Hausa novels

Halysaah Page 8 By Khaleesat Haydar

Har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, yana parking a garage ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka tana satan kallonsa, kofar entrance din parlor taga ya nufa without looking at her, hakan yasa tana tafiya a hankali ta bi bayansa, ya bude kofar parlon ya juya ya kalleta, ita ta fara shiga parlorn sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar, dakinta ta tafi bayan ta bude kofa ta juya ta kallesa, kwanciya taga yayi a kan 3 seater ya lumshe ido, ta shiga dakinta kawai ta kulle. Washegari da safe karfe takwas da ‘yan mintuna Khaleesat ta fito daga dakinta, zaune ta gansa da text books a gabansa alamar he is studying, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, har ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin kujera tana wasa da edge din mayafin jikinta, a hankali tace “Ina kwana” Ya ajiye pen din hannunsa yace “Good morning Halysaah” Still bata dago kanta ba kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, yace “How was ur trip?” Ta ɗan kyafta ido tace “Alhamdulillah” Yace “Sorry jiya ban tambayeki jikin Mama ba, i was sleepy hope she is better now?” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, tace “She is fine Alhamdulillah” Yace “Hope ur mind is now at rest?” Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, sai kuma ta ɗan gyada masa kai, wayarsa ne ya fara ring ya dauka sannan yayi picking ya kai kunne, ta ɗaga kanta tana kallonsa, taga shiru yayi alamar yana sauraron abinda ake gaya masa a wayar, after few seconds yace “It should be upstairs then” Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya daga kai, da sauri Khaleesat ta dauke kanta daga kallonsa, Yace “Hope nothing Halysaah?” A hankali tace “Kawai, i want to appreciate you, thank you so much, Allah ya saka da alkhairi….” Cikin calm voice yace “No, You need not to Halysaah, iya abinda zan yi ma kanwata na maki ai” Cikin sanyin murya tace “To Nagode Allah ya saka da alkhairi” Ya ɗan yi murmushi yace “To Ameen, so u can be this calm?” Ta wani kallesa, yace “Makarantar zaki tafi baza ki bari ki huta from ur long journey ba?” Ta sauke idonta tace “I am having presentation today” Yace “Ohk then, Allah ya bada sa’a” A hankali tace “Ameen” Ya nuna mata Trolley dinta da ya shigo mata da shi parlon yace “Ga boxes dinki can” Ta kallesu tace “Thank you” Yace “You are welcome” Daga haka ya ci gaba da abinda yake, Sai da ta kai su dakinta sannan ta dawo ta nufi kitchen, Tea kawai Khaleesat ta sha da Cookies sannan ta dauko jakarta zata wuce makarantar, makullin gidan ya mika mata yace “The house key….” Ta tsaya tana kallonsa, sai kuma tace “Ain’t u using it?” Ya daga kafada yace “Will sort my self out” Shiru tayi at first, can kuma ta nufesa ta amshi makullin tace “Thank you” Yace “You are welcome” Daga haka ta fita daga gidan ta kullo masa kofar. Khaleesat na tafe tare da Safiyyah dake mata mitar Ya Mustapha yace bata daga kiransa, ita dai Khaleesat tafiyarta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah ta tsaya tace “Ohh ga gantalalliya na maki magana ko?” Khaleesat ta tsaya tana kallonta tace “To me zan ce Sophie? Ke kanki kinsan ina da wanda zan aura to menene amfanin in daga wayar Yaya Mustapha? Beside wallahi ko da bani da wanda zan aura ni bazan kulasa ba, ai ana barin halaq ko don kunya” Da wani expression Safiyyah tace “Ban gane ba, as per cewar Surayya cousin sis dinki ce ko kuma kawarki