Gargadar So Chapter 131 By M Shakur
BAYAN 2 WEEKSGently yake bude idanunshi harya gama bude idanun tasss yakalli dakin dayake kafin idanunshi su sauna kan Ni’ima dake zaune sanye da abaya tana kallonshi sosai saikuma gently tace “ka farka”? Hannu Baban Yaseer yakai ya taba kanshi dayaji kaman yamai nauyi yaji duk bandage ne yace “how long nake nan?” Anatse tace “2weeks kenan” saikuma ta tashi tace “lemme call doctor” hartakai wajen kofa yayi magana but bataji ba sabida maganan shi bata fita da kyau dawowa tayi tace “na’am mekace?” Murya chan ciki yana kallonta yace “Hawwwa! Where is my Hawwa?” Shiru Ni’ima tayi tana kallonshi hawaye har suna fitowa daga gefen idanunshi sai kawai tajuya tafice bata jimaba tashigo tareda doctors aka dubashi wasu Nurses maza suka tayata chanzamai kaya aka cire bandges na kan nashi sannan aka wankemai baka akace tamai tea tamai tazauna bakin gado zata bashi yace “ina Hawwa”? Kaman ba ita yama tambayan ba tace “bude bakinka na samaka?”Kin budewa yayi yace “i just wants to know ina Hawwa na? Mijin nata ya saketa? Nasan yanda yaganmu da abinda na fadamai dole ya saketa, Ina so naje wajen Baba na nemi auren mu” tea Ni’ima ta ijiye a gefe tai folding hannunta tana kallonshi ganin yadawo hayyacinsa sarai yasan meyakeyi ahankali tace “at first bantaba so nayi blaming naka ba abubuwan dasuka faru cus na dauka somehow somehow Hawwa itace tai seducing naka harka fara sonta tana maka all those charming character, I was thinking maybe anytime kuka hadu duk tana fakan idanuna ta maka ire iren abubuwan nan” Ni’ima tace “I hated Hawwa so much dudda kaine ke sonta zuciyana yakijin haushinka yadingajin haushin Hawwa yana tsanan Hawwa cus na dauka she puts you on and make you to love her tunda kaine kadai option arayuwanta babu wani dake nemanta banda mijin aminiyanta” Ni’ima tai shiru tace “I was very very wrong, Hawwa cried, Hawwa tamini rantsuwa daban daban akan she has nothing to do with you naki yarda, I fetl duk karyane ayanda na Santa nasan saidai rana daya naji an daura muku aure, kishinka ya haddasamin mugun tsana, bakin ciki, kyashi, da so na hallakata da menene menene duka araina, I lost a very true friend and a sister a lokacin nan sabida kai Aliyu” Ni’ima tadan fuzar da iska saikuma takalli Baban Yaseer dake kallonta tace “I know everything you did tun bayan bikin Hawwa katare a layinsu ashe stalking nata kake wayanda family mijin suka turo to take care of your bill sun fadi komi ba karya, and nagani a wayanka, sunce mijin Hawwa ne yamaka shegen dukan nan, how could you try to kashema Hawwa aure eh?” Baban Yaseer nawani kalan kallonta yace “stop talking kaman you were not the first person data taba attempting takashe musu aure ba” ihu Ni’ima tamai tace “that’s because lokacin I felt betrayed naji anci amanata an yaudareni cus Hawwa kawata ce but she hid everything from me and mijina ya sota all of those things you see at least I have reasons kaifa? Wat is your reason eh? Akanme zakazo kashe mata aure?” Ihu yamata yace “sabida inason Hawwa! Inason Hawwa sama da yanda nakeson kaina da rayuwana! Ranan bikinmu dana daura idanuna akan Hawwa naji Allah ya dauramin sonta, I’m a loyal lover babu wanda zai iyama Hawwa kalan soyayyan dana mata and bari kiji saidai idan na dauki numfashina na karshe aduniya bazan taba son Hawwa ba! I will never give up! Wlh wlh saina sami Hawwa ko ta halin kaka ne!” Wani irin kallonshi Ni’ima takeyi saikuma ta fuzar da iska tace “Baban Yaseer you are sick! I’m not a doctor but ni nurse ce and I’ve worked a hospital, you need to see a psychiatrist you are mentally not sound” dasauri yace “ohhh sabida inason Hawwa zakice haka? To bari kiji abin alfahari nane ma na haukace kan Hawwa ko na mutu kan Hawwa! Kinga dukan nan da fasamin kan nan da akayi? I’m proud anmin kalan dukan nan akan soyayyan Hawwa! Dukan infact yasa nakara sonta ma, nakara sonta, the more anamin wani abu kan soyayyan Hawwa the more abin nakara karamin shaukin son Hawwa araina wlh tallahi, Doctor Doctor doctor” dasauri ‘Ni’ima ta tashi sabida yanda taga yana kiran doctor a haukace doctor ya shigo Baban Yaseer yace “Oya a sallameni naji sauki inada abinyi” Dasauri Dr yace “no no, infact anjima kadan zamu kaika ayi brain scan cus kanka yabugu sosai we