Zakuna Biyar Page 6 By Princess Teema
A shagwaɓe V ta ce. “Daddy’s boy mu idan an ɗauko mu a mota ba’a gudu saboda ina tsoro, please go slowly”. Ai ina bai ma san suna yi ba, bai canza daga yadda ya fara tafiyar ba har koma wajen barrack ɗin, a kusa da wasu zaratan sojojin da suka kame kam ganin motar GAT ya tsaya. Slowly ya sauke glass ɗin motar, cikin mutuntawa ya sara masu while suma ƙoƙarin sara mashi suke yi a tinaninsu GAT be tin da sun san shi yake ɗauko yaransa. Tambayarsu ya yi ina ne gidan GAT, kallon juna su V suka fara yi, sun ji daddaɗar murya, Angelina ce cike da mamaki ta matsa kunnen V, raɗa ta fara yi mata. “Buddy watau baya magana da mata ne shi? Kin ga yana tambayar wasu gidanmu, but yaki yi mana magana”. V da ta gama marairacewa ne ta amsa da. “I felt so bad my love, ni ban yi mashi laifi ba, but why yaki yi mana magana?”……… Dik basu ji daɗin yadda yaki ya yi magana da su ba, musamman V, Angelina and Manassa, sun fola mashi matuƙa, ya haɗu amma dan iskanci ya cika mashi ciki ko kallon in da suke bai yi ba.Suna nan suna gulmansa shi kuwa har mashi kwatance, dan haka ya figi motar da gudu, V tamkar zata yi kuma, ta sake cewa ya tafi a hankali ita da Manassa suna tsoro, ba’a gudu da su a mota, amma Leo tamkar babu shi a motar, bai tsaya ba har ya isa kofar katafaren ginin gidan GAT wanda tin daga nesa zaka hango wasu jiga-jigan sojoji wanda tamkar yakin duniya na uku za’a tafi, yanayin tsarin ginin ya yi matuƙar kyau sosai, bene ne hawa uku.Horn yai, a take wasu shirga-shirgan sojiji suka wangale katafaren gate ɗin, ba ɓata lokaci ya kutsa da su ciki. A katafaren parking lot na gidan ya faka motar, yadda kuka san gabaɗaya sojojin barrack ɗin a gidan suke, gidan cike yake da ƙosassun sojoji, ta ko’ina suna shawagi.Yana kashe motar ya ɗauki daddumarsa ya fito da sauri, bai sake bi ta kansu ba ya nufi gate, yana zuwa ya kame ya sarawa sojijin dake bakin gate ɗin, a matsayinsa na matashin soja kunga dole ya girmamasu tin da yanzu manya suke a kansa, sai sun kammala horo ya ga da irin result da zai fito, a nan ne zai san ya fi su matsayi ko sun fishi.Ɗan jinjina mashi kai suka yi, daga nan ya fice rike da key ɗin motar a hannunsa, kai tsaye ya wuce office na GAT dan ya mayar mashi da key ɗin motar kamar yadda ya bashi.Su Arya kuwa, yana kashe motar ya fito V tai saurin fitowa ita ma, bayansa ta bi da kallo tana yaba jiji da kai irin na guy ɗin nan, har sai da taga ya fice daga gidan, sannan ta juya, tana juyowa suka haɗa ido da Angelina da Manassa dake tsaye suna kallonsa suma, Arya ce kawai bata fito ba, saboda ya ɓata mata rai.Da sauri V ta wuce ciki tana murmushi, a ranta tana ayyana yadda zata sace zuciyar guy ɗin, sai kuma ta turo baki da ta tina baya kallon mutane ma. Angelina ce ta rufawa V baya cike da tinanin haɗuwarsa suka nufi ciki, ita kuma Manassa ta jawo hannun Arya tana tausanta, da kyar ta yarda suka fita, kai tsaye wani katafaren down parlo suka shiga, komai na cikin parlon ligh ash ne mai ɗan banzan kyau, ya ji komai na more rayuwa, ga wani fitinannen kamshi da yake tashi mai tsananin kwantar da hankali.Babu kowa a parlo, dan haka sama suka haye, wani katon parlo ne a saman mai ɗauke da manyan ɗakuna guda huɗu, ɗaya na daddynsu, ɗaya na su, biyun ɗaya na masu aikin dake kula da su, komai dare suka buƙaci abu masu aiki zasu kawo masu, shiyasa suke a kusa da su, ɗayan ɗakin kuma babu kowa, in case dan baki aka yi shi.Kai tsaye room ɗinsu suka shiga. Ya ilahi, room na ƴan’matan nan ya yi bala’in haɗuwa, komai 4 ne a cikin ɗakin, yana da girma sosai, beds ɗinsu guda huɗu ne, biyu ta left side na ɗakin, biyu ta right, a tsakiyar kuma glass door na balcony, daga side na left door na toilet yake, right side door na closet ɗinsu yake, komai na cikin room ɗinsu sky