Hausa novels

Zakuna Biyar Page 48 By Princess Teema

*It is about combining sperm and eggs to create children, and how the sperm of one man can be used to produce many children. The idea is presented in a different style. On the other side, there are soldiers fighting on the line between life and death, soldiers whose mission is to cleanse the world of corrupt and evil people. However, the path they have chosen to achieve this victory is filled with thorns: wicked people, traitors, oppressors, cruel individuals, and pure betrayal with no mixture of good at all.*Ya fara daddanna mata tsakiyar bayan wuyan nata. Sosai ta fara aiki da sauri. Aikin da ta ce zata yi in less than 40 mins sai ga shi ta yi sa in less than that 20 mins ta kammala. A gurguje ta rufe laptop ɗin, Leo ya miƙe game da bata hannunsa kan ta kama, da kyar ta iya kamawa ta miƙewa saboda gajiyar tsugunno, ganin haka sai ya karɓi rucksack ɗin nata, ya goya a bayansa sai ya ce ta yi tsalle kamar ɗazun ya ce ta kama katanga. Ai ina, ba zata iya ba, kafafunta basu miƙe sosai ba, dole suka ɗan tsaya a wajen na ɗan lokaci kafin ta samu kwarin iya tsalle ta haura katangar, barci ya cika idanunta, jikinta dik ya yi sanyi, haka ta dira ta baya ta tsuggunna har ya diro.Gaba ya wuce ta miƙe ta rufa mashi baya, haka suka miƙi wannan doguwar hanya dan komawa.A can cikin sansani kuwa. Zazzaɓi yana neman hallaka V babu wanda zata faɗawa, dan Noor yana bakin wuta, while ya fasa mata waya ba halin ta kirasa, ba zata iya taka kafafunta ta je ta same shi ba, sai ta kudundune cikin blanket ɗinsa tana kuka, ko abincin da ya kawo mata bata iya saukowa ta ci ba.Around 11 na dare Zaynish yasa aka kira mashi Angelina cikin tantinsa, ta je da laptop da sauran kayan aikinta. Yana zaune a saman mattress ɗinsa ta shigo, ba tare da ya kalli in da take ba ya nuna mata wajen zama, tana sanye da sleeping silky pjs a jikinta, a gefensa ta zauna tana ɗan satar kallonsa, musamman ligh brown African hair ɗinsa dake kara ɗaukar hankalinta. Ajiye wayar dake hannunsa ya yi game da mayar da hankalinsa a kan laptop ɗinta, a tare suka yi iya kokarinsu wajen ganin sun shigar da karamun drone na surrinsu mai kama da fly wajen hayakin nan amma abin ya faskara, dole ya juya akalar drone ɗin, ya duba cajin jiki, yana da cajin da zai iya kwana ɗaya a sama, hakan yasa ya ratsa da shi ta gefe-gefen wajen. Daga gefe ta gaba wannan tangamemen tekun ne, shiru Zaynish ya yi, a cikin ransa ya ce idan kuwa haka ne wannan in da hayakin yake fitowa a saman ruwa ne, gini aka yi a saman ruwa ta baki-bakin, ruwan na ratsawa ta ƙasan ginin yana wucewa. Na’am ya yi da hakan, sai ya cigaba da bin bakin ruwan dan ya ga me zai iya giftawa dik da ba wani haske sosai sai hasken farin wata dake tankar kamar rana.Angelina ta zauna shiru sai kallonsa take yi, ko ɗazun ta yi waya da Aunty Ummie again, dik shi bai sani ba. Ya jima a wajen tsaye bai ga motsin komai ba face jiragen ruwa manya-manyan dake can tsakiyar tekun. A cikin ransa ya ce dik yadda aka yi akwai jiragen ruwa dake ratsa wannan waje, to me suke kawowa ko me suke zuwa ɗauka a wajen? Gaskiya suna son sani, suna jiran umarnin gaggawa daga sama.A can kuma sauran sojojin suna shan ɗumi, Manassa da Vash suna hira a wajen, dan su basu fara aikinsu bama tukun nan. Ya ce sai gobe.A daidai wannan lokaci karfe 12 na dare AZURE ta yi kiran meeting na gaggawa kan lamarin MISSION NA DOL. BGA ya tura takarda office na GAT, ai GAT yana ganin takardan ya yi kiran meeting na gaggawa, a lokacin har ya tashi a aiki da yamma, amma da yaga BGA ya turo takarda kan DOL sai ya fasa tashi, ya bada lokacin around 12 na dare zasu yi zaman, ya gagara hakura sai gobe, dama tin tini yake jiran wani motsi daga wajensu.