Hausa novels

Halysaah Page 20 By Khaleesat Haydar

Jay na isa unguwan da gidansu Safiyyah yake sai ya mance apartment din da Khaleesat ta gaya masa, hakan yasa ya kira wayarsa dake wajenta, Khaleesat na zaune saman gado har sannan tana playing game da wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din wayar ganin image din hotonsa da number da yayi appearing, sai taga kamar shi din ne a gabanta take gani, sai da kiran ya katse ta zaro ido bayan tayi realizing bata yi picking ba har ya katse, bayan few seconds ya sake kira, dagawa tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace “Halysaah” Tace “Na’am” Yace “I think i forgot the apartment u told me” Gaya masa ta sake yi yace “Thank you” Daga haka ya katse wayar ya ci gaba da driving dinsa, dai dai gaban apartment din yayi parking don motar Mustapha baya nan, yana tsaye bakin kofa yayi knocking gently, after a minute aka bude kofar parlon, komawa baya Safiyyah tayi tana kallonsa da mamaki daga sama har kasa, ya ɗan mata murmushi yace “Hi Safiyyah” Ta bude ido sosai tana leka motarsa da taga yayi parking thinking may be he is together with Khaleesat, ganin motar ba kowa ciki tace “Hi, good afternoon” Yace “How are you doing Safiyyah?” Lokaci daya tace “Ko dai Khaleesat bata da lafiya ne?” Da damuwa sosai tayi tambayar, Yace “Yeah bata da lafiya” Tace “Wallahi yanzu na gama shiryawa nake son in ci abinci inje gidan naga miss call dinta jiya ina ta kira har yau wayar baya shiga, and i am disturb” Yace “Shi yasa na zo in dauke ki idan ba damuwa so you can be together with her she is sick, probably idan kin mata magana zata ci abinci ta sha magani” Da sauri Safiyyah tace “Sure, bari in dauko gyalena” Juyawa tayi da sauri ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma parking space, Surayya dake zaune a parlon ta kasa kunne duk tana jin conversation dinsu kafin Safiyyah ta shigo, Safiyyah ko kallon direction dinta bata yi ba ta tafi dakinta da sauri ta dauko jakarta da gyale sai wayarta sannan ta fice daga gidan, ganin Jay cikin motarsa yana jiranta ta bude gaban motar ta shiga tana cewa “Tun jiya ne bata da lafiyan? Kuma me yasa ta kashe wayarta?” Jay yace “Tace wayar ya fada ruwa ne” Safiyyah tace “Ohk” Sai da suka dau hanya sannan Jay yace “Amma tana can gidanmu fa, can za mu je yanzu” Safiyyah ta juya da sauri tana kallonsa da mamaki tace “Gidanku? Why? What happened?” Calmly yace “Before then za mu fara zuwa apartment dinmu sai ki dau mata kayanta da zata yi amfani da shi, we left yesterday with nothing” Safiyyah bata sake cewa komai ba tunani iri iri na yawo a ranta, to me ya faru? ta yaya Khaleesat da ta sani me shegen taurin kai ta yarda har ta bi sa can gidan nasu? Ko dai rashin lafiyar nata is critical ne haka? Da tunane tunanen nan suka isa apartment din, suka shiga ciki tare da Jay ta nufi dakin Khaleesat shi kuma ya zauna a parlor, bayan few minutes ta fito tace “Kala daya zan dau mata kayan ai ko?” Jay ya mike yace “No, 3 to 4 will be okay” Duk da confusion din da Safiyyah ta shiga bata dai ce masa komai ba ta juya ta koma cikin dakin, ta dau akwati ta saka ma Khaleesat kayanta da duk abinda zata bukata a ciki, tana fitowa daga dakin Jay ya mike yace “Kin dau mata duk abinda zata bukata?” Safiyyah ta gyada masa kai, suka fita daga parlon, duk ta kagu taje wajen Khaleesat ita dae, silently suka yi tafiyar har suka iso gidan, bayan Jay yayi parking ya sauka Safiyyah ma ta sauka, ya fiddo akwatin sannan suka nufi entrance din apartment din Safiyyah na biye da