Uncategorized

Macijine Shi Page 55-56 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 55/56

_________________”RASHAAADDDD” 

Aka kwallah kiran sunan Rashad,Wanda saida ɗakin ya amsa.gaba dayan mutanen da suka shigo ɗakin saida suka tsorata ,saboda yadda amon Muryar ya fito da mugun ƙarfi da sauti mai firgitarwa.

Ahankali fattu da ke neman macewa ta buɗe kunburarrun idanunta  da gyar,ta saukesu akan fuskar hammanta, wata shashshekar kukace ta zo mata ,numfashinta na hawa da sauƙa ,da gyar ta daga hannunta tana mikawa Adeeb ,

Da wani irin mugun sauri Adeeb yayi kanta yana mika mata nashi hannu,saidai kafin ya ƙara so tuni hannun nata ya koma ƙasa sharaff!! Ahankali kuma idanunta suka kulle ,duk wata jijiya dake jikinta tasaki,ataƙaice dai fattu ta sume.

Wani irin ƙara Adeeb ya kwalla mai matukar firgitarwa ,hayaƙi na fita ta bakinsa da hancinsa, hannun fattu ya kama ya riƙe cikin nashi tare da damkewa kamar zai balla hannun nata.

Jikinsa gaba ɗaya rawa yake  kamar ana kaɗa masa gangi,ɗago da kansa yayi afusace ya sauke idanunsa akan Rashad,Wanda tsabar tsoro ya kasa koda matsawa daga kan table ɗin gashi tsirara haihuwar uwarsa.

Da sauri Rashad ya runtse idanunsa,numfashinsa na wani irin hawa da sauka kamar shima zai shide tsabar tsoron ganin yadda idanun Adeeb ya koma,ga wani irin bakin hayaƙi daya fara cika ɗakin,

Wani ƙaran Adeeb ya sake kwalla,wanda yafi na farko sanya tsoro da razani,gaba ɗaya dakin yayi wani irin bakiƙirin ,baka ko ganin hannunka bare na kusa dakai.

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Novel

Su ammi da amma,nanny tareeƙ ,jakadiya,da Zulaihat wacce zuwan ta kenan,bangaren dan ta sami labari gurin yan s.i.d ɗinta.gaba daya tsoro ,firgici da tsantsar mamakin abinda ke faruwa yasa sun kasa koda motsine agurin ,bare suyi wani abu.

Sun ƙanƙame juna jikinsu yana wani irin bari,nanny Banda sunan Allah ba abinda take ambata”innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, meye wannan ke shirin faruwa haka,tareeƙ kana ina bana ganin komai fa ” nanny ta faɗa tana ƙanƙame tareek dake kusa da ita.

Shi kansa tareeƙ jikinsa rawa yake ,sam ya kasa magana sai rungume mahaifiyarsa da yayi sosai ajikinsa.

Ƙaran rashad ne ya karaɗe dakin ,cikin wani irin sauti na azaba,wanda kana jinsa kasan wanda ke wannan karan yana cikin azaba da halin ƙunci.

Kuka kawai amma ta sanya ,dan tasan yau kam ɗan ta sai abinda hali yayi,shikenan yau abinda ake shukawa agidan  ya dawo kansu.

Download>>> Budurwar Mijina Complete Novel Document

Ahankali ɗakin ya fara washewa daga tsantsar duhun da yayi  ,kusan minti uku suna cikin halin tsoro da razani kafin ,suka fara ganin komai tar-tar .

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”shine abinda Dukansu suka haɗa baki wajen faɗa,sakamakon ganin wani narkeken maciji mai girman gaske nannade da Rashad ,Wanda kallo ɗaya zakayiwa Rashad kasan cewa ba alamun numfashi atare dashi.

Kallon kallo ake tsakanin mutanen dake cikin dakin,wanda suka shiga tashin hankali fiye dana farko,dan kuwa ba Adeeb aɗakin sai wannan narkeken macijin,wato dai Adeeb shine ya zama wannan macijin.

Jikin nanny Banda rawa ba abinda yake ,haka ammi da amma,jakadiya da Zulaihat wacce tuni ta jiƙa jikinta da fitsari,tana tsaye ƙanƙame da amma wacce itama ta ƙanƙame Zulaihat ɗin.

Sun kasa magana sai kallon ikon Allah suke.

Macijin nan yana tsaye nannade da Rashad ya fasa kai yana wani irin huci da fesar da wani irin bakin abu daga bakinsa.juyi ya farayi da ƙarfi kafin ya maka rashad ajikin bango,ji kake timmmm!!Rashad ya baje akasan tyles,tuni jini ya fara zubowa daga kansa.hakan bai ishi macijin nan ba ya kara zuwa ya nannade Rashad tare da kara makashi jikin bango.

