Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 9 Hausa Novel

Captain Salim ya ƙira sunan nata cikin tausasawa, ta ɗaga ido ta kalleshi.”Akwai wani matsala ne?”Ta girgiza kai.”Na gode sossai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi”Yayi mata murmushi, bai bar ɗakin ba sai ga dattijuwar matar kuɗi masu kauri ya fitar ya ba dattijuwar saboda sayan abinci ya nuna mata kaya kala biyu dogayen riguna da ya siyo da man shafawa, macline, brush, turare da soson wanka ya roƙe ta da ta kula da ita don Allah har ya dawo, kaman kar ya tafi haka ya fice a ɗakin domin haka kawai ya tsinci kanshi cikin tsantsar tausayinta da har yana so ya yiwa zuciyarshi yawa.Baaba jummai macece mai faram-faram da saurin sabo duk yadda Afeefah ta yi shiru sai ta saka ta magana har da murmushi, tana kula da ita sossai sossai, bata maƙe kuɗin da salim ya bata ba ta kan sayo musu kayan daaɗi ta bajo musu tana cewa “Ke ‘yannan sa hannu maza ki ga mu ci kin ga ko mutuwa muka yi yanzu za’a ɗauke mu da nishi saboda nauyin mu ina amfanin kana da shi baka ci ba? Maza-maza sa hannu”Dole Afeefah take murmushi kuma ta biye wa Baaba ta ci sossai dare idan an gama duba Afeefar kan su kwanta bacci za ta shiga ba ta labarin aurenta da ma rayuwar da tayi har ma da irin kishin su na da chan baya da kissa kala kala da kan kashe Afeefah da dariya, kan kwana biyu ya zagayo har ta fara manta tarin damuwarta, duk Sallar ta kuwa bata taɓa mance iyayenta da Aunty zee ba ta kan kai wa Allah kukanta musamman cikin dare akan ya gafarta musu yayi musu rahama (Tana roƙon duk wanda ya zo across wannan littafi ya nema musu rahama domin Allah🙏)Kaman yau Dukda safiya ce bayan sun gama karyawa da doya da miya haɗe da shayi da duk a bakin asibitin Baaba ke sayo musu ta dubi Afeefar da ta ɗan yi shiru tana tunani tsoron ta ɗaya dawowar salim ina za tace ya kaita? Ina ta nufa? Ya zata yi? “Wai ‘yannan kin kuwa san abin da ke ƙara ba ni mamaki ma a wannan zamanin?”Afeefah ta girgiza kai tana ɗan kakaro murmushi don ta san zancen baaba bai taɓa wuce kan taɓarɓarewar tarbiya a wannan zamani ba.”Mu a lokacin mu ina mace ta isa ta ƙira ko mai irin sunan mijinta? Kai ko bayan ya mutu ko kun rabu mu kam ba ma iya kiran sunan ko da kuwa da kuskure amma ki ji mace yanzu gatsal tana cewa Ummaruuu a gaban yara ma da iyayenshi ko nata kai ko a gyalen su”Dariya Afeefah ke yi sossai tace “Yanzu Baaba ko sakin ki yayi ba za ki iya ƙiran suna mai irin nashi ba?””Eh mana! Ai da kunya ‘yannan””Tabb baaba ba dai irin sakin wannan zamani ba, komai fa akwai silar chanzuwarshi Baaba bai wuci mazan ma na da na yanzu ba ɗaya ba ne shiyasa ake ganin bambanci””za dai ki kare su ni dai na faɗa miki ki kiyaye, kin ga maza suna matuƙar son a ba su girma, idan za ki ba namiji girma toh tabbas mutuncin ki ma zai zama daban ne a idanunshi ko da kuwa ya auri wata ne”Tana murmushi sossai tana tuna wato gidan kawu Labaran ban da rashin tarbiya har da tarin jahilci da suke dashi, daga mu’amalar iyayen har ta ‘ya’yan gashinan dai gashi nan yo idan ta ciwo shi ai sai dai a ji suna dambe da mata…Fuskanta ɗauke da murmushi tana sake jinjina rayuwar da don baaba jummai na sake bata labarin yadda maƙota sai ya hukunta ɗanka baka sani ba idan ma ka sani ka je har gida ka mishi godiya amma yaran yanzu ko kanwarka ce ka mari yaronta gabanta sai ta maka Allah ya isa a gaban yaro to me yasa ba za’a lalace ba? Haka batun ƙarfafa zumunci Meyasa zumunci ba zai yi ƙarancin ba yara suna ‘yan pendo da ɗan kawu amma idan wanchan sun fi kuɗi sai ka ga yana nuna bai san yayyunshi cousins