Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 62 Complete Novel

*ASM Bk2062*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

……… Zama yay akan d’aya daga cikin chairs d’in sai lokacin ta tuno da bata d’aukko plates ba da d’an hanzari ta juya ta nufi hanyar corridor Slowly ya juya yana kallonta har ta shige sannan ya janye idon, bada Jimawa ba ta dawo hannuwanta ruk’e da plates da bowl sai serving spoon da kuma spoons da forks duk ta d’aurayo su don da alamun lemar ruwa a jikin su, bayan ta aje ta bud’e babbar warmer d’in ta fara zuba mashi tana sa kaman rabin plate taga ya d’an d’aga hannu alamar ya isa ta d’aukko k’atuwar tsokar nama ta d’aura tana niyyar k’ara wata nan ma ya k’ara dakatar da ita ta hanyar k’ara d’aga mata hannu ta tsaya, saka mashi fork tay ta tura gaban shi ta bud’e Warmer d’in farfesun ta zuba mashi kad’an ta tura mashi, Fridge ta nufa ta d’aukko bottle water da lemu ta dawo ta aje daga gaban shi ta sake juyawa ta koma ta d’aukko glass cups daga cikin fridge d’in ta dawo, tana niyyar bud’e robar lemu ya dakatar da ita a hankali ya furta ruwa kawae yake buk’ata ganin zata bud’e nan ma yace sai ya gama a hankali ta furta to, zuba nata abincin tayi bada yawa ba tasa fork ta d’auka tana niyyar juyawa ya d’ago ya kalleta suka had’a ido ta kasa tafiya,

 

“zaki je ina ki ci Abinci?” taji cool voice d’in shi ya tambaya, shiru kaman bazata ce komai ba ganin ya kafe ta da ido yasa tace d’aki zata je, still yay yana kallon ta can taji yace “shi nan don me aka yi shi?” Shiru bata ce komae ba ta maida idon ta k’asa, “Sit!” cike da bada umarni taji ya fad’a, ba yadda ta iya dole ta aje Abincin ta zauna, duk da tana jin yunwa ta kasa cin Abincin sosae don duk sai taji ya fitar mata a rai sai d’an tsakura take tana yi tana satar kallon shi yanata cin nashi a nutse, bata wani ci da yawa ba ta mik’e ta d’auki Abincin yana kallonta tun kan yace wani abu tace mashi ta k’oshi zata kai kitchen ne ya d’an d’age mata gira “da kika ci mi?” yanayin Fuskar ta ne ya sauya idanuwan ta sukai rau rau kaman zatai kuka yace ta zauna ta cinye shi, komawa tay jiki a sanyaye taci gaba da ci ba don tana jin dad’in shi ba don ta rasa mike mata dad’i kamar ta fashe da kuka take ji, ya rigata gamawa amman sai yay zaune ya kafe ta da ido har saida itama ta cinye sannan ya mik’e ta bi shi da ido, Fridge ya nufa ya bud’e ya d’aukko babbar robar ice cream da wasu daga cikin Snacks ya dawo, aje mata yay gabanta da sauri ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace suma ta cinye aikuwa kaman jira take ta fashe mashi da kuka ta kife kanta a kan table d’in kallabin ta ya zamo ya baro saman kan ta, bin ta da ido yay yana kallon ta da alamun mamaki ita kan ta kawai ji tay kukan yazo mata, d’an kwankwasa saman glass table d’in yay ta d’ago fuskar ta jage jage da hawaye ta kalle shi,

 

