Hausa novels

Kanwar Maza Page 56 Complete Novel By Ayshercool

Page 56

Adam bai taɓa ta ba, sai bin ta da ya yi da kallo, idanuwanta na neman su kakkafe, sai daddagewa take yi, jikinta yana cigaba da tsuma.

 

Usman ya ce “Lafiya kuwa?”

 

Mai sunan baba kuwa wani irin takaici ne ya mamaye shi, ganin rumaisa a jikin Adam gaba ɗaya.

 

Takawa ya ce “Ban san meya sameta ba, gani na yi ta haɗa kai da gwiwa tana bacci, kawai ta zabura ta faɗo jikina”.

 

“Iman! Iman ba ta da lafiya fa, Iman ba ta da lafiya” ta yi maganar cikin surutu da magagi.

 

“Wace kuma iman?” Mai sunan baba ya tambayeta a ƙule.

 

Haushi ne ya kama Adam, saboda yadda mai sunan baba ya raina wa kansa hankali, wai wace kuma iman, ya lura da yadda yake a ƙule, dan haka ya ture rumaisa daga jikinsa, ya ja da baya.

 

Mama tuni ta fito tsakar gida, dan jin abun da ya faru, amma ta kasa ƙarasawa soron, saboda jin nauyin adam.

 

Sosai take kuka tana neman abun riƙewa, “Iman fa, na gaya muku ba ta da lafiya”

 

Mai sunan baba ya saka hannu ya ɗagata tsaye, amma jikinta ya riga ya saki, tana neman ta faɗi.

“Ki buɗe idonki menene?” Ta sake rintse idanunta, kamar mai tsoron ganin wani abu.

 

Cak ya ɗagata ya shiga da ita cikin gidan, ya kwantar da ita a tsakar gida, gaba ɗaya suka rufu a kanta.

 

Adam har yayi niyyar tafiya, sai ya ga idan yayi haka bai kyauta ba, mussaman da ya ji tana ta ambatar sunan Iman.

 

Sallama ya yi ya shiga, ya tarar da su a kanta, mama tana girgiza ta, tana tambayarta menene.

 

Idonta dai a rufe, tana ta zubar da hawaye, ta ce “Iman, ba ta da lafiya sosai da sosai”

 

Mama ta ce “A’a jikinta da sauƙi ai, har an sallameta daga asibiti, tana gida”.

 

Ta ɗaga hannunta ba tare da ta buɗe idon ba, ta ɗora shi a saitin zuciyar mai sunan baba, idonta a rufe ta ɗaga kai in da yake ta ce “Mai sunan baba, ka ji bugun zuciyarka, ai kai ka yadda ba ta da lafiya ko? Ku yi mata Addu’a dan Allah kar ta mutu”.

 

Ya ce “To, kema ki yi addu’a”

 

Takawa ya ɗan yi gyaran murya ya ce “Ni zan tafi, Allah ya bata lafiya”

 

Mama da sai a yanzu ta lura da shi, ta ce “Yi haƙuri mai babban suna, wallahi tun da aka yi garkuwa da ita na kasa gane kanta, ina ga wani abun ta kwaso a zaman dajin da ta yi”.

 

Adam ya ce “Allah sarki, Allah ya bata lafiya, abun ya bani mamaki, lafiya take zaune, ta ce idan ban ci abincin da ta kawo ba, an ce za a zaneta, da ban ci ba sai ta ci, ta ce ba za a gane ba, sai ta haɗe kai da gwiwa tana bacci, shikenan kuma ta fara ihu” yayi maganar cikin ƙoƙarin wanke kansa, yadda gaba ɗaya ƙartan nan suka zubo masa ido,sun ga ƙanwarsu a jikinsa, ga mai sunan baba sai muzurai yake yi.

 

Mama ta ce “Bakomai wallahi”.

 

Usman ya ce “Lallai yarinyar nan baki da mutunci, dama zuwa ki ka yi ki ka cinye abincin?”