(Ni kam na ce ai ko dan su Angelina team DOL zaku rinƙa samu umarni da wuri daga GAT!)A wannan meeting room da suke zama dik end of the week su yi meeting kan tsaro aka shirya zaman. An tsara komai, kafin 12 ta cika dik wasu jiga-jigan generals sojoji sun hallara a wajen. Kamar kullum, GAT ne ya fara miƙewa, ya kunna mic na gabansa, a dake ya yi wa kowa barka da zuwa, kafin ya baiwa BGA damar gabatar da abin da ya tarasu. Dik kowa ya natsu tsit, BGA ya miƙe cikin mutunta kai, ya zaro farar takarda daga file na gabansa kan table, sai da ya fara yi wa kowa barka da zuwa kafin ya sanar dasu abin da Leo ya sanar da shi a waya. Bayan ya kammala bayani ne ya koma ya zauna sai MGR ya miƙe tsaye, cike da girmamawa ya ce. “A ina wannan waje yake? A ina su Nirash suke dama?”. Cike da ɗan mamaki Captain ya kalli MGR, cikin ransa ya ce. “Ko ina ruwansa da in da suke tin da ba a karkashin office ɗinsa suka tafi Mission ba?”. A fili kuma binsu da ido kawai ya yi yana mamakin halin wasu jami’an ba tare da ya yi magana ba.BGA ya rike mic ɗinsa game da cewa. “Bani da sanin takamamman in da suke, saboda bai faɗa mun ba, amma dai koma ina ne ina jin babban waje ne, kuma sun zaɓi waje mai kyau suka kafa sansaninsu”.MGR ya ce. “Wai dama su nawa ne a sansanin nasu? Da wasu sojoji suka tafi?”…….. General Ibrahim IB ne ya ce. “Ina ganin dik wannan ba shi ne ya tara mu a nan ba, umarni suke nema dan zuwa duba menene a wajen, so yakamata ne mu duba mu ga idan ya dace a basu izini sai a basu, a basu izinin su je su duba a sirrance, in sun ga me a wajen sai ayi zama kan abin da ya dace, either a basu umarni kan su tashi wajen in abin da bai dace ba ake yi a wajen, ko kuma a basu umarnin kama masu aiki a wajen, in kuma abin da ya dace ake yi a wajen ba shikenan ba”. Ya yi maganar yana kallon MGR. Tin da ya fara magana manyan generals suke jinjina kai alamar tabbas zancen General Ibrahim haka ne.Bayan ya kai karshen maganar ya juyo da kallonsa a kan GAT da ya yi shiru yana sauraren shawarinsu. General Ibrahim IB a dake ya ce. “Sir, ni a tinanina yakamata a basu izinin zuwa su duba menene a wannan waje, saboda mu san matakin da yakamata mu ɗauka”.MGR ne ya ce. “Amma kafin a basu izini yana da kyau mu fara sanin in da suke, saboda ko mun ji shiru a kai masu ɗauki”……. Uhm kai Captain ya jinjina, a cikin ransa ya ce. “Ko kuma a faɗa maka in da suke dan ka ji ko kana da alaƙa da wajen hayaƙin ba”…….. Shi dai GAT bai ce komai ba, shiru yana cigaba da saurarensu dan ya ji shawaran kowa.General Ibrahim IB ya ce. “No need MGR, ba sai mun san takamaiman daidai in da suke ba, umarni kawai za’a basu su kaddamar da aiki, mun basu makamai wadatattu masu lafiya, mun basu dik abin da zasu buƙata! To me na neman sanin ina suka kafa sansani? Dan kai masu agaji? Agajin me bayan wanda suke tattare da shi?”…….. MGR ya ce. “Kar ka manta rayuka ne suma, and bamu san wani irin hayaki ne a wajen ba, kada yazamana abin ya fi karfinsu yafi karfin makaman da suka tafi da shi azo a far masu, gara mu san in da suke ta yadda ko an fi karfinsu zamu tura masu wani agaji na gaggawa”. Kai General IB ya girgiza. “MGR wai me naka na son sanin in da suke? A ƙarƙashin office ɗinka suka tafi Mission ne? Ko dai kana da wani plan a ƙasa ne?”. Ib ya faɗa yana tsare MGR da ido…. Take MGR ya haɗa malaman jikinsa, ya ɗan yi shiru kafin ya ce. “No sir, ba wani plan, kawai na damu da rayukansu ne duba da yadda muke rasa sojojinmu a arewacin kasar nan, so ina tsoron rasasu ne”.”Dik sojan da ya fito daga nan AZURE na sani kun sani ba dai wani ɗan ta’adda ya fi karfinsa ba, kun san irin horon da muke basu, manyan ƙasashen duniya nan suke kawo sojojinsu dan mu horasu saboda ingancin horarwarmu, to me naka na jin tsoron rasasu? Baka yarda da kanka bane?”