Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 59 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

E59

“Tun da baka son mu zauna a kusa da kai, ku tashi mu je wurin ƴan uwan mu mata, su yi firar tare da mu,” haris na faɗin hakan kowannan su ya miƙe su ka nufi Dining carpet ɗin su, inda su Angel su ke zazzaune kowannan su Ya samu wuri ya zauna, cikin sa’a Naufal ya zuƙunna bayan Hannah da ke fuskantar Angel, da ya ke dogo ne shima tubar kalla, gaba ɗaya ya kare ma Danish Fuskar Angel, baya iya ganinta da kyau, takaicin duniya ya ishe shi, sai ya mayar da kallon shi ga Gabriel, su ka haɗa ido da juna, Jira ya ke yaga in gabriel zai miƙe da niyar yaje wurin su, kamar Gabriel yasan me ya ke ayyanawa acikin zuciyar shi, da gangan ya miƙe zai nufi wurinsu, a hanzarce Danish ya miƙe, komawa Gabriel yai ya zauna gefen gadon shi, sai gashi shima Danish ɗin ya koma nashi gadon ya zauna, Ikon Allah.

Su biyu ne basu je wurin ƴan uwan nasu da ke yin fira ba, hatta Majnun yana a tsakankanin Deeja da Rubina, Ya natsu kamar mutumin arziƙi, duk wanda yai magana acikinsu haka zai ƙurawa la66ansa ido har sai ya gama magana, wani lokacin sai ya tintsire da dariya, ko ba abun dariya aka faɗi ba.

“Tun da yanzu mun ƙara yawa, A faɗa mana waya fi kyau a cikin mu”? Acewar Yasmin, hibbe tace”wa zai faɗi? Sai dai ko Angel,’ girgiza kai angel tai
” a’a, a samu wanda yafi kowa hankali a cikin mu ya faɗa mana wanda yafi kyau,’ ta yi maganar tana nuna musu majnun da idonta, dariya su ka saki gaba ɗayan su, Deeja tace da shi”Chinonso faɗa mana waya fi kowa kyau a cikin mu, yau zamu tabbatar da idan kana da cikakken hankali”

murmushi suka ga ya saki yana murmura idanuwanshi, hada ƙoƙarin miƙewa tsaye yana kallon fuskokin su, tsawon lokaci sun kasa kunne suna sauraron shi, yadda kasan me nazarin wani abu, har wani leƙa fuskarsu yake yi, a ƙarshe yace”Haris” shiru su ka yi, haris ko sai tiƙar dariya yake yi, itama Deeja murmushi ta saki,

Jamima tace”Ƙarya kake yi, ba haris bane yafi kyau, ba ka ga shi baƙi bane,”

Harara chinonso ya watsa mata, tare da ruƙe qugunshi, ya turo ciki gaba yana faɗin”ke ne kike ƙarya, harisu ba baƙi bane, Fari ne fat,” waro ido su kai gaba ɗayan su suna kallon shi, Angel tace”Anya kuwa Majnun Ƙwaƙwalwarka tana aiki dai dai? Haris ɗin ne yafi kowa kyau kuma fari ne” jinjina mata kai yai fuskarshi a ɗaure yace”Eh mana, yafi kowa haske aciki ku, shi ne yafi kowa kyau” Mubeen na murmishi yace”anya haris ba wani abu ka yi mishi ba? Ko dai ka yi mishi ƙyafcen ido ne”? Haris na dariya ya ce”Ka tambaye shi mana sai ka ji idan ni ne nasa shi ya faɗi hakan”

Miƙewa mubeen yai tare da komawa gefen chinonso da ke a tsaye, ya duƙo yadda tsawon su zai dai dai ta”faɗa min wata irin barazana haris yai maka”? Ta6e baki majnun yai, ni bai min komai ba, gaskiya na faɗi yafi kowa kyau acikin ku, shine fari” fuskarshi a ɗaure yai maganar babu alamun wasa don shi har ga Allah gaskiyar shi ya ke gaya musu.

