan shi yay yana d’an murmushi yace “to wannan ba giya bane is non Alcoholic suna respecting addinin mu bazasu bamu giya ba saidae in mutum na sha yay Magana a bashi ko nama ma musulmai suke ba suyi processing nashi” shiru kawae tay still bakinta a ture yake can ya d’age gira yace “da giyan ne sai ki sha kenan?” Kikkafta ido tay tace “to ai in a rashin sani na sha ba wani abu ko” yace “to waya kai ki inda za’a bakin balle har kisha?” Shiru ta d’an yi kafin tace “kai ka kai ni kuma kasan za’a banin” yana murmushi yace “in nasan za’a baki bazan kai ki ba” shiru tay shima yaci gaba da driving d’in shi yana yi yana d’an kallonta still da murmushi a kan face d’in shi ganin yadda ta 6ata rai ita ala dole an mata laifi, a gaban wani babban soya spot ya parker Motar gefen titi ya fita part d’in gasasshen rago mai yawa yasa aka yanko mashi had’i da gasasshar kaza bayan ya biyasu ya dawo a back seat ya bud’e ya saka ya rufe ya koma driver seat d’in suka tafi, a gaban wani Cafe ya k’ara tsayawa ya fita bada jimawa sosae ba ya dawo ruk’e da k’atuwar leda mai tambarin wurin ya shiga suka tafi har lokacin bata washe ba sai fushi take, ganin sun bi wata hanya wadda ba ita suka biyo ba da zasu zo yasa ta d’an juya ta kalle shi yanata driving bata ce komae ba ta maida kan ta jikin seat har suka k’araso wata unguwa suka shiga Fatuu ta bi manyan gidajen da suke wucewa da ido lokaci guda mamakin ina ne suka zo ya cika ta tana niyyar juyawa ta tambayi ina suka zo idonta suka sauka agaban wani d’an sign board mai d’auke da sunan road d’in da Unguwar nan take ta gane G.r.a ne da mamaki ta juya ta kalle shi tace mi zasu yi a Gra kamar bazai tanka ba sai kuma taji yace saida ita zai yi ta tura baki, suna hawa wani titi ya tunkari wani tangamemen gate na wani katafaren gida ya tsaya yana latsa horn sau biyu wani mutum mai sanye da kayan yan sanda ya d’an manyanta ya lek’o ta k’aramar kopa yana ganin Motar ya koma da sauri ya zuge masu gate d’in Haisam ya shige, bai nufi k’aton parking space d’in ba sai ya parker ta gaban ginin gidan wanda mansion ne na Gaske ya kalli Fatuu yace ta fito ya kai hannu ya bud’e kopar ya fita itama ta bud’e ta fito baki bude take k’are ma gidan kallo duk da ba bene bane amman yana da girma sosae ga ginin kan shi abun mutum ya saki baki yana kallo ne ga had’addun shuke shuken da suka zagaye ko ina sun k’ara k’awata harabar sosae ta ko ina k’awatattun fitilu ne sun haske gidan security d’in ne ya iso gaban Haisam yana washe baki yay mashi sannu da zuwa ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Fatuu itama ya gaidata duk sai ta ji wani iri hakanan ta amsa, bud’e back door yay ya fiddo da ledojin ciki security d’in ya mik’a mashi hannu yace ya kawo ya rage mashi Haisam d’in yace ya bashshi bayan ya rufe kopar yana shirin wucewa security d’in yace “Yalla6ai mai gyaran nan ya dawo yace abun nan sai ya kai zuwa gobe dole sai a Kano aka samu goben za’a kawo sai ya idasa gyaran” kai ya jinjina sai kuma ya tambaye shi tun yaushe aka maido wuta yace mashi ai duk yau akwae wuta gaskiya Haisam d’in ya amsa da Ok ya juya shima security d’in ya koma gate kallon Fatuu yay bayan ya zagaya side d’in da take yace suje tay tsaye tana kallon shi har zai juya ya dakata yace bata ji bane d’an yamutsa fuska tay tace ina ne nan d’in wani kallo yay mata kafin ya bata amsa da inda zai sayar da ita ne ta d’an zaro ido