Assalamu Alaikum masoyan wannan shafi namu mai Albarka barkanmu da kasancewa daku a wannan lokaci, To kamar yadda kuka gani mun sanar wannan muhimmiyar sanarwa ce daga kamfanin MTN, wanda yadace duk mai amfani da layin mtn ya kamata ya sani.
Kamar dai yadda gwamnatin Nigeria ta sanar da hukumar sadarwa dasu garkame dukkan layukan daba’ai linking dinsu da NIN number ba, Wanda silar hakan yayi sanadiyar kullewa layukan mutane sama da mutane miliyan saba’in da biyu 72Millions.
Kamar yadda aka sanarwa kowane kamfanin layi dasu rufe layukan mutane wadanda ba’ai linking dinsu da NIN-Number ba kuma suka rufe din, to hakan ya sanya wasu gurbatattun mutane suka fito da wani sabon salo domin su yaudari mutane ta hanyar fitar da link wanda suke yadashi a kafafen sada zumunta na sadarwa wanda suke yadashi da cewa ka shiga link din domin ka hade layinka da NIN-Numbar ka, kokuma ka bude layinka idan An rufe maka shi.
Dalilin hakan ne yasa kamfanin MTN ya fitar da wata sanarwa ta mussaman a yau.
Kamfanin MTN din sun fitar da sanarwar gargadin cewa,” suna gargadin mutane akan wannan link din da ake turawa mutane subi domin su hada numbar su da NIN-Number, don haka Muddin kaci karo da irin wannan links karka shiga domin ba daga su bane, su basu fitar da wani links da zakabi ka hada layinka da NIN-Numbar kaba dan haka kar mutum ya kuskura yabi irin wannan links din da zarar ya ganshi, saboda links ne na ‘yan damfara masu satar bayanan mutane Dan haka a kiyaye”.
Ka Haɗa Nin Number Ɗinka Da Sim Ɗin ka Amman Har Yanzu Baka iya Yin Kira – Ga Yadda Zaka Yi
Daki-Daki: An sake Bude Shafin P-YES Domin Bada Tallafi Daga Gwamnatin tarayya
10 Things You Should Know About Mubarak Bala
Kamfanin MTN din sun kara dacewa indai bata wannan hanyar kayi linking layinka da NIN-Numbar ba to basu katurawa bayanan kaba dan haka ba ruwansu ga hanyoyi da suka bayar kamar haka:-
HANYOYIN DA ZA KUBI WAJEN HADA LAYIN KA DA NIN-NUMBER NA MTN SUNE KAMAR HAKA:-
(1) Zaka danna *785# sai NIN-Number
(2) Zaka iya tura sako ta hanyar rubuta NIN da manyan Baki, saika tura zuwa wannan number 👉785
misali kamar haka:- NIN 60835671490
Send to 785
(3) Ko kuma kayi magana da wakilansu koka kirasu ko kuma kayi magana dasu ta whatsapp da wannan numbar:- +234903300001
Domin a hadama layinka da NIN-Numbar ka
(4) Ko kuma ka ziyarci website dinsu kamar haka:- www.mtn.Ng
(5)ko kuma ka dauko Application dinsu Mai suna My MTN App ka hada NIN-Numbar ka da layinka ta ciki hankalin ka kwance.
Wadannan sune hanyoyi guda biyar da zaka iya hade layinka na MTN da NIN-NUMBAR ka, sabanin wadannan hanyoyi guda biyar da suka bayar to sunce ba daga su bane, dan haka ‘ Yan uwa sai a kula da kyau sosai-sosai.
Sannan a karshe sukace suna sake shawartar mutane akan duk abinda mutum bai gane ba game da hada layin sa da NIN-NUMBAR SA, Abu mai sauki kawai yaje office na MTN mafi kusa dashi.
Allah ya Ubangiji ya bada Sa’a Amin.!!!
Muna godiya da ziyartar wannan shafi Mai Albarka ‘Yan uwa kuci gaba da bibiyarmu a wannan shafi domin samun sabbin labarai daga sassa daban-daban da kuma samun sabbin abubuwa da suka danganci Technology da hanyar samun kudi online.
Mungode.!!!