“Yau naga ikon Allah, wai dole sai ya ƙaryata abunda ya faɗi? Nifa na sani dama, haris yafi kowa kyau a cikin ku”! acewar Deeja, haris ya kar6e da cewa faɗa mu su dai, Ni ɗin kyakkyawa ne, da alama kishi su ke yi dani, ‘

ruƙo hannun Majnun mubeen yai tare da jan shi zuwa gaban Danish da ke zaune gefen gadonsa, Yace”yanzu faɗa min tsakanin haris da Danish wanene fari”? Jin muryarsu yasa Danish kawar da idon shi daga kan fuskar Angel, ya dawo da dubanshi akan fuskar chinonso daya ƙura mishi ido, har wani kashe ido ɗaya yake yi.

“Idan har ya kasa banbance waye fari acikin su, to kuwa dole mu zubda chinonsu Cikin Kwandon shara, don banga amfanin shi acikin mu ba, abincin da yake ci ma ya tashi abanza,” parveen ce tai maganar, kowannan su ya saki murmushi, Angel tace”da alama ƙarya ta ƙare, Ya tasa Danish gaba sai kallon shi ya ke yi, yaƙi magana”

“Kai muke jira” acewar mubeen, girgiza kai chinonsu yai fuskarshi a hargitsa ya kalli mubeen'”to..ae na kasa ganewa, shima haris ɗin ya dawo gefen shi ya zauna, sai in banbance” Miƙewa haris yai tare da komawa gefen Danish ya zauna, Suka tasa chinonso gaba Akan saiya gano musu wanene fari acikin su, shifa bilhaƙƙi Haris fari ne, Ya dai ce musu Danish yafi kyau, matsalar shi ɗaya Baƙi ne wulik, Shiyasa Haris yafi shi kyau, wannan maganar ba ƙaramar dariya ta basu ba, Ga dukkan alamu bayan ta6in hankali da yake dashi Chinonso yana fama da matsalar Gani, yau sun tabbatar da hakan, tun da gashi ya tabbatar musu da cewa Danish yafi kyau, sai dai baƙi ne, har tambayarshi su ka yi shi fa wani kala ne, yace musu shima baƙi ne

Mutumin da ya ke albino, hasken ma ya wuce na lafiya, Amma yana kiran kan shi da baƙi, kusan mutun uku fararen Cikin su, su ka tambaye shi ya faɗa musu wani kala ne su, yace musu duk baƙaƙe ne. Ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba a ranar, Lokacin da dare yai, Kowannansu Ya canza kayan shi zuwa tsoffinsu, Wanda suka maida na bacci, Kafin suka haura saman gadajensu suka kakkwanta.

Gabriel ya kasa runtsawa Yana zaune tsakiyar gadon shi, Sarai Angel ta lura dashi, hakan yasa itama taƙi kwantawa tayi baccin, Haka zalika, Danishi yaƙi runtse idanuwanshi, Ga bacci yana ji amma yaƙi bari ya ɗauke shi, Saukowa tai daga saman gadonta, zumbur Danish Ya mike zauna, tare da kallon ta yace

“Angel where’re u going, ba zaki bacci ba” yatsina fuska ta ɗanyi tare da kallon shi” Addu’a nake so inyi maku kafin in kwanta….” tunkan ta ƙarasa maganar taga ya sauko daga saman gadon shi, Ya ruƙo hannunta acikin nashi tare da cewa”Nima zan ta ya ki, mu yi musu addu’ar a tare” dariyar yaƙe ta sakar mashi”kai da baka iya ba, taya zaka iya taya ni mu yi musu addu’ar?

“Ni dai muje,” duk yadda taso ta yi mashi wayau don ya koma ya kwanta ita kuma ta samu damar zantawa da Gabriel Ya hana hakan faruwa, Atare su ka bi gadajen su Hannu tana karanta musu addu’o’i tana tottofa musu saman bargunan su, hatta sarah da ke a kwance ƙasa sai da ta zuƙunna ta yi mata addu’a, kafin ta miƙe bayan ta kammala, ta tsaya a Tsaye tana satar kallon Gabriel da ya hana idon shi bacci tasan duk don saboda ita ne, Ganin tana kallon shi yasa Danish damƙar hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta, fuskarshi a ɗaure yace”ki kwanta ki yi bacci,” ba tare da ta yi mishi musu ba, ta hau saman mattress ɗin ta kwanta, tare da ɗaura kanta saman pillow, ‘ ta yi tsammanin zai haura nashi gadon ya kwanta amma sai taga ya zauna gefen gadonta, Ya tsareta da waɗannan kyawawan idanuwanshi nashi