shi, bai ga motar AJ a gidan ba alamar ya fita, suna haurawa sama Jay ya tafi dakin da Khaleesat take yayi knocking, ya mika ma Safiyyah akwatin yace “Zaki iya shiga, zan je inyi sallah” Safiyyah ta amshi box din tace “Ohk” Bude kofar dakin tayi Khaleesat ta dinga kallonta har ta shigo, Safiyyah ta ajiye box din hannunta ta nufeta da sauri tace “Me ya sameki Khaleesat?” A hankali Khaleesat ta sauke idonta ta kasa cewa komai don bata ma san ta inda zata fara ba, sai ga hawaye. Safiyyah na tsaye dakin kusa da window bayan Khaleesat ta bata labarin duk abinda ya faru, tsabar yanda labarin ya kidima Safiyyah kasa ci gaba da zama tayi gefen gadon, Safiyyah tayi shiru for almost 2 minute tana tsaye jikin window tana girgiza kafa, ita dai Khaleesat goge hawayen dake sauka idonta kawai take, can Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya me cike da takaici tace “A baya da nake gaya maki Abdul ɗan daba ne ba kin maida maganata abun wasa ba? Tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin ɗan iska kamar Abdul ba, yanzu da baki samu lambar kowa ba haka zai lalata maki rayuwa babu digon tsoron Allah a ransa? Ya kashe uban kudin zuwa USA kawai don ya zo yayi lalata? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, amma naji haushi da ɗan uwan Housemate dinki bai sumar da shi ba an maida sa Airport a haka, tirr da Abdul, tirr da halinsa, i am so happy that things turn out this way, in sha Allahu karshensa ne ya zo a rayuwarki” Khaleesat ta fashe da kuka tace “Sophie ban san next action dinsa ba idan ya koma Nigeria, i am so restless” Safiyyah tace “Next action dinsa? Sai ya koma ya gaya masu uban da ya kawosa USA da Intention dinsa, ke in zaki dena wannan crocodile tears din naki ki dena don ba tausayinki zan ji ba, tunda dai bai samu nasaran lalata maki rayuwa ba ni duk abinda zai faru ma ya dade bai faru ba, kukan uban me kuma kike ma mutane? Ko nasaran da bai samu a kanki bane ya dame ki? Kuma wallahi ya ci sa’ar baki sameni a waya ba don kafin in karaso gidan sai 911 sun riga ni, tuni zan kirasu ince gashi can za ayi fyade, banda iskanci duk karuwansa basu ishesa ba sai ya zo ya kara dake? Gaskiya ki rike Housemate dinki da ɗan uwan nan nasa da kyau don mutane ne su wallahi, da ba don su ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, don da na kai maki ruwan zafi yafi a kirga zuwa bandaki yanzu” Khaleesat dai bata sake ce mata komai ba tana share hawayen da yaki tsaya mata, Safiyyah ta rike haɓa har sannan tana mamakin Abdul, can tace “Kamar irin ya zo wajen matar nan tasa, ni wallahi da yaji suka barbada masa mu ga ta iskanci, shege kawai prostitute” Duk tashin hankalin da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya don ita bata taɓa jin inda aka ce ma namiji prostitute ba sai yau a bakin Sophie, Safiyyah tace “Ga dai katon daki an baki, kiyi karatun exams dinki cikin kwanciyar hankali, nima in abun duniya ya isheni in taho nan in sameki kafin dare yayi in koma den dina, don ko da wasa bazan ce ki dawo gidanmu ba ni kaina ban tsira gun tsinanniyar matar Yaya Musty ba kuma yaki kwatar min en ci, da zai bar ni ba nima sai in dawo nan kusa dake ba tunda ba rasa abincin da za su bamu mu ci za su yi ba, wannan dakin ai ya ishemu rayuwar America, bari kiji Khaleesat dama Allah ya riga ya rubuta Abdul ne silan zuwan ki Amurka ki hadu da mutanen arzikin ki, babu me canza haka ko yaki ko ya so dole sai ya kawoki ya hadaki da mutanen arzikin ki tunda Allah ya rubuta haka, iya role dinsa kenan a rayuwarki, kuma Allah ne zai basa ladan hakan bamu ba, ba shikenan ba?” Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza mata kai tace “Ni bazan zauna gidan nan ba Sophie” Safiyyah na mata wani kallo tace “Ohk, Apartment din naki zaki koma ki kai ma Abdul din kanki kenan?” Khaleesat ta sauke idonta kasa muryarta na rawa tace “Bazan iya jarabawan ba Sophie, gwara kawai in koma gida, i want to go home, i want to go to my mother” Safiyyah zata yi magana aka yi knocking kofar dakin, Safiyyah ta amsa aka bude kofar Jay ya shigo, kallon Khaleesat yake yace “Kin sha maganin Housemate?” Ta gyada masa kai without looking at him, Safiyyah ta kallesa cike da damuwa tace “Ashe kuma iftila’in da ya faru kenan jiya Yaya Housemate? To Allah Ubangiji ya tsare na gaba, ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi ya baku ladan hidimar da ku ke yi da kawata don bata da kowa a garin nan sai Allah sai ni da ku, kuma she is not longer safe in this state don Abdul can be cunning, azzalumi ne mugu, nasan har yanzu yana labe garin nan bai tafi ba, kuma ba imani ne da shi ba ina jin tsoron next move dinsa, Allah kadai yasan sau nawa ya koma apartment din nan yaga babu kowa ciki” Jay dai ya ɗan yi murmushi yace “She will remain here har ta gama exams dinta in sha Allah” Khaleesat ta kallesa ta girgiza kai cikin sanyin murya tace “Bazan iya exam din ba, Nigeria nake son tafiya” Safiyyah ta mata wani kallo kamar zata ce in tana da kudin jirgi ta tafi sai dai kuma kawai tayi shiru tana hararanta, Jay ya kwantar da murya yace “Saboda me baza ki iya exam ba Khaleesat, stop saying that pls, in sha Allah zaki yi jarabawan ki lafiya, in kun gama sai ki koma Nigeria” Safiyyah tace “Atoh shi dai na gani, kan wani tantirin ɗan iska take son lalata future dinta, duka duka fa shekarar karshe za mu shiga yanzu a makarantar” Khaleesat ta sauke idonta hawaye na sauka idonta don tasan baza su gane abinda take nufi ba, Jay ya sauke ajiyar zuciya yace “Try calming her down Safiyyah, and naga tun jiya bata wani ci abinci ba ban san ko tafi son abincin Nigeria ne ba, nasa cook din gidan yayi ordering ingredient din har an kawo, i don’t know ko zaki girka mata a kitchen tunda kina nan” Safiyyah tace “To ba damuwa, let me cook for her” Yace “Alright” a tare suka bar dakin Khaleesat ta bi su da kallo hawaye na bin fuskarta. Tunda suka shigo kitchen din Safiyyah ke bin ko ina da kallo don the kitchen is so big and well equipped, irin modernize kitchen din nan, bayan Jay ya fita cook din gidan ya nuna mata ingredients din shinkafa da miya sannan shi ma ya fita, tuni ta hau girkin a kitchen din. Wajen karfe biyar Safiyyah na daki tare da Khaleesat hira kawai take mata kamar ba abinda ya faru, ita dai Khaleesat tayi shiru tana kallonta amma gaba daya hankalinta baya kan hiran, wayar Safiyyah ya fara ring ta jawo jakarta ta ciro wayar ganin Mustapha ke kiranta ta wani turo baki sannan tayi pick ta sa handsfree tace “Ina wuni yaya” Ko amsa gaisuwar bai yi ba yace “Waye ya zo ya daukeki a mota Safiyyah?” Safiyyah ta bude baki tace “Ohh haka matar taka tace maka? to ta manta a jirgi aka zo aka daukeni ba a mota ba, kuma munafurcinta zai kare mata wallahi” Tsawa ya daka mata yace “Ina maki magana kina min maganar banza? Are you okay?” Ta wani murguda baki tace “Toh ba ina hanya bane wai, haka kawai dai babu dalili bazan kama hanya in fito cikin sanyin nan ba yaya, ko ka manta jibi za mu fara exams ne?” Kashe wayarsa yayi, Safiyyah tace “Allah dai ya tsine ma Surayya albarka, kuma wallahi kafin mu