Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 55 Complete Novel

*ASM Bk2055*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……Kauda idon ta tay daga kallon su ta nufo cikin d’akin cikin kame kai Fauzy ta gaishe da ita ta amsa tare da d’an kallon ta tay mata ya mai jiki nan ma ta amsa kafin ta nufi kujera, a jikinta ta janyo Hijab d’inta ta nufi hanyar fita daga d’akin tana kokarin sakawa, bayan ta fita Fauzy ta kalli Fatuu da yar damuwa tace “ta san kin yi wani abu ne don zubar da cikin?” d’an shiru Fatun tay fuskar ta duk hawaye tace bata sani ba ko likita ya gane ya sanar masu tunda ta dad’e bata farfad’o ba amman in ma ta sanin to bata nuna mata ba, ajiyar zuciya Fauzy tay tace “to k’ilan bata sani ba amman yanzu kaman ma taji abunda muke cewa” shiru kawae Fatun tay idon Fauzy akan ta wani irin tausayin ta ne ya kamata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa yadda take son Ya Haisam bazata ji dad’i ba ace ta samu cikin shi na halak kuma ta zubar da hannun ta gashi tace yayi Fushi, hannu Fauzy ta kai ta kamo nata ta fara lallashin ta “ki kwantar da hankalin ki Zarah nasan dole Kiji ba dad’i amman kada kisa damuwa a ranki ki d’auka komae rubutacce ne dama haka Allah ya k’addaro kuma shima Ya Haisam d’in na tabbatar zai fahimce ki kawae dae dama dole ne ya nuna maki 6acin ran shi Saboda zai ga kin k’i jin Maganar shine har hakan ta faru wanda nasan bai yi zaton hakan daga wurin ki ba a yadda kuke da shi amman dae komai zai daidaita in sha Allahu, ki daina damuwa ko don halin da kike ciki kada ki samu wata matsalar kuma” tana kai Maganar ta kai hannu tana goge mata kwalla daga baya tace bari ta sanar ma Aunty Mareeya, bayan ta kirata ta sanar mata zancen kwantar da Fatun Asibiti salati ta saka hankali a tashe ta hau tambayar Fauzy abunda ya samu Zarah nan ta kwashe komai ta fad’i mata tana jin yadda take zabga salati a rud’e tace tana nan zuwa wane Asibitin take ta sanar mata, bayan sun gama wayar yar hira Fauzy ta shiga yima Fatun duk don ta daina damuwa harda zancen irin shagalin da zasu yi in komae ya daidaita da kalar su ankon da za’ai daga baya kuma yanayin fuskar ta ne ya canza tace tasan ma d’auke Fatun zai yi su bar K’asar amman dae gaskiya a bari sai sun gama karatu lokacin tasan ta k’ara samun wani cikin harma ta haihu, harda Addu’ar Allah yasa next cikin da zata samu na twins ne, tun dai Fatuu na d’an murmushi sai gata harda su dariya, Bayan sallar Azahar sai ga su Feenah Abbas ya kawo su lokacin da suka shigo su Fatun na Zaune akan gadon Fauzy na gefen ta Abdul na hango ta ya nufi gadon da gudu ya fara k’ok’arin hawa Fauzy ta taimaka mashi yana hayewa ya fad’a jikin ta Feenah na fad’in bai ganin mara lpy ce, a gefen gadon Feenah ta tsaya bayan ta aje basket d’in kayan Abincin data shigo da shi tana sanye da doguwar rigar Atamfa tayi d’aurin kallabi mai steps ga gyale mahad’in kayan ta yafa a kafad’a hannun ta na dama ruk’e da hannun Nasreen da itama tasha yan kanti, da alamun damuwa Abdul dake kallon face d’in Fatuu yace “Aunty Fatuu ashe baki lpy” itama kallon shi take da d’an murmushi ta d’aga mashi kai alamar eh ya juya ya kalli ledar K’arin jini fuskar shi kaman zai kuka idanun shi har sun kawo kwalla yace mata sannu ta rungume shi ta gefe Feenah ma tayi mata ya jiki ta amsa mata kafin ta gaishe da ita Nasreen ta fara rigimar itama a d’aurata kan gadon Feenah tace ya duk zasu haye gadon mara lafiya Fatuu ta mik’o hannu tace ba wani abu ta d’auro ta Fauzy ta kai hannu ta d’aukko ta, ganin Feenah nata tsayuwa yasa Fatuu ce mata “Aunty Feenah ga kujera can ki zauna” d’an murmushi tay tace “bari in gama ganin ki to, ashe abu kuma haka ya faru jiya Dear ke fad’a man banji dad’i ba wllh nace da an sani ai da an tari abun da wuri duk da hakan bai faru ba, shima yace man bai san abunda ke faruwa ba sai jiyan” idanun Fatuu ne suka ciko da k’walla bata dae ce komae ba sai kikkafta idanu take don kada su zubo suna haka Abbas ya shigo dama yana waje wurin gwaggo suna gaisawa, bakin gadon shima ya tsaya Fauzy ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya karatu ya maida kallon kan Fatuu cike da kulawa yace “Mom Zarah ya jikin?” Kallon shi tay a sanyaye tace da Sauk’i,