 

“Ba cinyewa na yi ba, dama ba na gaya muku ba zai ci ba, na san halin sa fa hmmm” ta yi maganar kamar wadda ta sha ta bugu.

Duk suka tsira mata ido, ta miƙa hannu tana yi wa adam nuni da ya zo.

 

Ba musu ya taka ya ƙarasa, ya sunkuya, ta riƙo rigarsa a hankali ta ce “Iman babu lafiya, kar ku zata da wasa nake yi, kar wani abun ya sameta. Kuma, kuma daga yau ba zan sake baka ko ruwa ba, yau haka aka din ga azabtar da ni, wai sai an yi maka girki kuma ka ƙi ci, to daga yau babu ni babu kai, tun da duka zaka janyo mini, sarki mai koriyar alkyabba ” ta ƙarasa maganar tana murmushi. Sai kuma ta cigaba da zabura.

 

Ya kalleta ya ce “To, na gode, ba za a dake ki ba, zan tafi da abincin”

 

Ta kuma cewa “Yauwwa, wannan matar, da ta bamu ruwa ni da Sabir, ka tuna ta?”

 

Adam ya ce “Eh, na tuna”

 

“To ka san ta ce wai akwai gwagwarmaya a gaba, hmmm ba ka san fa me nake gani ba ko? To in gaya maka, wani abu na gani rannan a gidanku, kuma ma, wani zai je ya ɗebi turarenka baka sani ba, yauwwa har da maganin ka ma da ake shafa maka, ana nema”.

 

Gaba ɗaya surutan da take yi babu ma’ana a wurinsu.

 

Mai sunan baba ya ce “Ya isa haka ki yi mana shiru”

 

Takawa kuwa ya ce “To, kin gama na tafi?”

 

“Eh ka tafi, amma fa kana tafe wannan matar tana binka, saboda tsabar taurin kanta, amma da kaina zan mayar da ita gurguwa”

 

Adam ya ce “Eh yakamata, yanzu dai ki cigaba da baccin, dama ammi ce ta aikoni, zan kira Aliyu a waya mu yi magana”

Ta ce “To” ta gyara kwanciyarta ta cigaba da barci.

 

Gaba ɗaya abun ya ɗaure musu kai, Adam ya ce “To mama sai anjima, Allah ya ƙara afuwa”

 

Suka amsa da amin, ban da mai sunan baba.

Usman ya ce “Ka tafi da abincin nan, ka cika mata alƙawarin ta”.

 

Adam yayi murmushi, Usman ya bi bayansa.

 

***

Ko da ya ƙarasa gida, sashin Ammi ya wuce, dan gaya mata abun da ya faru, amma ya tarar ba ta nan, ya fito ya tambayi baba uwani, ta ce “Ai suna tare da iman, tana can tana ta fizge-fizge kamar za ta haukace”.

 

What! Ya faɗa cikin tashin hankali, da sauri ya nufi ɗakin iman, sai dai ya je ya tarar da ita, a kwance tana ta Addu’a, ammi na ta shafa mata ruwa a ka, tana yi mata Addu’a, Nusaiba kuma na riƙe da hannunta.

 

Da sauri ya ƙarasa yana faɗin “Iman, me yake faruwa?”

 

Ta miƙa hannu ta riƙe nasa ta ce “Yaya Adam mutuwa zan yi, dan Allah ku yafe mini, nikaɗai na san me nake ji a kaina, baku san me nake ji ba, kaina kamar ana kafa mini ƙusoshi.

 

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un” ya din ga maimaitawa, ya saka hannu ya janye piliown da take kai, ya kwantar da ita a kan gadon, ya din ga karanta mata duk addu’a da ta zo bakinsa, cikin ƙudirar Allah sai barci ya ɗauke ta.

 

Adam ya ce “Ammi, wai takamaimai me yake damun iman ne?”

 

“Takawa ina zan sani? Na ga na asibiti sam baya yi mata ma, na rasa in da zan saka kaina ma. To ya aka yi, kun tattauna ɗin, ya ka baro rumaisa? Ina son a satin nan idan iman ta warware a fara haɗa lefe, dan na turawa laila kuɗi, ta yi wasu sayayyar a can ƙasar”

 

“Babu lafiya” ya faɗa a hankali.