ce? Where did u know her from? Meye hadinki da ita da har za a bar halal don kunya? Can you hear ur self pls? If you are not interested in my cousin brother ba sai kin ta corner corner ba kina kawo zancen da hankali ma bazai dauka ba, meye hadinki da wata Surayya da zaki bar halal don kunya?” Khaleesat tace “Ni dai don girman Allah ki ma bar wannan zancen, Ya Mustapha kuma kiyi ma Allah ki gaya masa i am engage, ni bazan daga kiransa ba” Safiyyah tace “Wallahi bazan fada ba ai kina da baki ki gaya masa da kanki, ke da wa aka yi engaging da zance masa u are engage? Ai as far as i am concern ni ban san wannan batun ba, kawai nasan kina da wanda baki da wani option sai na aurensa, but as time goes on ke kanki zaki san kina da option, za kuma ki ji baza ki iya auren ba sai dai duk abinda zai faru ya faru” Khaleesat ta taɓe baki tace “Kin ga ni yunwa nake ji zan tafi gida, sai gobe in mun hadu” Safiyyah bata tanka ta ba ta ci gaba da tafiya ta bar ta tsaye a wajen, Khaleesat ta bi ta da kallo, to wai ma ta yaya zata daga kiran Ya Mustapha, ita a rayuwarta abinda tasan in an mata bazata ji dadi ba ko by mistake ne bata yi ma wani, ita Safiyyah in ita ce a shoe din Surayya ya zata ji, wannan ai son zuciya ne ma kawai, bin bayanta Khaleesat tayi tace “Ni dai tunda ba mu da aji mu je gida pls ki mana girki i am very hungry and at the same time tired from yesterday’s journey” A haka ta samu ta lallaba Safiyyah dake jin haushinta suka kama hanyar gidanta, suna sauka daga Uber ta nufi apartment dinta tana kallon Garage taga babu motar Housemate dinta, does this mean a bude ya bar kofar tunda makullin na hannunta, tana murda kofar taji sa a kulle, to ina ya samu key? ko dai magana yayi aka basa wani makullin, bude jakarta tayi ta ciro key ta bude kofar suka shiga cikin living room din tare da Safiyyah dake biye da ita, Safiyyah ta dinga bin parlon da kallo ta lumshe ido tace “Kai amma wannan turaren Housemate din naki ba dai dadin kamshi ba, the perf is so cool” Khaleesat dai bata ce mata komai ba, ta ajiye jakarta da mayafi ta zauna saman kujera tana ciro wayarta a jaka, Safiyyah ta zauna ita ma kan kujera tace “To kun hadu da Abdul din a Nigeria?” Khaleesat tayi shiru cause kawai taji ita ko maganar Abdul ma bata son ana mata yanzu, ganin yanda Safiyyah ta tsareta da ido, a takaice tace “Eh… me zaki dafa mana pls, wllhi yunwa nake ji” Safiyyah ta mike tace “Toh bari in je in ga what is available in the kitchen” Daga haka ta mike ta nufi kitchen, tana shiga bayan few minutes sai ga ta ta fito, tana kallon Khaleesat da mamaki tace “Kee wai Housemate din naki ne ke maku restocking abubuwa a kitchen haka? Look how ur kitchen is stocked up with costly food items, where is he getting the money to buy all this from?” Khaleesat tace “Baza dai kiyi girkin ba kenan in zo inyi?” Safiyyah tayi dariya tace “No wallahi mamaki nake naga abubuwa masu tsada yake siya, don ni dai nasan kudin da Abdul ke turo maki bazai taɓa siya maki wnn uban abubuwa dake kitchen din nan ba, anya bazan dawo gidan nan ba kuwa Khaleesat? Kinga wasu tsadaddun cookies da drinks da na gani, even the table water in this kitchen ba na yara bane wallahi, the fridge is full to the brim” Khaleesat taki tanka ta tana danna waya, hakan yasa Safiyyah ta juya ta koma kitchen tana kara jaddada anya bazata dawo gidan ba kuwa, Lafiyayyen girki Safiyyah ke yi a kitchen din komai baja baja malam, Sallah kawai Khaleesat tayi a daki ta dawo ta kwanta kan 3 seater tana danna