“na buge ki ne?” Ya tambaya had’i da d’age mata gira ta girgiza mashi kai alamar a’a, “then miye abun kuka?” cikin muryar kuka tace “ni na k’oshi” bin ta da ido yay can yace “shine na kuka, ko akwai abunda ke damun ki ne?” Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a’a, “Ok, kin ci wani abu ne before I came?” Kai ta sake girgiza mashi, “kuma shine har kin k’oshi?” tana d’an tura baki tace to ba ta ci Abinci ba yanzu, yanayin fuskar shi ne ya sauya kaman zai d’an yi murmushi “ai baki k’oshi ba so ki k’ara da wannan” kallon shi tay ba dama tay mashi musu don kuwa yasan yanayin yadda take cin Abinci, ganin ya kafeta da ido yasa da sigar shagwa6a ta d’an juya kai tana yamutsa fuska tace to ai sunyi mata yawa dare yayi sosae bazata ci Abinci da yawa ba tunda kwanciya zata yi, ganin yadda yake kallon ta tana Maganar yasa ta juyar da fuskar ta gefe can taji yay sigh ya furta Ok, komawa yay ya zauna duk abunda ya d’aukko ya raba biyu saidae d’aya yafi d’aya girma ya bata wanda suka fi girman shi kuma ya fara cin sauran itama ta fara ci tana yi tana d’an kallon shi har lokacin ba kallabi a kanta, kusan a tare suka gama ya bud’e mata robar ice cream d’in ya tura mata ganin yana niyyar mik’ewa da sauri tace to shi bai rage ba ai yayi mata yawa shi ma, wani kallo ya jefa mata sai taga kaman ya harareta ta d’an tura baki ta sauke idon ta k’asa, d’an guntun murmushin da iyakar shi lips d’in sa yay taji yace in ta rage tasa a fridge daga haka ya juya ta d’ago ta bi shi da ido, dakatawa yay ya juyo yace in ta gama yana buk’atar fruit bada yawa ba ta d’aga mashi kai ya juya ya tafi, sai gashi ta shanye ice cream d’in duka dama harda rashin sake mata fuska da ta ga baiyi ba yasa taji komae ya fitar mata a rai, bayan ta gama ta nufi Fridge ta fiddo ledar fruit d’in tunanin ko ta had’a mashi fruit salad tay tasan zai fi jin dad’in sha tayi ta juya tana ruk’e da ledar ta nufi hanyar corridor yana zaune a inda yake da kafin ya tashi ya d’an kai idon shi kanta kafin ya maida su kan tv, ba 6ata lokaci ta had’a mashi ba mai yawa ba sosae a cikin d’an bowl mai kyau ta bud’e fridge d’in cikin kitchen ta d’aukko k’ank’ara ta d’an kwankwatsa ta a ciki ba mai yawa ba don tasan bai son abu mai sanyi sosae, saka ledar fruit d’in tay a cikin fridge d’in nan ta d’auki bowl d’in ta nufi parlon, tunda ta fito ya maido idon shi kanta itama kallon nashi take tana isa ta d’aura saman c-table ta ja shi gaban shi ta d’ago suka had’a ido tace gashi nan da d’an murmushi ya jinjina kai tare da furta thanks, juyawa tay ta koma Dining Area ta fara kwashe kayan Abincin, wanda zata saka a fridge ta saka tay clearing wurin, saida ta wanke duk abunda suka 6ata a cikin kitchen ta maida su ma’adanar kowanne sannan ta fito ta nufi bedroom, tana shiga ta koma can bakin gado inda ta zauna d’azun ta zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, gajiya tay da zaman ta kai kwance amman k’afafun ta na a k’asa, har bayan wani lokaci tana a hakan can taji an bud’e kopar da sauri ta tashi zaune suka had’a ido, rufe kopar yay ya nufo ciki ya tsaya gaban dressing mirror ya fara k’ok’arin cire Diamond Watch d’in wrist d’in shi, bayan ya cire a saman wurin ya aje ta ya juyo idanunshi suka sauka cikin nata da take ta faman bin shi dasu taga ya nufi hanyar Laundry room tana ta kallon shi har ya shige sannan ta juyo, komawa tay yadda take kafin ya shigo taci gaba da wurga ido tana tunane tunane, kusan Mintuna 15 ya d’auka sannan taji ya turo kopar ya fito tana kwancen ya zagayo wurin gadon, wani irin bugu k’irjinta yay mata don kuwa daga shi sai towel d’aure a k’ugun shi ya fito, tunda take bata ta6a ganin namiji haka ba balle shi da yake Tubarkallah, a rud’e ta juya ta yadda ta bashi baya yana jin mutsu mutsun ta bai ko kalle ta ba ya nufi gaban dressing mirror, duk mayuka da turarurrukan da yake amfani dasu suna a wurin saidae an k’ara wasu dasu kwalaben humra da turaren wuta, mai din shi ya d’an shafa sama sama bayan ya gama ya hau feshe jikin shi da turare Fatuu da tay lamo tana ta kikkifta idanu tana jin yadda yake fesa turarurruka ta d’an lumshe ido had’i da d’an yin murmushi, yana da son k’amshi sosae har da hakan ke k’ara mata k’aunar shi gashi koda yaushe zaka ji k’amshin shi na daban ne, bayan ya gama closet ya nufa ya bud’e bayan ta zuge ya fiddo sleeping dress riga da wando ya juya ya k’ara nufar laundry idon shi akan Fatuu da ta takure guri guda ya d’an ta6e baki da yanayin murmushi kan face d’in shi ya wuce, jin k’arar k’opa yasa ta d’ago da sauri ta kalli kopar Bedroom d’in sai dai bata ga alamar ita aka bud’e ba nan ta gane laundry ya shiga, bada jimawa ba taji motsin zai fito aikuwa da sauri ta maida kan yadda take da, fitowa yay ya saka kayan baccin ya nufi k’opar fita, har ya kama handle d’in sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta, ta ji lokacin da ya kama k’opar amman bata ji ya rufe ba hakan yasa ta d’an d’ago zata saci kallon shi karaf suka had’a ido nan take ta kama kanta ta k’arasa d’agowa ta tashi zaune sai waro ido take tana d’an motsa baki,