“Why danish? What’s going on? Why don’t you go to bed? You’re bothering me.” A hasale tai maganar tana jifar shi da harara, cikin sanyin murya yace”idan kina so in yi bacci to ki fara yi, if not sai dai mu kwana idon mu biyu,” muryarta a takure tace”hakan ma bazata faru ba,” runtse idanuwanta ta yi, zuciyarta nata saƙa mata yarda zata yi mashi wayau, yayin da shi kuma Man ɗin Ya jingina bayanshi da bango idonshi akan Gabriel, Dake zaune tsakiyar bed nasa.

A hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, ta saci kallon fuskar Danish, miƙewa tayi zaune, Jin motsinta yasa shi kallon ta

Yamutsa fuska ta ɗanyi tare da cewa”Zan shiga toilet ne,” ruƙo hannunta yai acikin nashi”muje in raka ki” fusge hannunta tai fuskarta a ɗaure tace”Banaso, Ka zauna anan inje in dawo,” bai damu ba, tun da yasan ita kaɗai zata shiga, zai zauna ne ya tsare Gabriel kada ya motsa, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi sashen toilet ɗinsu, tana jiyo muryar Shi yana bata umarnin kada ta daɗe acikin toilet ɗin, idan ba haka ba zai biyo bayanta.

ta amsa mashi da toh, tana shiga ƙopar sashen toilet ɗin, ta juyo tana leƙen Gabriel, Dama abunda ya kai ta kenan, tun kafin ta shiga ran shi ya bashi cewar ba wani abu zatai acikin toilet ɗin ba, za ta je ne don ta samu damar yin magana dashi, Satar kallon Danish yai, ganin ya ɗan lumshe idanuwanshi yasa shi yin saurin kallon ƙopar shiga sashen toilet ɗin, cikin sa’a ya hango angel tana ɗaga mashi hannu, A hankali ya janyo pillow ɗinsa da ya jingina bayanshi da shi, Ya rungume shi a ƙirjinshi, Ya sanya hannu yana ta6a zip ɗin jikin shi, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta fahimci abinda ya ke son nuna mata, buɗe ido Danish yai tare da saukowa daga saman gadon shi, Ya nufi sashen toilet ɗin, da sauri Gabriel yai mata alamar gashi nan zuwa, kamar walkiya ta buɗe toilet ta shige, Yana shigowa wurin, ya soma kiran sunanta”Angel! Angel!” buɗe ƙopar tai tare da fitowa tana yarfa hannunta data wanko shi da ruwa, Kallon shi tai aranta tace”Jarababbe kawai” a fili kuma tace”lafiya”?

“Na jira ne baki fito ba, shine nazo in duba ki” harara ta wurga mashi, kafin taja hannun shi, suka koma ɗakin, tace mashi”ka hau gadon ka, ka kwanta nima in kwanta a nawa, in yaso sai mu fuskanci juna” Ya amsa mata da toh, bayan kowannan su ya haura saman gadonshi, suka ci gaba da kallon juna, tun yana ganinta biji biji, har ya kai ga rufe eyes ɗinshi, tsawon mintuna ta fahimci cewa bacci ne yai awon gaba dashi.

Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta miƙe ta ɗauki pillow ɗinta, ta zuge zip ɗin ta curo ƴar takardar da Gabriel ya ajiye mata, ta buɗe ta cike da fargabar kada Ya farka, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi tsakiyar ɗakin nasu tana karanta wasiƙar, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, wani irin ruɗani ne ya bayyana akan fuskarta, Takasa yarda da abunda Gabriel ya rubuta mata, Shin dagaske ne ya haura tagar nan ya shiga cikin prison ba tare da wani abu ya same shi ba? To ya akai ita ta kasa shiga? Can kuma ta koma tunanin yarinyar da ya ce mata ya gani tana neman taimakon shi, Anya kuwa Gabriel ba ƙarya ya ke faɗa mata ba? Sai dai kuma abunda zai sa ta iya yarda da maganar da ya rubuta mata, na farko bai yi kama da maƙaryaci ba, sa’annan idan har dagaske ƙarya yake yi mata to taya akai yasan da Tagar da aka cire glass ɗinta, nannaɗe takardar tayi tare da ɗagowa ta kalli shimfiɗar Gabriel, Har yanzu bai kwanta ba idanuwanshi na akanta, sai da ta fara juyawa ta kalli Danish da ke bacci, taga bai motsa ba, kafin ta maida dubanta ga Gabriel, Saukowa yai daga saman gadon shi ya tunkareta, hannunta ya ruƙo acikin nashi, Yaja ta suka shiga sashen toilet ɗin su, saboda su samu damar tattaunawa da juna ba tare da Danish Ya farka ba.

Ba acikin toilet su ka shiga ba, acikin sashen suka tsaya, muryarta da alamun mamaki tace”Abun da na karanta acikin wasiƙar nan taka dagaske ne? Jinjina mata kai yai”tabbas dagaske ne angel, naso tun time dana haura tagar na dawo ciki in sanar da ke amma Danish ya hanani yin hakan, Nasan ke kaɗai ce zaki iya taimaka min wurin nemo ƴar uwata tun da kema kina nema taki ƴar uwar, kuma naji awurin ƴan uwanki cewa, kina da burin fita daga Cikin kurkukun nan, shiyasa na ƙara samin ƙwarin gwiwar tunkarar ki in faɗa maki,’ Tun da ya soma magana Angel ta ke binshi da kallo mai tattare da tsantsar mamaki da al’ajabi, Shi dai gashi ba musulmi ba, amma wani iko na Allah, ya samu damar shiga prison ba tare daya fuskanci irin matsalar daga fuskanta ba, a lokacin da ta dira tagar, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease ta samu wani mai ra’ayin son guduwa daga prison, idan su ka haɗa hannu dashi zasu iya sama ma kansu mafita.

“Angel kin yi shiru bai kamata muna 6ata lokaci ba, wannan ce damar da mu ke da ita, ta taimakon yarinyar nan, ita ka ɗai sai garari take yi acikin prison” fuskarshi da alamun damuwa yai mata maganar.

“Gabriel, ina kokwanto fa, zai yi wuya ace mutunce ita, may be barazana aka yi maka da ita don a tsorata ka, Nima time dana fita an tsoratar dani ta hanyar nuna min daddyna wasu haluttu munana suna cin naman jikin shi, aranar nasha wahala, ba don Allah yasa Danish yaje ya ɗauko ni ba, da shikenan tawa ta ƙare” girgiza mata kai Gabriel yai”Bana tunanin cewa anyi min barazana da itane, mutunce ita Angel I saw her from the top of the third floor. She was running, looking for help. fara ce kamar ke, tana da yawan sumar kai kalar naki, itama nata, Nannaɗaɗɗe ne harma yaso yafi naki yawa da nannaɗewa…….’

Tun da ya suffanta mata matashiyar yarinyar, Hankalinta yai matuƙar tashi, Ta zazzaro idanuwanta waje, La66anta na kerma ta furta sunan”BATOOL” domin kuwa a bayanin da ya yi mata kaf irin suffar batul ne,

“Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Wlh inaji araina ƴar uwatace batul,” tuni hawaye sun wanke mata fuskarta, jikinta ya kama kerma.

“Gabriel why, ba ka taimake ta ba! Ae da ka sani ka taho da ita, Batul ce fa ƴar uwar mu” Shima aruɗe yace mata”Angel ni bansan cewa ƴar uwar ku bace, tun da bansan ta ba, naso na taimake ta, sai dai tsoro ya hana in ƙarasa wurinta, cos stairs ɗin dake kewaye da ground floor ɗin naga suna motsi kamar masu rai, that’s the reason why na rikice, cos abunda ban saba gani ba ne…..” shessheƙar kukanta ne ya katse mashi maganar tashi, ya zuba mata ido yana kallonta, sassauta muryarsa ya ɗanyi”Ki daina kuka, Danish zai iya jin sautin kukan ki ya farka, Yakamata mu tattauna akan abunda ya dace mu yi,” cikin matsananciyar damuwa tace”ae wlh Saina je na ɗauko ta, koda zan rasa raina ne, komai zai faru sai dai ya faru, amma bazan runtsa acikin daren nan ba, dole naje!!!’