ganin bata da niyyar tahowa yasa shi cewa shi ya shiga ciki tay ta tsayuwa har azo a tafi da ita aikuwa tun kan ya rufe baki tabi shi da sauri tana yi tana waiwayen bayanta ita duk sai ta tsorata da gidan ma da yayi Maganar, Wani jigunannan Parlor suka shiga mai d’auke da Sofas set biyu ya tsaru iya tsaruwa ya bi wani Corridor dake gefe Fatuu na bin shi a baya sai waige waige take har suka iso bakin wata babbar kopa ya tura suka shiga Fatuu tay tsaye tana bin d’akin da kallo wanda Bedroom ne amman mai girman gaske daga can gado yake da bedside drawers d’in shi sannan daga gaban shi inda table d’in gaban gado yake set d’in leather Sofas ne ta yadda sun sa gadon a gaba daga tsakiyar su lallausan carpet ne a bangon da suke facing k’atuwar plasma TV ce manne sai can gefe kuma dressing mirror yake daga d’an gaban shi wata budaddar kopa ce ta corridor a gabanta kuma akwae k’atuwar window a wurin kayan motsa jiki ne sai dae basu da yawa harda irin mai sa gudun nan wanda Fatuu ta hau sanyin Ac ta koina, suna shiga taja ta tsaya har ya nufi ciki ya dakata ya juya ya kalleta ganin tayi tsaye ya nuna mata inda kujeru suke yace taje ta zauna bata motsa ba ta bishi da ido hakan yasa ya dawo d’an gabanta ya tsaya yana kallonta ta sadda kai can ta d’an d’ago ganin ya kafeta da ido yasa a marairaice tace “baka gaya man ina bane nan d’in da muka zo” d’an kauda idon shi yay tana ta kallon shi ya juyo yace bata yarda dashi bane da sauri tace “a’a kawai dae ina son sani ne” sigh yay yace “gidan Dad d’ina ne a G.r.a” kai ta d’aga har zai juya ta k’ara cewa “to mi muka zo yi bazamu koma gida ba?” Idon shi a Kanta yay d’an murmushin gefe yace “zaki ida abunda na hanaki ne kike fushi sai mu koma” d’an tura baki tay yace taje ta zauna ta shige shima ya wuce saida ya aje ledojin kan Carpet yace mata yana zuwa ya nufi Corridor d’in cikin d’akin tabi shi da kallo har ya shige kafin ta maido su tana k’are ma d’akin kallo ya dae tsaru sosae sam ba hayaniya ga katafaren gadon yasha farin bedsheet gwanin burgewa, sanye da milk jallabiya mai gajeran hannu ya fito ya nufi hanyar da suka shigo ya fita Fatuu dae tayi tsuru a saman kujera bai dad’e ba ya dawo hannun shi ruke da plates harda yar wuka da glass cups ya nufi wurin kujeru ya d’aura akan Carpet ya d’ago ya kalleta yace ta saukko ta taso tazo wurin ta zauna, da kan shi ya shiga fiddo abubuwan da ya siyo yana sawa a plate d’in harda take away d’in Fried rice da irin lemun da tace ma giya yana fiddo shi ya d’aga ido ya kalleta yana d’an murmushi ta tura baki ta kauda fuskarta, bayan ya gama yace ta ci ya d’auki wasu da ya rage a cikin leda yace mata yana zuwa ya nufi hanyar fita don kai ma security, bata fara ci ba har ya dawo ya zauna kan kujera yana kallonta yace taci mana tana d’an kikkafta ido tace to shi fa yace zai ci ta gama tana d’an yamutsa fuska tace wato ita acici ko in dae bazai ci ba itama ta k’oshi d’an murmushin gefen baki yay yana kallonta itama kallon shi take can ya tashi ya sauka kan Carpet d’in ya lankwasa kafafun shi saida taga ya fara ci sannan itama ta sa hannu tun dai bata saki jiki ba har ta saki suna ci suna kallon Tv sai gashi sun ci sosae harda k’arawa bayan sun gama yace in bata k’oshi ba ta k’ara tace itama ta k’oshi ya bud’e mata lemun ya tsiyaya mata yana d’an murmushi yace ta d’auka ta kai hannu ta d’auka ta d’an sha sai taji shi lafiya lau lemu