Novel Document

Sawun Giwa Complete Novel Document

Description/Story:

Sawun Giwa Complete Novel Document

Written By Autar Alheri

 

Description

“Saudia yau maka cike take cinjim da jama’a ƙabilu kala,kala sakamakon ana cikin yanayin aikin hajji masallacin harami yacika cinjim babu Masoka tsinke. Cikin kwanciyar hankali danutsuwar da ɗan adam ke kasancewa acikin aduk lokacinda yake gaban ɗakin Allah take gudanarda dawafinta yarinya ce ƙarama wadda bazata wuce shekaru 17 ba aduniya yarinyar kyakkyawa ce sosai Black beauty nagano hakan kasancewar bata saka niƙab ba afuskarta. Tanada manyan idanuwa da ɗan tsiririn karan hanci me ban sha’awa idanuwanta farare ƙal dasu masu sheƙi kamar tatara ƙwalla aciki tanada ɗan Small mouth me ɗaukeda red lips masu santsi sosai, batada tsayi sosai kuma baza’akiratada gajeruwaba..ahankali take juya danƙaramin bakinta, amma bakajin abinda take faɗa, taɗauki tsawon lokaci tana dawafi seda tazo naƙarshe na bakwai tahango wata dattijuwa tsakiyar wasu ƴan coria duk sun matseta tafaɗi kuma suna neman takata suwuce. Cikin hanzari taƙarasa gunsu tare da kutsawa cikinsu kamar wani namiji yadda take bankesu ya’isa kasan cewar tanaji da ƙarfi kida take ƴar ƙarama, nantake tazo inda wannan baiwar Allah take cikin ƙarfin hali ta tattare mutane tare da duƙawa tatemaka mata tamiƙe tsaye, “sannu mama, tafaɗa cikin wata irin murya me masifar daɗi. “Yawwa sannu ƴarnan Nagode sosai. “Bakomai mama kingama ɗawafinne? A’a yanzu nashigo. “Okay kawai tace kana yariƙe hannun wannan matar da ɗaya hannuta ɗaya kuma tariƙe ƙugunta dashi tashiga zagayawa da ita, abin mamaki tadawo farko a dawafi da matar domin tasan bazata iyaba, seda ta kammala bakwai tukunnah ta fitarda ita daga wurin…tunda tafara ɗawafin yake kallonta har inda taje temakon wannan matar domin yana niyar miƙewa yate maketane yahangeta itama tazo wurin. Kallonta yakeyi atsanake harta fitarda matar daga wurin. Yana kallo wani dattijo yazo dasauri gun matar har wannan yarinyar zata balbaleshi da faɗa setaga babban mutunne domin yahaifeta sekawai tayi matar sallama tatafi. Komawa tayi cikin masallacin taƙarayin wani ɗawafin tukkunna tayi addu’a tafito, daga inda yake tsaye yaji wata mata tace *MAISOON* cikin sauri yajiyo sekuma tayi murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana tace “na’am anty meenah kin idar? “Eh tunɗazu muke nemanki bamu gankiba. Ƙara faɗaɗa far’arta tayi kana tace “wlh mata baiwar Allah nafitar daga cikin taronnan anty meenah. Okay mujeto in kingama. Toh muje tafaɗa tareda yin gaba abinta anty meenah nabiye da ita abaya.

 

Nannauyar ajiyar zuciya yasauke tare da lumshe ash color ɗin eyes ɗinshi, domin wasu irin idanuwane dashi kamar na mage gasu kuma manya domin masu idon mage basu cika zama manyaba amma nashi manyane sosai kuma kamarna mashaya hakan suke abin dai abin birgewa. Ajiyar zuciya yasauke babu adadi kafin yaɗauki Spicer dake gabanshi yafara huɗuba cikin wani irin voice me masifar ratsa zuciyar me sauraronshi kamar yadda yasaba acikin masallacin harami kafin sallar azahar…yajima yana huɗuba me ratsa zuciya cikin harshen larabci kafin ya’idar yatada sallah. *SHEIKH SUDAIS MUHMD BILAL* kenan ɗaya daga cikin limaman masallacin harami kenan matashin sauri kuma ɗa ɗaya tilo agun sarkin Dubai wanda kerayuwarshi gabaki ɗaya s Saudia agidan kuma Sarkin Saudia ɗin aminin mahaifinshi.

 

Nigeria

 

“Assalamualaikum mom farka da dare..”yawwa barka maisoon y kike y ibada? Alhmdllh mom nayi missing ɗinku wlh Allah bazan zauna gun anty meenah ba da angama aikin hajji zan dawo. Ikon Allah dama aikece kikace zaki zauna amma ba wanda yasaki dole. “Yeee my mom harnaji daɗi to shikenan kigaisarmun da dady nakirashi wayarshi baya shiga. “To shikenan zan gaya Mishi yaje gidan abbankune. Okay bye mom, tafaɗa tana yanke wayar. Murmushi mom ɗin tayi kana tace maisoon rigima Allah ya dawo daku lafiya.