 

Ammi ta ce “Kamar yaya?” Nan ya kwashe komai ya gaya mata, ammi ta yi shiru ta ce “Ikon Allah, Adam akwai aiki ja a gabanmu, babban fatana yanzu shine in ga an yi auren nan, kuma bana fatan a ɗaga ko da rana ɗaya”.

 

Adam ya jinjina kai Sannan ya ce “Bari na je na ga sabir, daga nan na wuce masallaci”.

 

Tun da ya fita yake ta jujju

***

Rumaisa sai magariba sannan suka samu kanta, ta tashi daga wannan baccin, ba ta iya tuna komai ba, ta cigaba da sabgoginta.

Mama hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, saboda gani take rumaisa aljanu ne ke son su hanata aure. Babu wanda yayi yinƙurin gaya mata abun da ya faru, suka biye mata aka cigaba da harkokin gidan kamar yadda suka saba.

 

Washegari Ammi ce ta kira mama da kanta a waya, tana tambayarta jikin rumaisa.

 

Mama ta ce “Jiki da sauƙi hajiya, na ce ko ɗaga bikin nan za ayi, a nema mata magani, alamu sun nuna iskokai suna damunta, kar ayi aure da larura”.

 

“A’a maman rumaisa, Allah zai bata lafiya, wataƙila da an yi auren ta samu lafiya, wallahi kin ganmu nima iman haryanzu jiki yaƙi daɗi, na rasa abun da yake yi mini daɗi, ciwon kai ko sauka ba ya yi”.

 

Shiru mama ta ɗan yi, kenan maganar rumaisa gaskiya ce?.

 

Mama ta ce “Allah ya basu lafiya baki ɗaya, in anjima zamu zo mu sake duba jikin nata”

 

Ammi ta ce “Ba sai kun wahalar da kanku ba, ayi mata Addu’a kawai”.

 

Mama ta ce “Haba, ai babu wannan a tsakanin mu, bari ayi sallar magariba, rumaisa ta dawo daga islamiyya sai mu zo”

 

Ammi ta ce “To shikenan, ta samu ta ga ɗanta ma”.

 

Bayan sun gama wayar, mama tayi ta Addu’a Allah ya sa ba aljanu ne suka buɗewa rumaisa ido ba, take gane-gane.

 

Da magaribar, tare da mai sunan baba suka je gidan su takawa, rumaisa na ta murna za ta ga Sabir.

 

Har ɗakin iman, aka yi musu izinin shiga, suka tarar da ita kamar mai shirin zarewa saboda surutai, duk suna kanta ciki har da Jabir.

 

Rumaisa ta ƙarewa ɗakin kallo, ta ce “Mama, ɗakin nan na yi mafarki fa jiya, ku cirewa iman pillown nan, mafarki na yi wata ƴar tsana tana soka mata allurai a kanta, yauwwa ba na ce muku iman ba ta da lafiya ba jiya?” Ta yi maganar tana ƙoƙarin tuna abun da ya faru jiyan.

 

Ammi ta ce “Rumaisa a ina ki ka ga ƴar tsanar?”

 

“Mafarki fa na yi, ki dafa pillown, ki karanta mata bisimillah da fatiha, amma dai wata ƴar tsana na gani a mafarki”

 

Abun sai da ya ɗaurewa kowa kai, Mai sunan baba kuwa tuni ya bar ɗakin, saboda yadda iman take, zaka san tana jin jiki ba kaɗan ba.

 

Ammi ta dafa pillown, ta karanto adduoi, Rumaisa ta riƙe hannun iman tana yi mata sannu.

 

Jabir ya tashi ya ce “Ammi, bari na je gida, Allah ya bata lafiya”

 

Suka amsa da Amin ya tafi.

 

Tattaunawa ammi da mama suka cigaba da yi, ammi tayi ta bawa mama ƙwarin gwiwa, a kan kar a fasa wannan auren.