blue ne, ko’ina tsab-tsab, da alama suna da bala’in tsabta sosai, ga wani kamshi mai daɗi da yake tashi.Left side Arya ta nufa, a saman bed dake shinfiɗe da tsadadden bedsheet na alfarma pink color ta zauna, hannayenta biyu ta sanya ta dafa kumatunta tana wani irin huci ƙasa-ƙasa, a ƙasan zuciyarta ita kanta yaba kyan Leo take yi, amma ji da kai yasa taki yardan shi mai kyau ne. A gefenta Manassa ta zauna tare da dafa shoulder ɗinta, a natse ta ce. “Sorry bloody, I feel your pain”. Angelina dake ƙoƙarin karisawa right side ne ta ce. “It hot me too”. Ta karisa magana tare da zama a gefen bed ɗinta. Watau da Arya da Manassa sun fi shiri, su ne a left side, da Angelina da V su kuma beds ɗinsu a right, su sun fi shiri, suna da saukin kai sosai.Wani irin nisawa Arya tai tare da miƙewa tsaye, cikin fushi ta ce. “Arya! Me Arya? This stupid zai walaƙanta? Wlh sai ya yi danasanin sanina, in dai boy ɗin daddy ne, sai na gigita rayuwansa, sai ya yi kuka, nasa ya durkusa ƙasa a gabana ya ban hakuru”. Ta dakata tana huci, sai kuma ta sake cewa. “Calm down Arya, calm down babyn daddynta”…… Watau ita da kanta ma rarrashin kanta take yi, kai Arya duniya. Da gudu su V suka yo kanta, rurrungumeta suka yi suna faɗin calm down, calm down.Sun ɗan jima a haka kafin su saki juna, a natse suka hau cire uniform ɗin nasu, babu kunyar juna suka cire kaya a gaban juna, ya rage daga su sai pant, kuma breast ɗinsu ya fara girma da zama na matasan ƴan’mata, but they don’t care suka tsaya ba riga a gaban juna. Da yake V bata kaisu tsawo, sun ɗan fita kaɗan, sai breast ɗinta ya fi nasu cika, ta ɗan fisu ƙiba, harta mazaunanta ya fi nasu cika, ga shape kam kamar su suka bawa kansu, cikinsu tamkar babu hanji a ciki.Dikkansu suka ɗauki white bathrobe suka sanya a jikinsu. A daidai lokacin wasu matasan ƴan’mata su biyu suka shigo room ɗin bakinsu a ɗauke da excuse.V ce kawai ta amsa masu, karisowa ciki ƴan’matan suka yi suka hau tattare uniform da su V ɗin suka cire, kai tsaye laundry suka kaisu, sannan suka sake gyare ɗakin fes kafin su shiga wajen closet ɗinsu. Su kuma one by one suka yi wanka, dik wacce ta fito a tsakar ɗaki take ajiye bathrobe ɗin ta hau shirinta, waɗan nan ƴan’mata suke tattare komai. Cikin wasu gajerun jeans trousers suka shirya, sai ƴan rigunar da suka tsaya masu a waist ɗinsu launin white, komai nasu iri ɗaya, fitowa suka yi, Angelina ta gyarawa V gashin kanta, ta shafa mata man kamfanin STARS LADIES HAIR CREAM, kayan gyaran gashinsu mugun gyara gashi yake yi, yana ƙara mashi tsawo da sheƙi, STARS LADIES LUSH zaɓin dik wani ƙasaitacce ko hamshaƙiyar mace mai ji da kanta! Dan ɗan karen tsada ne da shi, kuma kun san abu mai kyau dole ya yi kuɗi ai.Tana kan gyara mata gashin kan nata ne V ta ɗauki robar lotion guda ɗaya, a fili ta ce. “I wish ko sau ɗaya ne zan gansa, Angelina I really like this guy, mura ne”……. Siririn tsaki Angelina ta ja. “V ban san yaushe zaki daina wannan dream ɗin naki ba”……. Shiru ta yi dan babu wanda zai iya fahimtar zuciyarta sai ita kaɗaita. Shiru ɗakin ya ɗan yi na ƴan mintuna suna karisa shiryawa.Bayan sun kammala gyara gashinsu da shafa mayukansu, sai suka ɗaure gashin kamar yadda suka saba, su rabashi kashi biyu, su ɗaure ta sama su kuma kitsa jelar, sai ƙarshen bakin jelar ma su ɗaure da rebon kalar kayansu kafin su watso jelar ta saman shoulders ɗinsu, dikkansu kuma suna da wasu gajerun gashi ta gaban goshi wanda yake kwance masu luff tamkar an kifa hula har zuwa daidai kusa da idanunsu, dik bayan sati suna rage mashi tsawo dan kada ya yi tsawo sosai ya kamo na baya, musamman da suke amfani da STARS LADIES HAIR SHAMPOO AND HAIR CREAM, a take gashinsu yake ƙara tsawo over, dik da kowani sati suna rage tsawon gashin nasu, amma a haka yanzu ya kusa kai waist ɗinsu tsawonsa. Sun