ne yana murmushi yace saura ta k’ara gani tace giya ce tay d’an murmushi taci gaba da sha a hankali, wayarshi ce ta fara ringing ya mik’e ya nufi gaban dressing mirror ya d’auka da turanci yake magana bayan ya gama ya aje wayar ya juya ya nufi daga can gefen inda kayan Motsa jiki suke saman wani desk ya d’aukko laptop dake a sama ya dawo wurin kujerun ya zauna saman 3 seater ya aje laptop d’in a gabanshi bayan ya bud’eta ya fara operating nata Fatuu da itama ta koma saman one seater ta zauna tana kallon Tv bayan wani lokaci ta kalleshi ta kira sunan shi ya juyo ya kalleta tace ba yanzu zasu tafi bane gently yace ta d’an yi hak’uri ya k’arasa abu ana jiranshi ne tace to ta maida idon kan Tv can ta tuna da bata yi sallar isha’i ba da yake tayi wankan tsarki jiya zumud’in zuwa dinner ya hana ta tsaya tayi Sallar kallon shi tay tace tana son tayi salla ya d’ago ya nuna mata corridor d’in da ya shiga ya canzo kaya yace in ta shiga akwae kopa mai kallonta anan toilet yake tace to ta mik’e, lokacin data k’arasa ta tura kopar tasha mamaki don tayi zaton toilet d’in zata gani amman sai taga laundry room irin nashi na gidan Hajiya amman wannan yafi kayatuwa don aciki press d’in kayan shi take wadda ta glass ce kana kallon kan ka a jiki ga kuma wall cabinet a ciki su kayan wanka suke sosae wurin ya burgeta don ita bata san yana dashi a can d’in ba tunda ko bedroom d’in shi bata ta6a shiga ba, kopar da ta gani a cikin wurin tay tunanin nan ne toilet d’in ta nufeta ta tura aikuwa toilet d’in ne wanda ya amsa sunan toilet, bayan tayo Alwalar ta fito tsaye tay a bakin corridor d’in tana tunanin to da mima zatay sallar d’an gyalen data nad’a iya kafad’ar ta yake tana tsayen ya d’ago ya kalleta ya tambaye ta da matsala ne tace eh ba hijab yace ina jallabiyar ta tace ta baro ta a Mota mik’ewa yay yace yana zuwa bada jimawa ba ya dawo ya kawo mata tay mashi godiya ya d’aukko mata prayer mat ta tambayi inda gabas take ya nuna mata kafin ya koma yaci gaba da aikin shi, bayan ta gama sallar komawa tay wurin kujerun ta zauna kan 2 seater taci gaba da kallon a hankali kuma ta fara gyangyad’i tun tana yi tana bud’e ido har takai ta d’an kwanta ta fara baccin sosae can ya d’ago ya ganta tana baccin don bai ma san tayi ba juyawa yay yaci gaba da aikin da yake bayan wani lokaci Fatun ta bud’e ido da sauri kuma ta tashi zaune tana d’an murza ido tace “Ya Haisam yakamata mu tafi dare yayi sosae” kallon agogon jikin laptop d’in yayi yaga sha biyu saura saukko da d’ayar kafar shi yay ya mik’e yace suje itama ta mik’e ganin bai kashe laptop d’in ba yasa tayi mashi magana yace zai dawo ne in ya kai ta ta d’aga kai ta d’auki purse d’inta ta fita daga wurin kujerun shi kuma ya nufi gaban dressing mirror ya d’aukko cay key yana nufo ta kwatsam aka d’auke wuta aikuwa Fatuu ta saki k’ara tana fad’in “Wayyo ya Haisam kana ina don Allah ka kunna haske wllh ban ganin komae” shi Maganar tata ma dariya ta bashi sai kace wata yar k’aramar yarinya wai tsoron duhu ya lura da ita abunda bai kai ya kawo ba shi take ji ma tsoro jin baiyi magana ba yasa ta k’ara kware murya tana fad’in ta bani don Allah yayi magana abun ma shi nishad’i ya saka shi sai kawae yay shiru aikuwa ta k’ara rud’ewa dama ta tsorata da gidan tun farko cigaba da fad’in yana ina tay tana lalube duk ta firgice a haka har ta k’araso gabanshi tana kai hannu ta ta6a chest d’in shi ga