gama exam mu bar kasar nan sai na mata abinda bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta, ko da wasa kuma bazan ma gaya masa abinda ya faru dake ba kar yayi burgan cewa ki dawo gidansa ya kara ma matarsa extra nama” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta mike ta dau jakarta da gyale tace “Sai na zo gobe in sha Allahu, saura kar ki karasa cinye abincin ki zauna kina asaran hawayenki akan ɗan daba, ga lambata na sa maki a waya in da wani abu ko kuma kina bukatar komai kawai ki kirani” Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat ta sauke idonta kasa, Downstairs Safiyyah ta hadu da AJ wanda shigowarsa gidan kenan tana ɗan murmushi ta gaishesa ya tsaya ya amsa yana danna wayarsa yace “How are you doing” Tace “Alhmdlh ya karatu” Yace “Fine, ya naki” Tace “Muna ta fafatawa dai, to fa mun gode da hidima yaya, Allah ya saka da alkhairi da abinda ku ka ma kawata, Allah ya biya ku” Sai a sannan ya daga kai ya kalleta jin wai tana masa godiya, ita dai ta ci gaba da godiyar ta ba kakkautawa, Yace “Ameen” Tace “Yaya Housemate din ya fita ne, ni zan koma gida ne yanxu” Sai ga Jay ya shigo parlon from outside, ganinta yace “Ohk zaki koma Safiyyah?” Tace “Eh wallahi yamma tayi amma in sha Allahu zan shigo gobe da safe” Yace “To Allah ya kai mu, mu je inyi dropping dinki” Tuni AJ yayi wucewarsa sama, Safiyyah ta bi bayan Jay suka fita daga parlon tana mamakin inda karen gidan yake bata gansa ba tun daxu, sai bayan da suka dau hanya tace “Yaya Housemate….” Dariya ta ba Jay bai jira me zata ce ba yace “I am Jawwad Safiyyah” Tace “To ni dai don Allah kayi dubara ka amshe wayar da ka ba Khaleesat kar taje ta kira yan gidansu su gigita ta, kaga bamu san ko Abdul din na kasar nan ba ko ya koma Nigeria, in ta kira suka gaya mata wani maganar da kyar ta iya abun arziki a jarabawan nan” Jay yayi shiru cause he reason with what Safiyyah is saying, can yace “Haka ne kuma, i will tell her not to speak to anyone for now, amma bazan iya amsan wayar ba naga kamar it’s whiling away her time” Safiyyah tace “To in da kati a wayar don Allah ka kone sa, in da WhatsApp kayi uninstalling dinsa kaga ta haka babu wanda zata ma magana, the exams is just for a few weeks, kamar gobe ne za mu gama” Yace “Sure i will do so Safiyyah” A haka suka isa gidansu ta sauka daga motar ta masa godiya yace “Ki gaida mutanen gidan” Tace “To za su ji” Yayi reverse ya dau hanyar gida hoping Khaleesat bata riga ta ma kowa magana back in Nigeria ba. Washegari da safe Jay yayi booking appointment na ganin likita saboda daren ranan ma Khaleesat dai bata yi bacci ba, yasan dai ba lallai su samu ganin likitan a ranan ba, so he was just helping her to manage her self with the drugs available, da Safiyyah kuma ta zo sai taji ta nemi zazzabin ta rasa dama kadaici ne da damuwa suka mata yawa. Ranan monday da safe Jay yayi dropping din Khaleesat school for her first exam, and he stayed behind har zuwa sanda za su gama don su koma gida tare, kawai shi dai baya son barin ta ita kadai, Jay is trying his very best na ganin Khaleesat ta sake ranta domin tayi karatun jarabawanta da kyau kar ta samu matsala, ga kuma Safiyyah dake encouraging dinta a gefe ita ma, kuma hakan yayi tasiri sosai don ta ɗan sake ranta tana karatun, AJ dai tun ranan da ya shigo ya ganta zaune a daki har bayan da suka yi Exams uku bata sake saka shi a ido ba, bata san ko yana gidan ba ma ko baya gidan, ita dai 24/7 tana daki, hatta abinci cook din gidan ne ke kai mata sama yayi knocking ta fito ta