yi bala’in kyau cikin shigarsu, kamar ka sacesu ka gudu, sai tashin kamshi suke yi, ƙasa suka sauƙo a natse, dining room ɗinsu suka nufa. Already an shirya masu komai dan yin lunch. Zazzaunawa suka yi a saman chairs, dikkansu a tare suka fito da chain dake wuyansu, suka rufe idanu dan yin addu’a, bayan sun kammala suka ɗan manna chain ɗin a gaban goshinsu kafin su miƙa hannu suka ja plates ɗinsu da already aka yi saving ɗinsu. Kowa ya ja plate ɗinsa ban da Arya da tai shiru tamkar mai tinanin wani abin. Angelina ce ta katse mata shirun da cewa. “Bloody Is there any problem?”. Wani iska mai zafi ta furzar daga bakinta kafin ta amsa da. “Angelina, this guy made me feel ashamed, I will never forgive him, I will teach him a lesson, he will know that he touched Arya, the first daughter of GAT”. Da sauri dik suka miƙe suka yi kanta, rurrugumota suka yi, suka haɗe baki wajen tausanta, dakyar suka samu ta sauƙo ta fara cin abinci. Cikin nishaɗi game da class suka ci suka ƙoshi kafin su miƙe su koma sama. Suna shig room ɗinsu kowacce ta fito da haɗaɗɗen laptop ɗinta mai shegen kyau, sannan kowacce ta haye saman bed ɗinta, Arya ta shiga practical a kan aikinsu, V ta shiga karance-karance labaran soyayya abinta, dan ita mayyar soyayya ce. Dr Manassa kuma ta makale Arya wai tana son koyan aikinsu, Arya na koya mata, ita ma kuma tana koyawa Arya ɗin irin nasu aikin.Kowace ta natsa cikin abin da take yi sun maida hankulan su gabaɗaya kan laptop dinsu. Can V tayi yar kara mai cike da nishaɗi tana fadin. “Arya come and see, I tried something kuma da alama zan yi nasara………………. Mayun computer ba! Da sauri suka ɗago da kallonsu a kanta, Angelina ce ta fara saukowa kasan gadonta da gudu ta nufi gadon V. Tana zuwa ta haye tana faɗin. “Me kika samo mana……..”. Bata iya karasa maganar ba ta dakata cak a lokacin da idanunta suka sauka akan laptop dake gaban V. Zazzaro ido sosai tayi cike da mamaki ta ce. “V what am I seeing? Wannan ba hukumar su daddy bane? Akansu zaki fara aiki? Zaki musu kutse cikin kundinsu! Shi zaki datsa? meyasa to? Baki da hankali ko? Bari idan manyan jami’ai suka kamo ki fa kinsan hukuncin ki ko? Tin baki je koina ba kin fara datsa kundin su daddy? To me zaki yi a cikin da ki ka shiga?”. Cike da tashin hankali da ruɗu ta faɗi waɗannan maganganu. Hakan ya sa su Arya sukai gaggawar dirowa kasa daga saman gadonsu, gadonta suka haye su ma.Kowannensu burin shi kawai yaga me ta aikata, yarinyan akwai ƙwaƙwalwa na faɗa muku, akwai baiwa ne, dik cikinsu ita da Arya sun fi su kaifin kwakwalwar sosai, sauran ma ƴan baiwa ne, amma na Arya da V daban ne.Zazzaro ido Angelina da Manassa suka yi, ita kuwa Arya cikin gaggawa ta kai hannu kan laptop ɗin, da sauri ta rufewa bibiyar V kafin ta ce. “You’re not serious at all, kin bar komai a buɗe, bari GI (General na sashin secret service ɗin, shi ne GI, General Ibrahim) bari ya ankara da an kutsa cikin hukumarsu su bibiyeki zaki gane ne!”. Ta ɗan dakata tana harararta kafin kuma ta sake cewa. “Me kika shiga yi a kundinsu?”. Turo baki ta ɗan yi, wai bata ji daɗi ba an mata faɗa, kuma bata ji daɗi ba da Arya ta gyara mata, so take ace ta kware a kan komai ba sai an taimaka mata ba. A shagwaɓe sosai ta ce. “Guy ɗin ɗazun fa zan bincika, ina son sanin wanene shi? A wani sashi da wace tawaga yake? And Ina son pics ɗinsa”. Wani irin faɗuwar gaba Arya ta ji jin V ta ambaci Leo, Amma ta daure da cewa. “Uhm ba wani tsiya bane, for sure karan farautan daddy ne!”.V dake aikin kara kutsawa cikin kundin ne ta amsa da. “Impossible Arya, this guy doesn’t looks like Daddy’s boys, I think wani guru ne, but let me see”…………. Zuba mata idanu dik suka yi, ta cigaba da kutse…… Silent for like 3 mins ne ya biyo baya, lokaci guda V ta fasa kara mai cike da murna tare da cewa. “Yes! I got it, I am Vanisha General Thomas, the daughter of her dad, guys clap for me”. Tafa mata ɗin suka ɗan yi kafin Arya ta ce. “Who’s he?”