 

“Zaki kwanta haka ne?” taji ya fad’a, shiru tay tana kallon shi ba tare da ta ce komai ba, d’age mata gira yay “am I not talking?” abu ta d’an had’iya a hankali tace “a’a”,

 

“U should go and take bath” kai ta d’aga mashi alamar to ta mik’e sumimi sumimi ta nufi wurin wardrobe, towel d’in da ta gani saman jakunkuna ta d’auki wani light blue ta juyo idanun ta suka sauka cikin nashi yana tsaye har lokacin da sauri ta sauke kanta k’asa ta wuce, tana kaiwa bakin k’opar zata shiga taji k’arar bud’e kopar shi ta juya lokacin ya fita, After some minutes ta fito tana d’aure da towel d’in a k’irji da yake yana da d’an girma ya saukko mata ta yafo kallabin lace d’in da ta cire, nufar wurin jakunkuna tay ta duk’a ta bud’e wadda ke d’auke da kayan bacci, wata doguwar riga cotton ta fiddo cikin kayan da Hajiya ta aiko jikinta gwanin taushi ta bud’e cikin Akwatunan ta ta d’aukko hula ta mik’e ta koma bakin gado, saida ta d’an shafa mai sannan ta shafe jikinta da wata humra mai Masifar k’amshi don kuwa nan da nan k’amshin ta ya karad’e d’akin ta d’aukko roll on ta goggoga a hammata, bayan ta gama yan shafe shafen da goge gogen ta dawo bakin gado ta saka rigar, komawa tay gaban dressing mirror d’in ta hau feshe jikin rigar da turare saida ta fesa kaman kala ukku sannan ta dawo bakin gadon ta d’auki towel d’in ta nufi laundry don ta baza shi ya bushe, bayan ta fito zama tay a bakin gado tay shiru gaba d’aya bata jin bacci gashi dare yayi sosae don tuni k’arfe 12 tayi ko don Saboda bak’unta ne oho, tana ta zaune can ta idasa hayewa gadon ta kwanta tay k’uri tana kallon bangon da k’opa take, bata dad’e da kwanciyar ba ya turo k’opar ya shigo suka had’a ido ya tunkaro gadon har saida gabanta ya fad’i, yana isa bakin gadon ya kai hannu ya d’aukko babban pillow guda ya d’ago idon shi a Kanta ya furta mata “Gud nyt” kai ta jinjina mashi kaman yar k’adangaruwa, har zai juya sai kuma ya kai hannu jikin lamb dake gefen gadon ya kunna sannan ya juya Fatuu dai nata kallon shi, saida ya kashe switch hasken d’akin ya d’auke sai na fitilar da ya kunna sannan ya bud’e kopar ya fita, zuru Fatuu tay a ranta ta fara tunanin kenan a parlor zai kwana Saboda ita, sam ran ta bai mata dad’i ba ba kuma don wani abu ba sai don kwanan da zai yi a parlon tasan ba lalle yaji dad’in kwanciyar ba duk da kujerar nada taushi sosae amman zai iya takura, tana ta zancen zuci can zuciyar ta ta raya mata wani abu tay d’an jimm tana tunanin tayi ko kuwa, tashi tay zaune ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita har ta kusa kaiwa kopa sai kuma ta dakata ta juyo ta koma wurin kayanta, golden gyalen da ta cire ta d’auko ta yafa sannan ta nufi kopar fita.