“Allah ya baki lafiya ashe haka abu kuma ya faru?” Aikuwa kaman tana jira ta fashe masu da kuka dama daurewa kawae take, girgiza kai Abbas ya shiga yi cike da tausayi Feenah ma Fuskarta kaman zata sa kukan Fauzy kuwa tuni kwalla sun ciko mata, sosae Abdul ya rud’e ya d’ago yana fad’in “Aunty Fatuu don Allah kibar kuka zaki samu lafiya in baki yi shiru ba nima zan yi kukan” k’ok’arin shanye kukan ta fara tana girgiza ma Abdul kai alamar kada yayi ya kai hannu yana goge mata kowa jikin shi yayi sanyi Abbas ne yace “Kiyi hakuri Mom Zarah nasan an maki ba daidai ba don da kin sani hakan ba zai faru ba to amman komai ki ka ga ya faru dama rubutacce ne” kallon shi tay cikin muryar kuka tace “Amman Ya Abbas Saboda mi aka 6oye man ko kai ba sai ka fad’i man ba tunda ni ban 6oye maka komai” da alamun Damuwa kan face d’in shi yace “kiyi hak’uri don Allah haka aka tsara ne ba za’a sanar maki ba shiyasa…” Katse shi tay “to Saboda mi?” Shiru yay don bai son yace mata auran tsarawa akai don a taimake ta ba don ya d’ore ba, ba kamar kuma yanzu da abu ya shiga tsakanin su, Feenah ta fahimci Abbas bai son sanar da ita game da auren hakan yasa ta kai hannu tana share mata hawayen dake zubowa tana fad’in “Haba Mom Zarah d’in mu kefa nasan mai k’arfin hali ce kiyi hak’uri komae ya wuce ko ma samu ki warke da wuri a k’ara samo mana cikin wani Baby d’in in sha Allahu ma twins za’a maida mana tunda da yawa wani rabon ke kore wani” d’an murmushi Fauzy tay ta sadda kan ta haka ma Fatuu d’an juyar da fuskar ta tay Abdul kuwa k’ura ma Feenah da tayi Maganar ido yay can ya kasa jurewa ya d’ago daga jikin Fatuu yace “Momy Aunty Fatuu tayi aure ne?”
D’an shiru tay sai kuma tace mashi “Mi yasa ka tambaya?” yace “naji kin ce ta Warke ta haifo babies?” shiru Feenah tay sham ta manta dashi a wurin tay Maganar tasan shi bai ji ya k’yale Abbas kuwa d’an d’age gira yay yana kallon Feenah da murmushi alamar jiran yaji amsar da zata ba Abdul don ya kafeta da ido can ta d’aga mashi kai tace eh tayi aure, waro ido yay alamun mamaki ya juya ya kalli Fatun ya sake juyowa ya kalli Mom d’in tashi yace “Yaushe tay auren ni ban sani ba kuma waye ta aura?” ta biyun ta amsa mashi tana d’an murmushi tace “Baban ka Zakee” har saida yay wata yar zabura ya tsuke fuska cikin fushi yace “Kamm shine sukai auran ban sani ba kuma bani nace ma ya aure ta ba” a hak’ik’an ce yay Maganar sai bin su yake da kallo ya kumburo baki sigh Abbas yay yace mashi “ai ba’a yi bikin ba tukun an dai d’aura masu aure ne…..” Katse shi yay kaman zai kuka “to ni miyasa ba’a je dani d’aurin auren ba ba inada babban riga ba” har saida ya basu dariya su duka Fatun ma saida tay d’an murmushi wato shi a tunanin shi saida babban riga ake zuwa d’aurin aure, kafin wani ya bashi amsa aka turo k’opar da yar sallama k’asa k’asa ya shigo, Wow Tubarkallah Angon Fatuu shine abunda na fad’a, wankan bak’in Voile yay ana d’an hango hasken vest d’in shi kad’an hannun shi d’aure da Agogo ta bak’ar fata haka k’afafun shi dakakkun half cover ne masu kyau da tsada Sumar nan tasha gyara ta k’ara bak’i sai salk’i take, sosae yay kyau tun ma kafin ya k’arasa shigowa