. Ta faɗa cike da matsuwar son jin wanene shi!….. Jawo laptop ɗin da kyau V ta yi, a bayyane ta fara karanta masu waye shi. “NIRASH MUHAMMAD HAIZA’AN, sabbin jami’an dake kan horo, number ɗauka 1″. Ta ɗan dakata tare da ɗagowa ta kalli Arya. Manassa da Angelina kam sun mutu a kallon pic na Leo dake gaban screen na V, dan ta fito da hotonsa da dik wasu bayanansa tana dubawa, sai suka kura mashi ido, dikkansu sai santin kyansa suke yi, musamman hajiya Arya, gabaɗaya zuciyarta ta susuce, tin ɗazun dauriya ce kawai take yi, amma ko ido ta rufe fuskan Leo a kusa da ita take gani, musamman yadda ya ɗago idanu ɗazun ya kalleta, ya ilahil alamina, ya tashi kan ƴan’matan GAT.”Ainahinsa ba ɗan nan bane, ɗan Us ne, New York City, yana da mark a sunansa, which means jami’i ne na musamman a tawagarsu! But mark ɗin ma da alama jiya ko yau aka sanya mashi, in zan canka daidai daddy yana gwada shi ne saboda yana tinanin ɗan baiwa ne!”. A cewar V kenan, ta karisa koro masu bayanai a kansa, cike kuma da nata hasashen da kwakwalwarta ya bata.Manassa ce ta ce. “Meyasa kika ce daddy na gwada shi?”…… V dake ƙoƙarin ciro hoton Leo ne ta amsa da. “Saboda ya je ɗaukarmu mana, kin taɓa ganin daddy ya tura wani ya je ɗaukarmu ne? For sure dad yana gwada guy ɗin nan ne”. Arya dai ta yi shiru, ita kaɗai tasan me ainahin abin dake cikin zuciyarta, amma ta ji takaicin da ya kasance Leo ba boy ɗin daddynta bane, bata so haka ba, yanzu Leo yana kan horo ne, kila ya fito da result mai girma da ba z kaskanta a gaban daddynta bama bare har ta walaƙanta shi, takan iya yiwuwa ma ya fito a sashe na musamman.Ganin ta yi shiru ne yasa suka fara tambayarta meyake faruwa?. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu komai. V ta ce. “Bloody I wish mu samu number guy ɗin nan, da na mana kutse cikin wayansa mu sato hotunansa”…… Da sauri Angelina ta amsa da. “Let daddy comeback, zamu samu number ɗinsa a phone na dad”. Zamewa Arya ta yi ta koma saman bed ɗinta, ta zauna shiru, ita kanta bata san me yake yi mata daɗi ba, afkawa tai cikin tinanin da bata san na menene bane. Bata ankara ba sai ji ta yi an taɓata, da sauri ta ɗago kai, sun kewayeta suna kallonta cike da tausayawa. Manassa ce ta ɗan rungumota game da cewa. “Bloody you should stop thinking about this guy, we know he did wrong to you, amma tin da yanzu ɗaukar fansa ba zai yiwu ba ki bari mana akwai gaba ai”.Nisawa ta ɗan yi before ta ce. “Ba zaki gane bane, zuciyata tafasa take yi idan na tina yadda na yi magana ya shareni, kina ganin kowa so yake yi in kula shi, amma shi wannan har ya samu nai mashi magana, ya walaƙanta ni, okey yanzu da students suna nan ma haka zan ji kunya a gabansu?”. Tamkar zata yi kuka ta faɗa, da alama tana da riko da zafin zuciya.Hakuri suka dinga bata har ta hakura ta sauƙo, sannan suka koma kan abin da suke yi. Karfe 5 daidai suka fita zuwa mini gym ɗinsu dake ƙasa kusa da pool ɗin gidan. Sai da suka yi push-up guda 30, sannan suka fara ɗaɗɗaga ƙananan karafuna, dik sojojin dake gidan babu wanda yake ɗaga idanu ya kallesu saboda tsoron shiga matsala, amma kuma wlh dik sojan da ya yi aiki a gidan GAT sai ya so yaran nan kamar ya mutu, musamman Arya da V, suna da shegen shiga rai, sai dai soja ya yi ta dakon soyayyarsu ba samu zai yi ba.Dik in suka fito gabaɗaya hankulan sojojin nan tashi yake yi, su yi ta faman satar kallonsu, kuma dik masu tsaron gidan na GAT matasa ne masu ji da lafiya da karfi, kunga kuwa dole kunamar bindigarsu ta dinga harbawa idan suka gansu. 