still needs to monitor you na akalla 3good days” ahaukace yace “wlh bazan zauna har kwana uku anan ba” cikeda lallabawa Dr yace “calm down nasan babu mai son asibiti but is for your own good kaji” dauke kai Baban Yaseer yayi Dr yace “Ina zuwa” yawuce yafita Ni’ima ta share kwallan daya zubo mata sai kuma tazo wajen ta duka takai hannunta takama nashi murya chan kasa tace “Baban Yaseer” Juyowa yayi yakalleta tace “katashi baka tambayi yaranmu ba baka tambaya yaya nakeba ko ya iyayenka ba” fizge hannunshi yayi yace “sabida ba kune matsalata ba, Hawwa ce matsalata itace burin rayuwana, ko yanzu yaya take oho? Taci abinci? Maybe she must be crying, yaron nan yana samin matana kuka” kallon Baban Yaseer Ni’ima keyi sai kawai tajuya tafita daga dakin tawuce chan lobby ta zauna taciro wayanta tai dialing number Mama Ringing daya Mama ta daga tace “Ni’ima yamai jiki?” Ahankali tace “ya farka inaso Yaseer da Yasmeen?” Mama tace “gasu chan kinsan yau ba school wasa suke a tsakar gida, Ya jikin Baban Yaseer?” Hawaye Ni’ima ta share muryanta yayi sanyi sosai tace “Mama Baban Yaseer ya haukace ko yasami matsalan kwakwalwa zance…..” tashiga bawa Mama labarin komi, Mama tai shiru tace “Allah mun gode maka munga jarabawa” tace “yanzu ki kira iyayensa daga kano ki sanar dasu komi karkikai dansu asibitin mahaukata batare da sanın su ba kinji” Gyadamata kai Ni’ima tayi tace “toh” ta katse wayan tai shiruuu ta ta mike ta wuce daki babu Baban Yaseer ba alamunsa ga drip yacire, tayi ihu aka shiga nemanshi babu shi yagudu, gabanta yashiga fadi cus tasan gidansu Hawwa zaije again this time yayi attempting wani abu they will kill him, sai kawai tashiga danna wasu digits kafin tayi dialing number takai wayan kunnenta.Hawwa na kwance akan gadon Khaleel da yanzun nan yafita tanaji maranta na ciwo sosai dan yanzu after every sex sai maranta yayi ciwo but bataso ta nunamai cus tausayi yake bata this days he’s going through alot taga how he mises drinking da clubbing so most times idan abun yatasomai idan baiyi sex ba baya samin natsuwa, itama bata hanashi cus yana bata tausayi he’s really fighting hard trying to be a better man! Wayanta ne yashiga ringing dasauri takai hannunta tadauka cus tadauka shine but saitaga number datana gani tasan na Ni’ima ne cus number Ni’ima na kanta dan bugawa kirjinta yayi saida Ni’ima takirata kusan 5timez bata dagaba wayan na katsewa saitai dialing number Khaleel ringing daya ya dauka yace “Moonshine gani yanzu nake titin hospital namu” murmushi tamai tariga tai alkawarin bazata kara noyemai komiba ahankali tace “Baby that lady is calling me yanzu 5times kenan ban dagaba nace lemme tell you” ahankali Khaleel yace “wace lady?” Murya chan kasa Hawwa tace “Ni’ima!” Ranshi ne yaji yana baci dagajin sunanta yace “don’t talk to her! I hate her!” Murmushi tayi tace “okay” shima murmushi yayi yace “thank you telling me” ahankali tace “I will never hide anything from you, you’re my best friend Khaleel” murmushi yamata yashiga cikin hospital nasu yayi parking itakuma tana ijiye wayan tashiga tashi da kyar tana tafiya ahankali tashiga bayin shi tayi wanka da kyar tafito tabude kofa zata wuce dakinta kafafunta suka rike ahankali tace “Subhanallahi!” Saikuma ta daure tadaga kafan kadan zatai tafiya kaman an balla wani abu a maranta kawai sai jini dakesa maranta ciwo tabi cinyanta da kallo ta kwala ihu jiri na debanta. “Mommmmmmm” tai ihuuuu da duka karfinta amman ina babu mai jinta tacigaba da ihu.Mom na zaune a falo akai knocking takalli kofa Salman ne cikeda girmamawa yace “morning Ma” gyadamai kai tayi tace “ya akayi?” Anatse yace “Mrs Khaleel has been shouting and screaming your name in her flat I think wani abu yafaru and Oga yatafi aiki tun dazu” Dasauri Mom tadago kanta zatai magana saikuma ta tashi tace “PA biyoni” wucewa Mom tayi da sauri ta tun kafin takai fakat din takejin kukan Hawwa dasauri tabude kofa tai sama a kwace taga Hawwa da towel ga blood a legs nata dawani kalan gudu Mom tai wajen tace “meya sameki eh?” Arude Hawwa tace “Mommy period yakamani yanzun nan cikina da marana kaman zai fita bantaba hakaba Mommy” tarike Mom Mom tace “kawo mata riga PA” wucewa PA tayi idanun Hawwa suka shiga juyawa zata sume Mom na jijigata tana kiranta but shiru ta sume.