k’amshin turaren shi ya baza d’akin kai kace shi kadai kamfanonin turaren suke ma irin nashi don koda yaushe k’amshin shi na daban ne, tunda Fatuu tay arba da Fuskar shi gaban ta ya fara wani irin bugu gaba d’ayan su idanun su na akan shi yayin da Fauzy acikin ranta ta hau fad’in Tubarkallah sam bata ganin laifin Fatuu da take son shi ita a yadda take ji ma da itace abu ya shiga tsakanin su har ta samu ciki wllh bazata zubar da shi ba bari zatai har ta haife tunda tasan bazai ta6a wofintar da ita ba duk surutun da za’ai aje ai ta yi, Abdul na ganin shi ya saukko daga kan gadon ya nufe shi da sauri lokacin har ya zo tsakiyar d’akin a gaban shi ya tsaya yana kallon shi fuska a d’aure hakan yasa Haisam d’in tsayawa yana kallon shi Fuska a sake su Abbas nata murmushi daga inda yake yace ma Haisam “Baba Zakee yau fa ka ta6o d’an gidan ka kay mashi laifi” d’an kallon Abbas da yay Maganar yay sai kuma ya maido idon kan Abdul daya kumbura kamar zai fashe cikin cool voice d’in shi yace “What’s happening?” Ya kai hannu zai dafa kan Abdul d’in da sauri ya janye kan yasa hannuwan shi duka ya ruk’e k’ugun shi alamar dai abun yau baram baram za’ai Abbas kau mi zai yi in ba dariya ba haka ma su Fauzy still Haisam murmushi yake calmly ya furta “kaga dariya suke mana tell me laifin mi nayi?” Yana tura baki yace “ashe dana ce ka auri Aunty Fatuu ka aureta ban sani ba kuma ko d’aurin auren ba’a je dani ba!” Abbas ya amshe da fad’in “kuma dae yana da babban riga ato” duk sukai dariya shima Haisam d’in yar dariyar yay ya kamo hannun shi yana fad’in yayi hak’uri to ya fara bubbuga k’afa k’arshe Haisam d’in ya sunkuce shi ya d’aura shi a bayan shi sai k’unk’uni yake cike da shagwaba, yana zuwa bakin gadon Fatuu ta sunkuyar da kanta Fauzy dake kallon shi ta gaida shi ya amsa tay mashi ya mai jiki haka Feenah ma duk ya amsa Fauzy ta sauka daga kan gadon ta nufi Kujera Feenah ma ta bi bayan ta ya rage daga shi sai Abbas tsaye a bakin gadon, kai idon shi yay kan ta kaman ance ta d’ago suka had’a ido Slowly ya furta “Ya jiki?” a sanyaye tace da Sauk’i ya jinjina kai kawae still da canjin da take gani akan Fuskar tashi, mai da kallon yay kan Abbas dake mashi wani kallo irin na wanda yay abu ba daidai ba shi kuma ya maida mashi martani da nashi mai kaman harara suna haka Dr Habeeb ya shigo cikin d’akin da sallama su Feenah suka amsa had’i da gaishe dashi yay masu ya mai jiki ya nufi su Abbas, hannu ya basu suka gaisa gaba d’aya ya kalli Haisam yay mashi ya mai jiki k’asa k’asa yace da Sauk’i kafin ya d’an matsa gaban gadon da murmushi yace ma Fatuu ya jiki tace da Sauk’i ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay tana jin wani ciwo ko a marar ta haka tace a’a bata jin komae ya k’ara tambayar yanayin jinin da ke zuba da yanayin yawan shi a kunyance take bashi amsa tana yi tana d’an sadda kai don duk su Abbas na ji,
“To ya kike jin yanayin jikin ki?” tace “kawae ba k’arfi ne sosae” jinjina kai yay “Ok sai a hankali k’arfin zai dawo zuwa anjima sai a ida saka maki sauran jinin” kai ta d’aga ya juya kan Haisam yace “Yanzu ina ganin muje ai mata Scanning d’in mu ga” kai Haisam ya d’aga ya juya ya kalleta suka had’a ido sai taga kaman ma harararta yake da sauri ta sunkuyar da kan ta, Abbas ya yi ma Feenah magana kan tazo ta taimaka mata suje wurin scanning tace to ta mik’e su kuma suka wuce tare da Dr d’in, bayan ta saukko daga kan gadon Fauzy ma ta taso lokacin gwaggo ta shigo tazo wurin su tana fad’in bari a bata abunda zata yafa ta wuce wurin jaka ta ciro mata d’an gyalen ta dama kan ta da hula suka tafi Feenah ta tallabo Shoulders d’in ta, a kan hanyar su ne Fauzy ke yin Addu’ar Allah yasa aga cikin na