Hausa novels

Hajar Page 2 Complete Hausa Novel

💛 HAJAR💛

Hajar Hausa Novel Document txt

By Feenerh_feeche

 

{2…}

Fitowa yayi daga motar yana hangen mai mashin ɗin da ya shigo masa har ya bulale tsukun layin da hayaƙi ya fece, cikakken gashin kansa ya shafa yana ƙanƙance ido sai kuma ya kalli motar tasa da take cikin kwatami tsamo-tsamo, gefenta ya karkace wajen driver ne kawai bai shiga kwatamin ba, tsirarun mutanen da akai abun a kan idansu suka taso, Hajar da zuciyarta take tafasa tana kallon uniform ɗinta da bazasu taɓa tafiyuwa a wajenta a haka ba, wani ƙululu ne ya tsaya mata, what the heck isn’t he going to apologise, a hankali ta taka tana tsantsamin kanta ta isa gabansa inda yake ƙoƙarin buɗe motar zai shiga, ya kai hannu kenan zai buɗe ƙofar motar ta riƙe handle ɗin tace “malam ba kaga abinda kayi bane??”, da wani irin salo ta juya fararen idonta ta nuna masa uniform ɗin jikinta dasu, kallo ɗaya tak yayi mata yace “ohk sorry it was not my fault”, up and down ta kallesa ta tsugunna ta kwarfo ruwan dattin a duka hannayenta ta shaɓune masa a farar Tshirt ɗin jikinsa, ta kama hanya fagam-fagam zata bar wajen, wani mutum ne ya kalleta yace “amma wallahi ke dai baki da kirki..”, ta juya ta kallesa sai taga da ɗan girmansa zai iya kaiwa sa’an babanta hakan yasa ta mayar da asalin abin tayi niyyar fada tace “oh shi bakuga rashin kirkinsa da ya feshe ni da kwatami ba”, mutumin yace “amma ai ba sa’an ki bane kuma ya baki hakuri yarinya”, cike da tsiwa Hajar tace “banga zan iya hakura ba gaskiya” tayi gaba abunta, wani ne ya taso yace “au baka ganeta ba aii ƴar gidan gini ce zata iya aikata abinda yafi haka ma”. kawai gaban Tshirt ɗin jikinsa yabi da kallo lokacin da kunnensa yaji (au baka ganeta ba, ai ƴar gidan gini ce zata aikata abinda yafi haka ma). Hajar na shiga gida tin daga soro ta rushe da kuka, ita duk wannan tsiwar ta ta kuka baya mata wuya, daga zarar zuciyarta ta ɓaci tom sai tayi kuka take jin daɗi, da Sa’adatu ta fara cin karo hannunta riƙe da bokitin ruwa da kwandon soso da sabulu zata shiga bayi, Sa’adatu ta daka wani uban tsaki tace “da murya sai kace ta gardawa an cikawa mutane gidan uba”, Hajar ta sharce hawayen idonta tace “saiki nuna wanda ya diro daga sama jahila” ta ƙarasa shiga ciki, Sa’adatu ta mulmulo wata ashariya tace “ni yarinyar nan zata kira jahila” ta dire bokitin da kwandon ta biyota da gudu, kafin ma ta cimmata harta shige ɗakin umma, Mu’azzam da yake bakin ƙofa ya kalleta sama da ƙasa yace “ina makarantar??”, Hajar tace “ba ina tsaye a bakin titi ina jiran napep ba wani mai mota ya fesa min cakwalkwali”, ta cigaba da kukanta, Mu’azzam yace “A’a kinga malama ki rufewa mutane baki, ki canza wasu kayan ki tafi makaranta”, Hajar na shessheƙar Kuka tace “toh aii banida wasu uniform ɗin kuma ance kowa da kayan makaranta za ai masa online registration”, umma tace “Mu’azzam dan Allah daure ka rakata makarantar nan tinda kace yau bazaka aiki ba, ke kuma maza kije ki ɗauraye jikinki kizo ki canza kaya”, Mu’azzam yace “karki ɓatamin lokaci ina ƙofar gida”, ya fita daga ɗakin, Hajar ta wuce bakin rariya ta cire hijab ɗin jikinta ta ɗebi ruwa a buta ta fara ɗauraye inda cakwalkwali ya ɓata ta, cikin sanɗa Sa’adatu ta taho ta cakumo wuyanta tace “yanzu sai ki gayamin wace ce jahilar??”, Hajar tace “dalla malama sake ni..”, Sa’adatu tace “anƙi a sake kin, me zaki iya??”, Maama ta yaye labule ta leƙo tace “naɗi ƴar iska, ki canza mata kamanni”, Sa’adatu ta sake maƙure wuyan Hajar har saida idonta suka firfito amma baki nan bai mutu ba cewa take “Allah ya isa, muguwa azzaluma mai bleeching”, mai bleeching ɗin nan shi yafi ƙonawa Sa’adatu rai don haka ta kamata da kokawa, Hajar da take ganin bazata ɓata lokacinta a nan wajen ba ta daddage ta danna mata wani mugun cizo a damtse, Sa’adatu da zafin cizo ya ratsa mata kwakwalwa da sauri ta saketa ta lailayo ashar tana kallon damtsenta da haƙoran Hajar suka fito ainun, cizon ya shigeta sosai domin ƙiris ya rage wajen bai fashe ba domin kuwa jeka huda yayi, Hajar ta manna aguje ta shige ɗakin umma tana waiwayen Sa’adatu.