tana ƙarasa maganar ta nufi toilet ɗin da tagar take da sauri Gabriel yabi bayanta yana fadin”ki tsaya Angel, kada mu yi gaggawa, yanzu dare ne, why ba zamu bari sai gobe ba”? Ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace”In bari sai gobe, salon sai wani abu ya cutar da ita, Ina ji araina Allah ne ya taimaki batul ta gudu daga wurin su, shiyasa ta ke neman hanyar da zata dawo cikin mu, wannan munafukin ginin bazai bari ta iya gane komai ba, wahala zata sha ƙarshe ma ta rasa ranta,’

Ba ƙaramin daɗi Gabriel yaji aranshi ba, dama abunda yake so kenan, Su je atare da ita su nemo ƴan uwansu, dama koda yace mata kada su yi gaggawar yin hakan ya faɗi ne kawai ba don yana nufin hakan ba.

“Amma angel kina ganin zamu iya shiga lafiya lou? Na fahimci cewa ginin yana da rikitarwa, ga ban tsoro.

“zan roƙi Allah ya kare ni daga sharrinsu, in sha Allah zamu je mu dawo lafiya ba tare da wani abu ya same mu ba” da ƙwarin gwiwa ta bashi amsa da alama ta manta abunda ya faru da ita, saboda amakance take burinta kawai taje ta nemo batul,.

“Amma Baki tunanin Danish zai iya hana mu? Suna tafiya suna magana har ta isa bakin tagar, ta bashi amsa da cewa”Shi da yake bacci, koda ace ya farka, bai isa ya hanamu ba, Akan batul ba abunda bazan Iya yi ba” tana magana tana jan majina.

Ganin tsayinta bai kai wa yasa Gabriel matsawa bakin tagar, tun da yana da tsayi, Ya soma ƙoƙarin cire glass ɗin.

“Idan muka ga sister ɗinki, Nima zaki taimaka min in gano ƴar uwarta Gabriella, ” ta amsa mashi da eh,” ajiyar zuciya ya sauke, yayin da yake cigaba da ƙoƙarin cire glass ɗin, Lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wani irin mugun bugu, nan take ranta ya bata cewar, Danish Ya iso inda suke, Kafin tayi yunƙuri Juyawa, Muryarshi ta ratsa kunnuwansu

“Bazan ta6a bari ku haura tagar nan ba! ” da sauri Gabriel ya zame hannun shi daga saman glass ɗin, kusan atare suka juya baya suna kallon shi, Ya ɗaure fuskarshi sosai, tare da goya hannayen shi saman ƙirjin shi, mamaki ne akan fuskar Gabriel, Taya akai ya farka har yazo inda suke yaji abunda suke Shirin yi?

Anya kuwa wannan cikakken mutun ne? Muryar angel tamkar zata fashe da kuka tace”wlh Danish bazan saurare ka ba, dole nabi shi mu haura tagar nan, da kanshi ya faɗamin cewa ya bi ta cikinta jiya, har ya ga wata yarinya tana gudu a hawa na uku, tana neman taimakon shi, kuma a yadda ya suffanta min ita, sak batul ce”

matsawa tai kusa dashi, ta sassauta muryarta”pls Danish, ka bamu haɗin kai, muje mu ɗauko batool, kana da damar da zaka iya taimaka mana dan Allah, Ni idan ma kayi min alƙawarin zaka je ka dauko min ita, sai in koma ɗaki in jira ka…..” cikin shessheƙar kuka ta ƙasa maganar, hawaye ta ko’ina saman fuskarta.