nan Feenah tace ai gaskiya da wuya ne Saboda Dear ya fad’a mata ta zubar da jini sosae gashi cikin dama d’an k’arami ne zai wuya ya tsaya kuma already Dr ma yace masu ya fita, lokacin da suka isa a bakin wurin suka iske su Haisam tunda ta kalle shi sau d’aya ta kauda idon ta Abbas ne yace mata ta shiga Dr d’in na ciki ta d’aga kai ta shiga suma su Feenah suka tsaya a bakin kopar don su jirata daga baya Dr ya fito yace ma su Abbas suje Office, sai bayan wasu mintuna Fatun ta fito Feenah ta tambayi an gama tace mata eh ance za’a tura ma Dr tace Ok ta k’ara kamata suka tafi, Suna zaune a Office suna yar hira aka turo result d’in ya fad’a masu gashi an turo ya fara dubawa bayan wani lokaci ya d’ago ya kalli Haisam yace “ya nuna ba sauran wani abu mahaifar ta is empty so ina ganin kawae taci gaba da shan magungunan tunda tace jinin ma ba mai yawa bane ke zuba yanzu a hankali zai d’auke, in kuma kun fi so ayi mata D&C d’in to wani lokacin yana taimakawa wurin k’ara conceiving da wuri amman dama ciki k’asa da 10 weeks ba dole sai an yi ba indai ba wata matsala haka” Wani kallo Abbas yay ma Haisam cike da shak’iyanci yace “H,Zakee ina ganin ayi matan ko Saboda ai saurin k’ara samun wanin” banza yay ma shi cikin cool voice d’in shi yace ma Dr shikenan ba sai anyi ba ya gode yana fad’in hakan ya mik’e Abbas ma ya tashi yana mashi dariyar iskanci shima Dr Habeeb d’in mik’ewa yay yana yin dariyar don daga baya Abbas yay mashi bayani game da auran da yadda aka samu cikin, saida ya rako su bakin Office d’in yace tayi duk abunda zata yi bada jimawa ba zai zo ya sa mata jinin Haisam ya amsa da Ok kafin suka tafi, Bayan su Fatuu sun koma kan kujera Feenah tasa ta zauna don taci Abinci cikin wanda ta kawo mata ta zubo mata tace ma Fauzy itama ta zuba tana murmushi tace to, tasa Fatuu gaba tay wai sai ta ci shi sosae Abdul ma na gefen ta yana fad’in taci ta k’oshi ta warke su tafi gida tare tay yar dariya suna haka Hajiya ta shigo harda Saude ruk’e da k’aton Basket din kayan Abinci da kuma Tk, Feenah ta mik’e taba Hajiyar wuri don ta zauna, bayan ta zauna idon ta akan Fatuu ta kai hannu ta dafa kafad’ar ta tace “Sannu Fateema kin ji an ja maki jinyar dole” d’an murmushi kawai Fatuu tay ta gaisheta bayan ta amsa taci gaba “an gode ma Allah daya tashi kafad’un ki, jiyan nan ai hankali na ya tashi sosae wllh yarinya tamkar ba rai ga uban jini da kika zubda, to ya jikin naki yanzu?” tana d’an murmushi tace da Sauk’i sosae Hajiya tace “to Alhamdulillah Allah ya k’aro sauk’in, su Dije sun auna Arziki don da wani abu ya same ki duk sai nayi k’arar su an bi maki hakk’in ki wllh duk da haka ba k’yale su zan ba” kowa yay murmushi su Sauden sukai mata ya jiki ta amsa masu ana haka gwaggo ta shigo cikin d’akin d’auke da plastic chairs guda biyu ta aje tace ma Saude su zauna, bayan sun zauna duk suka gaishe da ita Sukae mata ya mai jiki ta amsa masu dama ta gaisa da Hajiya tun a waje tana ta tura baki ta amsa mata, lokacin Abbas da Haisam suka shigo Hajiya ta bisu da wani wani kallo fuska a tsuke Abbas ne kawae ya gaishe da ita ta amsa mashi ba yabo ba fallasa ya kalli gwaggo yay mata bayanin da Dr yayi game da scanning d’in yace ba sai anyi Mata wankin cikin ba taci gaba da shan magani gwaggon tace to in sha Allah Hajiya tace “ai gwara dae kada ayi matan a kyaleta da wahalan da aka d’ora mata ba sai an k’ara mata wata Azabar ba” kowa dae murmushi kawae yake banda Haisam dake tsaye can ya juya zai fita Abbas yabi bayan shi,