2 hours suka ɗauka suna gym, sai karfe 7 suka ɗan yi linƙaya cikin pool saboda gumin da suka haɗa na wahalar motsa jikin, sannan suka fito, jikinsu dik ruwa suka nufi cikin gida. A zahiri idan kuka ga soldiers ɗin nan zaku zaci ƙasa suke kallo, amma dikkansu harta waɗan da suke shawagi a tsakar gidan, na bakin gate dik kowani taku nasu Arya ɗaya a kan idanunsu, su kuwa bama su san suna yi ba, sai hira suke yi cike da kaunar juna suka wuce ciki.Zuna zuwa suka sake yin shiri cikin kaya iri ɗaya, sannan suka ɗan taɓa karatu kafin su je yin dinner.A ɓangaren Leo kuwa, ransa gabaɗaya a ɓace, dama ga wahalar da suka ci yau, tin da ya zo GIDAN SOJA bai taɓa cin wahala irin na yau ba, kai tsaye office na GAT ya nufa. Da ya je sai da ya tsaya a waiting room, ya tura saƙonsa na son ganin GAT, sannan ya yi zaman jiran a bashi izini. Izinin da bai samu ba kenan tsawon awa biyu, kuma GAT na zaune cikin office ɗin yana kallonsa ta camerar dake waiting room ɗin, so yake ya gwada hakurin Leo, dan yasan irinsu suna da zafin kai da rashin hakuri. Amma ga mamakinsa sai ya ga Leo ya jure zaman jira, in short ya gagara gane alkiblar Leo ɗin ne ma, kansa ta ɗaure gaskiya, sai ya ce bari sun kullah kenan, sai ya san shi ciki da waje. Bayan awa biyu yasa aka shigo mashi da Leo ɗin. A gabansa ya tsaya tare da sara mashi, jinjina kai ya yi kafin ya umarcesa da ya ajiye mashi makullin. Ba musu Leo ya ajiye. Shiru GAT ya yi yana jiran jin ko Leo zai yi mashi wani karin bayani, irin ya ce ya je ya ɗaukosu ya kaisu gida, amma sai ya ji shiru bai yi magana ba, hakan ba karamin mamaki ya sake baiwa GAT ba, wai wannan wani irin mutum ne?.Dan ya gwada shi sai ya ce. “You can go”…….. Sara mashi Leo ya yi tare da juyawa ya fita. Da kallo GAT ya bisa yana mamakinsa, watau dai magana ce ba zai yi ba, to lallai yakamata a gyara mashi zama.Kasancewar lokacin dinner ɗinsu ya wuce sai Leo ya nufi room ɗinsu kawai, bai yi dinner ba yau saboda GAT. Can ƙasan maƙoshi ya yi sallama a lokacin shigarsa ɗakin, su Zaysh suna ta faman yin waya da gida, yau suna da damar kiran kowa da rana. Vash ne ya ce yau Friday zai yi sadaka, amma da ƴan room ɗinsu zai fara, to a ƙaidar GIDAN SOJA ɗin in dai zaka zo buɗe maka account nadaga cikin list na kuɗin da zaka kashe a farko, dan haka suna da account na ƙasar amma kamar students account.Dan haka dikkansu Vash ya basu kyautar 1k dollars, Noor ya ce ba zai karɓa ba, da Vash ya matsa sai ya ce ya baiwa Zaynash nasa, haka ya haɗawa Zaysh. Da yake Noor yana da kyawawan zuciya sai ya ce da Zaysh. “Bro ka kira Aunty Ummie mu gaisa, I really like her, Ina jin daɗin yadda kullum take ce mana mu kula da kanmu, mu ci abinci kuma mu yi barci a kan lokaci, tana da kirki sosai kuma tana sonmu sosai”. Vash ne ya amsa da. “Gaskiya nima I really kike her, tana da kyakkyawan zuciya”……… Sosai Zaysh ya ji daɗin yadda suke yabon Aunty Ummie ɗinsa, sai ya samu kwarin gwiwar danna mata kira da sauri bayan ya duba time 4:40, yanzu ba jimawa suka dawo daga masallacin sallar la’asar, shi ne suka tashi Noor daga barci.Wucewa ciki Leo ya yi, kai tsaye ya nufi toilet dan shi bai samu sallar jam’i ba, GAT ya sanya shi zaman jira. Bayan ya yi alawala ya zo ya shinfiɗa dadduma ya tada sallah. Bugu ɗaya Ummie ta ɗauka, a lokacin ta gama sha kukan walaƙancin dangin miji, Auntynsu ne ta zo ta dinga zaginta wai taki haihuwa sai cinyewa ɗansu arziki take yi tana kiba, ta mata zagi ta uwa ta uba na cin mutunci, shi ne ta shiga ɗaki take ta faman kuka. Ganin call ɗin Zaysh yasa ta yi gaggawar goge hawayenta, har tana sauke ajiyar zuciya, dan a duniya idan akwai abin dake kwantar mata da hankali bayan karatun Alkur’ani to sai Zaysh, a kowani hali take ciki idan ta tuna tana da kani kamar shi wani irin farinciki take ji.Gyaran murya ta yi ta yadda ba zai gane tana cikin damuwa ba, sannan ta ɗauka tare da kara wayar a kunne. Cike da farinciki ya ce. “Assalamu alaikum Aunty”……. Sai da ta ɗan sake daidaita natsuwarta kafin ta amsa da. “Wa’alaikassalam Zaynish, ya yau ka kirani da rana? Baku aiki ne?”