 

Lokacin da ta fito cikin Corridor d’in tsayawa tay tana kallon cikin parlon ya kashe hasken cikin shi sai na wasu da ya bari na gidajen wurin su Tv sune suka d’an haska parlon, nufar cikin parlon tay sai kace mai yin sand’a ta hango shi kwance kan L-shape side d’in da ya fi zama, tunda ta bud’e k’opa ta fito ya hangota ya zuba mata ido yana ta kallon ta har ta k’araso, daga bakin kujerar taja ta tsaya tana kallon shi ta gane kallon ta yake shima, kasa isa wurin shi tay tayi tsaye sai d’an wasa take da yatsun hannunta tana d’an kikkafta ido had’i da motsa baki alamar tana son fad’in wani abu, yunk’urawa yay ya tashi zaune idon shi akanta yay mata alamar ta zo da hannu ta matsa a d’ayan side d’in ta tsaya ya k’ara mata alamar ta zauna a hankali ta d’an d’osana ta zauna,

 

“Any problem?” Ya tambaya, cikin yar inda inda tace “D…dama cewa nay kaje ka kwanta ciki ni zan kwanta anan” da k’yar ta k’arasa Maganar Saboda kallon da yake jefa mata mai wuyar fassaruwa ba Arzik’i ta sunnar da kan ta bayan tayi Maganar, maida bayan shi yay jikin kujeran still idon shi na akanta kaman bazai ce komae, jin shirun yayi yawa yasata d’an d’agowa suka had’a ido, sigh yay “ba wani abu kije ki kwanta” yanayin fuskar ta ne ya sauya hakanan taji kaman idanunta na son tara k’walla da sauri ta maida fuskarta gefe tana kikkafta idanu don kar su tarun,

 

“Fatuuh” ya kira sunanta ta d’an yamutsa fuska had’i da d’an cije lower lip d’inta ba tare da ta juya ba, hakanan bata son Fatuu da yake kiranta duk da sunan ta ne kuma yafi kowa iya fad’ar shi don a gayance yake furta shi amman duk da haka bata so sai take ganin kaman bai huce bane yasa yake kiran ta haka ko kuma matsayin da take dashi a wurin shi da yanzu ya ragu, k’ara kiran ta yay sai lokacin ta juya suka had’a ido fuskar shi a d’an sake yace “Don’t worry am comfortable here kije ki kwanta it’s already late” ba tare da ta ce mashi komai ba ta mik’e ta nufi hanyar corridor walking very slowly don duk jikinta ya mutu, idon shi na kanta still yana zaune bai kwanta ba har ta shige cikin Corridor d’in yana ji ta bud’e kopar Bedroom d’in ta shige, maida kanshi yay jikin kujera ya d’age shi yana facing sama had’i da lumshe ido ba zaka iya karantar yanayin shi ba a lokacin, ya d’an d’auki lokaci a haka kafin ya maido kan k’asa ya koma ya kwanta.

