Labarai

Mr Romantic Book 2 Complete Document

Description/Story:

Mr Romantic Book 2 Complete Document,  Hausa Novel Document Written By Maman Teddy

 

Description

💋MR.ROMANTIC💋*
_Multi dimensional story._

 

Maman Teddy.

 

11.

_____________________

Rawa idanun ta keyi haka hannun ta da take nuni zuwa ga inda take ganin abun tamkar Almara ko a mafarki . Yanda take ƙwaɗa sunan Rayyanu yasa Sectary ɗin sa na hannun dama Tayi saurin shigowa tare da nufo inda Sakina take . Cike da Tsawa da masifa irin na Sectariyan tasa Ta fara cewa ” Shiyasa tun farko ban barki kin shigo ba ,don na lura Ba hankali ne dake ba , tabbas Ƙwaƙwalwar ki da matsala ko daga yanda kike mun magana a waje . Sakin baki Sakina tayi tana kallon Sakatariyar kana cikin sarƙaƙƙiyar murya tace ” Wannan shine Rayyanun dana sani ko kuwa dai Mai kama dashi ne ?. Ke Da’allah taho ki fita ,nan company ne ba wurin hayaniya ko tashin hankali ba , fita maza kamin nasa securities suyi mun waje dake . Wannan kin ga yayi kama Miki da mijin ki ? Hauka ake yi , Ko don kinji sunan sa Sir Rayyan? . Futa da Allah .!

Cikin Sanyayyar Muryar nan nasa mai narkar da zuciyar duk wani mai sauraren ta ,Muryar da Sakina ba zata taɓa mancewa da ita a Rayuwar ta ba ya katse Su da cewa ” No…Ki barta kuje ki Bata kalan aikin da tazo nema.

Sir ” Tazo nema ko kuma wanda ya dace da ita dai kake magana ? . Lumshe idanun sa yayi wanda da’alama shi mutum ne ba mai son Hayaniya ba . Ku fita ke da ita ,abun da ya dace kiyi mata amma…..Kamin ya kare wata magana tuni Sakatariyar nasa ta ja Sakina kiiiiiiii suna Ficewa daga Office din , Ita kuwa Sakina kasa Wani tasiri tayi idanun ta wasu irin hawaye ke tsiyaya mata ,gaba ɗaya Ƙwaƙwalwar ta baya kai mata Wani saƙonni , Muryar Sakatariyar ne ya katse ta wacce take doka mata Tsawa ” Kinci Albarkacin Yallabai Rayyan xamu dauke ki a companyn mu, kin san dai nan wuri ne na duk wani abu da ya shafi mechanics. Don haka aikin ki shine Tsaftace duk wani wuri da yake buƙatar A tsaftace shi . Wannan Form ne idan kin koma gida ki cike shi gobe zaki fara aiki sai ki taho dashi . Bama ƙazanta a kula da tsafta . Tayi Maganan cike da rainin hankali .

Wani irin numfashi Sakina Ta sauke mai nauyi kana tasa hannu tana amsa Form din , A hankali ta furta ” Na gode ” tana juyawa ba tare da ta jira jin mene sakatariyar zata ce ba .

**
Ganin yanda Hankalin Maleek yayi ƙololuwar tashi tabbas taga hakan a ƙwayar idanun sa , kuma sosai Munaya tayi mamakin ganin hakan ,don bata kawo mutum mai ji da kai irin shi a kwai maganan da zai firgita shi irin haka ba . Hasali a yanda take ganin sa ta dauka babu mai tankwarashi a doran duniya , sai ga shi kuma taga tashin hankali kwarara a ƙwayar idanun sa bisa ga kiran da Mahaifin sa yayi masa .

Miƙewa tayi cike da salon bariki ko ina na jikin ta karkaɗa shi take yi , cike da salon jan halin da namiji . Ƙare mata kallo yayi yana kauda kan sa gyefe ,wani irin huci na Fitan daga zuciyar sa . Hannun ta yaji tana shafa Sarauniyar sa cikin wani irin salo tana matsata tare da kumshe idanunta tana Alamar shan yaji shiiiiiii……Keeee!

 

Taji wani irin tsawar sa bisa kan ta , wanda sai da Hantar cikin ta ya kaɗa . Matsa ki bani wuri .! Yayi maganan yana ƙoƙarin ingizata gyefe . Yanda ya koma mata tamkar namijin zaki yasa Munaya saurin yin baya tana yin tazara dashi .

Wani irin duba yake ƙara mata na nuna tsanin tsana kana a fusace cikin ɗaga murya irin na mafaɗacin namiji yana ƙara doka mata Wani irin gigitaccen Tsawar da sai da Munaya numfashin ta ya kusa ɗaukewa don tsoro .

Kin san me yasa zan rabu dake ? , saboda a yanzu bana cikin natsuwa ta , wannan daman kadai ya ceceki da sai naga Waye uban ki ? Naga Me kika taka har kike ƙoƙarin ganin kin tarwatsa Rayuwa ta ni Maleek .

Mintuna biyu na baki ki tattara ki fice daga nan yanzu.! Kamin tayi wata magana tuni taga ya juya yana kokarin bin hanyar da suka shigo mai kamar lift. Da gudu ta biyo bayan sa jikin ta ko ina Rawa yake yi na tsoro Tabbas yau taga namijin damisa wanda bata taɓa ganin irin sa ba . Ɗanɗanon sa ya zarce namijin zuma , Tijara kuwa Ba’a magana indai iya wannan ne.

**
Kayi haƙuri Daddy , Lamarin Maleek abin kullum gaba yake yi ,sai dai mu cigaba da Addu’a . momyn Maleek tayi maganan tana Girgiza kai na damuwa , tabbas suna cikin ɗimuwa bisa ga bayanan da Jenny ta labarta masu akan ta da Maleek.

Sosai Ran Daddy yake ɓace wannan yasa shi a fusace cewa ” ba wai ina yi masa fada bane don bana son shi ko wani Abu ,a’a i just don’t want him to forget his manners” . Maleek Halin shi ya fara kaini makura , shi ba ƙaramin yaro bane , ban san yaushe ya fara Wannan banzan Ɗabi’ar ba . Amma Ni nasan mafita , Aure shine zai kimtsa mana shi ko mun ki ko min so , dole muyi masa Aure .

Tsaida Idanun ta tayi bisa na Daddy kamin Momy ta ɗan sauya fuska cike da damuwa tana cewa “A iya sani na Maleek mutum ne mai taimako da son alheri da tallafa mawa marasa ƙarfi . Bana tunanin Maganan Wancen Baturiyar Jerry take ko wace ? Ya zamana gaskiya ne .

Wani irin duban tsanaki Alhaji Jibo yayi mata , kaman mai son hasashen wani Abu yana nazartar kalaman ta , kana ya juya yana cewa ” Maganan Ita yarinyar ƙarya ce , to maganan Nihla fa ? . Sosai yake jin ran sa na masa zafi . Maleek…!

“ya furta cikin wata irin murya marar karsashi .

Kamin Mommy tayi masa Wata magana tuni ya juya yana barin falourn ….’

Mr Romantic Book 2 Complete Document

 

File Name  Mr Romantic Hausa Novel Doc
Title   Mr Romantic Com
Author    Maman Teddy
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    30/10/2024
File Size    172KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Mr Romantic Complete Novel Document By Mmn Teddy 

Click the below green button to read the novel online

READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button