. Tin daga maganarta ta farko ya gane tana cikin damuwa, amma sai bai nuna ba tin da yaga tana ƙoƙarin ɓoye mashi ne…….. “Yau karfe 2 muke tashi horo, shiyasa na kiraki, ya gida ya kowa da kowa? Ina yayana? Jiya mun yi waya ma da shi”……….. Take murmushi ya bayyana a kan face ɗinta, dan in tana magana da shi wani irin daɗi take ji, dik damuwarta ya gudu. “Kowa lafiya lou ya horon naku? Ina abokanka masu kirkin nan?”. “Komai lafiya lou, ai su suka ce ma in kiraki, suna son gaisawa dake”. Ya faɗa tare da ɗan cire wayar daga kunnensa……. “Ina son yin hira da su amma ban iya turancin sun nan ba, wayasani ma ko basa gane kwaɓata”. Ta faɗa tana ɗan murmushi. One side smiling ya saki kafin ya ce. “Suna ganewa mana, ai kema kin iya turancin fa Aunty”. “Uhm ni kada ka wani zugani, ina turanci a wanda bai je makaranta ba, kawai waɗan da ake yi a gari na tsinta na iya”…… Nisawa ya ɗan yi. “Kai Aunty, waye ya ce maki turanci wata tsiya ce da har sai an je makaranta ake iyata? Yare ce fa kamar kowacce yare! Sai ki ga wani ga tarin ilimi sosai amma baya jin turanci, wani kuma sai ɗan banzan turancin amma kansa fanko ne, ƙasar da suka san ciwon kansu ma basa amfani da turanci Aunty, sai dai yaren ƙasar!”. “Haka ne, to yanzu ina Noor? Basu waya mu gaisa”……… Miƙawa Noor ya yi, yana wani irin bosy smelling ya karɓa tare da karata a kunnensa. Cikin kwararriyar turancinsa ya fara ɗaga mata gaisuwa, daga nan suka ɓige da hira, Zaysh yana fassara mata wasu manyan kalmomi, idan tana son faɗar wani babban magana kuma sai ta faɗa da hausa ya fassara masu Noor da turanci”. Sun jima suna waya kafin su yi sallama Noor ya kira Auntys ɗinsa shi ma, cikin ƙanƙanin lokaci ta waya suka saba da family ɗin juna, har in ɗaya ya kira gida a gidan kowa yana haba-haba ya haɗasu da abokansa su gaisa, sun zama kaman ƴan uwa na jini da dangin juna, dangin Leo ne kawai babu wanda ya sansu, ba su taɓa ganin ma ya kira gida a gabansu ba, amma su kowa a gidajensu yasan da ƴan ɗaki, sai dai kuma ahalin kowa basu san da Leo a ɗakin ba.Haka suka kasance cikin farinciki har dare, bayan sun yi dinner sun dawo, dikkansu suka yi wanka suka yi shirin kwanciya. Sai da suka sake kiran gida suka sha hira har zuwa 10 na dare, sannan ne ɗakin ta yi shiru tsit alamar sun yi barci. Leo yana kwance rike da waya yana chatting da gida, shi baya kiransu sai dai chat kawai, saboda shi ƴan gidansu ba zaman banza suke yi ba, dik suna da aikin dake gabansu, basu da lokacin ɓatawa wajen yin wasa saɓanin su Noor masu yi har da video call. So shi idan ya tashi yana dropping masu message ne, dik time da suka zo su yi reply, haka suke. Around 11 duniya ta yi shiru, kowa ya yi barci, kunna light na wayarsa Leo ya yi tare da sakowa kasar bed ɗinsa, kai tsaye bed na Noor ya nufa. Hannu yasa ya fara tashin Noor. Da yake ɗazu da rana ya sha barci sai ya farka a natse, slowly ya waro idanunsa a kan kyakkyawan fuskan Leo dake ta faman sheki. Ya yi mamakin ganinsa, hakan yasa ya tashi da sauri yana kai hannu saman ido.Mustsuke idanun nasa ya yi dan ya tabbatar da abin da yake gani. Tabbas Leo ne, cike da mamaki ya ce. “Bro what brought you here?”……. Baya kaɗan Leo ya ja tare da yi mashi alamar ya sauƙo ƙasa. Ba musu ya sauƙo yana cigaba da kallonsa. Hannunsa Leo ya kama suka nufi door. Noor bai musa ba ya fara binsa, buɗe kofa ya yi suka fita waje.Yana fita ya kashe light na wayansa ya zura a aljihu, a cikin duhu suka cigaba da tafiya har izuwa gym na barrack ɗin. Ko kaɗan Noor bai ji tsoro ba, bai kuma damu da ya tambayi ina za su je ba.Kasancewar Leo yasan gym ɗin tana can baya ne daga idanun mutane, sai ya kunna light na wajen, take haske ya gauraye wajen. Sake hannun Noor ya yi tare da ce mashi ya shirya. Sai a lokacin ya ɗaga idanu ya kalli Leo da kyau, muryansa na rawa ya ce. “Bro me za mu yi a nan?”