k’amshin jikinshi kuma aikuwa ta fad’a mashi ta fashe da matsanancin kuka tana fad’in shine yana jinta zai yi banza da ita sosae ta k’ank’ame shi jikinta sai kerma yake sai kuma duk bai ji dad’i ba baiyi zaton ta tsorata haka sosae ba slowly ya kai hannu bayanta alamar rarrashi ya shiga furta mata “am sorry” lamo tay a hankali rawar da jikinta keyi ta fara raguwa cikin muryar kuka tace ya kunna haske su tafi ya furta Ok bari ya duba wayan bai san takamaimai inda take ba aikuwa ta k’ara rikeshi gam ganin haka yasa ya fara moving da ita a kokarin shi na su koma inda kujerun suke don yafi tunanin anan ya aje wayar bayan da aka kira shi cikin rashin sani ashe ta bayan kujerun suka bi har baisan sun zo bakin gado ba kawae sai jin su sukae sun fad’a saman shi rikica gaba d’aya hankalin su ya tashi don abu ne da basu tsammaci faruwar shi ba tsit kake ji kowa na maida numfashi ba kamar Fatuu da yake a samanta sun dan d’auki lokaci a haka kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi tamkar anyi glueing nasu da k’yar Fatuu cikin rawar murya ta ambaci sunan shi shiru bai amsa ba ta kai hannu da niyyar ta d’aga shi hannun ya nutse acikin sumar kanshi wani irin shock yaji a jikin shi da sauri Fatuu ta janye hannun tana breathing rapidly wannan d’agawa da saukar da chest d’inta keyi ya fara turning nashi on slowly ya d’ago face d’in shi ta yadda numfashin su ke had’uwa gaba d’aya kasala ta lullube Fatuu da k’yar ta iya k’ara bud’e baki tace “Ya Haisam ka……” Cak ta tsaya tana zare ido jin abunda bata ta6a zato ba lips d’in Haisam a saman nata a rud’e ta fara kokarin k’ara yi mashi magana kawae sai jin tongue d’in shi tay cikin bakinta bata ankare ba sai ji tay ya fara mata hot French kiss lokaci guda Fatuu ta rud’e ta kidi’me ta gigice, gaba d’aya Haisam ya gama gigita yar Mutane har bata san ta zura hannunta acikin sumar shi ba tana squeezing nata hakan da take ya k’ara turning nashi completely on hot romances ya shiga yi mata tamkar yana operating laptop d’in shi to Fatuu dae ba k’arfe bace cikakkar mace ce da jini ke yawo a jikinta tana cin mai kyau ta sha kuma mai kyau dole kota k’i ko taso jikinta na buk’atar abunda ke faruwa da ita hakan yasa kwata kwata ta kasa hana shi abun har ya kai wani mataki da ita kanta bata ankare da an kai ba ba abunda take sai sakin numfashi da k’arfi had’i da nannauyar ajiyar zuciya a wata kalar duniya take jin ta da babu gwaggo babu Kawu Amadu ba Hajiyar sanata ba ba….., Fatuu bata tashi dawowa hayyacin ta ba saida taji wani rikitaccen Al’amari dake shirin faruwa da ita wanda sam bata san an kawo nan ba aikuwa a gigice ta kai hannu ta kama damtsen shi tana girgiza mashi kai tana fad’in ya bari ba kyau abunda suke Allah zai kama su kada ya cutar da ita, da alama Haisam fa ya rasa control kokarin penetrating d’in ta yake ta k’arfi ganin haka yasa Fatuu ta fara k’ok’arin kwatar kanta ta hanyar kai mashi bugu da yakushi amman sam kamar bai jinta ma abunda yasa gaba kawai yake as if his life depends on it cikin k’araji Fatuu ke fad’in “Don Allah Ya Haisam na rok’e ka in kana k’aunar iyayen ka kana k’aunar Hajiyar Sanata ka k’yale ni kada ka cutar dani ni fa kanwarka ce……” bata k’arasa Maganar ba ta saki wata irin razanannniyar k’ara koma in ce kururuwa……….. innalillahi Wa’inna ilaihir raji’un! Jama’a miya hwaru ne😳..

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button