Idon Danish akan fuskar Gabriel, wani irin haushinsa yake ji, saboda shine silar komai, cikin kakkausar murya yace”Ba gaskiya ya fada maki ba, yarinyar daya gani ba batul bace, cos babu yarda za’ae batul ta iya fitowa daga inda aka killace ta, shin ko kin manta ranar da kika dira window din abunda ya faru dake? Let me remind u, Kin ga daddynki, alhalin bashi bane, idanuwanki ne suke nuna maki hakan, that mean shima Gabriel abunda idon shi su ka gane mashi ba gaskiya bane……..” tunkan Danish ya rufe bakinsa gabriel yace”Dama na lura da kai tuntuni kaƙi bani dama in yi magana da Angel, saboda kai ɗin munafuki ne, baka son gaskiya, shiyasa zaka ƙaryata abunda idanuwana suka nuna min, Angel karki ce zaki yarda da kalamansa, kada hakan yasa kice kin fasa bina mu shiga cikin kurkukun, Ki tuna halin da ƴar uwarki take aciki, zata iya rasa ranta…..

Gaba daya sun rikita mata tunaninta, kowa yana ƙoƙarin jan ra’ayinta, ta rasa wa zata bi acikin su, domin kuwa sun raba hankalinta gida biyu, zuciyarta na raya mata cewar tabi Danish su koma ɗaki, saboda akwai ƙamshin gaskiya a maganarshi, zai iya yiwuwa ba batul bace Gabriel ya gani, anyi amfani da matashiyar ne don a tsoratar da shi, kamar yarda itama a ka yi mata amfani da daddynta, yayin da awani sashen na zuciyarta yana raya mata cewar, tabbas Gabriel baiyi mata ƙarya ma, Ƴar uwarsu ce ya gani, kada Tabi Danish azo asamu matsala idan ya kasance dagaske Ita dince, tana fargabar halin da zata shiga, ita kaɗai acikin prison, zaifa iya yiwuwa Danish Yasan gaskiya Gabriel yake faɗi, Tun da baison dama tana dira tagar shiyasa zai kafe akan cewa ƙarya ya ke yi mata.

Ta yi zurfi acikin tunaninta, taji an damƙi hannunta, da sauri ta kalli hannun wanda ya ruƙeta, Danish ne ke ƙoƙarin fusgarta don su koma ɗaki, rai a matuƙar 6ace, Gabriel Ya damƙi ɗayan hannun nata yana huci, Zuciyar kowannansu takai wuya, A shirye suke da su farmaki junansu.

“Ka sakar mata hannu tunkafin ranka ya 6aci!” Danish ne yai maganar fuskarshi a murtuke, tsoki Gabriel yaja

“bazan saki ba, saboda ba hannunka na ruƙe ba,”

“Bana so ka yi danasani, tun wuri ka ajiye makaman yaƙin ka, kazo mu koma ɗaki, mu sasanta kanmu, amma idan ka nace akan sai ka ƙwaci hannun Angel ta ƙarfi don kuje ku dirar tagar can, Zanyi maka abun da ba ka ta6a tunani ba” Gabriel na huci yace”kai duk abunda kaga dama, bazan ta6a sakin hannunta ba, saboda ba mallakin ka bane, ni ban ta6a ganin mutun mai ƙarfin hali irin naka ba, Yarinyar nan fa ba dangin ka ba ce, Zaman Prison ne ya haɗa ka da ita, we’re all prisoners babu wata alaƙa ta jini, don haka yadda ka ke taƙama da ita, nima haka nake taƙama da ita……..”

zaro eye balls ɗinsa yai jin abunda
Gabriel ke faɗa masa, maganar ta ƙona masa rai, wato har yana da bakin da zai ce Hannun Angel ba mallakinsa bane? To na wanene idan ba nashi ba? sannan yace bai da alaƙar komai da ita, me hakan ke nufi,? Shima yana da iko akanta kamar yadda yake dashi? Ta ya hakan zai yiwu! Girgiza kai ya somayi yana huci ya furta”Kada ka kuskura ka maimaita kalaman da ka yi min Ayanzu, Domin kuwa Angel tawace ni kaɗai, ba wani mahaluƙin da ya isa ya shiga tsakanina da ita….” yana ƙarasa maganar Ya fusgi hannun Angel, ta fashe musu da kuka saboda raɗadin da taji, An rasa wanda zai haƙura yabarma wani, shima Gabriel yaƙi sakin hannunta, suka dinga janta kamar wata ɗiyar roba, Har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata sai dai ba yadda zaiyi ya lallasheta, don bai jin zai iya haƙura yabar wa Gabriel ita donsu haura taga, duk a bunda ya ke yi yana yi don ita ne baison abunda zai cutar da ita, A ƙarshe da ta gaji ta fasa ƙara mai tsiwar gaske, Ta zame hannayenta daga cikin na kowannansu, tana kuka tace”ya isa haka! Ya isa, Ni ku ƙyale ni inji da abunda ke damuna, so ku ke ku kashe ni ne! ” cikin sanyin murya Danish yace”Am sorry angel, laifinsa ne, kizo mu koma ɗaki,” harara ta wurga mashi da idanuwanta wadanda suka rune zuwa ja,