 

Atsiyace motocin suka shiga yankowa akan ƙwalta titin daze sada mamallakin motocin da gidansu, seda suka gama shigowa kana sojojin dake tsaro shi suka shiga doriwa daga kan motar cikin hanzari suka buɗe Mishi motar dayake ciki. Fitowa yayi cikin sauri yatunkari cikin gidan nasu waya manne a kunnenshi, seda yashigo perlor gidan tukunnah yayanke wayar yana tunkarar mutanen dake perlor. Good evening Dady Abba nasameku lafiya? Murmushi Dady yayi kana yace lafiya qalau fawan yagajiyar tafiya? Alhmdllh Dady. “Son andawo lafiya? Lpy qalau Abba ina mama? Tana ciki. Okay yafaɗa tareda miƙewa yanufi pert ɗin mahaifiyar tashi. Fawan kenan kyakkyawan saurayi mejida kyau da kuɗi gakuma isa kasan cewar shi soja, ɗane awurin Abba yayan dadyn maisoon. “Bara natafi yaya tunda haryanzu yaya Ishaq bezoba maybe akwai abinda yatsayard dashi idan yazo duk yadda kukayi seka gayamin, dadyn maisoon yafaɗa yana ƙoƙarin meƙewa tsaye. Okay badamuwa Usman Allah yakaika lpy agaida yarana. In sha Allah zasuji. Daga hakan Dady yafito.

 

Bara kuji yadda ahalin suke tunkafin muyi nisa yadda zaku fahimta.

 

Alhaji Umar Mainq da Alhaji Usman Maina dakuma Alhaji Ishaq maina yaya da ƙane ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya suduka ukku kuma iyayensu sun rasu sune kawai kerayuwarsu tare da ƴaƴansu…kowanne yanada nashi yaran dakuma matarshi. Alhaji Ishaq shine babba yanada yara huɗu, Mubarak, muhseen, jafar, Zainab…. Alhaji Umar yaranshi ukku fawan, fadeel, A’isha….Alhaji Usman yaranshi ukku shima jawwal, Ameenah, se autarsu maisoon.

 

Dukkansu suna gudanarda rayuwarsu cikinsu da ƙaunar juna dakuma biyayya wa junansu acikin waƴannan ƴaƴa masu mata biyu kawai sukayi aure mazanma biyu sukayi aure, Zainab yar wurin Alhaji Ishaq tayi aure a anan cikin garin Abuja,,, yayinda Ameenah kezaune a Saudiy itada mijinta dake aiki acan..mazan kuma Mubarak da jafar sunyi aure muhseen ne beyiba…a ƴaƴan Alhaji Umar kuwa fawan beyiba A’isha ma datake sa’ar maisoon itama tabayiba. Dagacikin waƴannan zaratan samarin fawan da muhseen Dukansu sojojine kuma manya kowannensu naji da kuɗi dakuma isa… dukkan waƴannan ahalin kyawawan gaske ne domin Asalinsa fulanine kuma daga cikinsu daga maisoon se Zainab ne kawai basuda hasken fata irinta Fulani sedai dukkansu Black beauty ne wato chocolate color. Wannan kenan. Acikin wannan family sunada wata dabi’a konace al’ada dukkansu umurnin mutun ɗaya sukebi wato Alhaji Ishaq kuma yakasance mutun me tsauri darashin ɗaukar wargi acikin lamarinshi….kunji asalin yadda suke mukoma cikin labarinmu.

 

Saudia

 

Bayan tagama wayada mahaifiyar Tata tamiƙe tare da faɗawa bathroom kusan minti 30 tukkunna tafito ɗaura da towel aƙirjinta. Wow Masha allah tabbas na yadda bakuma jinjina kyawun maisoon da cikar halittar ta domin tanada ƙira da diri meɗaukar hankali tabbas Allah yayi halitta awannan wurin… mirror tanufa tashiga gyara jikinta bayan tagama taɗauki ƙananun kaya tasaka basu kamata ba amma duka sun bayyana surar jiminta inaga bawai kananun kaya ba ko atamfa ce ajikinta wannan halittar bazata ɓoyuba, zama tayi taɗauki wayarta tare da kunnah karatun Alkur’ani tana saurara ko minti 10 batayi dazamanba anty meenah tadoka mata kira, hakan yasa takashe wayar tare da ɗaukar dogon hijab ɗinta tasaka tukkunnah tafita….!

 

SAWUN GIWA paid book ne 1k ne kuɗinshi kibiya kikaranta abinki cikin salama karki bari abaki labari.

Sawun Giwa Complete Novel Document Txt

 

File Name  Sawun Giwa… Hausa Novel Doc. 
Title   Sawun Giwa Complete Novel Document
Author    Autar Alheri 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    15/01/2025
File Size    100KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦1000
Phone No   07037092176
Download Sawun Giwa Complete Novel Document By Autar Alheri

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button