NA
AISHA ALIYU GARKUWA
Hakanne kuwa yasa suka bishi da kallo dukansu harsaida ya b’acewa ganinsu.
Ahankali Rayyern da Ramadan suka dawo da kallonsu ga Mamy wacce itama tayi zugum, da dukkan alama kuma bata da abuncewa.
Naseer kuwa mik’ewa tsaye yayi, kana jikinsa amatuk’ar sanyaye ya kalli Mamy, cikin bayyana godiyarsa agaresu yace.
“Zan tafi Mamy, mungode sosai da karramawarku agaremu nida abokina Riyyam.”
Jin abunda Naseer din ya fad’ane kuma yasa Riyyam ma saurin mik’ewa, tare da cewa.
“Naseer jirani mu tafi asibitin tare.”
Kai Naseer din ya girgiza tare da kama kafadun Riyyam, cikin sanyi yace.
“A’a Riyyam ka zauna, kada kace zaka bini, saboda asibitin Mai-nasara bak’aramin asibiti bane, ko ni da zanje yanzu sainasha tambaya kafun zan iya gano ward d’in da suke, kayi hakuri kaji duk yanda ake ciki zan kiraka awaya Insha Allah ina dai zaka gane hotel ɗin da ka sauka?.”
Kai Riyyam yadan jinjina batare kuma daya soba, haka yabar Naseer ya tafi shi kad’ai.
Ganin fitan Naseer dinne kuma yasa, Rayyern mikewa ahankali, cikin kuma takin dake bayyana nutsuwarsa, ya nufi dakin Abban nasu kai tsaye.
Ajikin k’ofar ya tsaya tare da daura hannunsa akai ya d’anyi knocking.
Daga ciki Abba dake zaune akan wata kujera ya jingina kanshi ya rumtse idanunshi ya bada izinin shigowa.
Ahankali Rayyern ya tura kofar dakin ya shiga, bakinsa dauke da sallama.
Amsa masa sallamar nasa Abban yayi, tare kuma da kafesa da ido.
Shikuwa Rayyern anutse ya karaso ya zauna agaban Abban nasa.
Rank’wafar da kansa k’asa yayi, sannan aladabce yace.
“Kayi hakuri Abba, duk da bansan manufarka ta aikata hakan ba, amma Ina mai rokonka daka bani daman zuwa duba lafiyar Malam Mai-nasara, yau akaron farko yazo hospital dinmu, yana kuma cikin halin buk’atar wanda zai kula da lafiyarsa, dan Allah Abbana kayimin wannan alfarmar, domin kuwa hakkina ne na kula da duk wani marar lafiyar da yazo asibitin mu, aiki na ne hakan, nabawa duk wani marar lafiya kulawa, Dan Allah Abba karkace a’a, domin yin akasin hakan tamkar wulakanta marar lafiya ne.”
Idanu Abba ya lumshe, tare da sakin ajiyar zuciya, domin kuwa Tabbas yasan cewar shi ya d’aura Rayyern din, akan turban da duk yanda abu yake, idan aka rokeka da Allah da Manzon sa to zaka aiwatar.
Yasani kwarai ya gina ƴaƴan nasa, akan tubalin tausayawa duk wani mai neman taimakonsu.
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa akaro na biyu, kana cikin tausasa murya yace.
“Shikenan tunda ka had’ani da Allah Rayyern, kaje ka dubashi, amma iya taimakon daya kamata kawai zakayi mishi, da zaran yaji sauki kuma, ayau nakeso ka sallameshi banason ya kwana acikin asibitin.”
Dagowa Rayyern yayi fuskarsa dauke da murmushin jin dadi, yace “Insha Allah Abba, idan yaji sauki ayau yau zan sallameshi, nagode sosai da wannan alfarmar!”
Kai Abban ya jinjina, kana shikuma batare da wani b’ata lokaci ba ya tashi ya fice daga cikin dakin.
Direct bedroom d’insa ya nufa, Yayinda ya d’auko wayoyinsa da kuma yan k’ananun abubuwan da yasan dole zai bukata.
Koda ya sauko kasa, haka ya samu Mamy Ramadan Riyyam sunyi zugum.
Kallon Ramadan din yayi, cikin yanayin saurin da yakeyi kuma yace.
“Ramadan zo mu tafi hospital din.”
Ai kuwa jin haka yasa Ramadan mikewa cikin sauri, ya marawa Rayyern din baya, kasancewar tuni harya fara tafiya.
Koda suka fito cikin mota d’aya suka shiga, ak’agauce kuma Hadi drivern yaja motar suka fice daga cikin gidan.
Ak’alla saida sukayi tafiyar 17mn, kafun suka iso babban katafaren Mai-nasara Hospital d’in, wanda aka k’awata gininsa kamar ak’asar turai.
Koda driver yayi parking Rayyern baijirayi komai ba, cikin hanzari ya bude murfin motar ya fita.
Yayinda Ramadan ya take masa baya.
Sulaiman da yanzu fitowarsa daga cikin office dinsa, hango Rayyern din da yayine yasashi k’arasowa da sauri.
Rayyern kuwa ak’agauce, batare ma daya bari sun gaisa da Sulaiman din ba yace.
“Awani ward aka kwantar da Malam Mai-nasara?”
“Emergency ne, amma kuma abisa tunanin ba zai samu ganinka yau ba, yasa Manyan ya’yansa suka daukeshi zuwa wani hospital din na daban.”
Idanu Rayyern din ya kankance tare da dafa kansa, dake sarawa da d’an k’arfi yace.
“Shitt! Why Sulaiman? Meyasa bazaka ce musu sujirani ba?”
Kai Sulaiman yad’an girgiza tare da cewa.
“Nakira duka wayoyinka is not available, gashi jikin nasa yana ta tsananta, kuma kaine wanda ya dace ka dubasa, domin mu munyi iya yinmu, yan uwannasa kuma sun kasa hakurin jiran zuwanka, shiyasa suka daukeshi zuwa wani asibitin daban.”
Idanunsa da suka d’anyi ja ya rumtse, saboda Sam ba haka yaso ba, hakika yaso ace shida kansa ya duba mutumin.
Juyawa yayi ya nufi office d’insa, yana maijin ransa duk a jagule, ga kuma ciwon kansa da a yanzun yake sake karuwa.
Koda ya zauna acikin office din, ji yayi gaba daya zaman asibitin ya ishesa, hakan yasa shi tashi ya fito.
Anan yasamu Ramadan ma na shirin komawa gida, saboda yasan sunbar Riyyam shikad’ai acan.
Kamar yanda suka zo kuwa atare suka koma.
Inda Koda suka shigo cikin falon gidan, azaune suka iske Riyyam-nsra kan lallausan carpet din dake malale a tsakiyar falon, agefensa kuwa Mamy ce, Yayinda shi kuwa yake rik’e da wayarsa yana sana’arsa ta chatting.
Saidai kuma duk da chatting din yake, amma bakinsa baiyi shiru ba, labarai kawai yake ta bawa Mamy kala kala, wanda kuma duk rabin labaran nasa akan Mammynsa da kuma Zaytoon abokiyar tagwaicin sa ne.
Mamy dai itakam zamanta da yaron ya sata nishadi sosai, saboda labarai ne na abun dariya yake bata.
Kallon Riyyam-nsra da Mamyn Rayyern yayi, batare kuma da yace wani abuba kaitsaye ya haura sama, saboda so yake yasha magani ya kwanta, ko zai samu relief na headache din dake damunsa.