“Ni banzan bika ba danish, dole inje in ɗauko batul ɗinmu, idan har kai bazaka iya zuwa ka ɗauko min ita ba, to ka ƙyale ni inbi Gabriel mu je” Muryarshi araunace yace”Angel ki fahince ni, ba gaskiya bane abunda ya gaya maki, bana so ne ku yi danasani,”

Harara Gabriel ya watsa mashi tare da cewa”idan har dagaske ƙarya na ke yi akan abunda na faɗa mata, to ka bari muje tare da ita mu duba, idan har bamu ganta ba, shi ne ka ke da damar da za ka iya ƙaryata ni,”

rai a6ace Danish ya nuna shi da yatsa

“Ka yi min shiru! Bana so na ƙara jin maganarka, wawa kawai, kaine silar komai, kuma bazan ƙyale ka ba,”

Gabriel ya daki ƙirjinshi da hannu tare da cewa nima bana so ka ƙyale ni, Ɗan rainin wayau, dama daga ganin fuskarka ba mutumin kirki bane, wama yasani ko ɗan leƙen asiri ne kai acikin mu…….”

Ɗaya daga Cikin abunda Danish ya tsani Ya ji an faɗa mashi kenan, aiko ranshi yayi mugun 6aci har baisan time daya damƙi wuyan Gabriel da hannu biyu ba, ya tura shi zuwa jikin bango ya matse shi, Da gudu Angel ta nufe su da niyar ta dakatar dashi, sai dai kafin ta isa, tai tuntu6e ta kife ƙasa, Kafin ta yi wani yunƙurin ɗagowa

faɗa ya kaure a tsakanin Danish da Gabriel, Yadda kasan dawakai suna kokawa, dunƙule hannu Gabriel yai ya dinga naushin cikin Danish, Don ya sakar mashi wuyanshi daya shaƙe mashi amma yaƙi saki, duk da irin jahilin naushin da yake kaima Cikin shi, ko girgiza baiyi ba tamkar baisan ma ya na yi mata, ganin dagaske so yake ya kashe shi yasa Gabriel daddagewa Ya sauke mashi naushi saman idon shi na hagu, nan take Danish ya saki wuyan Gabriel Gaba ɗaya ya faɗi ƙasa hannun shi dafe da idonshi, kamar zaiyi hauka, shi kanshi Gabriel da ya yi silar jefa shi cikin halin da yake ciki sai da gabanshi ya faɗi, ganin Jini yana gangarowa ta cikin idon nashi daya nausa, wata irin gigitacciyar ƙara Angel ta saki, A matuƙar razane ta miƙe daga kwancen da take akasa ta watsa da gudu ta zube sama gwiwowinta agaban Danish, Hannu biyi ta sanya wurin ɗago dashi ta ƙanƙame shi ajikinta, Sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, Gaba ɗaya tabi ta gigice, ta ruɗe ganin yadda idon shi ke fitar da jini jawur dashi,

“INNALALLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN! Gabriel ka kashe mishi idonshi, Ka kashe min Danish ɗina! wayyo Allah na! nashiga uku na bani na lalace!!” Hankalin Gabriel idan yai dubu to ya tashi, Kamar ya ɗaura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, la66ansa sai kerma suke yi, ya haɗa uban gumi, Muryarshi aruɗe yake faɗin”Angel bada son raina na aikata mishi hakan ba, shine ya shaƙe min wuyana! sosai ta ƙanƙame Danish ajikinta, Jikinshi yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyacin, ko ina kerma yake yi, ga wani irin nishi da ya ke fitarwa.