. General IB ya faɗa, babu wasa a tattare da shi.BGA ya ce. “Shi nima na gani, no need mu damu da abin da muka san mun fi karfinsa, koma menene sojojin AZURE suna iya tinkararsa ba tare da tsoro ko shakka ba, ko kai da kanka baka yarda da horon barrack ɗin namu bane?”. MGR ya girgiza kai game da cewa. “Sorry sir, ni dama saboda damuwar rasasu ne, amma ba komai, nima ina bada goyon bayan a basu izini su je zubasu”….. Shiru ne ya ɗan biyo baya a room ɗin, kafin General IB babban General na AZURE, sojan da baya ɗaukar wasa kuma baya wasa, jami’in da gaskiya da aikinsa suka kawo shi kujeran da yake kamar dai Captain Onbish, jami’in da baya karɓar cin hanci, baya bin bayan rashin gaskiya, ko ɗan uwansa na jin yakama da laifi sai ya hukuntasa daidai da hukuncin da ake yi wa kowa!.A dake ya ce. “Sir ni a nawa shawarar a basu izinin a sirrance su je su gano menene a wajen, in suka bamu information na abin dake wajen sai mu san matakin dayakamata mu ɗauka”. Ya faɗa yana kallon GAT dake ta binsu da ido.Jawo paper neman umarnin GAT ya yi. Ya buɗe ya ɗan duba rahoton da BGA ya rubuta kan DOL ɗin. Pen ya ɗauko, cike da kwarewa ya rattaɓa hannu kan ya bada izinin su je su duba. Daga nan ya miƙawa General IB paper. Karɓa IB ya yi, ya ɗauki pen ɗinsa shi ma ya rattaɓa sign ɗinsa. Daga nan ya miƙawa Lieutenant General shi ma ya sanya hannu, sai aka miƙawa Major General shi ma ya sanya hannu, sai Brigadier General watau BGA shi ma ya sanya hannu, sannan aka baiwa Colonel ya rattaɓa nasa hannun, sai Lieutenant Colonel, sai Major, daga nan aka baiwa Captain, yana sanya hannu aka baiwa First Lieutenant, bayan ya sanya hannu sai Second Lieutenant, yana sanya hannu suka maidawa BGA takardan.Karɓa ya yi, dikkansu suka haɗa maki wajen yi wa team DOL fatan alkhairi da fatan nasara, daga nan GAT ya ce a rufe masu taro da addu’a, kasancewar General IB musulmi ne sai ya riga kowa miƙewa ya fara kwararo masu addu’a har da na fatan ALLAH yasa GAT ya musulunta, dan mutumin kirki ne sosai, ga kaunar kasa da ƴan kasa, yasan aikinsa matuƙa.Daga nan aka tashi wannan zama around 1:30 na dare, GAT ne ya fara fita kafin su General suka rufa mashi baya. Yana komawa gida ya isko Aunty Lisa tsaye a parlo sanye da sleeping dress tana ta faman jiransa, ta ɗan kiba sosai, da alamar tana da ciki. Yana shigowa ta tafi ta rungumesa tana mashi welcome, shafa kanta ya yi game da cewa. “Ya shirye-shirye?”…… “Welcome my oga sir”. Ta faɗa kafin ta bashi amsar tambayarsa na ya shirye-shirye da cewa. “Komai yana tafiya daidai a nawa ɓangaren kai fa?”. Rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak yana amsa mata da. “Komai daidai, amma party biyu kawai za’ayi sai soldiers day shi ma ɗaya”. Ya faɗa a lokacin da suke shigewa room ɗinsu. Watau jama’a shirye-shirye bikin GAT da Aunty Lisa ake yi, ana shirin party, yanzu ya fitarwa da duniya cewa zai yi aure, shi ne ake shirye-shirye, ga alamar kuma Aunty Lisa na da ciki, har ma ya ɗan fara girma. Akwai shagali, su Arya sai dai su dawo su samu Aunty ɗinsu da baby, dan cikin Aunty Lisa zai iya kai 3 month ma. Gaskiya daddy GAT yana sha’aninsa, ya tura yara mission shi kuma yana buga nasa mission ɗin a gida, bari dai in yi shiru kada ace na ce, to ban ce ba!.D——O—–L.Tin Arya tana iya jurewa ta taka da kafafunta har ta gagara, abin yai mata yawa, ga barci ga gajiya. Wani irin jirin gajiya da ya ɗebeta bata san lokacin da ta tafi gabaɗaya ta faɗi ƙasa ba. Intently Leo dake gabanta ya juyo, ganin ta faɗi ƙasa yasa ya juya ya kalli hanya, sun kusa isa sansaninsu, duba time ya yi a wayansa 