Ramadan kuwa zama yayi suka sha hiransu, kafun daga bisani ya kama hannun Riyyam din, suka haura dakinsa dake sama.
Acan b’angaren Jannart kuwa, sunyi waya da Salman.
Inda yake shaida mata cewar.
Ya samu information akan sunan hospital din su Rayyern din, da kuma yanda za ayi su samu ganinsa idan sunje hospital din.
Ajiyar zuciya Jannart ta sauk’e adai-dai lokacin da ta zare wayar daga kunnenta.
Cikin kuma halin Kosawa tace.
“Yah Allah Kataimakeni, ka had’ani da wannan mutumin, da nemansa yafi na kud’i wahala, mutum shiba Diamond ba amma ace wai ganinsa ya zama aiki, yau shine can Gobe shine nan, wai dole saikabi wasu matakai kafun ka iya ganinsa, babban ma abun takaicin shine Kwata-kwata, ko a social media babu wani information akansa, baya Facebook baya Instagram only Twitter kawai, still kuma a Twitter dinma, babu wani information akansa, ko hotonsa babu.”
Yar siririyar tsuka taja, tare kuma da turo dan karamin bakinta gaba, kana ashagwab’e tace.
“Idan ma ba munafurci ba da rashin gaskiya. Meyasa yake boye kansa, da har za’ace kwata-kwata babu wanda ya tab’a ganin fuskarsa? A jaridu ko a TV Maybe ma shidin irin ɗima-ɗiman alhazawan nanne masu tafiya da kyar da kuma katon ciki ne, shi yasa yake boye kansa.”
Momy dake tsaye abayanta ne tace.
“Lafiyarki kuwa Jannart keda wa kike ta tashin k’ananan maganganu?”
Juyowa tayi tare da Kallon Momyn kana ta kwab’e fuskarta.
“Momy aiki aka bani a office, gashi kuma aikin sai wahalar dani yakeyi.”
Ta kare maganar tana me zare earpiece din dake kunnenta.
Dan Murmushi Momy tayi hade da cewa.
“To Allah Ya baki sa’a, amma dai yanzu kam ki ajiye aikin kitchine dinnan haka kije ki huta, zan karasa dafa pepper meat din da kika fara.”
“To Momy.”
Tafad’a a sanyaye tare da ajiye baban spoon din dake hannunta.
Momy kuwa da kallo ta bita harta gama ficewa daga cikin kitchine din, Allah yasani duk da cewar ba itace ta ta haifi yarinyar ba, amma tana matuk’ar so da tausayinta.
Saboda yanda rayuwar yarinyar yake cike da sarkakiya mai daurewar hankali da tunani.
Wanda kuma ita kanta haryau ta kasa gano gaskiyar hakikanin abunda ke boye.
Jannart kuwa Koda ta fito daga cikin kitchine din, anutse take tafiyar ta batare kuma da ta lura da Yah Junaid dake zaune acikin falon yana shan shisha ba, direct ta wuce bedroom dinta.
Dan dauro alwalan sallan Magriba.
Junaid dake zaune kuwa da idanunsa yabi manya manyan hips dinta harsai da ta b’acewa ganinsa,
(Yana ɗaya daga cikin illolin da sa suturun banza suke jawa ɗiya mace, koda kuwa a cikin gidanku ne).
Kafun ya iya rumtse idanunsa, tare da shakawa cikinsa hayakin shisha.
Allah Yasani yana matuk’ar so da buk’atar kanwartasa fiye da komai aduniya.
Domin akanta yakanji kamar ana ingiza sa kowacce rana.
Haka kuma idan dai zai ganta sau dubu da irin shigar data zame mata ɗabi’arta to Tabbas zaiji sha’awarta sau dubu yanayin shigarta ke ingiza lafiyar samartakarsa.
Mikewa tsaye yayi kamar zai bi bayanta kuma sai ya fasa, tare da komawa ya zauna ya cigaba da bankawa cikinsa hayakin shisha, duk da kuwa yanajin ana kiran sallan magriba, amma haka yayi biris tamkar ba yaji.
To dama sallan bawani damunsa tayi ba.
Acan gidansu Rayyern kuwa har akayi sallan Isha suna tare da Riyyam.
Wanda kusan atare ma sukaje masallaci sukayi sallan magriba dana isha.
Yanzu ma kammala dinner dinsu kenan, Riyyam din ya mike tsaye, tare da duban Abba da Mamy.
Cikin girmamawa yace.
“Abba Mamy zan koma masaukina, na kuma nagode da karramawarku sosai.”
Ramadan dake zaune ne ya rik’o hannunsa tare da fadin.
“Haba Riyyam-nsra a daren nanne zaka koma hotel, please ka kwana anan mana, ai duk munzama daya….”
Sauran maganan dake bakin nasane ta makale amakoshinsa, sakamakon mummunan kallon da yaga Abba ya watsa masa.
Shikuwa Riyyam-nsra da bai lura da Kallon da Abban yayiwa Ramadan dinba, murmushi yayi.
Kana cikin nuna godiyarsa yace.
“Kayi hakuri Hamma Ramadan watarana ai Zan dawo.”
Kai Ramadan din ya jinina, Cikin waskewa kuma yace.
“Shikenan ba matsala To muje na saukeka.”
Saida safe Riyyam din yayiwa Mamy da Abba, inda suka amsa masa amutumce.
Kallon Rayyern dake zaune Riyyam din yayi, kana ya dan rankwafo ya rungumesa, cike da k’aunar Rayyan din da yakeji acikin zuciyarsa yace.
“Saida safe Hamma Rayyan.”
Kai Rayyern din yadan jinjina masa.
Yayinda Ramadan kuwa ya kama hannun Riyyam-nsra din suka fice.
Saida suka hau titi ne kuma Riyyam-nsra din yake fadawa Ramadan hotel din da zai kaisa.
Yayinda acan gidannasu kuwa , bayan tafiyar su Ramadan din Rayyern tashi yayi ya wuce bedroom d’insa.
Wanka yayi bayan ya fito ne kuma ya d’auki system d’insa, ya soma latsawa, Yayinda akai akai yake saka nutella chocolate abakinsa.
Agaban babban Hotel din na Taheer Guest Palace Ramadan ya sauke Riyyam, tare dayin exchanging phone number atsakaninsu.
Bayan kuma Ramadan din yace da Riyyam Gobe yazo suyi breakfast tare ne, suka sakeyin sabuwar sallama, Yayinda Riyyam kaitsaye ya wuce cikin hotel din.
Shikuwa Ramadan juya akalar motarsa yayi zuwa gida.
12:30 am dai-dai Rayyern ya kashe laptop dinnasa, tare da mirginawa ya kwanta akan gadonsa.
Wanda daga zaman nasa awajen zuwa yanzu yashanye fiye da rabin Kwalban Nutella chocolate.
Idanunsa yadan lumshe saboda yanda yakejin bacci na game cikinsu.
Sannu Ahankali kuma ya soma ambaton sunan Allah ahaka har baccin ya daukesa.
Acan sashin Riyyam-nsra kuwa, koda ya shiga dakinsa na hotel din, haka ya tarar da komai nead.
Wanka yayi tare da zuwa ya fada kan gado, hade da jawo wayarsa ya runguma, bayan ya kunna data ne kuma ya shiga whatsapp sama sama yayi chatting acikin whatsapp din, kana daga bisani kuma ya dawo ta inda yafi karfi Wato Tiktok.