wayarta waiting for the food to be ready, kiran Abdul ne ya shigo wayar hannunta, sosai gabanta ya fadi lkci daya mood dinta ya canza ta hade rai, ta dinga kallon screen din wayar fuskarta babu fara’a tana jiran sai ya kusa katsewa kafin tayi picking call din, dai dai nan taji alamar ana bude kofar parlon, ta mike zaune tana gyara scarf dinta sai ga Housemate dinta ya shigo parlon, sallama yayi ganinta zaune living room din, ta ajiye wayar hannunta ta fasa picking call din Abdul din ta amsa sallamar House mate din nata, yana cire takalman kafarsa yace “Good evening” Ta sauke idonta tace “Ina yini” Yace “Alhamdulillah, bakuwa kika yi?” Double foot wear da ya gani bakin kofar yasa yayi tambayar, tace “Um she is my course mate” Yace “Good” Daki ya nufa, sai a sannan ta kalli wayarta taga kiran Abdul har ya katse tuntuni, she wasn’t bothered at all kuma bata yi attempting bin kiran nasa ba ta ajiye wayar kawai, mikewa tayi ta wuce kitchen, tare suka fito kitchen da Safiyyah bayan Safiyyar tayi dishing masu abincin a plate daya, Safiyyah na bin parlon da kallo tace “Ko dai Housemate din naki ya dawo ne kamshin turaren nake kara ji a parlon” Khaleesat ta dau spoon ta fara cin abincin tace “Ko dai kin san sa ne Safiyyah?” Dariya Safiyyah tayi tace “Ina kuwa na san sa, kawai so nake in gansa ne wallahi, irin wannan kayan alatu a kitchen haka, where is he even getting the money shi da ya zo ta scholarship” Khaleesat dai cin abincin gabanta kawai take taki ce mata komai, Safiyyah ta dau spoon ta fara cin abincin ita ma, basu jima da fara cin abincin ba sai ga shi ya fito daga dakinsa, bai kalli direction din da suke ba ya nufi kofa rike da laptop dinsa, Safiyyah ta bi sa da kallo kamar idonta zai fita ya bi sa, ita dai Khaleesat kallo daya tayi masa ta ci gaba da cin abincinta har ya fita daga parlon ya kulle masu kofa, Safiyyah ta ajiye spoon din hannunta tace “To fa, shi kuma haka yake? Ji wani ɗaga shoulders da yake ko kallon inda muke bai yi ba, haka yake maki a gidan dama?” Khaleesat tace “You can be funny Safiyyah” Safiyyah ta hade rai tace “No like seriously haka yake feeling kansa? Ko don abincin da yake ajiye maki na yan gayu a kitchen ne ya ja haka? Ta yaya zai wani wuce mu babu ko Hi, ni fa bana son harkan walakanci” Khaleesat tace “Look Safiyyah ni ba shi ya ajiye min duk abinda kika gani a kitchen ba, shi baya ma zaman gidan nan, jifa jifa kawai nake ganinsa, beside ai mun gaisa da ya shigo kina kitchen, to kuma kallon me zai yi mana don zai fita?” Safiyyah zata yi magana wayarta ya fara ring, mikewa tayi ta dauko wayar, ta ɗan buda ido tana kallon Khaleesat tace “Ke Abdul ne ke kirs” Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta ajiye cokalin hannunta ta dinga kallon wayar Safiyyah, Safiyyah ta rike haɓa tace “Ikon Allah, ko ya kiraki baki daga bane? Let me pick dai inji me zai ce” Da sauri Khaleesat ta kamo hannunta zuciyarta na bugawa tace “Safiyyah kar ki ce masa naje Nigeria plss cause bai sani ba wallahi” Safiyyah ta saki baki tana kallonta hangangan, da mugun mamaki tace “Ban gane bai sani ba? To wa yayi sponsoring tafiyar taki? Ina kika samu kudin tafiya” Sosai hankalin Khaleesat ya tashi a lkcn, tana girgiza ma Safiyyah kai tace “Just don’t tell him pls, nace maki bai sani ba” Safiyyah da mamaki ya kasa barin ta tace “Ai kiran nasa ma ya katse” Khaleesat taji gaba daya abincin ya fita ranta, sai ga kiransa ya sake shigowa wayar Safiyyah, Safiyyah ta gwalo ido tace “Abdul ne da