Sai da akayi la’asar Abbas ya kira Feenah ta fito su tafi lokacin an k’ara sama Fatuu jinin Abdul yasa rigimar bazai tafi ba shi anan zai tsaya dama da yaga za’a saka mata jinin harda kukan shi da kyar gwaggo ta lalla6a shi tace Asibitin ba’a barin yara su zauna da an ganshi za’a zo a tafi dashi ya bari in suka koma gida sai yazo ya zauna har ta warke gaba d’aya yace to yaushe zasu koma gidan tace bada dad’ewa ba da an sallame su zata kira daddy d’in shi ta gaya mashi sannan ya yarda suka tafi Fauzy tay masu rakiya har bakin Mota, tana niyyar dawowa ciki sai ga Aunty Mareeya mai Keke Napep ya tsaya da ita Fauzy ta nufe su tana murmushi tay mata sannu da zuwa ta amsa tace ta d’aukko basket a ciki tace to, bayan ta d’aukko ta sallami mai Napep d’in suka nufi cikin Asibitin, lokacin da suka shiga d’akin Aunty Mareeya ta gaida su Hajiya da Gwaggo tay masu ya mai jiki suka amsa sannan ta nufi gadon Fatuu na kwance jinin nata shiga ta kalli Aunty Mareeyar da d’an murmushi ta gaishe da ita saida ta zauna a bakin gadon da alamun damuwa tay mata sannu da jiki Fatun ta amsa bayan Fauzy ta aje basket d’in tazo daga d’ayan gefen itama ta zauna Aunty Mareeya ta kalleta k’asa k’asa da murya tace “d’azun kina gaya man abun Al’ajabi ashe duk abunan mutumin nan mijin Zarah ne” gyad’a kai Fauzy tay kawae ta sake cewa “amman dai ni kun yi man rashin hankali wllh haba kaman baku san halin shi ba ai bai kamata kuyi saurin zubar da shi ba” cike da damuwa Fauzy tace “wllh nima Aunty ban so akayi saurin zubar dashi ba…” Nan ta fad’i mata yadda sukai da Fatuu kan zubar da cikin gaba d’aya k’asa k’asa suke Maganar yadda baza’a ji su ba, bayan ta gama fad’i mata ta kalli Fatuu tace “na fahimci dalilin ki Zarah haka Allah ya k’addara amman dae da kin bashi dama kin ji abunda zai ce wllh tunda mutumin nan kin fi kowa sanin halin shi bai kamata ki k’i saurarar shi ba koda ace babu auran yayi maki haka na tabbatar zai yi abunda ya dace ya samar maku mafita bazai ta6a bari ki wulakanta ba nasan k’arshe ma cewa zai ya aure ki kuma ai mu abunda muke so kenan” shiru kawae Fatuu tay ita kanta yanzu dana sani kawae take ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri amman tasan Saboda son da take mashi ne shi kuma sai taga kaman ya fara sha’awarta ne can taji muryar Aunty Mareeya tana fad’in “ni wllh dana san da Maganar bazan bari a zubar ba, ni in nice ma wllh bazan yi tunanin zubar dashi ba yaushe ma ai ko shi yace a zubar bazan yarda ba adai nemi mafita kawae” hannu Fauzy tasa ta gumtse Dariya ta kai hannu ta bugi shoulder d’in ta tace “to uwar gulma ai don kar a akaita laifi biyu na fad’i hakan” cire hannun Fauzy tay tana ta dariya Fatuu ma saida ta d’an yi, Sai bayan Magrib duk suka tafi har da Fauzy tace nan zata kwana gwaggo tace a’a taje gida ta huta tunda ta wuni, a daren Abinci saidae gwaggo ta ba wasu don yayi yawa sosae,
Misalin karfe tara na daren Fatuu na kwance jikinta sanye da english wears riga da skirt bayan tayi wanka ta saka su gwaggo kuma na kishingid’e kan kujera ta kunna Radio d’in wayarta tana saurara aka kwankwasa kopar d’akin gwaggo tace a shigo kopan a bud’e take, da sallama ya shigo bayan ya turo kopar tana ganin shi ta yunk’ura ta tashi zaune tana murmushi ta hau yi mashi sannu da zuwa, shima yayi wanka ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt hannuwan shi ruk’e da manyan ledoji ya nufi daga can wurin drawer ya aje ya juyo yana gaishe da gwaggo ta amsa tare da mik’ewa tace ya zauna ita kuma ta koma gefen gadon ta zauna shiru ta biyo baya Fatuu dae tayi zuru can ya d’ago a nutse yace ma gwaggo yanzu Abbas zai zo zasu koma gida da sauri ta tari numfashin shi tace “a’a baza’a yi Haka ba yau dae ni zan kwana ka koma gida kai baccin ka zurga zurgar da ake ma ta isa tasa a gaji ai” d’an shiru yay yana kallon gabanshi shi bai iya gardama ba can ya d’ago yace mata ba