3:30 ya yi……. Matsawa dab ita ya yi, a cikin ransa yana faɗin dole ya bata ainahin horo ba horon kare kai ba, in dai zai yi aiki da ita dole ta iya jurar dik wani wahala, dole ta zama kaman shi, dan haka daga gobe dole ya fara horar da ita.Cike da wannan tinani a ransa ya rage tsawonsa, ya gyara hannun rigansa kafin ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya juya suka cigaba da tafiya. Hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa, bata san time da ta kwanta shiru a jikinsa ba, har barci ya fara ɗaukarta, bama ta san lokacin da suka isa sansani ba, sai ji ta yi ya kwantar da ita saman mattress ɗinsa kasancewat ta baya ya shigo dan kada kowa ya gansu, and ya yi tinanin ta yi barci shiyasa ya kwantar da ita wajen, bai tasheta bane kuma dan kada ya yi magana a waje sojojinsu su fahimci baya nan ya fita, dan wannan aiki na bincikar hukumar navy aikinsa ne shi kaɗai da yake yi wanda baya son kowa ya sani, shiyasa ya wuce cikin tantinsa da ita.Da ya kwantar da ita sai ya suke rucksack ɗinta dake bayansa, ya tsaya kusa da mattress ɗin, murya can ƙasa ya fara kiranta da ke ta tashi ta tafi cikin tantinsu…….. Da kyar ta yunkura ta miƙe zaune, ganin ta farka yasa ya koma gefe ya zauna a ƙasa game da fito da laptop ɗin nata, aiki zai dasa yi, babu alamar barci a tattare da shi. Miƙewa ta yi, jikinta dik a mace ta nufi hanyar fita, har ta kai kofa muryansa ya katseta da cewa. “Zoki cire password na laptop ɗin”……. Nan fa ta ji kirjinta ya buga, dan kuwa ɗazun ta canza password na laptop ɗin daga sunanta ta mayar sunansa, tana zaune kawai bata san ya aka yi a lokacin ta tsinci kanta da sanya sunansa a password ɗinta ba.Ƴan kame-kame ta fara yi, ta ɗan sosa kanta kafin ta juyo ta dawo, wannan shi ake cewa ɓoyyar soyayya, ɓoyayyar zuciya, hiding love ba. A gefensa ta tsugunna, zuciyarta cike da tinanin yadda zata sanya wannan password ɗin a gabansa. Cikin ikon ALLAH sai ya juyo mata da laptop ɗin saitinta yadda ba zai ga me take yi ba, ai a bayyane ta sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya har tasa ya ɗan ɗago yai mata kallon second ɗaya ya ɗauke idanunsa.Cikin girmamawa a hanzarce ta shigar da password ɗin game da juyo mashi da laptop ɗin. Bai ko ɗago ya kalli in da take ba ya fara ƙoƙarin buɗe bayanan da suka sanƙamo. Cike da shakkarsa game da tsoro da girmamawa ta ce. “Sir, zan iya taimaka maka?”. Barci take ji kamar zata mutu, amma kunji wai zata tayasa aiki, kai soyayya wahala ce wani lokaci.Shi kuma da ba’a mashi abin arziki da wani kansa tin na haihuwa irin na Lion ya ɗaga mata hannu, ko kallon in da take bai yi ba mata alama da hannu a kan ta fice mashi daga ɗaki…… Jikinta ya yi mugun sanyi na abin da ya yi mata, ta yi tinanin yanzu tin da suna aiki tare zai ɗan rage share mutane da jiji da kai, Arya bata san cewa shi ɗin jinin sarauta bane, a jininsa jiji da kai da izza take.Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi waje, tana fitowa suka ci karo da Zaynish dake ƙoƙarin shigowa. Baya ta ja game da kamewa ta sara mashi. Ko kallon in da take bai yi ba ya wuce ciki. A cikin ranta ta ce ita tsakanin Zaynish da Leo ɗin ma bata san wanene gwamma ba, halinsu sai su. Wucewa tantinsu ta yi, a lokacin Jehan da Manassa sun yi barci, while Angelina ta shigo tantin yanzu, sun kammala aiki da Zaynish, sai farinciki Angelina take yi saboda Zaysh ya yabawa aikinta, ya ce ta yi namijin kokari.Gyara shinfiɗarta ta yi ta kwanta tana kallon Arya da ta shigo yanzu, sai wani layi Arya take yi tamkar zata faɗi, jiki dik ya yi tsami. Sai da Arya ta duba Jehan, ta sumbaci yarinyar kafin ta kwanta a gefenta, ko sannu bata cewa Angelina ba. Ai tana kwanciya sai barci. Ita ma Angelina tana kwanciya sai barci.A can gefe kuwa, Noor yana ankare da komai, ya ga fitar Leo kuma yaga dawowansu, dama saboda jiran dawowansa yasa bai yi barci ba, dan haka yana ganin Leo ya dawo ya miƙe ya nufi tantin nasa.Baki ɗauke da sallama ya shiga cikin tantin, zaune ya isko Zaysh da Leo suna tattaunawa kan wannan hayaki, Leo yana aiki da laptop na Arya. A gefen Leo Noor ya zauna game da cewa. “Bro ina ka je?”