Ihu suka farayi ganin macijin nan na ƙoƙarin  tarwatsa kasusuwan Rashad.

Da gudu jakadiya ta juya tayi waje tana ihu ,ta nufi part ɗin mai martaba,tana faɗuwa tana mikewa,gaba ɗaya bata cikin hayyacinta.

Zulaihat ma silalewa tayi agun ba alamun numfashi atare da ita.

Karanta Littafin : Raɗaɗi By Sa’adatu Waziri Gombe

“Wayyo jama’a ku taimaka min ,zai kashemin yarona,wayyo Allah na na shiga uku ku taimaka min”amma ta faɗa cikin ficewar hayyaci,dan tsabar tsoro gadan gadan take nufar cikin dakin gurin da Rashad ke kwance ayashe, aikuwa kafin ta ƙarasa  kaiwa inda Rashad ke kwance, saijin wani abu tayi mai kama da bulala ya fyadeta a gadon bayanta,wani ihu amma ta kurma tare da faduwa sakamakon azabar  raɗaɗin da taji gadon bayanta ya ɗauka.da rarrafe ta koma inda take tsaye. Jikinta na rawa .

Ammi fa tsoro ya gama kasheta,dan ko tsayuwar kirki ta kasayi, sam batayi tsammanin haka abin yake ba,ashe dai da gaske mutum yana iya komawa wata halittar ta hanyar asiri?lallai yau taga abinda ya fi ƙarfinta , sam bata tsammaci abun haka yake ba, amma dole tayi wani abu dan gudun zargi.dan haka cikin bugawar zuciya da tsananin tsoro ta fara takawa zuwa gurin da Adeeb ke tsaye yana zagaya Rashad yana huci.

“A…a.ddd..ee.e.bbb.”ammi ta kira sunansa cikin tsinkewar numfashi, shikuwa baiko kalli inda take ba ,burinsa kawai yaga Rashad yayi motsi ya kara karairaya masa inda bai gama lalacewa ba.

“Ka nutsu Adeeb ɗana,.n…i.cce ammin …ka, ka …ka…ji.”ta faɗa tana matsawa cikin tsoro da firgici.

Ai kuwa jin takunta da adeeb yayi ,afusace ya juyo tare da kai mata tsafka, cikin sa’a kuwa ya damketa,ihu ta farayi tana neman taimako,”wayyo Allah na taimako jama’a taimako”ammi ta faɗa lokacin da Adeeb ke nannaɗeta kamar buhun goro.saida yagama naɗeta sannan ya fasa kansa saitin fuskar ammi yana huci.tsabar firgici tuni ammi ta sume ,kura mata ido Adeeb yayi kafin ya fara dakinta ahankali ,ta faɗa kan gado.

Download>>> The Governor Wife Book 3 Complete Document


Gurin fattu ya koma tare da hawa gadon bayanta, nade ta yayi tare da mirgina ta ta juyo rigingine,kallon fuskarta yake wani irin farin Ruwa na zubowa daga idanunsa ,kwanciya yayi akan cikinta yayi lamo yana mai juya kansa ,tare da yin wani irin ƙara  yana bude bakinsa.

Al’amarin yayi matuƙar tsorata dukkan wadanda ke cikin dakin,dan nanny ma tuni ta sume ,amma ce kawai mai ƙarfin hali ,dan tana zaune riƙe da bayanta da tasha bulala.

Tareeƙ kuwa hawayene ke zuba daga idanunsa.yana matukar tausayawa yallabai ɗin nasa. 

Ana cikin wannan halin ne,abie ya shigo dakin tare da waziri da  manyan faɗa ,sai Shaikh lateef ,babban malamine dake koyar da ilimin addini sannan masani akan abinda ya shafi jinya da maganinta, ya ƙware sosai wajen magance abun daya shafi sihiri.

Lokacin da jakadiya ta kaiwa abie labarin,shikuma suna tare da su waziri suna ɗan tattauna wata magana mai muhimmanci,shine suka garzayo gaba ɗayansu, ɗan ganin abinda ke faruwa.