ba ko ya fi karfinsu uwa kuma ta kasa kwaɓa saboda tana ganin hakan ce daidai daga mutum mai kuɗi ne level nashi ya fi karfin talaka ko da kuwa cikin umma ɗaya ne.Turo kofan yayi bakinshi ɗauke da sallama a kanta idanunshi suka soma sauƙa, ajiyar zuciya ne ya kufce mishi ba tare da ya san dalili ba murmushi na yalwatuwa a fuskar tashi ganin ko da suka hada idanu murmushin bai kau daga kan fuskanta ba, fara’a na yi mata kyau ya ayyana hakan a ranshi maganan Baaba ne ya yanke mishi tunani “Bawan Allah sannu da dawowa, lale maraba”Ya saki murmushi ya ɗan rankwafa ya shiga gaisheta ta amsa cike da kulawa tana tambayar shi aikin da sanya mishi albarka, Afeefah ya duba da ta ɗan duƙar da kai tana kallon yatsun hannunta”Na shigo kuna ta raha me yayi miki daaɗi haka Afeefah?”Ta ɗago tana murmushi “Ni da Baaba ne, barka da dawowa”Yana zama gefen gadon tuni ɗakin ya cike da sassanyar kamshin shi ya ce “Yauwa ya jikin? Hope kin samu lafiya?”Ta gyaɗa kai tana dorawa da “Alhamdulillah na gode”Da Baaba suka cigaba da hira akan jikin nata ita dai sai murmushi bata magana har Dr. Sulaiman ya shigo, sai da suka dan sake hira kan ya miƙawa salim takardar sallamar ta “My patient is good to go, kawai dai ta kiyaye sa damuwa a ranta and gaskiya ku kula da ita sossai da sossai Dukda SG Ryan yayi mugun ƙoƙari a kanta babu wani traces na guba a jikinta amma don Allah ku sake kula, ke kuma Afeefah ki saka a ranki komai yayi zafi maganinshi Allah. Manzon Allah S.A.W ya ce; “Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana nan madawwami a cikin Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwadar ta a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani karfe, to karfensa na nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109)”.”Allahu akbarr” Baaba jummai ta zabga kabbara Afeefah dai kanta ƙasa zuciyarta na sake shiga cikin tsantsar nadamar wannan yunkuri da tayi da ta mutu ta shiga ukunta. Godiya sossai ta musu haka salim yayi wa Sulaiman da Baba godiya murmushi kawai Sulaiman yayi yana shaida wa Baaba akwai driver waje zai mayar da ita gida sai ga Baaba na hawayen rabuwa da Afeefah Dukda zaman nasu na kwana biyu ne amma sanin ranar sake haɗuwa sai Allah, Afeefar ma sai ta kama hawaye, a duk sadda ta ga wani ya kaunace ta Saboda Allah ta kan ji son shi fiye da yadda shi ya kaunace ta don masu hakan a gareta basu da yawa, bata yi shiru ba ko da Baabar ta tafi sai ma zuciyarta da ya tsinke, tsoro da fargaba suka lallaɓo suka rufe ta.Daram! Haka zuciyarta ya buga a sadda Salim ya ɗauki ‘yan kayanta yana furta”Mu je ko Afeefah?”Jiki a saɓule ta sanya kafafunta ƙasa ta shiga takawa har ta wuce shi yana riƙe mata da ƙofa bayan ta fita ya ja kofan a bayanta ya rufe suka jera a tare har motar shi, ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya buɗe baya ya ajiye kayanta kan ya zagaya ya shiga ya ta da motar suka fice daga cikin asibitin, cikin natsuwa yake tukin kan ya ɗan kalleta”Anchau muka nufa ko?”Kamar mai karyayyen wuya haka ta gyaɗa kai gabanta na dukan tara-tara, bata fata Uncle ya raba ta da su suhail bata fata su tashi a hannun kishiyar uwa, daga shi har yaran wani irin tausayinsu take ji har ɓargonta bata ga laifin uncle ba don ta tabbatar dole mutuwar Aunty zee ta jijjiga shi fiye da ƙima tana fata da adu’ar Allah ya sa ya sassauto ya karɓeta kar ya kore ta.Salim ya gyaɗa kai shima, motar ya ɗauki shiru na seconds kan yace “Afeefah!”A hankali ta amsa”Na’am””Na san kowa abinda yake faɗa miki jarrabawa, kaddara haƙuri. nima ba zan chanza ba don akan hakan Allah ya halicce mu haƙuri kuma da kaddara ibada ne kaman yadda ya halicce mu don mu bauta masa, idan kika ga na wani Afeefah sai kin yi hamdala wani jarabawar shi ‘ya’yanshi, wani za ki samu jarabawarshi Mata ne, wani talauci, wani dukiya hatta Mahaifiya ta kan iya zama mummunar jarabawar ɗa, kaman yadda rayyan ya faɗa kuma Sulaiman ya ba ki har hadisi, da kashe kai shine mataki mafi sauƙi a yayin da duniya ta yi wa bawa tsanani da ba za mu tarar da miliyoyin mutane ba a raye, akwai wani hadisi da Manzon Allah S.A.W ya tashi tsoratar da masu yunkurin kashe kansu da ko tunanin aikata hakan ka yi to ka yi gaggawar tuba ka tsarkake zuciyarka daga shaidan. Ban san irin naki ƙalubalen ba amma ina sake jan hankalinki da ki kiyaye dokokin Allah ki duƙufa da Adu’a In shaa Allahu komai yayi farko yana da ƙarshe kinji ƙanwata?”Kai ta gyaɗa mishi a hankali cikin sassanyar Murya tace “Yaya Salim hakika ba ni da bakin gode muku, kun ceceni daga azabar Allah da baku zo ba a lokacin da ban san a yanzu wani hali nake ciki ba. Na gode Na gode Allah ya yaye maka naka matsalolin ya saka maka da gidan Aljanna”Ya amsa da Ameen yana ɗan murmushi.Kaman yadda ta zata isar su Anchau kai tsaye gidan uncle suka yi, ko da ya tura yaro yayi mishi sallama da uncle ba’a jima ba sai gashi ya fito idanunshi na sauƙa kanta yayi mugu-mugun ɗaure fuska bai tsaya ma salim ya gama bashi haƙuri da koro mishi jawabin da ya sa bai dawo da ita kan lokaci ba ranar ya shiga karta musu rashin mutunci yana kwashe mata albarka duk yayi wani irin susucewa, sai jefanta yake da munanan kalamai da suka zama tamkar rurin garwashi a zuciyarta, ya shiga tuna mata Alkhairin Aunty zee a rayuwarta da mugun sakayyarta, ya kuma yi alkawarin muddin bata bar mishi kofan gida ba wallahi shi zai kawo karshenta yayi ajalinta. Kokarin bashi hakuri salim ya shiga yi ganin tana wani irin kuka amma ina tuni ya soma tara musu jama’a babu arziki suka koma mota, ta haɗa kai da gwiwa tana ƙara fashewa da wani kukan mai taɓa zuciyar duk mai saurare.A hankali salim ya ja motar sai da suka yi nisa sossai yayi parking tare da jingina bayan sa da jikin kujerar ya lumshe idanu yana sauraren kukan nata da idan har ka ji ka san duniya bata yiwa mai yinsa daaɗi. Sai da tayi ma’ishi bai ce mata komai ba da kanta ta ɗago ya miƙa mata ruwa ta fita ta wanke fuskanta ta dawo ta sha kaɗan kan ta miƙa mishi ba tare da ta kalleshi ba ya sa hannu ya karɓa.”Ki yi haƙuri Afeefah!”Ta gyaɗa kai “Yanzu ina kuma kike da shi da zan kai ki?”Hawaye ne ya sake cike idanunta a sadda take furta”Akwai kawuna a Dutsen-wai”Cikin dasasshiyar muryarta da ya dishe saboda kuka.Motar ya ja tare da miƙa hannu ya kunna musu ƙira’a domin zuciyarta yayi sanyi.Awanni kaɗan ya sada su da kauyen, ita tayi ta nuna mishi hanya har gidan kawu Labaran. Yana zaune rumfar kofar gida yana cinikin Nono da wata bororuwa ganin tsayuwar mota ya sa ya shiga shafa rantalin kanshi da babu gashi ko guda sai maiƙo yake a rana, a tunanin shi ɗaya daga samarin yaranshi ganɗa-ganɗa da suke zaune ba aure ne domin sun rantse sai mai maiƙo iyayensu mata kuma sun ba su goyon baya alhali gidanshi ko keken hawa mai kafa biyu babu.Idanu ya ƙura mata bayan sauƙowarta yana tunanin inda ya santa kan ya zabura ya runtuma a guje sai cikin gida, ganinshi da gudu ya sa mata da ‘ya’yanshi kowa ya fara yin ta kanshi don tsallake su kawai yake bai tsaya ba sai da ya dangana da ɗakinshi ya zaro sandar goran shi tare da wasu manyan layu ya zura a wuya, wasu ya saka a hannu kan ya fito ya nufi waje da saurinshi har yana kifawa….

Back to top button