Amfanin Bagaruwa Ga Budurwa Da Ya Kamata Ku Sani
Menene amfanin bagaruwa ga budurwa? Bagaruwa bishiya ne da aka fi sani da Acacia ko Gum Arabic da turanci. Bagurawa bishiya ne mai matukar amfani ga jikin danAdam. Bayan haka kuma, ana amfani da ya’yan bagaruwan a wurare da yawa. Duk da cewa a Afrika a ke samun bishiyan, amma saboda tsananin amfaninta, ana amfani da ita a fadin duniya. To wasu amfanin bagaruwa ga budurwa ne ya kamata ka sani? Kar ka damu, ga su nan mun jero ma su a kasa, ciki har da amfanin bagaruwa ga mata.
Amfanin Bagaruwa Ga Maza da Mata
1. Bagaruwa Na Maganin Ciwon Ciki
A cikin amfanin bagaruwa da ake da su, wannan ya na daya daga cikin manya-manya. Bagaruwa na da abin da ake kira Anti inflammation properties, wato ya na iya tafiyar da kumburi.
Saboda wannan ne bagaruwan ke amfani wajen tafiyar da ciwon ciki, kumburi, tsutsan ciki da dai sauransu.
2. Bagaruwa na Maganin Ciwon Makogwaro
Karon bagaruwa na maganin ciwon makogwaro, sarkewar makogwaro ko murya, tari da sauransu.
3. Bagaruwa na Taimakawa Wurin Rufe Ciwo
Daya daga cikin amfanin bagaruwa ga budurwa shi ne ya na taimakawa wajen rufe ciwo. Masana kiwon lafiya sun gano dalilin hakan kuwa shi ne, bagaruwan na kunshe da sinadaran alkaloids, glycosides, and flavonoids,wadanda ke taimakawa wurin saurin rufe ciwo ko tabo.
4. Bagaruwa na Maganin Gudawa
An tabbatar ‘ya’yan itacen bagaruwa na maganin gudawa, domin ya na yakar kwayoyin halittun da ke jawo gudawa.
Idan aka samu bagaruwa guda uku, aka tafasa kuma a ka sha sau biyu a rana, lallai gudawa za ta tsaya. Hakazalika idan mutum ya na yawan zuwa ban daki, to lallai daya daga cikin amfanin bagaruwa shi ne magance wannan. Za a iya jikawa a ruwan zafi a sha.
5. Bagaruwa na Maganin Ciwon Hakori
Akwai nau’i na bagaruwa da ake amfani da shi wajen maganin ciwon hakori. Idan aka nika wannan bagaruwan ya zama gari, za a iya amfani da shi wajen goge baki.
Bincike ya nuna hakan na taimakawa wajen magance ramin hakora da ma warin baki.
6. Bagaruwa na Kara Lafiya
Bagaruwa na kara ma jiki lafiya, ta hanya karfafawa wurin ba jiki kariya. Bagaruwa na taimakawa wajen magance wasu cututtuka, musamman a jikin gajiyayyu ko kuma yara.
Amfanin Shan Ruwan Bagaruwa
Ya’yan bagaruwa na da matukar amfani ga lafiyar mata da maza, domin su na kunshe da sinadarai masu gina jiki da kuma ma kitse. Haka nan ma, ana iya amfani shan ruwan bagaruwa domin taimakawa kwayoyin halittun bacteria masu amfani a ciki.
Har ila yau dai, bagaruwa na amfani wurin magance hawan jini, ciwon sukari da dai sauransu.
Amfanin Bagaruwa ga Mata
Duk da cewa akwai wasu amfanin ganyen bagaruwa ga mata ko amfaninsa ga budurwa, mafi yawancinsu ba su tabbata ba. Hasali ma, abinda aka tabbatar shi ne mata masu juna biyu ko shayarwa kar su sake su sha bagaruwa, domin watakila ya yi masu illa.
Abin da kawai aka tabbatar na amfanin bagaruwa ga mata shi ne wajen rage kiba. A wani bincike da aka yi, an tabbatar da matan da su ka sha bagaruwa sun rage kiba kuma nauyinsu ya ragu.
Wasu binciken kuma sun nuna bagaruwan na maganin ciwon mara ga budurwa.
Wasu kuma su na ganin bagaruwan na magance kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata, wanda har yau wani bincike bai tabbatar ba.
Amfanin Bagruwa ga Maza
Kaman yanda bagaruwa na amfani ga mata, bagaruwa na amfani wajen kara karfin mazakuta.
Amfanin Bagaruwa A Masana’antu
Shin ka san cewa ana amfani da bagaruwa a wajen yin kayan daki? Saboda karfinsa da kuma jure wahala da ganin cewa gara ba su iya cinye shi, ana iya amfani da bagaruwa wajen yin gadaje, kujeru da sauransu.
Haka kuma ana amfanin da bagaruwan dai wajen yin takardu, kayan sawa da ma dai wasu abubuwan.
Ana Iya Shan Bagaruwa?
Eh, Ana iya shan bagaruwa domin magance matsalolin da mu ka ambato a sama. Amma fa sai an yi hattara, domin masana sun gano cewa yawan shan bagaruwan yakan iya yin illa ga mutum.
Da zarar ka fuskanci wani sauyin yanayi yayin shan bagaruwan, to lallai ka gaggauta daina sha kuma ka tuntubi masana kiwon lafiya.
Shin Bagaruwa na Da Illa?
Bayan amfanin bagaruwa, shin ya na kuma da illa? Amsar ita ce eh, bagaruwa na da illa. Kadan daga cikin illolin sun hada da yawan gyatsa, yawan zuwa ban daki. Wasu kuma sun koka da cewa jikinsu na susa bayan amfani da bagaruwa.
Kaman kuma yanda na fada a baya, ba a so mai juna biyu ko mai shawarwa domin zai iya tasiri ga irin magungunan da su ke sha mai kunshe da sinadarin Iron. Hakan zai sa bagaruwa ya yi illa ga mace mai ciki ko kuma shawarwa.
A jikin budurwa kuwa, ba wani illa da aka tabbatar bagaruwa na yi, in dai har an yi amfani da shi yanda ya kamata.
A Takaice…
Bagaruwa dai na da amfani ga jikin Dan Adam, domin ya na maganin ciwo da kumburin ciki, warin baki, ciwon hakori, rage kiba, warkar da ciwo, maganin gudawa da kuma kara lafiya.
Hakazalika amfanin bagaruwan bai takaita akan wadannan ba, domin ya na taimakawa maza wajen kara karfin mazakuta, kaman yanda daya daga cikin amfanin bagaruwa ga mata shi ne wajen rage kiba.
Amma fa duk da haka sai an bi a hankali, domin an gano cewa bagaruwan zai iya ma mata masu juna biyu ko shayarwa illa. Wasu kuma zai iya jawo masu feshin kuraje a jiki. Duk wanda ya fuskanci wannan, sai ya yi maza ya tuntubi masana kiwon lafiya.
Ci gaba da ziyartar shafinmu idan ka ji dadin wannan rubutun.