 

Tana shiga d’akin ta nufi bakin gado ta zauna ta zuba ma wuri guda ido, ta d’an d’auki lokaci a hakan can ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta ba tare da ta cire gyalen ba, kwata kwata bacci ya k’aurace ma idanuwan ta sai juye juye take ba kuma wai don tana son wani abu ya kasance tsakanin su ba kawae dai ta rasa mike mata dad’i ne, sam ta kasa gane mashi har ta fara kokonton anya yana son Auren ba Hajiya ce ta matsa ba kuwa, haka tay ta tunane tunane zuciyar ta na sak’a mata abubuwa har dare ya tsala da k’yar bacci ya d’auketa shima kuma ba mai nauyi ba,

 

Akan kunnanta aka fara kiraye kirayen farko na sallar Asuba ta bud’e ido saidae bata tashi ba tay zuru, ba’a dad’e da gama kiran sallar ba taji an turo kopar ta kai idanun ta wurin tana ganin shi ya shigo da sauri ta rufe ido, saida ya kalleta sannan ya wuce wurin closet ya bud’e, jallabiya ya fiddo yana ruk’e da ita ya nufi laudary room jin k’arar bud’e kopar yasa ta bud’e idon nata, bayan few minutes ya fito ta sake rufe idon nata, saida taji k’arar bud’e kopar Bedroom d’in sannan ta d’an bud’e idon taga ya saka jallabiyar ya fita da alamun Alwala yayi, bayan fitar shi bada jimawa ba itama ta tashi ta saukko ta nufi laundry room d’in, Alwala tayo bayan ta fito ta wuce wurin jakunkunan ta ta ciro wata doguwar riga tare da hijab d’in da sukai salla da Haisam ta dawo bakin gado don ta saka, bayan ta gama ta shimfid’a prayer mat ta kabbara raka’atanil fajr, tana zaune tana ta tasbih har lokacin sallar Asuba yayi ta mik’e don tayi, bayan ta gama tayi Addu’oi ta shafa, zaune tay a wurin kaman an dasa ta ta kasa tashi can sai ma ta kwanta a wurin cikin sa’a bacci ya d’auke ta. Bayan an gama salla saida gari ya d’an fara washewa ya dawo daga Masallaci, a bakin kopar parlon ya cire takalman shi ya nufi kujera ya zauna, had’e hannuwan shi yay ya d’aura ha6ar shi yana kallon wuri guda ya d’an d’auki lokaci a hakan can ya mik’e ya nufi hanyar corridor, Slowly ya tura kopar Bedroom d’in ya shiga idanuwan shi suka sauka akan ta kwance kan Carpet ta takure cikin Hijab d’in kaman mai jin sanyi, tsaye yay a bakin kopar yana ta kallon ta can ya idasa shiga ciki wurin Ac ya nufa ya rage mata ita sannan ya dawo inda take, kiran sunanta yay shiru bata motsa ba ya k’ara nan ma bata farka ba, d’an jimm yay sai kuma ya rankwafa ya kai hannu ya d’an bubbuga shoulder d’in ta nan ta fara motsi ya d’ago, a hankali ta bud’e idanun ta ta d’an d’ago suka had’a ido da sauri ta k’arasa d’agowa ta tashi zaune tana gyara hijab, kallon shi ta d’an yi k’asa k’asa tace mashi ina kwana ya d’aga mata kai,

 

“taya zaki ji dad’in bacci anan, ki koma kan bed mana” taji cool voice d’in shi ya fad’a, bata ce komae ba ta mik’e ta d’auke abun sallar ta maida sannan ta nufi gadon idon shi akanta, ganin zata hau ba tare da ta cire k’atuwar hijab d’in ba yasa shi k’ara yi mata magana kan taya zata kwanta da ita zai iya shak’e ta nan ma ba tace komai ba tasa hannu ta cire, saida ta linke ta ta mayar wurin kayan ta sannan ta dawo still yana a inda yake ta hau saman gadon sannan ya juya ya fita, da k’yar ta koma baccin shima parlon ya koma ya kwanta, ba laifi ta d’an yi baccin don sai k’arfe tara saura ta farka ta tashi zaune tana yin yar mik’a da hamma, sosae ta ji dad’in baccin da tayi jin jikinta ba k’arfi yasa ta saukko daga kan gadon ta wuce laundry don ta shiga toilet tay wanka, d’aure da towel a k’irji kanta sanye da hular wanka ta yafo wani short a kafad’arta ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana k’ara goge ruwan jikinta bayan ta gama ta aje short towel d’in ta fara shafa mai cike da fargabar kar ya shigo ya iske ta haka, bayan ta gama ta shafa su humra nan da nan k’amshin su ya karad’e Bedroom d’in, wurin jakunkunan kayan ta ta nufa bayan ta gama ta duk’a ta janyo babbar mai d’auke da kayan sawa ta bud’e nan ta fara tunanin kayan da zata saka tsakanin lace shadda da kuma atamfa ga kuma jallabiyu, ta d’an d’auki lokaci tana ruwan ido can dae ta fiddo wata hadaddar atamfa mai red flowers riga ce da straight skirt tana ganin kayan ta gane kb ne ya d’inka su don yasan kalan d’inkin da tafi so kuma dama ba’a amshi ko measurement d’in ta ba tunda yana dashi, maida jakar tay ta bud’e mai d’auke da undies ta fiddo wanda zata saka, bayan ta fiddo komae da take buk’ata ta maida jakunkunan ta dawo bakin gado, d’aura kayan tay ta fara k’ok’arin sakawa gabanta na d’an fad’uwa don kar a maimaita na Asibiti, har ta gama bai shigo ba ta koma gaban mirror tana kallon kanta abun saidae ace Tubarkallah, sosae kayan suka amshe ta shape d’inta ya fita kamar an zana ta gashi straight skirt d’in irin mai tsaga ta gaba ne rigar ma tayi mata k’yam k’yam daga wurin hips d’in ta ya bud’e sosae kaman zai fashe yadda ya kamata, d’an jujjuyawa tay tana k’are ma kanta kallo har saida ta d’an yi murmushi don ita kanta taga yadda kayan suka mata kyau, yar light make up tayi tasa red janbaki wow just Ma sha Allah, gashinta ta warware ta sharce shi har zata kulle wata zuciyar ta bata ta bar shi haka a sake tay d’an jimm tana tunanin yin hakan don bata yi mashi haka, can ta yanke barin nashi taga in zata yi kyau ta d’aukko k’aton kallabin atamfar ta lankwasa shi ta gaba ta kashe d’auri gaban sai yay kaman daurin Zarah buhari duk da bata sa komae ba ciki amman ya yi sosae da yake atamfar sabuwa ce, Jama’a ku zo kuga Fatuu ta fito sak Amarya ita kanta sai d’an sakin murmushi take wani irin kyau da bata ta6a ganin tayi ba taga yau tayi ga bak’in gashinta mai santsi yay mata rumfa a k’afadun ta abun dai sai wanda ya gani, turarurruka ta feffesa bayan ta gama ta nufi gefen gado ta kwashe towels d’in da tay amfani da hulan wanka ta wuce laundry don ta kai su, baza su tayi yadda zasu sha iska ta nufi hanyar fita, daidai tana fitowa Haisam ya turo kopar Bedroom d’in ya shigo idanun shi suka sauka cikin nata tay tsaye cak kaman an dasa ta da alamun yar razana take kallon shi shima yanayin kallon da yake Mata irin na baka tsammaci ganin mutum ba balle kuma a yadda take, sakin fuska yay yanayin d’an murmushi ya bayyana itama d’an murmushin tay da hannu yay mata alamar ta wuce ta tafi a nutse, saida ta wuce sannan shima ya wuto ya shiga laundry room d’in, a gefen gado ta zauna a ranta tana raya kar fa yace Saboda wata manufar tay kwalliyar wata zuciyar ta sake raya mata amman dama can ai yasan dai tana yin gayun ta ko, yin wannan tunanin yasa ta kauda wanccan tunanin sai kuma ta k’ara yin tunanin k’ilan wanka zai yi yakamata ta fita ta bashi wuri in ya fito ya shirya koma ta je ta had’a masu Breakfast, mik’ewa tay har zata nufi kopa sai kuma ta wuce wurin kayanta ta bud’e inda takalma suke ta curo wasu flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta saka su sannan ta tunkari kopar fita don zuwa Kitchen.