…….. “Training”. A taƙaice Leo ya bashi amsa. Shiru Noor ya ɗan yi, yana son tambayar dalili amma yana shakka. Ɗaure fuska Leo yai alamar babu wasa a tattare da shi, sannan ya umarci Noor da ya wuce ya fara push-up, dan wlh ba za su yarda da wannan ragon tan nasa ya dinga sanyawa suna ɗaukar karshe ba, dole ya horar da shi horo na musamman wa shi kaɗai. Ganin babu arziki a kan fuskan Leo yasa ya wuce ya fara yi, waya Leo ɗin ya fitar ta duba time, sannan ne ya ce ya baiwa Noor 10 mins yai push-ups guda 100. Zazzaro idanu ya yi, a ransa ya ce to ai ko Captain almost 20 mins ya basu kuma har three times, shi kuma 10 mins at once? Gaskiya wannan zallar mugunta ce, ganin dai babu wasa a tattare da shi ne yasa bai yi gigin yi mashi magiya ba, sai kawai ya fara. Gefensa Leo ya tsata yana kirgawa, tin Noor na iya kirgawa har ya dawo yi kawai yake yi. Abin mamakin kuma shi ne sun fi tsoron Leo a kan Captain ma, dan kuwa dik wahala da gajiyar da Noor ya yi bai dakata ba, yana tsoron tsayawa ne. Haka ya dinga yi, tin yana daurewa har ya saki ya fara kuka, ko a jikinsa Leo kam, bai damu da kukan ba, sai ma rungume hannaye a kirji da ya yi yana kallonsa. Ko guda hamsin bai cika ba mintuna goman nan suka cika, nan fa Leo ya ce ya sake farawa daga farko, yau ba zasu tashi daga nan ba har sai ya yi guda ɗari a mintina goma. Haba kuka sosai Noor ya fara yi, hawaye bibbiyu, daga karshe majina da yawu dik suka fara zuba, Leo ko kaɗan bai ji kamar zai kyalesa ba, haka bawan ALLAHN nan ya dinga maimaita almost sau takwas, amma ya gagara yi a ƙasa da mintuna goma, dik wani sauran karfinsa ta kare, jikinsa ya jigata, kafafunsa da hannayensa kerma sosai suke yi, sai haɗa uban gumi yake yi.Shi kuwa Leo ya ce ko mutuwa zai yi yau sai ya yi a kasa da mintuna gomar nan, ko kwana ne sai sun yi a nan. Tin 11 ake abu ɗaya har karfe 1 sannan ya samu ya yi a ƙasa da mintuna gomar, sake cewa ya maimaita Leo ya yi, ya maimaita ya kuma yi a ƙasa da mintuna goma, da alama ta shiga kansa sosai wannan horo.A maimakon Leo ya barsa haka ya huta, sai ya sake sanya shi 100 sit-ups and 80 burpees, yaron nan kuka yake yi tamkar ransa zai fita, Leo bai ɗaga mashi kafa ba, har ta kai dakyar yake numfashi, har yana neman sumewa a wajen, amma Leo bai tausaya mashi ba har sai da ya yi waɗan nan training ɗin dikka. Around karfe 3 ya kammala cikin ƙaida, sannan ne Leo ya ce su tashi haka nan sai kuma gobe….. Babbar Magana, kenan Leo kullum dare zai dinga hora Noor? Lallai Noor yana cikin lukutar musifa, ga horon rana ga kuma na dare, bawan ALLAH ba hutu kenan.Gagara miƙewa a kan ƙafafuwansa ya yi, dan jikinsa dikka wani iri ɓari mai ban tausayi yake yi, idanunsa har sun kumbura, tsinin hancin nan nasa jajir kamar an shafa wani abin, ƙasan idanunsa dik sun yi jajir. Ganin ya gagara miƙewa ne yasa Leo tura wayansa a aljihu, sannan ya saɓesa a kafaɗa suka nufi waje. Kai tsaye room ɗinsu suka koma. A saman gadon Noor ya kwantar da shi tare da wucewa nasa bed ɗin. Har ya kwanta sai ya ji Noor na numfashi sama-sama tamkar zai mutu, hakan yasa ya sauko ƙasa, jakarsa ya ɗauko, tare da fito da wani drugs, sannan ya ɗauko bottle water, dan su da shi suke amfani, iya matsayin kuɗin iyayenka iya shagalinka!. Wajen gadon Noor ɗin ya dawo, miƙar da shi zaune ya yi tare da ɓalle drugs ɗin guda bibbiyu, ya ɓalle bakin robar ruwan, sannan ya bashi a baki. Dole ya buɗi baki ya karɓa, bayan ya sha Leo ya koma bed ɗinsa, ya mai da sauran drugs ɗin, ya kuma ajiye ruwan kafin ya haye ya kwanta. Shi ma Noor kwanciya ya yi, kusan a tare barci yai awon gaba da su.Washegari, yau ta kama