kirana har sau biyu? Anya lafiya” Khaleesat tayi gathering courage tace “Just pick, in ya tambayeki ni kawai kice masa bani da lafiya yanzu ma kika baro gidana” Safiyyah tace “Ohk” Picking call din tayi ta saka handsfree, ita ta masa sallama ya amsa yace “Ya kike?” Safiyyah tace “I am good” yace “Are you together with Khaleesat?” Babu bata lkci Safiyyah ta sanar masa exactly abinda Khaleesat tace ta gaya masa, ya dan yi shiru at first, sai kuma yace “Tun yaushe ne bata da lafiya?” Safiyyah ta kalli Khaleesat, da sauri Khaleesat tayi mata alamar sati daya da fingers dinta, Safiyyah tace “Yau ina jin sati daya kenan” Daga daya bangaren yace “Sati daya? Me yasa ba a gaya min ba, and what’s wrong with her?” Safiyyah tace “Oh ni na zata ai ta gaya maka” Abdul yace “Wani irin rashin lafiya take haka dake hindering dinta from picking calls?” Safiyyah ta wani yamutse fuska jin useless question din da yake yi taki basa amsa tana kyabe baki, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa yake, Yace “Where is she now?” Sounding uninterested with the conversation Safiyyah tace “Tana gidanta mana” Da sauri Khaleesat tayi typing a wayarta sannan ta nuna ma Safiyyah, bayan Safiyyah ta ga abinda Khaleesat ta rubuta tace “Jikin nata dai da sauki sosai fa” A takaice yace “Thanks” Daga haka ya katse wayar, Safiyyah ta ajiye wayarta tace “Tirrrr, ki ji wani magana gatsau gatsau kamar dan daba, ko tashi hankalinsa fa bai yi ba, ni wallahi da ina da yanda zanyi ku rabu rabuwa na har abada da Abdul din nan wallahi yi zan yi, ko kadan bashi da features din miji na gari, babu caring babu tausayi babu affection, so pompous and full of himself always, nonsense and ingredient, wallahi in wani mutumin kirki ne da yanzu hankalinsa ya tashi duk ya birkice min a waya amma kiji yanda yake magana a tsattsaye kamar ubana daga karshe wai Thanks, kamar wanda nayi ma albishir me dadi wai Thanks, ke ki ji fa wai thanks” a hankali Khaleesat tace “Baza ki gane ba Safiyyah, nima naji i am fed up with him, na gaji da halinsa yanzu” Safiyyah ta rike haba da sauri tace “Ke Khaleesat, anya kece ke fadin haka kuwa?” Khaleesat ta wani taɓe baki ta jawo abinci ta fara ci tace “Kawai naji na gaji all of a sudden wllhi” Safiyyah ta sako baki tana mata kallon mamaki, can tace “Ni ba wannan ba ma, Khaleesat wa yayi sponsoring flight dinki zuwa Nigeria?” Khaleesat ta daga kai tana kallonta amma tayi shiru, Safiyyah tace “Kin yi shiru, waye ya biya maki kudin jirgi?” Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma tace “Housemate dina ne ya siya min Ticket” Safiyyah ta gwalo ido da wani expression na mamaki sosai tace “Ban fahimta ba Khaleesat, Housemate dinki as how?” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “Eh shi ne ya biya min ticket din jirgin….” Khaleesat bata boye ma Safiyyah duk yanda aka yi Housemate din nata yayi sponsoring tafiyarta ba, Safiyyah was totally speechless and Surprise, after few seconds tace “Did you know what flight ticket is saying from USA to Nigeria Khaleesat?” Khaleesat tace “I went to Nigeria in business class and came back in Business class Sophie” Buda baki Safiyyah tayi ba tare da ta san tayi hakan ba tana kallon Khaleesat kamar idanuwanta za su fito, a hankali tace “Business class fa kika ce Khaleesat?” Khaleesat ta gyada mata kai, Safiyyah ta fara bin gidan da suke ciki da kallo that is for the average here in America, da wani Expression tace “Business class? To me yake yi a wannan gidan if he is doing this well that he can afford to pay for business class to and fro? Dama ni tun daga irin abubuwan da na gani a kitchen nasan wannan mutumi might be trying to disguise himself for a reason best known to him, idan ba haka ba why share an Apartment bayan zai iya affording shi kadai ya zauna a gidan, beside zai iya samun wanda ma yafi wannan in a more better area” Ita dai Khaleesat kallon Safiyyah kawai take ganin yanda tayi concluding lokaci daya, Safiyyah ta wani juya ido tace “Or did he have any mission here da bamu sani ba?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Daga sanda nayi misplacing makullina ne ya fara kwana gidan nan tunda yasan bani da makulli, amma tun da yayi move in zuwa gidan nan i can count sau nawa ya kwana if i remembered well, baya kwana nan wallahi, ba har na gaya maki ba….” Safiyyah tayi dariya tace “But i am trying to understand me yasa yake zaune a gidan nan, ko dai ya sanki from somewhere ne shine ya dawo nan saboda ke?” Khaleesat tace “Ji fa wani magana, bai san ni a ko ina ba wallahi, ni bamu taɓa haduwa da shi ba, ranan da suka fara zuwa gidan i overheard him asking if his housemate is a Male or female, lkcn ina dakina, kilan he is in a haste to settle down ne shi yasa kawai he opt for this, amma bai san ni ba wallahi” Safiyyah dai tayi wani murmushi tace “Ae shikenan we shall see” Sai kusan karfe bakwai Safiyyah ta bar gidan shi ma saboda azababben kiran da Ya Mustapha ke mata ne, tana mita haka ta bar gidan, bayan Khaleesat ta rakata ta dawo tayi sallahn magarib a nan parlon tana zaune saman darduma bayan ta gama azkar ta dau wayarta don dubawa ko Ummanta tayi mata reply, tun Safiyyah na nan suke Voice chat da Ummanta da kannenta, ganin Umma bata yi reply ba ta gane wayar ya mutu don dama Umma tace mata babu caji wayar ta kusa mutuwa, mamakin Abdul kawai Khaleesat ke yi a ranta, duk da ce masa da Safiyyah tayi bata da lafiya amma har yanzu bai kira wayarta ba, ko ta Whatsapp bai mata magana ba, tana cikin wannan tunanin taji an bude kofar parlon, juyawa tayi Housemate dinta ya shigo, sallama yayi ganinta a parlon, ta dauke idonta ta amsa, ya karaso cikin parlon without looking at her ya tafi inda Books dinsa suke yace “Kawar taki ta tafi kenan….” Khaleesat tace “Ina yini” Yace “Good evening Halysaah” Bayan ya gama daukan text books da zai dauka ya dawo cikin parlon yace “Alright Good night” Ta bi sa da kallo, sai da ya nufi kofa ya sake juyowa yace “Sai da safe” Ta sauke idonta tace “Allah ya kai mu lafiya” Daga haka ya bude kofar ya fita tana jin ya kulle kofar da makulli daga waje. Washegari Khaleesat bata da karatun da za su yi a makaranta, don haka har karfe goma bata fito parlor ba tana kwance, ita har sannan fa ta kasa daina mamakin Abdul don har sannan bai kirata ba, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta shirya, wajen karfe goma da minti arba’in ta fito daga dakinta, kwance taga Housemate dinta saman 3 seater yana bacci, kulle kofar da tayi ne yasa ya bude ido a hankali, walking slowly ta karaso cikin parlon, juyawa yayi bayan ya sake rufe idonsa as if murmuring yace “Good Morning Halysaah” Tace “Ina kwana” Bai bude ido ba bai kuma amsa ba alamar ya ci gaba da baccinsa, ita dai ta wuce kitchen. After an hour Khaleesat ta fito daga kitchen bayan ta gama girkin da take, zaune ta gansa a parlon ya dafe kansa, tsayawa tayi tana kallonsa, ya daga kai suna hada ido ta ɗan koma baya tace “Is everything okay?” 07087865788✍🏻

Back to top button