 

Bayan da ta shiga cikin Kitchen d’in duk iya dubawar da tayi bata ga wasu kayan abinci ba da zata yi amfani da su sai iya su cincin da dublan kawae, tsaye tay ta jingina da drawer tana k’are ma Kitchen d’in kallo a ranta tana k’ara yaba kyan shi ganin abun take har yanzu kaman al’mara wai nan Kitchen d’in ta ne, idanunta ne suka sauka akan drawer d’in da Aunty Mareeya ta nuna mata da ta zuba mata magungunan ta, a yadda ta fad’a mata yakamata da safen nan ta sha amman sai taji kaman bazata sha d’in ba tunda tasan dalilin shan magungunan, tana ta tsaye k’arshe ma sai tay d’an tsalle ta haye saman drawer d’in ta zauna sai yan kalle kalle da yan tunane tunane take, ta d’auki kusan minti talatin a haka ta jiyo k’amshin Haisam cikin hancin ta da sauri ta kalli kopar shigowa daidai lokacin ya sawo kai cikin wurin wato tun ma kafin ya shiga wuri Kamshin shi ke sanar da isowar shi, ya yi wanka ya shirya cikin k’ananun kaya bak’in jeans da farar t-shirt daga gabanta an d’anyi style d’in bak’in rubutu, sosae kayan suka amshi jikin shi yay wani Fresh sumar nan sai kyalli take tasha gyara haka sajen shi ya kwanta luf, daga can bakin kopar ya tsaya tana ganin shi ta diro k’asa tana kallon shi, tambayar ta yay mi take yi a nan ba ga parlor ba,

 

“Dama na shigo inyi breakfast ne amman na duba banga kayan Abinci ba” a sanyaye tay Maganar sai faman bin bakin ta da ya sha jan jambaki yake da kallo har ta gama, ganin yadda yake ta kallon ta kaman ba zai ce komae ba yasa ta d’an sunkuyar da kan ta, “Ba sai kin yi ba za’a kawo” taji ya fad’a, d’agowa tay ta d’aga mashi kai alamar to suka ci gaba da kallon juna tana yi tana d’an maida idanunta k’asa da d’an motsa baki,

 

“ko kina buk’atar wani abu ne?” da sauri ta girgiza mashi kai ta nufi inda yake don ta fita ta gefen shi ta wuce, bin bayanta yay shima ya fito ganin zata shiga bedroom yasa shi ce mata taje ta zauna a parlor mana, juyowa tay ta kalle shi tace zata gyara d’akin ne ya d’aga mata kai ya wuce cikin parlon ta bi bayan shi da kallo yana tafiyar shi mai cike da k’asaita, d’an murmushi tay ta tura Kopar ta shige…………

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button