wani abu ai zai kwana da sauri ta sake cewa “yau dae da wani abu gaskiya d’ana Haisam” har saida yay d’an guntun murmushi tace ya kira Abbas d’in yace basai ya zo ba kar yay wahalar zuwa ya furta Ok sai kuma ta mik’e ta nufi hanyar fita, bayan ta bud’e kopar ta fita suka rage su biyu d’akin yay tsit Fatuu dae na kwance lamo can ta d’an d’aga ido ta saci kallon shi yana zaune idon shi na kallon gaban shi tana ta kallon shi can taga yana niyyar juyowa da sauri ta maido idonta, gaban ta ne ya fara fad’uwa Jim k’amshin shi ya fara cika mata hanci alamar kamar yana tunkaro ta har dai taji k’amshin ya gama cika ta gaba d’aya hakan yasa ta d’aga ido da sauri ta ganshi tsaye a bakin gadon hannuwan shi zube a cikin Aljihunan jeans d’in shi gabanta ne ya hau fad’uwa suka k’ura ma juna ido ta fara d’an motsa baki ganin irin kallon da yake mata a dabarbarce tace mashi ina wuni shiru bai amsa ba hakan yasa ta sauke idanun ta k’asa cikin mutuwar jiki, saida ya mula yasha iska sannan taji yace ya jikinta ba tare data d’ago ba ta amsa mashi da Sauk’i taji ya k’ara cewa ko akwae abunda take buk’ata da turanci ta girgiza mashi kai alamar a’a still bata d’ago ta kalle shi ba,
“So this is d result of being stubborn” taji ya fad’a ba shiri ta d’ago suka had’a ido ya d’aure fuska kai kace bashi yay Maganar ba, idanun ta ne suka ciko da k’walla kan kace mi suka fara zubowa shar cikin raunanniyar murya ta furta “kayi hakuri” shiru bai ce komae ba idon shi akan ta itama kallon shi take k’wallan na cigaba da zubowa can kawai sai ya juya ya nufi hanyar fita ta bi bayan shi da kallo yana ficewa ta kife fuskar ta a jikin pillow ta saki kuka mai cin rai, sai bayan wani lokaci taji shigowar gwaggo hakan yasa tay saurin shanye kukan ta gyara kwanciyar ta ta yadda taba gwaggon baya, ledojin da ya kawo ta shiga bud’awa su Fruit ne da uban nama harda su shawarma da ice cream har saida gwaggo ta d’an girgiza kai ta d’auki shawarma guda da ice cream ta nufi gadon, a gefe ta zauna ta kira sunan Fatun shiru bata amsa ba har saida ta k’ara sannan ta amsa k’asa k’asa tace ta tashi ga shawarma da ice cream tasan zata ji dad’in su ba tare data juyo ba tace mata ta k’oshi gwaggon tace “to ai in aka bar su lalacewa zasu yi” daga yadda take tace mata ai akwae fridge ko sai a saka bazasu yi komae ba, shiru gwaggon tay tana kallon ta kaman mai nazarin wani abu can ta kira sunanta ta amsa tace ta tashi zaune har saida gabanta ya fad’i bata da yadda zatayi dole ta yunk’ura ta tashi kan ta a k’asa,
“Kuka kike yi ne?” Gwaggo ta tambaya da sauri ta girgiza mata kai tana k’ara d’ukar da kanta, d’an jimm gwaggon tay kafin tace “miya faru ne ko kina jin wani ciwo ne?” Nan ma kai ta girgiza,
“in baki fad’a man damuwar ki ba wa zaki fad’a mawa ko kin fi son ki 6oye abu har wani ciwon ya kama ki?” jin yadda tay Maganar a tausashe yasa ta d’ago ta kalleta idanunta cike da k’walla cikin karyayyar Murya tace “Ya Haisam ne ke fushi kan abunda ya faru” d’an guntun murmushi gwaggon tay tace “to ba dole yay fushi ba ko ke baki ga laifin da kika aikata mashi ba, ba d’azun nan naji kina fad’a ma Fauziyya saida yay ta kiran ki harda sak’o ya tura maki amman kika k’i saurarar shi sai ke yanzu kike son ya saurare ki kome?” Shiru bata ce komae ba k’walla na zubo mata gwaggo taci gaba “ni kaina da naji hakan in fad’a maki gaskiya ban ji dad’i ba wllh nayi zaton zaki amfani da hankali kafin ki yanke hukunci” cikin muryar kuka tace “Gwaggo ni ban sani bane nayi zaton hakanan hakan ya faru shiyasa naji tsoron abunda zai biyo baya gashi Makaranta har an fara gulman ciwon da nike ina tsoron abun ya fito in samu matsala ga kuma ke da kuma zumuncin dake tsakanin ku