 

Bacci iman ta samu, mama ta kalli Adam ta ce “Takawa, kai rumaisa part ɗina, ta ga Sabir, sai ka tambayeta abun da take buƙata na bikin”

 

Adam bai fiye yin jayayya da ammi ba, balle kuma yanzu da yake a gaban mutane ne, bai ce uffan ba, ya tashi ya fita, rumaisa ta bi bayansa tana murna, jin an ce za ta ga Sabir.

 

A hanyar sashin ammai, suka haɗu da baba uwani, cikin girmamawa ta risuna ta ce “Takarwarka lafiya magajin galadima, baƙuwa muka yi ne?”

 

“Eh” ya amsa a taƙaice yana fatan kar rumaisa ta yi wani shirmen, amma ga mamakinsa, ko kallon baba uwani ba ta yi ba balle ta gaishe ta.

 

Sai da suka yi gaba sannan ya kalleta ya ce “Baki iya gaisuwa bane?”

 

“Wa zan gaisar?”

 

“Matar da muka wuce, meyasa baki gaisheta ba? Gidan sarauta ba wuri ne da zaki gwada rashin ɗa’a ba, akwai girmamawa da karamci, ko da kuwa kai ne kake gaba da mutum”

 

Ba kunya ba tsoro ta ce “A hakan? Sau nawa na gaisheka a rayuwar nan baka amsawa, gidan sarautar da watarn wanda kake gaisarwa daban masu amsawa daban, ana ce maka an gaisheka ɗan talakawa, wannan ba wulaƙanci bane ba, ban kula kowa ba balle ayi mini wulaƙanci na ji haushi, ammi da wanda suke amsawa kawai zan din ga gaisarwa”

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

Wato ya fuskanci ita dai wannan yarinyar, defeating ɗin ta, ba abu ne mai sauƙi ba.

 

Sai da suka shiga ɗakin ammi, in da babu idon mutane, sannan ya dubeta ya ce “Idan ki ka cigaba da wannan taurin kan, ina gaya miki abu kina mayar mini da martani, zaki yi dana sanin aure a gidan sarauta, dan zai zame miki tamkar kurkuku mafi azaba, kowa zai yi ƙoƙarin yin amfani da ke wurin cimma burinsa, dole ki kiyaye”.

 

Rumaisa ta ce “Na sani, gidan sarauta ba irin normal gida bane, ina gani a film, na indiya da sauransu, daga tsafi sai munafunci, abun ban tsoro, kowa ba abun yadda bane ba, da an ga baka da wayo, sai a cuceka, da ka yadda da wani, sai ya nemi ganin bayanka. Ai ni a duniyar nan kurku mafi azaba ita ce zamana a hannun ‘yan bindiga, abu mafi razani kuma ganin mutuwar matar da ta bani kulawa kamar ƴar ta a lokacin da ake yi mini ƙamshin mutuwa. Abu mafi tsayawa a rai shi ne tunanin idan har gawarta tana da muhimmancin da za a kasheta a ɗau gawarta a mota a bar wurin da ita, saɓanin sauran mutanen da ake kashewa wurin, to waye ya saka ayi garkuwa da ita a kasheta, kuma ayi umarnin kashe ɗan ta? Abu mafi ban tausayi shi ne haihuwar jaririn da bai san komai ba, na din ga wahalar da shi da sunan kulawa, har koko na bashi, ya shafe kwanaki da ƙazantar haihuwa a jikinsa, bayan mun kuɓuta a ka yi yinƙunrin rabani da shi.

A tunaninka akwai wani abu mai wahalar mantawa kamar wannan? Ko wani irin ƙalubale ne, zan jure shi na rayu da sabir, kamar yadda na yi wa anty aisha alƙawari, amma ka ƙyaleni a yadda nake, ni ba ƴar sarauta bace ba, lokaci ɗaya ba zan iya zama irin ku ba”. Tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta taka a hankali ta ƙarasa gaban gadon Sabir, ya ƙara zama ƙato sosai, sai bacci yake yi.