Saturday, babu horo suna off. Tin da sassafe suka tafi yawace-yawacensu a cikin barrack ɗin, dan ba’a yarda su fita waje ba idan suna karar horo. Zaynash ya ce bari ya je yawo ta wajen dajin da suke zuwa horo ya gani, sai ya ɗauki camera ɗinsa wai zai ɗaɗɗauki wajen horon nasu hoto, in sun yi passing out ya kaiwa Ummie ta ga wuraren, dan haka sai ya nufi ma’ajiyar kekunan horonsu, ya ɗauko keke guda ya haye kai, sanye yake da three quarter jeans baki da lallausan t-shirts ash color, ya yi kyau sosai, sai ya ɗaura army p-cap a kansa. Vash kuma fita ya yi dan ya samu damar kallon sauran matasan sojojin. Noor har yanzu yana ta faman barci wahala, Leo yana kwance saman gado bai sauƙa ba tin bayan sallar asuba da ya dawo, idanunsa biyu kuma!. A natse Zaysh yake tuƙa kenan nan nasa yana ɗan kalle-kalle, ya sanya helmet a kansa wanda ya ɗauka a jikin keken, kowani kenen akwai hular kwanon a ɗaure a jikinsa, dan dokace basa hawa keke babu shi. Wata doguwar hanya ya miƙa, nan yaga matasa dayawa a kan keken, wasu suna dawowa, wasu kuma suna tafiya, a ransa ya ce yau ba training sai yawo, watau kowa ya je ganin wuraren da muke zuwa horo dan ya ɗauki hoto ya ajiye tarihi. Yana sharan wata kwana da zata sada shi da cikin dajin suka ci karo da wata keke da ta sharo kwana ita ma, hakan yasa sarkan keken ya zube ƙasa, saura kaɗan su faɗi daga shi har wancan ɗaya mai keken. Amma suka yi saurin sanya kafafunsu a ƙasa. Kusan a tare suka ɗauko ƙasa, ya tsayar da kekensa a gefe, shi kuma wanda suka yi karon ya tsugunna yana ƙoƙarin gyara sarkar keken nasa da ta zube. Da yake yasan shi ne da laifi da ya shiga kwanar da gudu, sai ya yi saurin tsugunnawa a wajen tare da kama sarkar yana faɗin. “Sorry bari in gyara maka”………. Miƙewa tsaye ya yi ya bar mashi sarkan ya gyara. Tsab ya mai da shi ya gyara tare da rike kan keke ya miƙe tsaye, a sanyaye ya ce. “Sorry ba da gangan na yi ba, na shiga duniyar tinani…….”. Bai iya karisar da maganar ba ganin cewa macece ba namiji ba.Zazzaro ido ya yi, ta cire hukar kwanon kanta, ta kuma ɗan buɗe zip na ƙatuwar jacket ɗin jikinta da ya hana ake iya kallon kirjinta har a gane macece, daga ta ƙasa wandon jeans dogo ne a jikinta, kafafunta da Boot bakake, hannunta da army hands gloves, ba ta yadda zaka iya gane macece har sai da ta cire hular kwanin dogon gashin kanta da kyakkyawar face ɗinta ya bayyana. Ai kusan suman tsaye ya yi a kallonta, ga shi da helmet a kansa mai cover, bata iya ganin face ɗinsa, hakan yasa ya zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu, bai iya ɗauke kallonsa daga kanta ba, sai da ya ga ta motsa ta miƙa hannu zata karɓi kan kekenta da ya rike ne yasa ya farga, da sauri ya ɗauke kallonsa daga kanta tare da fara juye-juye yana neman namijin, dan bai gama yarda ita ce mai wannan keken ba yafi tinanin da ya tsugunna gyara sarkan ne namijin ya gudu mace ta zo. Kun san a matasan sojojin harda mata? Ban taɓo maku ɓangarensu bane saboda labari bai biyo ta nan ba, amma harda matasan mata dake sha’awar shiga aikin.A ransa ya ce. “Yanzu wannan kyakkyawan mai zubin taliyar ma a training na soja take kenan? To yanzu wannan ba zata karye bane ma?”. A fili kuma karɓar kan kekenta da ta yi ne ya dawo da shi daga tunanin da ya afka. Ya gagara sake yi mata magana, yana gani ta mayar da helmet ɗinta a kanta, sannan ta gyara ta haye kan keken ba tare da ta yi mashi magana ba. Sai da ta gyara hands glove na hannunta kafin ta fara tuƙa keken ta bar wajen.Mutuwar tsaye ya yi yana kallonta har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo nasa keken, ya hau ya cigaba da tafiya zuciyansa cike da tinanin dama akwai kyawawan ƴan’mata a barrack ɗin nan kenan? Kaga wata zaka ce an kure halitta a kanta! STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥


