NASIHA GA MA’ABOTA HANKALI
MU GODEWA ALLAH ABISA NI’IMOMIN DA YAYI MANA
Hakika da yawa cikin mu ‘yan Adam bama sanin ni’imar Allah gare mu har sai ta gushe mana: Ku duba nawa cikin mu ke gode wa Allah game da ni’imar musulumci su bautawa Allah da gaskiya, su tsare iyakoki da aka Hana mu ketarewa?
Nawa cikin mu ke mallakar dukiya su godewa Allah kuma suyi Ibada da ita?
Nawa ke samun ilimi suyi aiki dashi kuma su ilmantar?
Nawa ke samun dama ta daukaka ko mulki su Kare hakkin bayin Allah wajen adalci da kin sabawa Allah da baiwar da yayi musu?
Nawa ke dacewa da abokan zama nagari wato iyalai amma su tozarta hakkin junan su?
Nawa ke amfani da dama da faraga wajen bautawa Allah da kulawa da addini?
Nawa cikin mu ke samun ‘ya ‘ya sukula Sosai da tarbiyyar su, da basu hakkin su cikin adalci da tausayawa?
Nawa cikin mu ke godewa ni’imomin lafiya, gani, ji, kafafu, hannu da sauran gabobin mu harmu bautawa Allah dasu, kuma mu guji saba wa Allah dasu?
Nawa ke samun uwa da Uba su kula da
hakkin su wajen girmamawa da taimaka masu da yi masu da’a da addu’a?
Yan uwa mu sani duk za’a tambaye mu kan wadannan ni’imomi, don haka mu ji tsoron Allah mu kula, mu kyautata, mu nemi yardar Allah mu tuba gareshi. Allah yasa mu dace, Ameeen