da Hajiya da kuma surutan mutane in aka sani shiyasa na k’i saurarar shi don nasan yana iya cewa in bar shi” 6ata rai gwaggo tay sosae tace “wato kin fi tsoron wad’annan abubuwan akan Mahalliccin ki? Ko baki san girman laifin zubar da ciki ba?” d’an yarfa hannu tay “na sani gwaggo naga cikin k’arami ne sosae kuma bada son raina na same shi ba sannan in na barshi zan fuskanci matsaloli da yawa shiyasa naga gara in zubar” d’an ta6e baki gwaggo tay “baki tunanin matsalolin shi kuma zubar da cikin ba? Baki tunanin har ranki zaki iya rasawa ba?” shiru tay ta sadda kai gwaggo taci gaba “nayi mamakin duk irin yardar dake tsakanina dake har kika iya 6oye man wannan babban Al’amarin ashe zaki iya cutar dani har haka Fatuu??” A rud’e ta fara girgiza mata kai k’walla na zuba ta kai hannu ta kamo hannunta guda tace “a’a gwaggota don Allah kar kice haka wllh tallahi kin ji na rantse bada son raina nayi hakan ba saboda gudun matsalolin da zasu biyo baya ne kuma wllh ke na fi ji ma Saboda ni bansan ya aure ni ba nayi tunanin in kika ji zaki shiga mawuyacin hali ne Saboda kina yawan gargadi na da bani misali da yar wajen aikin ki gashi naga kuma shi an yarda dashi an amince mashi hakan yasa naji tsoro don nayi tunanin zuciyar ki ma zata iya bugawa wllh wannan ne dalili amman Allah ne shaida ta ban ta6a yunkurin aikata abu makamancin wannan ba, wllh gwaggo ko saurayi bani dashi duk da ana yawan nuna ana so na amman ban saurarar su balle ta kai ni ga aikata wani abu ba daidai ba shi kan shi koda muka je can G.r.a d’in raina bai so in shiga ba kawae don na yarda dashi nasan bazai cutar dani ba yasa na bi shi” yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace “amman miyasa tunda abun ya faru baki sanar da ni ba in har akwae yarda a tsakanin mu, washe garin ranar har d’akin ki nazo da safe kika nuna man kan ki na ciwo miyasa baki fad’i man ba sai kika za6i ki 6oye man k’arshe ma kika gudu Makaranta wannan abun ya ta6a ni Sosae bazan 6oye maki ba yasa na fara tunanin zaki iya cuta ta” idanunta ne suka ciko hakan ya k’ara tada hankalin Fatuu ta k’ara k’ank’ame hannunta dake cikin nata a rud’e tace “a’a gwaggota kar ki wannan tunanin a kai na don Allah wllh bansan taya zan fad’i maki abu irin wannan ba ina tsoron wata matsala ta biyo baya ne banson in rasa ki kaman yadda na rasa Mahaifiyata ke nike gani madad’in ta ban son rasa ki gwaggota ganin Al’amarin na da girma, ki yarda dani Don Allah wllh ban taba munafuntar ki ba kinji na rantse” sosae take kuka itama gwaggon har kwallan sun fara zubo mata can ta sa hannu ta fara goge ma Fatun k’wallan ta tace “shikenan ya isa kar kija ma kan ki wani ciwon amman daga yanzu kar ki k’ara 6oye man koma miye da ya shafe ki zan fahimce ki tunda ai ni musulma ce na yarda da k’addara mai kyau da kuma mara kyau komi ya faru da bawa dama can an riga da an rubuta tuni alkalumma sun bushe ko wata matsala gare ki kar Kiji komae ki fad’a man in inada iko sai in maki maganin ta in kuma ban iyawa sai in taya ki rok’on mai kowa da komae tunda shi yace mu rok’e shi zai amsa mana wannan shine amfanin Mahaifiya daga inda ta gane kana 6oye mata abubuwa kana rushe yardar da ke tsakanin ku ne” da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tace “in sha Allahu bazan k’ara 6oye maki komai ba mahaifiyata” hannu gwaggon ta bud’e mata tana murmushi ta fad’a jikinta ta rungume ta sosae wata irin natsuwa zukatan su suka samu sun d’an d’auki lokaci a haka kafin gwaggo ta d’agota tana fad’in tasan halinta yanzu ta kama yin bacci Fatun tay murmushi, warware mata shawarmar tay tace “ki saki jikin ki kici tunda dae shi ba sanin baki cin zai yi ba nasan kawae yana maki hakan ne don ki