 

★Sanye take cikin fararen kaya riga da wando sai wani ɗan ƙaramin hijab V-shape, ta ɗora kimono a saman kayan, hannunta riƙe da mug mai ɗauke da coffee, a hankali take tafiya har tazo ƙofar office ɗin tayi knocking a hankali, daga ciki akace “come in..”, ta murɗa handle ta shiga ciki da ƴar sallama, secretary ta amsa tace “welcome Nurse Ruqayyah..”, tace “yawwa Halima Doctor bai ƙaraso ba ne??”, Halima tace “yes i think he is on his way”, Ruqayyah tace “Ohk, bari na jirasa aciki”, Halima tace “ohk then”, Ruqayyah ta shiga babban office ɗin da ya gama ƙawatuwa, ga wani ƙamshi da sanyin Ac da yake tashi a cikinsa, Mug ɗin hannunta ta ajiye kan table ta ɗauki hoton da yake dirke a gefen table ɗin wanda ya haska fuskar wani mutum wanda yake sanye da lab coat ya rataya stethoscope a wuyansa, hannayensa zube a pocket ga kuma wani murmushi da yake shimfiɗe a fuskarsa, Ruqayyah ta zauna kan chair still looking at the picture, 20mins passed amma bata gaji da kallon picturen ba, ƙofa aka murɗa mutumin da yake cikin picturen ne ya shigo, hannunsa riƙe da briefcase, a hankali ya mayar da ƙofar ya ƙaraso ciki yana kallon Ruqayyah da take riƙe da hotonsa, briefcase ɗin ya ajiye akan table sannan ya cire lab coat din jikinsa ya ratayeta ajikin kujerar zamansa kana ya zauna, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace “good morning babe.. tinda yau ba za a gaishen ba”, ta kallesa a fakaice ta zumɓuro baki tace “Dr yau mesa ka makara?, kuma nasan kanada surgery scheduled yau at 12pm”, with a soft smile on his face yace “really akan surgery nan kika damu ko kuma mai yin surgeryn?”, wani irin cuno baki tayi tace “of course not i care for the surgery not the surgeon”, murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa yayi yace “My coffee ko yau rowa za ai min?”, ta mayar da hoton mazauninsa ta ɗauki Mug ɗin da ta ajiye ta miƙa masa tace “Here”, ya amsa yace “thanks”, one sip yayi ya ajiye yace “ya huce aii”, tace “tinda ka makara yau mai sanyi zaka sha, now tell me, mene ya makarar da kai?”, yace “ohh Mami ce ta turani na amso mata wani saƙo shine nabi wrong way, har car na ya samu matsala, you know yesterday anyi ruwa toh wani ruwa na faɗa a street ɗin, i wasted my time there looking for a solution”, tace “ohk, Allah ya kiyaye”, yace “Ameen, har yanzun ma coffee mai sanyi zan sha?”, juya idanunta tayi ta miƙe ta duba wrist watch ɗinta tace “Byee, zan shiga surgery da Doctor Mansoor, see you later after the surgery..” ta fita ta rufe ƙofa. wasa ya farayi da yatsun hannunsa yana juyi a kan kujera idonsa a lumshe yana tunanin the girl he encounter with this morning, her face look so innocent but she’s stubborn, ƴar gidan gini………✍️

Download Hajar Hausa Novel Document By Nafeesa Yusuf Nagoda 

Click the below green button to read the novel online

 READ HAJAR PAGE 3 COMPLETE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button