Download : Walijam Complete Novel

Ba ƙaramin kaɗuwa abie yayi ba,lokacin da ya wannan kumurcin macijin amatsayin Adeeb ɗinsa,hawaye ne kawai ke zuba cikin idanunsa, ya ƙurawa Adeeb ɗin ido.tunanni kawai  yake ,waye wanda yayiwa adeeb wannan aika -aikar?me yatsarewa wanda yayi masa haka?ace yaro mai gata dan sarauta kamar Adeeb yana zama maciji?duk yadda Adeeb ya kasance mai tausayi da taimakon al’umma ,amma ashe wasu suna can suna shirya masa mugunta.lallai dole ya tsaya tsayin daka ,wajen bawa yaronsa abin sonsa kariya ta ko wacce siga.yasan ammi na ƙoƙarin wajen yiwa adeeb addu’a ,kuma tana sawa ayi masa kamar yadda take faɗa amma dole shima ya dage ta bangarensa.

Abie ne ya kalli Shaikh lateef,cikin damuwa da zubar hawaye yace “Shaikh kaga Adeeb ga ,kaga halin da yake ciki,menene abinyi ?abie ya faɗa yana mai share kwalla.

Shaikh lateef kuwa wanda tun shigowar su yake kallon Adeeb,kallo na tsinake,sai lokacin yayi ajiyar zuciya kana ya kalli abie,yace” ranka shi daɗe lallai Adeeb yana cikin tsaka mai wuya ,da tuggun maƙiya ,amma In Sha Allah komai yazo ƙarshe,yanzu dai ayi ƙoƙarin diban bayin Allah dake kwance dan akaisu ga likita,sannan sai musan abinda ya kamata muyi”Shaikh lateef ya faɗa yana mai kallon abie.

Nan da nan kuwa aka kwashe su ammi da nanny,Zulaihat ,sai dai ko yaya akayi yunƙirin zuwa inda Rashad ke wance kamar gawa,take macijin nan zaiyo kan mutum afusace.

Ganin haka ya sanya abie cikin ƙarfin hali ya tunkari Adeeb dake fagen fattu yana fasa kai,ya kasa ya tsare,

Ahankali abie ke kallon Adeeb da idanuwansa masu fidda hawaye kafin yace”habeebee kayi hakuri adauke dan uwanda,dan asuba lafiyarsa, koma me yayi maka nine nan,zan ɗaukar maka mataki,bazan taɓa yarda da zalunci ba”Abie ya faɗa cikin sanyin murya yana kallon Adeeb.

Huci kawai Adeeb keyi yana kallon Abie kafin ya maida kansa ga fattu yana kallonta,sannna ya ɗago kai ya kalli abie,

Jinjina kai abie yayi cike da fahimtar Adeeb ɗin yace “na fahimta habeebee,dole zan ramawa yarinyar nan abinda rashad yayi mata,dan kasan ba’a zalumci amasarautata” abie ya faɗa yana mai ƙara sawa kusa da Adeeb ɗin ahankali ya sanya hannunsa yana shafa bayan Adeeb.

Shikuwa Adeeb sai huci yake yana guri da wata iska mai matukar zafi.haka aka samu aka lulluɓawa Rashad Abu ajikinsa kafin kayi waje dashi, amma duk yadda akayi ƙoƙarin ɗauke fattu Adeeb ya hana ,dan hatta mai martaba ,da yayi yunƙurin daukar ta saida Adeeb ya kai masa tsafka.haka suna ji suna gani ba yadda suka iya,sai lulluɓe mata jiki da sukayi itama ,dan kuwa yaƙi barin jikinta ma.

Karanta Littafin>>> Matar Hariji Hot Romantic Hausa Novel

Shaikh lateef ne zaune gaban Adeeb yana karanto wasu addu’oi yana tofa masa,lokaci guda jikin Adeeb yayi laushi, gaba ɗaya baya ko kwakwkwaran motsi,sai huci da yake fiddawa ,ya dora kansa akan ruwan cikin fattu dake lulluɓe,jikinsa sai wani bakin hayaƙi ke fita.

Ci gaba Shaikh lateef yayi da addu’ar sa yana tofawa Adeeb,yayin da su abie ke gefe guda suna kallon ikon , Allah,dan zuwa lokacin murƙususu kawai macijin nan keyi,kafin wannan hayaƙin ya turnuke dakin,baka iya ganin komai tsabar duhu.

Su abie suma addu’a suka fara,lokacin da suka ga wanan hayaƙin,dan Shaikh lateef yace karsuji tsoron komai ,duk abinda zasu gani kawai suyi addu’a.

Can kusan wucewar mintuna biyar suna ta addu’oi ,dakin ya fara haske yana washewa har ya gama washewa tar, kamar ba shine yayi wannan duhun ba. 