hannunta data ɗaura saman nashi hannun daya rufe idon da ke bleeding dashi, tuni ya jima da jiƙewa sharkaf da jininsa, wa’iya zubillahi, Lamarin tamkar a mafarki yake faruwa, sun yi fatan ace mafarki ne su ke yi ba agaske ya faru ba, ta yi Danasanin Biye ma Gabriel da tai da duk hakan bata faru ba, da tasan Danish zai rasa idonshi silar yunƙurinsu na haura taga da bata yi gigin yin hakan ba, Yanzu gashi dare ɗaya sun ja mashi bala’e, Gabriel ya naƙasa shi, akan abunda bai taka kara ya karya shi ba, duk wannan koke koken da suke yi na cikin ɗaki basu farka daga baccin da suke yi ba, kamar waɗanda suka sha sleeping pills, tana kuka tana faɗin Gabriel ya zamuyi Dashi kada ya mutu, jinin shi sai zuba ya ke yi, Ya Allah kasa mafarki ne nake yi, bazan iya jure ganin danish cikin mawuyacin halin nan ba! Bazan ta6a yafe ma kaina ba, da kai kanka Gabriel kaine silar komai, Ga shi zan rasa ɗan uwana….

Da gudu Gabriel Ya nufi igiyar shanyarsu ganin mayafin azeeza da ta manta Tun ranar da akazo aka tafi ƴar gidan daddy, Angel ta shanya shi don ya bushe bayan ta kammala sanyaya mata jikin ta dashi, aranar suka barshi saman igiyar, ɗaukowa Gabriel yai jiki na 6ari garin sauri hada tuntu6e ya ƙarasa inda Angel take a zuƙunne ta ƙanƙame shi ajikinta, daƙyar Gabriel ya iya 6an6aro kanshi daga saman ƙirjin Angel, ya dawo dashi saman jikin shi, ya sanya mashi mayafin ya tamke mashi idanuwanshi dashi, sai nishi ya ke yi yana yarfa dogayen yatsun hannayenshi, Bawan Allah shi kaɗai yasan irin raɗaɗin azabar da yake ji acikin idonshi, jijiyoyin hannanyenshi dana wuyanshi shatunsu yafito ruɗu ruɗu saman fatarshi, hatta saman goshinsa jijiyoyinne, gwanin ban tsoro, sosai Gabriel ya ɗaure mashi mayafin duk don jinin ya dakata da zuba, haƙiƙa na yi baƙin Cikin ganin kakkyawar fuskar Danish da jini ya wanke ta, har saman wuyan shi, Gabriel na gama daure mashi idon nashi, angel ta sanya hannu biyu ta dawo dashi jikinta, ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka mai cin rai, tana faɗin”ɗan uwana rabin raina dan Allah kada ka mutu kabarni Danish ɗina, na gane kuskure na, ban da wayau, ga shi naja maka ka rasa idanuwanka, duk laifina ne, namanta cewa duk abunda ka ke yi kana yi ne don ka kare ni daga faɗawa halaka amma saboda taurin kai irin nawa nagaza fahimtar hakan, mun cuce ka Danish mune silar komai!!…….. Sosai ta fashe da kuka, Shima Gabriel ɗin kukan yake yi tamkar ranshi zai fita, tashin hankalin da ba’a sama shi date!!

Mexai faru da danish? Ga ido yana ta bleeding zai mutune ko zai rayu a matsayin makaho mara ido ɗaya? Wani irin hukunci su haris zasu ɗauka idan suka gane cewa Gabriel ne silar da Danish ɗinsu Ya makance? Wani hali zasu tsinci kansu? Alƙamina Ya tsaya Cak! sai mun haɗu next page in Allah yakaimu da rai da lafiya, amma fa ga dukkan alamu Danish ɗinku saiya leƙa treatment room! Daga nan kuma.6arna zata auku, Don angel bazata juri zama babu shi ba, dama shine mai tsawatar mata akan karta haura taga, inaga idan babu shi……..😳 hasashe na ne kawai🥱

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button