……. Ba tare da Leo ya kallesa ba ya ce. “Idan na gama haɗa bayanai na tabbatar da abin da nike zargi zan faɗa maku in da na je, yanzu dai ya naku ayyukan?”……. “Komai na tafiya daidai”. Suka haɗa baki wajen faɗe. Leo ya ce. “Zamu raba sojojinmu zuwa kaso huɗu, a cikin team 2 kowannenmu zai ɗauki mataimaki guda ɗaya, sannan 34 soldiers da suka rage zamu rabasu kaso huɗu”. Jinjina kai suka yi, a daidai lokacin Vash ma ya shigo cikin tantin, a kusa da su ya zauna, maimaita abin da Leo ya faɗa yanzu ya yi dan Vash ya ji, sannan ya cigaba da cewa. “A team two muna da UNAYS, JURAIZ, AMEER AND FAHAD”. Ya ɗan dakata yana dawo da kallonsa a kansu.Sai ya ce. “Zan yi aiki tare da Unays, Zaynish kana tare da Juraiz shi ne mataimakinka, Arvash kana tare da Ameer, Nooriel kana tare da Fahad, gobe da safe In ALLAH ya kaimu zan sanar dasu hukuncin da na yanke, sojoji 34 da muke dasu kuma kowannenku zai ɗauki sojoji 8 a karkashinsa, sojoji biyun da suke rage za’a barsu dan gadin sansaninmu”. Jinjina kai suka yi, Zaynish ya ce. “Wannan hukunci ya yi”…… Noor ya amsa da. “Sosaima, hakan ya yi”. Kai Vash ya jinjina, kasancewar Leo yana son yin aikin sirri shi kaɗai sai ya ce. “You can go”…… Da okey suka amsa mashi, a tare suka mimmiƙe kowa ya yi cikin tantinsa. Noor na shiga ya ɗauko blanket ɗin V daga cikin rucksack ɗinta, bai je in da take ba, ya shunfuɗa a ƙasa ya kwanta, ba zai kwanta da ita ba, ALLAH sarki, rashin sani yafi dare duhu, bai san bata da lafiya ba, ga barcin wahala ya ɗauketa, jikinta ya yi zafi raw tamkar wuta.Yana kwanciya ba jimawa barci tai awon gaba da shi, sansanin nasu ya yi tsit, dik sun yi barci sai sojojin dake wajen wuta da kuma Leo. ASUBA TA GARI. ————————🧠🔥IRON FIST. The blood of power, the blood of authority and honor, the blood of bravery and leadership!!.Suna fira wajen CRYSTAL PALACE daddy Champion ya ɗauge saman motarsa, ya saukesa, wani irin niimantaccen iska ne ya fara ratsasu. Ai wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta ɗan rungumesa ba, ta manna mashi sumbata a cheek kafin ta sakesa ta miƙe tsaye, hannayenta ta buɗe tana shaƙar iska mai niima.Ta ɗan riko waist ɗinta kafin ta ce. “Daddy i wish Rimsha tana tare da mu a wannan waje, I wish tare muke jin wannan daɗi, da na yi farinciki, ita ma tana son irin wannan yanayin”. Shi dai bai ce mata komai ba, sun zo sauƙa bridge ta hango irin turawa masu ice cream mai shegen daɗi a ƙananan motar nan, ai da sauri ta ce. “Daddy tsaya ka saya mana”…… Yana ƙoƙarin rage gudun motar ya ce. “In saya maki dai sarkin son zaƙi ba in saya mana ba”. Dawowa mazauninta ta yi, ta zauna tana sakin one side smiling kafin kuma ta ɗan cukule fuska tana turo baki. Tsayawa ya yi, ya kira mai ice cream ɗin. Wani dattijo ne a irin waɗan nan motoci da ake haɗawa ɗin, ya zo da sauri, cikin girmamawa yana risinar da kai ya ce. “Wani irin za’a baka sir”.Carap ta capke kafin Aryan ya yi magana ta ce. “Milk and mango flavor”…… Da okey dattijon ya amsa game da fara kokarin ɗauko roban zuba mata. Dakatar da shi Aryan ya yi yana harararta kafin ya ce. “Give her chocolate or strawberry”……. Turo baki ta yi. “Daddy irin wannan ice cream ɗin milky ya fi daɗi”…… Banza yai mata bai sake magana ba, dattijon ya zuba mata a robar ya miƙo mata, kin karɓa ta yi, ta make kafaɗa tana turo baki har da juyawa Aryan baya wai ta yi fushi.Hannu Aryan ya miƙa ya karɓa, sannan ya zaro kuɗi daga jikin kujerar motar, ya miƙawa mai ice cream ɗin dala 100. Dattijon ya ce. “Bani da canji”. Aryan ya ɗaga mashi hannu alamar ya je kawai. Godiya ya dinga yi, Aryan ya tada motar da hannu ɗaya suka fara tafiya. Juya mashi baya ta kara yi tana kallon hanya, taki yi mashi magana. Oh manyan kasashen duniya sun cigaba, dare tamkar rana, ha rashin tsaro ba hayaniya, wlh ko’ina ka gani lantarki tankar kamar rana, abin gwanin ban sha’awa, ALLAH ka gyara mana kasarmu ta zama fiye da hakan! Ku ce Amin.Ya ɗan yi tafiya mai ɗan nisa kafin ya tsai da motar a wani haɗaɗɗen waje da ake sai da flowers, kun san su ƴan rose ne, akwai iya baiwa flower muhimmanci.Wani haɗaɗɗen bunch of flowers ya saya tare da karɓa ya ajiye a gefensa. Ice cream dake ɗayan hannunsa ya kai saitin ɗan bakinsa, baya shan irinsu ice cream da kayan zaƙi, amma yau saboda ita zai sha…….. Kaɗan ya ɗan lasa, sai ya ɗan tsuke fuska alamar batai mashi ba. Ɗan daurewa ya yi game da sake ɗeba mai ɗan yawa a bakinsa. Bai gaɗiye ba ya rike a bakin nasa, ya kai hannu ya jawota jikinsa, tana tirjewa aikuwa ya matse ɗan bakinta game da sunkuyowa kanta, ya tura mata ice cream ɗin dake bakin nasa cikin nata. Ji kake diff ta natsu ta daina ƙoƙarin kwace kanta, ta kwanta a jikinsa tana turo baki, sai kuma ta hau haɗiye ice cream, harda ɗan lashe baki. Zuba mata ido ya ɗan yi kafin ya ce. “Sarkin kwaɗayi, me na lashe baki kuma bayan kin ce ba zaki sha wannan ba?”. Turo baki ta yi. “Saboda daga bakinka ya fito yasa na sha, ba dan haka ba bana so, test na bakinka ya kara mashi daɗi da armashi shiyasa, amma ni nasan strawberry bashi da wani daɗi”….. Ai gabaɗaya sawa ta yi ya ji shi a wani yanayi, wai dan daga bakinsa ya fito, kai wannan yarinya sai shiru. Miƙa mata ragowar ya yi yana faɗin. “Na hanaki shan milk baki ji ko?”…… “Kai daddy kai daddy, to ai wannan bashi da yawa, and ni ka faɗa mun meyasa ka ce in daina shan milk kaki”. Ta faɗa tana miƙewa zaune. Kama hannunta ya yi ya damka mata ice cream ɗin kafin ya ce. “Gaba zaki san dalilin hanaki sha milk, yansu dai karɓi ice cream ɗinki ki shanye”. Make mashi kafaɗa ta yi. “A’a daddy, ni in dai ba na bakinka ba to ban so”….. Wani irin hararar kauna ya wurga mata kafin ya ce. “Wannan already ya taɓa bakin nawa, please my cherry ni bana shan zaƙi, karɓa ki sha kayanki”…… Har lokacin bata kula da rose dake gefensa ba, ta sake make mashi kafaɗa kan ba zata karɓa ba. “Karɓa in baki wani gift”. In a low way ya faɗa…… Tana turo baki ta karɓa tana kallonsa. “Close your eyes”. Ya faɗa ta hanyar motsa laɓɓa kawai ba tare da fitar wani sauti ba. Da sauri ta datse violet eyes ɗinta. Rose ɗin ya fito da shi kafin ya ce. “Open your eyes”.Ai tana sauke kallonta a kan rose ɗin nan bata san lokacin da ta kai hannu ta karɓa ba, da sauri ta ɗan rungumesa tana murmushi. Raba jikinsu ya yi kafin ya ce. “Sha ice cream ɗinki bari mu je wajajen yawo sosai”. Ya faɗa yaka ƙoƙarin tada motar.A shagwaɓe ta ce. “Daddy ni kam ka bar kaini ko’ina mu je ka mu hau fly board please”…….. Ɗan zaro mata idanu ya yi, sai kuma ya ce. “Fly board a daren nan? Baki tsoron ruwa ko?”…….. Kai ta gyaɗa. “Yes daddy, ruwa is the most favorite thing da nafi so, please mana my gentle chaos”. Ta marairace fuska tamkar zata sa mashi kuka. Zai yi magana ta rigasa, ta dinga mashi magiya har sai da ya aminta, haka ya juya kan motar suka koma beach na cikin CRYSTAL PALACE. A in fa ya faka motarsa ɗazu yanzu ma ya faka, ya fito ita ma ta fito, yarinyar nan sanyi tamkar zai busar da ita amma take kiran su hau fly board. A bakin ruwan ya tsaya tare da kira guard dake tsaron wajen, ya ce su haɗa mashi flye board bari ya hau da matarsa. Sun yi mamakin ganin da daren nan zasu hau, around 1:30 yanzu, amma basu da zaɓi ya wuci bin umarni, haka suka shirya mashi. Hannu yasa ya ɓalle botirin after dress na jikinta, ya zare rigar gabaɗaya, ya ce ta ɗaure gashin kanta da veil na rigar. Ba musu yi a hanzarce.Hawa kan fly board ɗin ya yi, ya ɗaure kafarsa da kyau kafin ya miƙo mata hannu, kama hannunsa ta yi, ta hau ita ma ya gabansa, sai ta juya ta ƙanƙame shi ta haya, shi kuma ya riko waist ɗinta ta saman mazaunanta da kyau, ta ɗan ɗaga hannunta ɗaya sama tana murnushi, daɗi kamar ya kasheta.Ni ban ma san ya zan kwatanta maku fly board ɗin nan da hausa ba, matsalata ban iya kwatance bane. Bari dai in gani ko zan iya, kada ku mun dariya. Yauwa fly board zaku gansa a cikin teku, masoya suna hawa su ta yawo a saman ruwa, kai wannan kwatance na rasa ta ya zan yi fa……… 💔😭😂Haba juyi ya fara yi da ita a cikin ruwan, tin suna baki-bakin gadar beach ɗin har suka fara natsawa can tsakiyar ruwan, daɗi kamar ya kasheta, sai ma sun tashi sama sosai, sai ta ɗaga hannu tana ƴar ƙara, fatanta ta ganta a tsakiyar teku zata je garin da rana yake fitowa, ya ALLAH, a wannan rana ta san ko rintsawa ba zata yi ba. Kara ƙanƙame shi da hannu ɗaya ta yi, tana cigaba da ɗaga ɗayan hannunta tana murmushi, shi kam kallo fine face ɗinta kawai yake yi, yana jin tamkar ya haɗe bakinsu, yadda suke a tsakiyar ruwan nan gasu a saman iska, iska mai daɗi sai kaɗa su yake yi, gabaɗaya ya canza mashi yanayin mood ɗinsa, ya shiga romantic way, yana ɗan lumshe ido. Suna saman iska ta ce. “Daddy barci kake ji ne?”. Da yake hasken dake baki-bakin gadan na haskasu sosai. Kai kwai ya iya girgiza mata, gabaɗaya ya rasa natsuwansa, barema yadda kirjinta ke haɗe da nasa. Hannunta da ta ɗaga sama ta sauke game da ɗaurawa a kan kyakkyawan cheek ɗinsa kafin ta ce. “Daddy naga eyes ɗinsa tamkar kana jin barci”. Nisawa ya ɗan yi game da juya fly board ɗin suka nufi bakin beach ɗin, dan tana neman jefasa cikin wani al’amari, gara ma kawai su sauƙa. Kukan shagwaɓa ta saka mashi tare da cewa. “Daddy kada ka saukeni yanzu”…….. Ko sannu bai iya ce mata ba, wasa ya kare, sauketa ya yi shi ma ya sauka. Ya kama hannunta sai cikin mota, sai kuka take yi yai banza da ita. Da gudun gaske ya tada motar suka nufi benensu. Yana tsai da motar ya fita game da fito da kayan da suka yi shopping, ya kama hannunta sai cikin elevator. Suna haurawa ɗaki ya wuce da ita, bai yi mata magana ba ya ajiye mata kayanta ya nufi waje. Yana fita ya rufe kofar fita gida nasu, ba mai iya sake fita ko shiga. Daga nan ya wuce benensu yana jin cikinsa wajen mararsa na murɗa mashi sosai. Ita kuwa ta zauna a bakin gado tana cigaba da kukan shagwaɓarta har da cewa daga yau ba zata sake kula shi ba.A hankali ta kwanta kan gadon tana ta faman kunkuni har barci ya saceta a wajen.Shi kuwa Aryan gida ya koma, zaune ya isko Lion a tsakiyar bed yana rike da laptop yana bibiyar su guru da suka fita aiki yau, ya sanya bluetooth a kunne suna magana da juna. Ai Aryan na shiga ya haye gado ya kwanta ba tare da ya yi wa Lion magana ba. Ya kwanta ruff da ciki yana dafe mararsa da hannu ɗaya, serious ciwo marar tasa take mashi, in ta murɗa sai ya datse idanunsa. Kallo ɗaya Lion yai mashi ya ɗauke kansa, ya cigaba da abin da yake yi na ƙoƙarin kwatantawa su Vir location da containers ɗin suke….. Tsabar yarda da kansu da IRON FIST suka yi babu bindiga babu wuƙa a hannunsu, daga su sai key ɗin motar da suke driving guru and Vir suka tafi. Kuma cikin daji can border da ƙasar suka kutsa.Tin da suka sako hancin motarsu cikin wannan dajin suke sharara gudu, guru yake driving dan dik cikinsu ya fisu iya mota sosai, Vir ya kwantar da kansa a jikin kujerar mota yana danna waya, hankalinsu a kwance mutanen nan, tamkar basu san cewa waje mai haɗari zasu shiga ba.Jikin motarsu ta gaba akwai camera, ta wannan Camera Lion yake kallon kan hanyar da suke a laptop ɗin gabansa………. Suna dab da isa wajen containers ɗin ɗaya daga cikin motocin da suka ɗauko container ɗin driver ɗin ya zare kansa daga layin da motocin suka jeru su 5 suna ƙoƙarin shigowa cikin ƙasar. Canza hanya wannan container ta yi, kuma ba kowa bane driver ɗin wanna mota face Dr Mark, in baku manta ba ai ya fito da kwari cikin mota mai ɗaukar container. To tin shigowarsu Vir wannan dajin Camera da 3D suka sanya a kofofin shige da fice na dajin ta nuna masu cewa mota ta shigo, da Dr James ya bibiyi su Vir sai ya gane motar jami’ai ne, dan da motarsu na SSO suka fito sakamakon kada ma ƴan sanda su taresu a hanya su ɓata masu lokacin.Ganewa da Dr James ya yi cewa jami’ai ne dik da bai san su waye ne a cikin motar ba, sai ya ce kira Dr Mark a waya, ya ce mashi ya canza hanya akwai matsala a wajen, to shi ne ya zame kansa daga cikinsu. Tsabar 3D sun shahara dik wasu dajukan da suke bi dan aikata ɓarnarsu a hanyar shige da fice sun sanya Camera dan gudun raja irin ta yau, watau ko an so kama su ba zasu kamu ba, Dr James munafuki yana tsaye gaban computer yana kallon komai yana baiwa Dr Mark information kamar dai yanzu.Robar ruwa Vir ya ɗauko, ya fasa ya ɗaɗɗakawa cikinsa rabi sannan ya rufe sauran. A daidai lokacin suka yi kiciɓus da containers ɗin, da karfi direbobin dake jan motocin containers ɗin suka ja birki har motar karshe ta daki wacce ke kusa da ita. Horn suka fara dannawa su Vir cike da takaicin tare masu hanya da suka yi.Kashe motar guru ya yi, suka ɗan kalli juna, Vir ya ƙara kwantar da kansa a jikin kujerar motar, basu yi alamar zasu motsa daga in da suke ba. Ganin haka yasa driver ɗin container gaba ya buɗe ya diro ƙasa, wani shirgegen kato da shi, ga tsawo ga ƙiba, jikinsa a murɗe sosai kamar ɗan dambe, yana wani nishi tamkar wanda ya yi gudu. Cikin takun dake nuna namijin gaske ne ya nufi motar su Vir. Sake kallon juna suka yi kafin su buɗe kofar motocin a tare su fito, lokacin chaskalewa ya yi. Wannan driver na zuwa ya dunkule hannu zai kaiwa guru punch a fuska, ai cikin zafa guru ya rike hannunsa. Vir ya daka tsalle ta kan motar ya kai mashi wani bahagon punch a bayan kunne, Vir bahago ne kaman Lion, sun fi amfani da hannun hagu sama da dama.Ai wannan driver ji ya yi duniya ta tsaya mashi cak, ya ji dukan hannun maza, gabaɗaya jijiyoyin dake baiwa jikinsa jini tsayawa suka yi cak, lokaci guda ya durkushe a kan kafafunsa, jini ya fara fita ta hancinsa saboda duka a bayan kunne ba wasa ba, ko kai da kanka kasa hannu ka ɗan danna bayan kunnenka ta ƙasa gefen kumatu sai ka ji azaba bare IRON FIST su kai maka naushi a wajen ai dole a samu tsayawar jijiyoyon jini.Ganin haka yasa sauran direbobin dik suka diro waje, ɗaya ya gudu da yake ya san basu da gaskiya, biyu kuma suka tsaya, dikkansu kartin maza ne masu rai da lafiya madaka karti, sun horu iya horuwa. Da zafansu suka nufo su Vir, suna wani dam-dam-dam a ƙasa. Tsayuwar jarumta IRON FIST suka yi. Guru ya ce. “Vir ba zan barka ka ji da su in kamo wanda ya gudun nan ba kuwa?”. Kai Vir ya jinjina. “Jeka kamo shi bari in ɗan basu a jikinsu”. Shoulder ɗinsa guru ya buga tare da wucewa ya bi bayan motarsu ya nufi hanyar da wancan driver ɗin ya bi ya gudu. Shi kuma Vir ya gyara tsayuwa yana jiran direbobin su iso.*Jama’ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba’ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

Back to top button