amsa, in ta gama still shi yake zuwa ya amshi tray din, bayan sati biyu da fara exam dinsu ranan suna da interval Safiyyah ta zo gidan da yamma, abinci ta kawo ma Khaleesat, Khaleesat taji dadi sosai ganin tuwo ne don dama tun jiya take sha’awan tuwon, Safiyyah tace “Kinga ba dadewa zan yi ba yanzu zan tafi kafin mutumin can ya fara kirana kamar Surayya ce ta bar gida” A hankali Khaleesat tace “Baza ki bari anjima kadan ba pls” Safiyyah tace “Wallahi yanzu Ya Mustapha zai fara kirana, bai ma san na fito ba, kuma nayi order din Lyft ma da zai maidani gashi nan ya kusa karasowa nan, tashi ki rakani kofar gida” Khaleesat ta girgiza kai tace “Kawai ki tafi za mu hadu schl tomorrow in sha Allah” Safiyyah tace “Wai ke baki gajiya da zama ke kadai a daki, don Allah ni dai tashi ki rakani kema ki ɗan yi strolling kafafuwanki” a hankali Khaleesat tace “Baza ki gane ba Sophie, wallahi i am not comfortable staying in this house, na kagu mu gama jarabawan nan in koma Nigeria” Safiyyah tace “Ae ranan Housemate dinki ya gaya min wai kince masa zaki koma apartment dinki nace lallai baki da hankali, Allah ma yasa Abdul bai sake gidan ba” Tana dariya ta kare maganar, sai kuma ta kwantar da murya tace “Kiyi hakuri kawata, nan da sati kadan zaki ga mun gama exams din in sha Allah, ki kwantar da hankalinki pls, yanzu dai tashi ki rakani” a hankali Khaleesat ta sauko daga kan gadon ta dau gyalenta suka fita dakin tare da Safiyyah, suna saukowa downstairs suka tarar da AJ a parlor da Jay, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta don sai yau taga AJ for almost 2 weeks, ita ta zata ma baya gidan ne, Jay na kallon Safiyyah yace “Are you going soon Safiyyah?” Safiyyah tace “Eh wallahi Yaya Jawwad Lyft dina yana hanya ya kusa” Yace “Alright, ki gaida mutanen gidan” Tace “In sha Allah za su ji” Sallama tayi ma AJ ya amsa mata, sannan ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna tsaye waje suna jiran karasowar Lyft wata mota ta shiga gidan bayan matukin motar ya fito daga cikin motar ya bude gate, Safiyyah tayi kasa da murya bayan sun shiga ciki tace “Ke kinga wani Ride me suna ride Khaleesat? Su dai da masu kudi kawai suke harkar su a kasar nan, in kin bibiya abokansu ne ‘ya yan masu kudi irinsu” Khaleesat dai bata ce komai ba, bayan kusan minti uku sai ga Lyft din Safiyyah ya iso, Safiyyah ta bude bayan motar ta shiga, Khaleesat ta daga mata hannu, Safiyyah na mata murmushi tace “Sai mun hadu a schl kawata, kiyi karatu da kyau fa” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata sannan ta koma cikin gidan, duk a dar dar take tafiya a babban compound din gidan, har yau ita dai ta kasa sakin jiki a gidan nan gani take kamar a kaya ma take she is so very uncomfortable, a haka ta isa parlon gidan ganin baki biyu dake parlon tare da su Jay wanda da alama abokansu ne Khaleesat ta sauke kai ta gaishesu, suka amsa da fara’a, ita dai ta nufi stairs, daya daga frnds din nasu taji yace “Bakuwa ku ka yi a gidan” AJ dake shan fruit salad yace “Eh, yarinyar wani abokinmu ne a Nigeria ta zo jarabawa” Jay ya saki baki yana kallon AJ da ke ta shan fruit salad dinsa ko ajikinsa, Ita kanta Khaleesat sai da ta ɗan juya ta kallesa sannan ta wuce sama, abokin na gyara zama yace “Waow, amma da gani da wuri abokin nan naku yayi aure, ya huta abunsa gashi mu duk mun kasa har yanzu” AJ dai ya ci gaba da shan fruit salad dinsa yace “Ai kam ya huta, mu ma da munyi auren da wuri duk da mun haifi kamarta ai”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button