 

Takawa kuwa kamar an gina shi, wasu gaɓoɓi ta taɓo masu muhimmanci, amma ya san yanzu da yayi yinƙurin ya cigaba da yi mata maganar, zata koma masa ainihin rumaisanta, ta fara rashin kunya.

 

Ta riƙe ƙafar sabir, tana kallonsa tana murmushi.

 

Adam yayi gyaran murya ya ce “Ammi ta ce, na tambayeki idan da abun da ki ke buƙata na shirin biki”

 

Maimakon ta amsa kawai sai ta hau dariya ta ce “Ni fa mantawa nake yi aure za ayi mini, ni bana buƙatar komai, su yaya Aliyu suna saya mini kaya, su mama kowa sai mini kaya yake yi”.

 

Ya jinjina kai ya ce “Good, that’s their part, a ɓangarena nake nufi, wanda ni yakamata na yi”

 

Ta girgiza kai ta ce “Za a saya mini komai, ni fa bana son ayi mini abu azo daga baya ana yi mini gori, komai za su saya mini, har da turmin ƙarfe”

 

Ya ce “Shikenan, na gaya mata ba kya son komai, tashi mu tafi na san ke suke jira”

 

Ta sumbaci goshin sabir ta ce “Ka yi mafarkina babyna” sannan ta yi gaba ta bar takawa a baya.

 

Aikuwa ta tarar da su a falo har sun fito, Ammi ta ce Adam ya mayar da su gida, mama ta ce ba ta yadda ba, ba zata iya hawa motar siriki ba, ƙarshe aka saka direba ya mayar da su, mai sunan baba ya ce za shi wani wuri, dan haka bai bi su ba.

 

 

A daren sai da baba uwani ta kai wa mummy tsaigumin zuwan su mama, tare da sanar mata ba ta san ko suwaye ba amma suna yawan zuwa gidan.

Mummy ta ce lallai ta sanya ido, ta gane ko suwaye, ta zo ta gaya mata.

 

Tun da Allah ya sa rumaisa, ta gaya wa ammi abun da ta gani a mafarki a kan iman, suka dage da addu’a, kuma cikin ikon Allah ta samu lafiya.

Ɓangaren su mama shiri suke sosai da sosai, a kan bikin da yake gabato su, sai dai rumaisa ta cigaba da mafarkai barakatai, da razana, har da ganin ta a wurin ƴan bindiga.

 

Mama ta sanarwa da Gwaggo, in za Gwaggo ta yi ta faɗa a kan ta sha cewa a nemawa rumaisa maganin tsari, amma maman tana yin burus da ita.

 

Danginsu rumaisa kowa da abun da yake kawo wa na gudunmawarsa, sai dai ƴan unguwa basu san me ake ciki ba.

 

Kwanci tashi asarar mai rai, ya rage saura kwanaki goma sha uku, auren rumaisa da adam, yayyen rumaisa da dangin mahaifinta, da na mama sai rawar gani suke yi.

Gefe ga masu kawo gudunmawar magunguna na gyaran jiki, da gyara aure, mama ta kasa bawa rumaisa, gani take kamar idan aka bata za a cutar da ita, shekarunta basu kai ba, ba ta da tabbacin ma shi kansa mijin ya saurareta.

Sai dai mussaman babar hauwwaliya, ta biya mai gyaran jiki, take zuwa gida yi wa rumaisa gyaran jiki, shi ma ta din ga tamɓele kenan tana guje-guje tana ihu, wai ana azabtar da ita, za’a rina mata fata da azaba.

 

 

Tun zuwa ɗayan nan da takawa yayi zance, bai kuma zuwa ba sai yau, da dole ce ta kawo shi.

 

Yau tun da ya zo, ba a kula shi ba, balle a gaishe shi, wasanninta ma kawai take yi, har da duwatsu. Ya lura ta yi wani kyau na musamman, fatarta ta yi haske, sai zuba ƙamshi take yi.

Yayi gyaran murya ya ce “Haryanzu kina zuwa makaranta ne?”.