gane kin yi mashi ba daidai ba amman nasan zai fahimce ki sai kuma muga abunda Allah zai yi dangane da Al’amarin auran na ku” shiru Fatun tay ta mik’a mata shawarmar ta amsa ta fara ci a hankali, tana cikin ci tace ma gwaggo itafa in ba wata shawarmar su ci tare tace akwae zata ci, matsa mata tay saida ta d’aukko harda youghort ta k’aro ma Fatun, suna cikin ci Fatun ta tambaye ta yadda akai Ya Haisam d’in ya aureta tana murmushi ta fara bata labari tiryan tiryan har ta gama, sosae Fatuu ta jinjina abun a ranta wato ashe ma taimakon ta yay ita dama abun ya matuk’ar d’aure mata kai data ji wai ya aureta gashi yanzu abunda ya k’ara bata mamaki irin kud’in da ya biya matsayin sadaki nan take taji bata ji dad’i ba data 6ata mashi rai saidae ta wani bangaren kan ta ne ya kulle kan tunanin dalilin da ya sa bai sake tan ba kamar yadda aka tsara har abu yazo ya shiga tsakanin su, kamar gwaggo tasan abunda ke ranta taji tace “nayi zaton bayan auren zai sake ki to amman sai bai yi hakan ba k’arshe har Abbas na tuntu6a don yay mashi Magana Saboda kar kici gaba da karatu ga auren da baki sani ba akan ki amman sai ya nuna a k’yale shi kawae tunda ai yasan da hakan aka tsara k’arshe ma sai ya nuna shi dama yafi son auran ya d’ore to farko dae ni gaskiya ban so ko don Saboda Matar shi ganin amincin dake tsakani to amman kuma daga baya sai nay tunanin in hakan Allah ya k’addaro ba yadda za’ai” kallon Fatuu tay da ke taunar abu a hankali tana saurarar ta wani murmushi tay tace mata “Ke ma kina son auren ya d’ore ne??” Waro ido Fatun tay ta dakata da taunar abun bakin ta batay tunanin zata mata wannan tambayar ba, ganin yadda ta kafeta da ido alamar jiran amsar ta yasa ta girgiza kai a hankali alamar a’a, wata dariya taga gwaggon tayi har saida ta tsargu ta bita da ido can ta furta Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi daga haka ba wanda ya k’ara cewa komae suka cigaba da cin abubuwan da Suke ci har fruit da naman gwaggo ta k’ara d’ebo masu saida suka ci suka k’oshi sauran ta saka acikin Fridge dake a d’akin, bayan sun gama Fatuu taje tayo brush lokacin data fito har gwaggo ta gyara mata gadon ta maida brush d’in ta haye gado ta kwanta gwaggo ma saida ta wanko bakin bayan ta fito ta d’aukko bargo ta rufa ma Fatun kafin itama ta fiddo wani bedsheet ta nufi kujera tana fad’in tunda harda fruit suka sha tasan zai taimaka wurin saurin narkar da abunda suka ci tunda ba’a son da an ci Abinci a kwanta gashi bacci take ji ta haye kujerar bayan tayi Addu’oi ta tottofe a 6angarorin d’akin ta kwanta, lamo Fatuu tay tana tunanin masoyinta ta ayyana tunda take dashi ba abunda ke shiga tsakanin su face Alkhairi amman bata ta6a tunanin zai amince ya aureta ba don kawae ya taimaketa wani kalan son shi taji ya ratsa zuciyar ta har saida ta lumshe ido Slowly ta furta “Am so sorry for my mistake Ya Haisam and my beloved husband also” wani irin murmushin dad’i ta saki nan ta fara tariyo abunda ya faru tsakanin su a G.r.a tun farko da suka fad’a saman gadon da lokacin da tay mashi magana taji shiru bai ce komai ba ta kai hannu ya nutse cikin sumar shi mai taushi ga santsi wani irin dad’in ta6awa ne da ita, a hankali ta gangaro kan lokacin da ta bud’e baki don sake yi mashi magana bata samu damar k’arasawa ba ya had’e lips d’in su wannan karon kankame jikinta tay tunowa da yadda ya rink’a bata hot and deep French kisses the way she felt at dat moment was like her breathing would cease, haka tay ta tunano abubuwan da suka faru wani lokacin tay murmushi wani ta tsuke fuska wani ta kankame jiki a haka har bata san lokacin da bacci yay awon gaba da ita ba………..
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.