Adeeb ne durƙushe agaban wannan table ɗin da fattu ke kwance,kansa har lokacin yana kan cikin fattu.

Hamdala Abie da su waziri sukayi,ganin Adeeb ya dawo asalin halittarsa, dan abie yayi matuƙar tsorata, kar ace ahaka Adeeb ɗin zai zauna.

Ahankali Adeeb ke buɗe idanunsa ,da har zuwa lokacin basu gama komawa normal ba.

Kanshi ya daga da gyar yana ɗan yatsine fuska tare da dafe kan,dan ciwo yake masa sosai.

Sai kuma yayi saurin zabura ya mike tsaye “Hulwa” shine abinda ya faɗa cikin  daga murya yana waige waige,

” Habeebee ka nutsu kaji ga hulwar taka nan kusa da kai “abie ya faɗa yana mai mikewa shima tare da riko kafadun Adeeb.

Sai lokacin Adeeb ya ga su abie aɗakin,kallon abie yayi  kafin ya kalli inda abie ke nuna masa,zaro ido yayi ganin hulwarsa kwance kamar gawa,”Hulwa ” Adeeb ya faɗa yana mai girgiza fattu,amma ina Hulwa tayi nisan zango.

Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsanani ciwo da zafi.irin kukan da Adeeb keyi kaɗai zai fahimtar da kai yadda yake jin Hulwa da kuma ciwo acikin ransa.

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Hausa Novel

“Rashad !

Rashad !!

Rashadddd!!!ka tabka babban kurkuren ƙoƙarin tabamin mata,kayi kurkure,idan  Hulwa ta mutu”yayi shiru yana mai goge hawayen dake kwatanta cikin idanunsa,kafin ya ɗago idanunsa da suka yi wani irin mugun jaaa,ya kalli Abie sannan yaci gaba”wllh billahi,saina kashe Rashad ,idan har matata ma mutu sanadin sa”Adeeb ya faɗa cikin karfafa murya da nuna gaskiyar abinda yake fadi har cikin ransa.

Kallonsa kowa keyi acikin ɗakin,dan kuwa sun zama speechless,matarsa yake ta kira,kodai yarinyar nan amatsayin matarsa take?ko kuma yana nufin ita zai aura?

Shine abinda yake ta yawo cikin zukatan su Abie.

“Ya kamata akai yarinyar asibiti yanzu,nikuma zanje gida domin yin bincike akan larurar prince ranka shi dade”cewar Shaikh lateef yana mai mikewa tare da shafa kan Adeeb,dan yana tausayawa yaron sosai.

” Haka ne Shaikh bari akaita asibiti yanzun nan ” cewar abie yana mai kallon  Adeeb dake ƙankame da Hulwa kamar zai maidata cikinsa.

Kafin su ankara tuni Adeeb ya sungumi fattu yayi hanyar barin dakin da ita.” Habeebee kayi hakuri akai yarinyar asibiti,kaima fa ba cikakkiyar lafiya gareka ba” cewar abie kenan ,ganin Adeeb na ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.

” Ba wanda zai kara tabamin mata abie ,domin itaɗin mallakina ce mata tace  ta Sunnah,hakkin kula da ita yana kaina,dan haka bana bukatar taimakon kowa,karka manta ,likitanci bangarenane” yana faɗin haka yayi waje da fattu rungume aƙirjinsa.

Kai tsaye fart ɗinsa ya nufa da fattu ,yana zuwa ya shimfiɗeta akan lafiyayyen gadonsa, kallo yabi jikinta dashi,cikin wani irin zafi da ƙunar zuciya,gaba ɗaya glasses sun maƙale ajikinta ,jini duk ya bata mata jiki.hatta fuskarta baka ganewa.

Gimbiya suhaimat ce tsaye tana bin Adeeb da kallon sabe da yarinya akafadunsa,haka kawai gabanta ke tsananin bugawa,so kawai take taga yarinyar,

Ko menene ya sameta oho?ahankali ta juya taci gaba da tafi zuwa dakin ammi,dan su basu san abinda ke faruwa ba.

Zuciyarta gaba ɗaya taki samun nutsuwa ,ba abinda take son gani sama da wannan yarinyar,gaskiya bazata iya jurewa ba dole taje taga yarinyar,sannan ta san meke damunta?me yasame haka gaba ɗaya jikinta jini…

Download>>> Dr. Bobby Complete Novel Document

Masu karatu ku biyoni dan jin gimbiya suhaimat zata je ganin fattu ne ko yaya?

Taku anty mammy

Mrs babi  💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment more typing

Back to top button