Atakaice dai saida yakai kusan 2am yana sheke ayarsa kafun bacci barawo ya daukesa, haka kuwa yayi baccin yabar data d’insa akunne.
Washegari.
Kamar koda yaushe yauma 7:30 am ya gama shirya kansa tsab, cikin royal high quality black suit, tare da white long sleeve wacce tayi masa kyau sosai.
Kasancewarsa mai kyau ne kuma shiyasa komai ya saka saiyayi masa kyau.
Ahankali yake saukowa daga kan steps din falon, Yayinda briefcase d’insa ke rike ahannunsa na dama.
Mamy dake tsaye tana shirya dining table ne ta dago ta kalleshi.
Ɗan guntun Murmushin gefen baki yayi, wanda ya ɗan bayyana fararen haƙoransa, kana cikin nitsuwa yace.
“Good morning Mamyna.”
Murmushi itama Mamyn tayi, cike kuma da soyayyarsa tace.
“Morning My beautiful son, kafito a dai-dai maza zokayi breakfast dinka.”
Karyar da wuyansa gefe yayi, tare kuma da duban agogon hannunsa.
Muryarsa adan sanyaye yace.
“I’m sorry Mamyna yau sauri nakeyi, amma idan Ramadan yazo fita ki hada masa breakfast dinnawa a basket ya kaimin office.”
Murmushi Mamy tayi tare da cewa.
“To ba matsala adawo lafiya Allah ya tsare ya kuma bada sa’a.”
Da “Ameen.” Ya amsa kana cikin jin dadi ya Sakai ya fice daga cikin falon.
Dai-dai fitowarsa compound din gidanne kuma, Riyyam da Ramadan suka shigo atare.
Cikin sauri Riyyam ya karaso, tare Da dan rungume Rayyern din, fuskarsa dauke da Murmushi yace.
“Good Morning Hamma Rayyern!”
Idanu Rayyern din yadan lumshe tare dasa hannu ya shafa kan Riyyam din, cikin kuma yanayinsa na rashin sabo dayin magana yace.
“Morning Riyyam, Ina fata kunyi waya da Naseer yau, ya jikin Malam din?”
Kai Riyyam din ya jinjina tare da fadin.
“Eh munyi waya dashi, ya kuma tabbatarmin cewa jikin Malam din da sauki.”
Kai Rayyern din ya jinjina tare da cewa.
“Okay bani numbern Naseer din.”
Yafada yana me mikawa Riyyam wayarsa dan yasa masa numbern Naseer.
Ramadan kuwa kai ya jinjina cike da gamsuwar lallai Hamman nasa ya dauki lamarin malam da matuƙar mahimmanci.
Hakan kuwa akayi domin cikin abunda bai wuce 1mn ba Riyyam ya sakawa Rayyern din numbern.
Ramadan kuwa dake tsaye fuskarsa dauke da dan mamaki yace.
“Hamma Rayyern me zakayi da numbern Naseer kuma?.”
“Zanje na duba Malam Mai-nasara ne, tunda har Abba ya a mince dana dubasa din, tofa Tabbas saina duba sa, zan kira Naseer din idan basa hospital har gidansa zanje na dubasa.”
Rayyern din ya fada in full confidence.
Ramadan kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, sai kuma suka hada baki atare shida Riyyam wajen cewa suma zasuje gidan Malam Mai-nasara din.
Kansa kawai ya kad’a, adai-dai kuma lokacin da yake shiga cikin motarsa yace.
“Okay nidai yanzu hospital zan wuce, sai Idan na tashi ne zan biya can gidan nasa, amma idan kuna da chance zaku iya zuwa maybe mu hadu acan .”
Yana gama fadan hakan yaja murfin motar ya rufe, batare kuma daya saurari mai zasu sake cewa ba, yasa Hadi driver yaja motar suka bar wajen.
Su kuwa Ramadan da Riyyam kaitsaye cikin gidan suka wuce.
Koda suka karasa cikin falon Riyyam aladabce ya gaishe da Mamy da kuma Abba wanda yake yanzu fitowarsa daga daki.
Cikin farincikin ganinsa Mamy ta amsa, Yayinda Abba ma ya amsa masa fuska asake.
Anan kan dining table sukayi breakfast.
Bayan kuma sun kammala ne Riyyam da kansa ya gyara wajen, tare da kai plates din da suka bata kitchine ya wanke.
Mamy kam cike da mamaki take kallonsa, domin kuwa duk da ta hanashi saida yayi, inda yake bata labarin cewa ai yanayiwa Mammynsa ma, saidai watarana dagangan sai yakiyi dole Zaytoon ce zatayi.
Mamy dai itakam dariya kawai takeyi, saboda daga jiya zuwa yau din kawai, zama da yaron ya zame mata sabo.
Abba kuwa ido ya zuba musu da inda yake zaune can tsakiyar falon yana nazartar ƙarfin halin Riyyam-nsra da shisshiginsa garesu anya kuwa!?.
Ya ɗiga ayar tambaya a kan yaron.
Acan hospital kuwa Rayyern bayan yadan duba wasu daga cikin patients dinsa ne, ya d’auki waya ya kira Naseer.
Bayan sungaisa ne kuma yake tambayar Naseer din, jikin Malam Mai-nasara.
Tofa ananne Naseer din yake fada masa cewar.
“Ajiyan ankai Malam din Zanna Hospital, amma kuma an sallamosu Yanzu dai Malam din yana gida, kuma babu laifi jikin da d’an sauki. “
Kai Rayyern din ya jinjina, tare da cewa Naseer din ya turo masa adireshin gidan Malam din zaizo anjima.
“To.” Naseer din ya fada cikin minti kadan kuwa ya turowa Dr Rayyern din, da text message na address din gidan Malam Mai-nasara.
12: am dai-dai Rayyern ya kammala duk wani abu abunda yakeyi acikin hospital din.
Haka ya fito daga cikin office dinnasa yana taku cikin nitsuwa da kuma zarransa dake kara bayyana kwarjininsa da haiba na cikakken da na miji.
Kaitsaye compound din asibitin ya nufa, yana zuwa kuwa ya shige cikin motarsa batare da bata lokaci ba, driver yaja motar suka fice daga cikin asibitin gaba daya.
Bayan sun hau titi ne kuma drivern ya juyo yadan kallasa, kana aladabce yace.
“Ranka ya dad’e Ina muka nufa?.”
“Hausawa sabon titi.” Ya fada atakaice.
Tare da sanya hannu ya zare glass din dake manne a idanunsa.
A dai-dai wannan lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer ne, acikin motar Ramadan din kirar Range rover velar 2019, inda suma kaitsaye suka nufi Unguwar ta Hausawa sabon Titi, wanda suna tafiyar ne kuma bisa jagoran Naseer.
After some 20mn suka iso gaban wani gate din makeken gida mai tsananin kyau da girma.
Wanda kuma yake nanne gidan Malam Mai-nasara.
Horn Ramadan dake driving ya danna.
Jin karan horn dinnasa ne kuma yasa maigadi, Dan lekowa ganin dalleliyar motar da yayi ne da kuma Naseer a gaba ne yasashi karasawa da hanzari ya wangale babban farin gate din.
Wanda hakan ya bawa Ramadan daman tura kan motar tasa ciki.
Wanda shigansu cikin gidan kuwa. yayi dai dai da wani irin masifeffen bugawar zuciyoyin Riyyam-nsra da Ramadan.
Kokarin maida gate din maigadin yasomayi saidai kuma ganin wata dakekkiyar motar again BMW ta faso kaine, yasashi wangale gate din.
Inda matukin motar ya tura hancin motar ciki.
Wanda saukan tayoyin motar acikin gidan, yayi dai-dai wani irin azabebben harbawa da zuciyar Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yayi.
Cikin wani irin matsanancin faduwar gaban da yakeji, da kuma dukan da zuciyarsa keyi ya bud’e idanunsa inda ya saukesu A…!
Akan motar su Ramadan, wanda tuni Naseer ya fito daga cikinta, Yayinda Ramadan da Riyyam ke kokarin fitowa suma.
Tsumammun eyes d’insa masu dauke da wasu sinadarai na musamman ya lumshe, tare da sanya hannu ya dafe dai-dai saitin zuciyarsa.
“Yah Allah kabani nutsuwa, k’arfi da kuma k’warin guiwa ako da yaushe!”.
Yafad’i hakan acan k’asar zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri.
Kwata-kwata baisan meyasa agaba d’aya y’an kwanakin nan, zuciyarsa ke yawan harbawa da k’arfi ba.
Saidai kuma koma meye yana fatan ya zame masa alkhairi.
Bud’e murfin motar yayi ahankali tare da zuro kyakyawan k’afafunsa waje.
Dai-dai lokacin da ya gama fitowa acikin motar kuwa, su Ramadan da Riyyam suka k’araso.
Riyyam-nsra kuwa da murmushi ya kasa buya akan fuskarsa ne yace.
“Laa Hamma Rayyern kaima ka iso?”
Kai Rayyern din ya jinjina masa alaman.
“Eh.”
Naseer kuwa dake tsaye agefe, wayarsa ya zaro tare da dannawa lambar Uncle Mustapha (Kawunsa, yayan mamansa) kira.
Bugu daya kacal kuwa Uncle Mustapha ya d’aga wayar.
Jin an d’aga wayanne kuma yasa Naseer cewa.
“Uncle Mustapha gamu nan cikin compound tare da Dr. Rayyern din dana gaya maka cewa zaizo ya duba jikin Malam.”
Uncle Mustapha dake zaune acikin falo, kuwa saurin mikewa tsaye yayi, batare kuma daya katse wayan ba yace.
“Masha Allah to Naseer ka shigo dashi mana, ku shigo ku shigo.”
Yanayin yanda yayi maganar yana me nufar hanyan fita daga cikin falonne kuma, yasa sauran yan uwansa dake zaune acikin falon suka dan kalleshi.
Daga waje kuwa Naseer ne ya kalli Rayyern din, hade da cewa.
“Hamma Rayyern mu shiga..”
Bai gama rufe bakinsa ma baiyi ba, saiga Uncle Mustapha d’in ya fito, fuskarsa dauke da yalwatacciyar murmushi ya soma takowa inda su Rayyern din suke.
Idanu Rayyern da kuma Ramadan suka ɗan zuba mishi.
Kamar kuwa yanda suka zuba mishi idanu, haka shima ya zuba musu nashi idon, musamman akan Rayyern da kuma Riyyam, wani irin kallo yake musu mai dauke da mamaki, da kuma yanayi mai bayyana alhini., ciki kuwa harda fuskar Ramadan da yakewa kallon ya taɓa sanin mai irin fuskar farin sani.
Isowar Kawu Mustapha’n kusa da sune kuma yasa, duk tunanin da suke suka tsaya cak.
Hannu Rayyern ya mik’awa kawu Mustaphan, wanda shima ya mik’o masa nasa hannun fuska asake, sukayi musabaha.
Bayan sun gaisa da Rayyern dinne kuma, Kawu Mustapha’n ya bawa su Ramadan da Riyyam-nsra hannu suka gaggaisa.
Cikin kuma yanayin dake bayyana zallar farinciki da mutum tawa, Uncle Mustapha’n ya dubi Rayyern, kana atausashe yace.
“Masha Allah Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara barkanka da isowa.
Cikin ikon Allah Jiya iwarhaka munata fama da neman damar yanda za’ayi muganka, sai gashi kuma yau kaida kanka ka tako k’afarka izuwa inda muke, kai Masha Allah sannunku ku iso mu shiga daga ciki.”
Murmushi Rayyern yayi kana anutse yabi bayan, mutumin da ayanzu kawai ya shaida da karamcinsa.
Su Ramadan ma rufa musu baya sukayi, Yayinda Riyyam ke tafiya yana k’arewa katafaren gidan kakan abokin nasa kallo, wanda aka matuk’ar k’awatasa, kasancewar kuma gidan nada part-part da yawa ne, shiyasa ya zama kamar wani mention, Yayinda Kota ina dake cikin gidan, aka cikasa da shuke shuken korayen trees.
Isowarsu bakin kofar da zai sadaka da babban falon dake cikin gidanne, yasa Rayyern d’an lumshe idanunsa, saboda hakan yaji harbawar da zuciyarsa keyi na sauk’a, Yayinda zuciyar tasa kuma keyi sanyi.
Haka kuma yakejin wani irin abu na ratsa cikin tafukan hannaye da k’afafunsa.
Kasancewar kuma shike bayan Uncle Mustapha dinne, yasa shiyayi na biyun shiga cikin falon, da girmansa yayi a had’a manya manyan faluka guda biyu awaje daya.
Taka k’afarsa ta dama da yayi acikin falon kuwa, shiya sanya shi jin wani irin sanyi na game duk jikinsa.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali, wanda yayi dai-dai da sauk’e ajiyar zuciyar Ramadan da kuma Riyyam-nsra suma duk alokaci daya.
Kamar kuma yanda Rayyern din yaji azuciyarsa, haka suma sukaji.
Shigowarsu cikin falonne kuma, yasa gaba d’aya ahalin Mai-nasara da y’ay’a da kuma jikokinsa dake kewaye dashi, duk suka d’ago kai suna kallonsu.
Atake kuwa tsananin mamaki da tu’ajjudi ya bayyana akan fuskar wasu manya daga cikin mazauna falon.
Inda suka kafe su Rayyern din da ido, basa ko k’yaftawa, hakan yafaru ne kuma saboda wani tsananin kama da suka hango.
Kawu Mustapha ne yadanyi murmushi saboda Kallon da yaga y’an uwannasa nayiwa su Rayyern, wanda kuma shima yasan dalilin da yasa y’an uwannasa ke kallonsu haka.
D’an juyowa yayi ya fuskanci y’an uwannasa cikin kuma bayyana farin cikinsa yace.
“Manyan bak’i mukayi, domin babban Doctor din da ya shahara, ya kuma yi kaurin sunane da kansa yazo dan duba Malam, Wannan shine Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.”
Yakai karshen maganan yana meyi musu nuni da Rayyern dake tsaye.
Ajiyar zuciya suka sauke gabaki d’ayansu tare kuma da had’a baki wajen yiwa su Rayyern din iso.
Karasa shigowa cikin falon su Rayyern din sukayi, kana kuma cikin girma da mutumtawa Rayyern ya shiga bawa, manyan mazan dake zaune acikin falon hannu suka soma gaiggaisawa.
Kowannensu fuskarsa dauke da murmushi.
Bayan kuma sun gama gaisawa da Rayyern dinne, su Ramadan suma suka matso suka gaggaisa dasu.
Yayinda Rayyern kuwa ahankali ya sauk’e idanunsa akan fari kuma kyakkyawan Dattijon dake kwance, wanda ayanzu ya soma d’an yunkurin tashi, musamman saboda jin shigowar su Rayyern din.
Dattijo ne mai matuk’ar kamala, mutumci da kuma haiba, haka kuma duk da yana da yawan shekaru da y’ay’a, amma hakan baisa tsufansa ya yawaita ba sabida hasken Addini da riƙo da ibada.
Idanu Rayyern yadan lumshe tare kuma da budesu alokaci guda, yana me ambaton sunan Allah da ya sauk’ar masa da wata iriyar nutsuwa, acikin y’an mintunonin da basu wuce 5 ba.
Su Uncle Mustapha kuwa ganin Malam Mai-nasara dake kishingid’e akan lallausa kuma tattausan sofa, na kokarin tashi zaune ne, yasa cikin tsananin kulawa da kuma kauna suka taimaka masa ya tashi zaune.
Idanu Malam Mai-nasara din ya zubawa kyakkyawan matashin saurayin dake dan nesa dashi wato Rayyern.
Wanda kuma shima Rayyern din kallonsa yakeyi.
Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin sanyi, da kuma rauni mai tsananin gaske.
Ga kuma wani abu da yakeji na game dukkan mashigan ramin iska dake jikinsa.
Yanaji ajikinsa tamkar wata duniya ce sabuwa ya shigo.
Yayinda Ramadan da Riyyam dake bayansa suma sukejin thesame irin abunda Hamma Rayyern dinnasu yake ji.
Wanda kuma bawai iya sukad’aine sukejin hakan ba, harda shi kansa Malam Mai-nasara, domin kuwa har izuwa yanzu ya kasa dauke idanunsa daga kan Rayyern.
Sannu ahankali kuma ya d’aga hannunsa tare dayin alama akan Rayyern d’in yazo kusa dashi.
Aikuwa Rayyern din kamar jira yake, cikin nutsuwar da ya zame masa jiki, ya matso kusa da Malam din sosai, hakanne kuwa ya bawa Malam din daman kamo hannun Rayyern d’in ya rik’e acikin nasa.
Nannauyar ajiyar zuciya mai sauti suka sauƙe atare shida Rayyern d’in, saboda had’ewar hannayensu waje d’aya shiya haifar da daidaiton bugun zuciyoyinsu.
Kai Dr. Rayyern ya d’an rank’wafar cikin kuma muryarsa mai tsananin taushi, dake bayyana nitsuwa da mutumtawarsa ga Dattijon mai tsananin karama a idanunsa yace.
“Malam barka da rana, ya ƙarfin jikin naka?”
Idanu Malam Mai-nasara ya lumshe tare dajin wani irin sanyi acikin zuciyarsa, wanda lokaci guda ta d’auki soyayyar Rayyern din ta ajiye awani waje na musamman.
Tabbas fuskar Rayyern din ta ratsa shi, Yayinda ta kuma so tono masa wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya masu yawa.
Sake rik’e hannun Rayyern din da kyau yayi, tare da cewa.
“Alhamdulillahi jikina da sauki, kaine Dr. Rayyern Basheer Muhammad Mai-nasara ko?”
Kai Rayyern ya jinjina masa, tare kuma da cewa.
“Eh Malam ni ne Dr. Rayyern Basheer Muhammad Mai-nasara.”
Ya kare maganar yana me fadada murmushin dake kwance akan fuskarsa, tayaya ma zai iya boye farincikin da yake ciki ayau din? Bayan gashi ga mutumin da yake matuk’ar so da kauna, fiye da duk sauran Malama’n da yake sauraran wa’azinsu, Dattijon da yake son gani akullum, kana Dattijon dako kallonsa yake acikin tv ko laptop yakanji sanyi acikin zuciyarsa.
“Alhamdulillahi! Masha Allah!! Lallai godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai!!!”
Malam din ya fad’a adai-dai lokacin daya sauke idanunsa akan Ramadan da kuma Riyyam, wanda suke gaidashi.
Fuskarsa cike da tsananin mamaki ya amsa musu, tare kuma da dawo da kallonsa ga Rayyern dake zaune agabansa, har yanzu kuma suna rik’e da hannun juna.
Rayyern kuwa ganin irin Kallon da Malam din keyi masa ne, yasashi yin ƙasa da kanshi.
Malam Mai-nasara kuwa, fuskarsa dauke da mamaki yace.
“K’annanka ne?”
Kai Rayyern din ya jinjina, cikin halinsa na girmamawa kuma yace.
“Eh k’annena ne, wannan Ramadan, k’aramin kuma shine Riyyam.”
Idanu Malam Mai-nasara yadan lumshe hade kuma da jinjina kansa, Cikin yanayin gamsuwa kuma yace.
“Masha Allah. Allah Ubangiji ya d’ayyabaku ya kuma ci gaba da rayaku cikin aminci dajin dad’i amman Riyyam kuma sunane cikekke!?.”
Da “Ameen.” Gaba d’aya falon suka amsa.
Kana Ramadan da Rayyern kuma suka ɗan kalli, Riyyam-nsra.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
“Cikekken sunan *Zakariyyah* ne”.
Murmushi Malam dasu Uncle Mustapha sukayi, wato sunan gayu ko?.
Malam yace cikin barkwanci.
Murmushi ya kumayi tare da gyaɗa mishi kai.
Gyara zama Rayyern yayi, tare da fuskantar Dattijon, kana atausashe yace.
“Malam yanzu inada inane yake maka ciwo? sannan yakakejin yanayin ciwon naka idan ya tashi?”
Idanu Malam Mai-nasara yad’an lumshe, tare kuma da tankwashe kafafunsa waje daya.
Ahankali kuma yace.
“Sau dayawan lokuta nakanji ciwon kaine kawai maitsanani, sai kuma jiri amma ba wani mai yawa ba, baya ga haka kuma sai k’afafuna da idanuna wanda nakejin watarana sunayi min nauyi, da kuma zazzab’i, amma dai yanzu kam Alhamdulillah jikin nawa isashshen k’arfi ne kawai babu.”
Ajiyar zuciya Rayyern ya sauk’e, tare da kuma gyara zamansa, kana anutse yace.
“Eh kamar dai yadda su Dr Sulaiman suka shaida min cewa.
Hawan jini da kuma ciwon sugar ne ke damunka Malam a binciken da sukayi maka, kuma hakanne.
Domin shi yawan ciwon kai da kuma jiri hadi da zazzab’in da kakeji duk alamane na hawan jini, sannan kuma shi yanayin ciwon kan yakan iya sauyawa, domin watarana zakaji ciwon agefen kanka ta b’ari d’aya ne, watarana kuwa zakaji ciwon kan asaman goshinka ne, wanda idan yayi karfi har yakan iya sauk’owa ya rik’e jijiyoyin idanun mutum, wannan duk cases ne da hawan jini kan haifarwa, shi kuwa nauyin da kakejin k’afafu da kuma idanunka nayi da yawan haɗa zufa, suma alamace ta ciwon sugar, wanda kuma suma bako da yaushe ne suke tashi ba, domin zaka iyajin hakan da safe, kafun zuwa rana kuma sai kaji abun ya lafa, baya ga haka kuma zaka iyajin hakan da yamma idan maraice ya rufa, sannan kuma akwai yawan fitsari da zakaji kanayi akai akai, koda kuwa ace baka sha wani ruwa mai yawa ba da jin kamar wani abu na bin jikinka…”
D’an numfasawa yayi kana ahankali ya sake rike hannun Malam Mai-nasara daya zuba masa idanu yana mai gyaɗa mishi kai alamun duk abinda ya faɗa hakane.
Atausashe yace.
“Insha Allah zaka samu sauki Malam, sannan kuma ciwon naka bai wani zama abun tashin hankali ba, saboda mafi akasarin mutane suna samun hakan idan girma ya cimmusu, kamar dai kai ayanzu daka tara manyan y’ay’a da jikoki, akwai kuma magunguna da zan rubuta maka, wanda zasu taimaka k’warai wajen kawo maka Sauk’in ciwon, sannan kuma akwai kalolin abincin da ya kamata ace su zakana ci, saboda zasu bada nasu taimakon sosai wajen Inganta lafiyar jikinka.”
Gaba d’aya falon kai suka jinjina cike da gamsuwa akan abunda Dr. Rayyern din ya fad’a.
Shikuwa Dr.Rayyern abun rubutu ya ciro daga cikin aljihunsa, tare da wata yar farar takarda.
Rubutu yayi asaman takardar bayan kuma ya kammala rubutun ne yayi sign acan k’asan takardar.
Alhaji Ibrahim wato babban dan Malam Mai-nasara din dake gefe kad’an ya mik’awa takardar, tare da cewa.
“Way’annan sune magungunan da ya kamata yana shansu a koda yaushe, Insha Allah zai samu lafiya nan bada jimawa ba.
Karb’an takardan Alhaji Ibrahim din yayi, tare da yiwa Rayyern d’in godiya maitarin yawa.
Saidai kuma baikai ga ida godiyar tasa ba, muryarsa ta mak’ale a kasan makoshinsa, sakamakon daura idanunsa da yayi akan sign din da Dr. Rayyern din yayi acan kasan paper’n.
Idanu ya k’urawa sign din cike da ɗan mamaki hadi da al’ajabi, ya d’ago ya kalli Baban nasu, wato Malam Mai-nasara da kuma sauran y’an uwansa.
Cikin tu’ajjudin da yake ciki dinne kuma direct ya mikowa Malam Mai-nasara din takardan.
Aikuwa Malam Mai-nasara na karb’an takardar idanunsa suka sauk’a akan signing din dama salon rubutun kanshi.
Cike da mamaki wanda har saida ya kasa b’oye hakan ya d’ago ya kalli Rayyern.
Rayyern kuwa da Sam bai fahimci komai adangane da irin Kallon da yaga sunayiwa takardar ba, kwata kwata sam baidamu ba.
Saima juyowa da yayi ya kalli Ramadan.
Cikin kuma bada umarni yace.
“Yauwa Ramadan yanzu amshi takardar sunayen magungunan Malam ɗin kaje ka d’auko masa a pharmacy.”
Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa.
“To.”
Cikin abunda bai wuce 2 minute ba kuwa Uncle Mustapha ya miƙawa Ramadan takardar sunayen magungunan.
Hakan yasa batare da wani b’ata lokaci ba, Ramadan din ya juya ya tafi, dan d’aukowa Malam din magungunan da zai nasha.
Bayan fitar Ramadan dinne kuma, Naseer ya kama Hannun Riyyam-nsra suma suka fice daga cikin falon.
Haka kuwa mutanen dake cikin falon suka dinga fita daya bayan daya.
Hardai saida falon ya rage daga Malam Mai-nasara sai Rayyern da kuma Uncle Mustapha, Alhaji Ibrahim, da kuma dayan kaninsu mai bimusu Alhaji Abdallah.
Alhaji Abdallah’n dinne kuma ya kalli Dr.Rayyern kana cikin sakin fuska yace.
“Masha Allah Dr. Rayyern munji dadin zuwanka k’warai, mun kuma gamsu da duk wasu bayanan da kayi mana, amma kafun zuwan ka da har mun gama yanke shawarar cewa zamu fitar da Malam din waje, can k’asar Egypt, Saboda ya samu kyakkyawar kulawa, amma dai yanzu Alhamdulillah tunda ga kanan, domin dama da way’anda zamu gani acan din da kuma kai d’in duk abu daya ne.”
Murmushi Rayyern yayi, kana anutse yace.
“A’a basai an fitar dashi ba, sauk’i na Allah Ne kuma Insha Allahu zai samu lafiya.”
“Allah Yasa.” Duk suka amsa cike da gamsuwa.
Yayinda Uncle Mustapha yad’an muskuta had’i da cewar.
“To Dr. Rayyern ka fad’amana kud’in maganin sainayi maka transfer ko.”
Kai Rayyern d’in ya girgiza, tare da hade kafafunsa waje daya ya tankwashe su.
Hannunsa na dama ya d’aura akan na Malam d’in, Cikin yanayin mutumtawa yace.
“A a ku barshi banzo nan dan abiyani ko sisin kobo ba, haka kuma duk wani magani dana sa Ramadan ya kawowa Malam banyi hakan dan abiyani ba, Malam mahaifi ne agareku ni kuma Kaka ne agareni, saboda haka komai da nayiwa Malam nayisa ne saboda matsayi da kuma darajarsa, fata na dai shine Allah Yabashi lafiya.”
“Ameen Summa Ameen.” Gaba ki d’ayansu suka had’a baki wajen fad’an hakan, Yayinda suka sake shaida mutumci, karamci da kuma kyakkyawar tarbiyar da Rayyern din ya samu, Lallai acikin zuk’atansu sun gamsu da cewar Rayyern d’in mutumin k’warai ne, wanda kuma ya taso a hannun iyayen k’warai.
Shikuwa Malam Mai-nasara murmushi ne ya fadada akan fuskarsa, domin kuwa alokacin da yaji Rayyern din ya kirasa da sunan Kaka, bakaramin sanyi yaji acikin zuciya da gangar jikinsa ba, Lallai Tabbas shima ya d’aukesa amatsayin jikansa.
Hannunsa na dama ya d’aura akan Rayyern d’in, Cikin kuma yanayin nuna godiyarsa agaresa yace.
“Masha Allah Allah Ubangiji yayi maka al’barka Rayyern, ya tsare gabanka da bayanka, ya kuma dauwamar da farinciki acikin zuciyarka da na ahalinka.”
Da “Ameen.” Duk suka amsa.
Inda Malam din ya sake d’ago Kai ya kalli Yayan nasa, cikin aminci yace.
“Tabbas Dr. Rayyern ya gwada mana karamcinsa, saboda haka kamar yanda ya daukeni amatsayin Kaka nima na daukesa amatsayin jikana, zan kumayi masa kyauta da karamci kamar yadda yayi mini, Ibrahim shiga cikin dakina, ka bude wajen da nake ajiye kayana na musamman ka d’auko masa sabbin alkyabba da hirami.”
Murmushin farinciki dukansu sukayi inda Alhaji Ibrahim kuwa ya mik’e cikin girmama maganan mahaifinnasu kaitsaye ya nufi dakin Malam Mai-nasara din dake cikin falon.
Har yakai bakin kofarne kuma ya juyo tare da Kallon mahaifin nasu, kana aladabce yace.
“Malam alkyabba da hiramin guda nawa za’a d’auko masa?”
“D’auko masa kala bakwai, saboda zasu fi isansa domin zai saka guda daya acikin kowacce rana, Kaga kenan kala bakwai zasu isar masa har sati guda yana sawa yana tunani.”
Kai Alhaji Ibrahim ya jinjina, tare da bud’e kofar dakin mahaifinnasu ya shige.
Cikin abunda bai wuce mintuna goma ba, kuwa sai gashi ya dawo hannayensa dauke da manya manyan alkyabba, da hirami irin wanda limaman makka suke sakawa ajikinsu, alkyabbu ne masu kyau da kuma tsadar gaske.
Mikawa Malam din Alhaji Ibrahim yayi, Yayinda shikuwa Malam din ya mikawa Rayyern dake zaune, wanda fara’a da kuma farincikinsa ya kasa b’uya.
“Wannan kyautace agareka Rayyern domin kuwa nasan zasuyi maka kyau sosai, shigace irin ta kamala.”
Kai Rayyern ya jinjina cike da tsananin jin dad’i kuma yace.
“Godiya nake maitarin yawa Malam, Allah ya kara arziki da lafiya.”
“Ameen.” Malam Mai-nasara din ya amsa cikin jin dadi.”
Dai-dai lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer suka shigo cikin falon.
Karasowa Ramadan yayi ya mik’awa Hamman nasu babban ledan magungunan dake hannunsa.
Karb’an magungunan Rayyern yayi, hade kuma da mik’awa Ramadan alkyabba bakwai din daya same su amatsayin kyauta daga Malam.
“Kyauta na samu daga wajen Malam.”
Yafad’a adai-dai lokacin daya gama mikawa Ramadan din kayan.
Idanu Ramadan din yadan zaro fuskarsa cike da tsananin farinciki yace.
“Masha Allah Malam godiya muke.”
Hararan wasa Rayyern ya watsa masa, kana cikin sigar tsokana yace.
“Godiya muke kaman yaya, nawa nefa ba namu ba.”
Dariya kusan gaba dayansu suka sa, ciki kuwa harda Malam.
Riyyam kuwa jin hakanne yasashi, d’an shagwab’e fuska, tare da matsowa kusa da Malam din yace.
“Ayyah Kaka Malam toni Ina nawa alkyabban.”
Murmushi Malam Mainasara yayi, tare dasa hannu ya shafa kan Riyyama din.
“Kaima taka tananan tana jiranka amma sai ka ƙara girma, yanzu idan na baka yawa zasuyi maka.”
Malam din ya fada da matuk’ar kulawa.
Aikuwa Riyyam kamar dama abunda yake jira kenan, cikin yanayinsa na sakewa daya zame masa sabo, ya kalli Ramadan tare da cewa.
“Yeh za’abani ba za a bawa wani ba.” Ya kare maganan yana meyiwa Ramadan din gwalo.
Abunda ya matuk’ar bawa su Alhaji Ibrahim dariya kenan.
Shikuwa Ramadan durk’usawa agaban Malam din yayi, cikin sigarsa ta shagwab’a shima yace.
“Shikenan na fahimta yanzu wariyar launin fata za’a nunamin, da farko an bawa Hamma Rayyern alkyabba, yanzu kuma an shafa kan Riyyam amma ni ba a shafa nawa ba.”
Ayanzu kam Dariya Malam Mai-nasara yayi, har saida hakwaransa suka bayyana, cikin matsanancin kauna da kuma soyayyar yaran da yakeji acikin ransa, ya sa hannu ya dan jawo Ramadan din jikinsa.
Kansu ya shafa dukansu tare dayi musu addu’a, domin hakanan yakejinsu acikin zuciyarsa tamkar jikokinsa na gaske.
Rayyern kuwa duk abunda kannen nasa sukayi kallonsu kawai yakeyi, bayan kuma ya gama bare magungunan da ya kamata ace Malam din yasha ne, yasa Naseer ya miko masa bottle water marar sanyi.
Da kasan ya bawa Malam magungunan yasha.
Tare dayiwa su Alhaji Ibrahim bayanin yanda akullum Malam din zaina shan maganinsa.
Godiya sukayi mishi sosai, ganin da yayi kuma lokaci yadan ja sosai ne, yasa shi kallon su Ramadan tare da cewa su tashi su tafi.
Cikin aminci sukayi wa Malam din sallama, inda Rayyern ya shaida masa cewar zaidawo ya sake dubashi.
Koda suka tashi tafiya kuwa har wajen motocinsu Uncle Mustapha da kuma Alhaji Abdallah suka rakasu.
Basu koma cikin gidan ba kuma harsaida suka ga tafiyansu Rayyern din.
Daga b’angaren su Raayyern kuwa kaitsaye gida suka nufo.
Direct Rayyern dakinsa ya wuce, saboda yana son yin wanka, sannan akwai kuma wani aiki da zaiyi a laptop d’insa.
Yayinda su Ramadan da Riyyam kuwa, anan falo suka zauna inda Mom ta kawo musu abinci suka ci.
Bayan sun gama cin abincinne kuma suka wuce masallaci danyin sallan azahar, ciki kuwa harda Rayyern wanda ya sanja shigarsa zuwan wata farar jallabiya.
Jannart.
Kwance take akan makeken gadonta, wanda akoda yaushe yake shumfud’e da lallausan bedsheet na alfarma.
Irin kwanciyarnan ta rubda ciki tayi, Yayinda ajikinta take sanye da wata baby gown marar nauyi.
Lumsassun Idanunta ta ware ahankali tare kuma da sauke wani ajiyar zuciya mai
Cike da tarin damuwa.
Lallai Tabbas tana da buk’atar y’anci acikin rayuwarta, rayuwar da har yau ta kasa tantance wacce kalar rayuwa ce, rayuwar da kwata kwata babu haske acikinta sai tarin damuwa, kunci da kuma kadaici.
Mirgina wa tayi a hankali kana taci gaba da tunani.
Yayinda akowanni kwanan duniya da irin kalubalen da take fuskanta, acikin kowanni sa’a kuwa zuciyarta na bugawa da tarin tsananin tsoron abunda zaije ya dawo.
Lallai Tabbas tana da buk’atar haske acikin rayuwarta, haka kuma tana da buk’atar abokin rayuwar da akoda yaushe zai debe mata kewa, Sam arayuwarta batasan wani abu Waishi ingantaccen farinciki ba, akullum damuwa kawai da tsoro ta sani.
Haka kuma akowani bayan minti guda tsoronta yakan rub‘anya, tare da mummunan bugun zuciya akan abunda Yayanta Junaid ke neman aikata mata.
Saudayawan lokuta takan tambayi kanta, cewar shin Ya Junaid wani irin d’an uwane? Meyasa akoda yaushe bashi da fata ko buri saina keta haddinta?
Tabbas tunaninta yakan neman watsewa aduk lokacin da ta tuna cewar Ya Junaid din yayanta ne Uwa daya Uba daya.
Shin Meyasa Rayuwa take garari da ita?
Karar wayarta dake aje bisa bedsite ne ya katse mata duk wani tunanin da takeyi.
Ahankali tasa hannu ta share dan guntun hawayen dake kwance agefen Idanunta, wayartata dake ta faman tsuwa ta dauka, ganin kuma sunan Salman ne ke yawo akan screen din wayar yasata picking da dan hanzari.
“Y’ar Hutu wato kinanan kina hutawa agida ni kuma kinbarni da wahalan aikin ki ko.”
Cewar Salman.
Itakuwa Idanunta ta lumshe tare da d’an gyara kwanciyarta.
Cikin muryarta da tayi sanyi sosai tace.
“Sorry Salman gaba d’aya yau banajin karfi sosai ajikina ne, Impact ma nina fara sarewa da wannan aikin wallahi, I’m tired because mutumin nan kamar bazamu samu daman ganinshi ba.”
Murmushi Salman yayi tare da d’an gyara zamansa kana cikin son bata karfin guiwa yace.
“No Jannart don’t stress your self, Insha Allah yau zamu had’u dashi, kinsan na samo mana information akansa, so Yanzu dai anjima kishirya muje hospital d’insa, Insha Allah zamu samu ganinsa.”
Idanunta dake alumshe ta bud’e tare da sauke ajiyar zuciya.
“Thank you so much Salman Insha Allah zan shirya by 3 pm sai muje, zanzo office saimu tafi aboye batare da kowa ya sani ba.”
(Hattara garemu iyayen yara, yawan tsaro baya hana yaranmu yin abinda suke so. Tsananta addu’a da jawo yara a jiki yafi tsananta tsaro da zafi),
“To saikinzo.”
Salman din ya fada tare da kashe wayar.
Itakuwa Jannart bayan ta ajiye wayartata agogon dake sakale ajikin Bangon dakin ta kalla.
Wanda ya nuna mata 2:30 pm.
Zuro kafafunta kasa tayi daga kan bed din, batare da ta tsaya sanya ba kuwa ta shige bathroom danyin wanka.
Sanin da tayi cewar basu da enough time ne kuma yasa bata wani bata lokaci awajen yin wankan nata ba.
Koda ta fito mai kawai ta shafa ajikinta, sai kuma powder and oil lipstick.
Yayinda tabi zara zaran eye lashes dinta da mascara.
Bayan kuma ta feshe jikinta da sassanyan body spray ne.
Ta karasa gaban Sif din kayanta, inda ta zaro wani dogon wandon pallazo white and white colour roba t shirt wanda yake da ɗan fadi kaɗan ta kasa kuma yazo kusa da guiwarta.
Cikin nutsuwa ta sanya kayan ajikinta, tare da daukan wani hill shoe mai kalan blue ta saka ak’afanta, kana kuma ta yane kanta da wani dan vail shima mai kalan blue.
Akan tsintsiyar hannunta kuwa wani anklet ta saka mai kyau.
Wanda ya sake kawata kyaun kwalliyar tata.
Murmushi ne ya dan bayyana akan fuskarta, saboda Kallon irin kyaun da tayi acikin madubi, Yayinda kayan jikin nata kuwa sukayi matukar amsarta tana matuƙar son ƙananan kaya, ta gaza gano illar sasu a ko ina.
Tabbas ayau din ko makiyinta bazaiyi mata kallo daya ya dauke kansa ba sosai kam tayi kyau.
Wata yar madaidaiciyar handbag blue colour ta rike ahannunta bayan ta rike wayarta ahannunta na dama ne kuma ta juya ta fice daga cikin dakin.
Anan Cikin falo ta samu Momy da kuma Abdull zaune.
Ganin ta cikin shiri da sukayi ne kuma yasa Momy cewa
“A’a Jannart fita zakiyi ne.”
“Eh Momy zanje office amma bazan jimaba Zan dawo Insha Allah.”
“To adawo lafiya”
Da Ameen ta amsa, Yayinda Abdull kuwa yace idan tazo dawowa ta kawo masa abundadi.
Da to kai ta amsa masa kana tasa kai ta fice daga cikin falon.
Tana fita compound din gidan kuwa, kattin samudawan guard dinta suka tattaso.
Har acikin ranta Allah Yasani kwata kwata batason wayanann mutanen da suke tsaronta, saidai kuma babu yanda ta iya.
Haka ta shiga mota suka fice daga cikin gidan.
Direct Nasarawa G.R.A ta nufa inda anan wajen aikin nasu yake.
Suna isa kuwa ta fito daga cikin motar, kaitsaye ta wuce cikin Arewa 24 din ɗan madaidacin ma’akatane, wanda yake kamar irin manyan gidajen nan ne na al’farmar.
Sam wurin gidan TV’n bai cika girmaba, dan bazaifi wani gidanba, ma, sai dai zubi da tsarin wurin shine mai tafi da hankalin mai kallo, kota ina ka wulga shuke-shuke ne masu kyau da ɗaukar hankali kamar a kasashen turawa, Gate ɗinsu daya ne ta inda ka shiga ta nan zaka fita, can ciki kuma Office-office. Masu kyau ma dai-dai-ta na al’farmar da hall ɗinsu sai ɗakunan haska shirye-shiryen su.
Duk inda ta gilma kuwa sai abokan aikinta sun bita da ido, Yayinda kowa ke yaba irin baiwar kyau da Allah ya bata manya daga ciki irinsu Aunty Fa’iziyya D Sulaiman kuwa ƙuruciyarta suke gani a fili da illar shigarta da ta meda jikinta.
Direct office dinsu ta wuce kaitsaye.
Inda ta samu Salman da kuma Aysha Lawan suna zaune.
Nanfa ta tsaya gaisawa da Aysha kawartata.
Acan gidansu Rayyern kuwa.
3:00 am dai-dai ya fito daga wanka, inda ya shirya kansa cikin wani black tracksuit, masu kyaun gaske, da suka matuk’ar amsar jikinsa.
Yayinda ak’afansa kuwa ya saka wasu had’add’un sneakers shoe masu kyau da taushi.
Bayan ya gama kimtsa kansa ne kuma, ya shafa wani irin fitinannen turare mai tsananin kamshi.
Bud’e drawer’nsa yayi.
Shiru ya ɗan
Tsaya yana mai kallon Alkyabbun dake jere a saman kayanshi.
Haka nan yaji yana son gwada sa alkyabbar a jikinsa yaga ya shigar zatayi mishi.
Numfashi ya ɗan fesar a hankali inda anutse ya zaro daya daga cikin alkyabbun da Malam Mai-nasara ya bashi.
Warware alkyabban yayi tare da soma kare mata kallo baƙace mai kyau irin mai sheƙin nan gefe da gefenta an ƙawayashi da zare golding, kai ya jinjina saboda shi kansa ya yaba da kyau da kuma haduwarta, musamman daya fahimci cewar ba karamin kudi aka saka wajen sayan duk alkyabbun ba fuska ya dan yamutsa dan sun cika nauyi.
Addu’an sanya sabon kaya ya karanta, “Alhamdulillahil laxee kasani haxal saubah warazaƙani min gairi hauli minni walaƙuwah”.
dai-dai lokacin daya ke daura alkyabban akan kayan dake jikinsa.
Tare kuma da daukan harami ya daura akansa.
Ya Allah!
Bakaramin kyau Dr.Rayyern Mai-nasara yayi ba, alokacin daya gama kimtsa kansa Cikin alkyabbar.
Kyau yayi sosai da sosai, wanda shi kansa saida ya sake yiwa Allah Godiya daya halittosa amatsayin bil’adama musulmi mai shiga ta kamala.
Koda ya kalli kansa amadubi numfashi ya ɗan fesar a hankali saboda yanda yaga ya fito tamkar Limami.
Wayarsa da kuma wata yar jaka dake gefen gadonsa, wanda ya kusan cika cikinta da chocolates ya d’auka, tare da rik’e jakan ahannunsa, kaitsaye ya fice daga cikin dakin.
Ahankali yake saukowa daga kan steps d’in…!