 

“An yi hutu”

 

Ya numfasa, ya ɗauko wayarsa a aljihunsa ya kira iman, ya jira ta ɗaga sannan ya bawa rumaisa, suka gaisa iman na ta tsokanar ta amarya.

 

“Yauwwa anty rumaisa, lefenki ya kammala haɗuwa, dama size ɗin undeas ɗinki zaki faɗa da za a saka” ta kalli takawa taga yana danna ɗaya wayar ta sa sannan ta yi ƙasa da muryarta ce “Ni bana saka underwear, sai gajeren wando”

 

Iman ta ce “Ok, size ɗin phant fa?” Ruma ta buɗe baki, tana kallon fuskar Adam ko yana jin me iman ke tambayarta.

 

“Wannan kuma mama za’a tambaya”

 

“Brezia fa, ko ita ma a tambayeta?”

 

Rumaisa ta ce “Amma dai anty iman kawai dai tsokanata ki ke yi, idan aka saka wannan ai sai dai yayanki ya saka, tun da da nace a bani sabir, cewa yayi bani da abun bashi nasa ma yafi nawa girma, sai dai idan shi zai saka, ni bana saka komai, bani da su”

 

Dariya Iman ta yi ta ce “Allah ya baki haƙiri. Akwai kaya da zai baki, kalar da ki ka zaɓa ne, wanda zaki rabawa ƙawayenki, zamu saka ranar bridal shower, sai kuma na dinner, kayan lefenki na ji su mama sun yi magana sun ce kawai a kai miki gidanki, idan kin tare sai ki gani, kayan da zaki saka ma duk ya taho da su”

 

Rumaisa ta ce “To, sabir fa wanne zai saka?”

 

Iman ta yi murmushi ta ce “Iri ɗaya da babansa”

 

Rumaisa ta yi murmushi ta ce “To ki gaishe mini da ammi”. Ta miƙa masa wayar, ba tare da ta kalleshi ba.

 

Mayafin kanta ne yake zamewa, gashinta baƙi ƙirin, har gaban goshinta, tamkar zai haɗe da yalwatacciyar baƙar jagirarta.

 

“Me ki ke cewa na ce nawa yafi naki?”

 

“Au kasa kunne ka yi ka ke jin me ake faɗa? To me ka ji iman ta tambayeni?” Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

 

“Size ɗin brezia take tambayarki, kuma tun a gida na gaya musu, baki da abun sakawa”

Buɗe baki ta yi tana kallonsa da mamaki, shi ko nauyin faɗar brezia ba ya ji a bakinsa, a haka sai ka rantse da Allah ba ya magana.

 

Ya ce “Ba kin ce mata, na ce nawa yafi naki ba, ai ba ƙarya na yi ba, ko baki gani ba”

 

‘Wallahi na kusa daina rufa maka asiri, zan fara faɗar maganganun da kake gaya mini na batsa, bana so ni ba ƴar iska ba ce ba”

 

Guntun tsaki ya ja, ya tashi tsaye ya ce “Mu je ki karɓi kayan nan, ina da wurin zuwa” tashi ta yi ta bishi tana haɗe rai, saboda kar ya kuma kawo mata maganar banza.

 

Ko da suka fito ƙofar gidan, ɗan ƙare mata kallo ya yi, mayafi ne a jikinta yau, ɗan ƙarami, siririya ce mai matsakaicin tsayi, ƙirjin nan fayau babu komai, sai dai daga ƙasa ƙugunta ya buɗa, ko ta zama cikakkiyar budurwa, zata kasance a cikin mata masu diri daga ƙasa.

 

“I just wish you are that big enough, a kece raini tsakani na da ke, in ga ƙarshen fitsara, unfortunately look at you, ƙwaila mara jin magana, ban san ma iya adadin lokacin da za a ɗauka kan ki zama mace ba, baki da magana sai ce mini ɗan iska, ba zan manta ranar da ki ka gaya mini haka ba, amma zaki ga ɗan iska ganin idon ki, zo ki kwashi kayan nan zan tafi ”

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 57 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button