Hausa novels

Kanwar Maza Page 77 Complete Novel By Ayshercool

Page 77

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

 

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

 

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

 

(*Ina ma’abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma’ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

 

 

 

Shiru yayi ya cigaba da kai lomar abinci bakinsa, suka tsare shi da ido suna jiran yayi magana.

 

Yaya Abubakar ya tashi zaune ya ce “Malam magana fa ake yi maka”

 

Mirsisi yaƙi magana, ya cigaba da cin abinci, Aliyu dama ya daɗe da gano yayan na su, ya afka kogin soyayya, magana ce kawai bai yi ba.

 

Sai dai ya gama cin abincin, sannan ya ce “Mama, ba ɓoye miki nayi ba, komai ya zo mini a bazata ne. Hasalima tausayinta da na ji ne, ya sanya na ji zan iya aurenta, amma kin san ni dai ban taɓa kula ƴar kowa ba”.

 

Aliyu ya ce “Wai wa ce ne?”. Harar da yayi masa ya sanya shi yin shiru.

 

Mama ta ce “To, wai an ce turakin kano yana son ganinka, zai gana da kai, a kan maganar, kuma suna buƙatar ka fito ne”

 

Mai sunan baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Mama bani da abun aurenta yanzu, kin san komai a kanta, dan ina wurin lokacin da rumaisa ke baki labarinta.

An fasa aurenta da wani, kuma a yadda take gaya mini, shi ne karo na huɗu, duk saboda waccan matsala, dalilin haka kuma, an ce wa mariƙiyarta idan ba ta aurar da ita nan da watanni uku ba, ta mayar da ita in da ta tsinto ta. Magana ake ta shekaru goma sha tara da riƙonta, wurin wa za ta kai ta. Ban san ya aka yi na ji ina son na aureta ba”.

 

Aliyu shi tausayi ma ya bashi, har yanzu bai gama yadda soyayya ce tayi masa kamun kazar kuku ba.

 

Mama ta ce “Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi ɗa na kowa ne, yadda hajiya binta ke riƙe da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaɗai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ƙaunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaɗan”.

 

Abubakar ya ce “Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ƙanwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la’akari da yadda mutum ya faɗa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan ɗin sa, zan yi magana da su baffa, a ɗaga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ƙarasa nasa”.

 

Mai sunan baba ya galla masa harara.

 

Abdallah ya ce “Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yinƙura abu namu maganin a kwaɓe mu”.

 

Yasir ya yi murmushi ya ce “Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah”

 

Huzaifa ya ce “Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal ɗin da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa”.

 

“Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni

 

 

zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir ɗin ɗinki, banda shegiyar ƙarya da saɓa alƙawari”.

 

Mama ta ce “To zakaru, ai kun ci kun ƙoshi, dole ku yi mini faɗa”.

 

Umar ya ce “Duk na ji ta bakin ku, na kuma gode sosai, amma babu wanda zai rabu da wani abun sa saboda ni, kai habu ba za a ɗaga bikinka ba in sha Allah, ina fatan nima wannan ɗin ba zai gagara ba, zan ƙara ƙoƙari”.

 

Abubakar ya ce “Wai dan an haife mu lokaci ɗaya ni sa’anka ne? Bana magana biyu kai ka sani, gidan nan ya zama naka, dama kaine ƙarfin ginin, ni ba gaggawa nake yi ba, ita ma haka in sha Allah ita da iyayenta za su fahimce ni”.

 

Mai sunan baba zai sake magana mama ta ce “Ka riga ka ɗaukki aiki babana, idan ba hakan aka yi ba, ni ban ga mafita ba, garbatina ɗan albarka, Ubangiji Allah ya ƙara haɗa mini kanku, ya kau da abun ƙi a tsakanin ku, a duk lokacin da abu ya tasowa ɗayanku, na ga kun haɗa kanku, ba ƙaramin daɗi nake ji ba”.

 

Usman da tun da ake maganar bai ce komai ba sai yanzu ya ce “Mama duk jajircewarki ce ta kawo haka, Allah dai ya ƙara miki lafiya da nisan kwana”.

 

Suka amsa da Amin, Abdallah ya ce “Mai sunan baba, idan abu ya taso maka, bamu yi maka ba, wa zamu yi wa? Sadaukarwar da kake yi domin farincikinmu ai tana da yawa, komai ka samu mu, kai ne wa, kuma kai ne uba, kowa ya kwaso matsalar sa, mai sunan baba, dan haka muna bayanka a kowane ƙadami Allah ya iya maka yayi riƙo da hannunka”.

 

Karar da ƴan uwan nasa suka nuna masa, ba ƙaramin daɗi tayi masa ba, har sai da hakan ya sanya shi murmushi, kuma ya kasa ɓoye farin cikinsa.

 

***

Ko da labari ya iske dangin mahaifinsu Umar, sun yi murna, tare da tsokanar mai sunan baba, dama zai iya yin budurwa yayi soyayya.

Wan mahaifinsu ya ce zasu yi ƙoƙari, amma abubakar ma ba za a ɗaga aurensa ba.

Sai dai yayan mahaifinsu ya jinjina lamarin auro ƴar gidan sarauta yana talaka.

 

Tare da shi da umar, da yaya Abubakar da ƙanin mahaifinsu, sai mijin iya baffa musa da ya zo daga, suka je gidan turaki bisa jagorancin Mahmud kamar yadda ya buƙata.

 

Sai dai sun ga karramawa, da mutuntawa da basu taɓa tunani ba, turaki ya ƙara jaddadawa mai sunan baba matsayin iman, mai sunan baba ya ce ya amince.

Turaki ya tambayi ƴan uwan mahaifinsa, a kan idan sun amince su ma, suka ce ai shi ne zai zauna da ita, kuma tun da ya ce ya ji ya gani, suma sun amince ai ɗa na kowa ne, a tarbiyyar da umar yake da ita, sun san ba zai kawo abun da zai cutar da shi ba.

Baffa Musa wa ga mahaifinsu ya ce “Sai dai mu ma wani hanzari ba gudu ba, yaron nan maraya ne, bashi da ƙarfi saka biki nan da watanni uku yayi kusa da yawa, ga ɗan uwansa nasa bikin muke hari, muna fatan a ƙara mana ya zama watanni shida, gaba ɗaya ya mayar da hankali ne a kan auren ɗan uwansa bamu zaci nasan zai zo haka ba”.

 

Turaki ya ce “Babu laifi, kar ku damu. Ubangiji Allah ya yi mana jagora, kuma a hakan nan ma kawai, na yaba da tagwayen sosai, ba dan ance shi ma ɗan uwan aure zai yi ba, ai da sai na bashi ƴa ta, ai duk wani wanda ya fito daga tsatson ƴa ta rumaisa, duk abun da yake so, in dai ina da shi zan yi masa.

Allah ya sanya musu albarka, ya nuna mana lokacin lafiya”.

 

Baffa musa ya ce “Amin, ranka ya daɗe tun da har an samu daidaito, ina ga ba sai mun ja lokaci ba kawo kuɗin aure, ga kuɗi mun taho da su”

 

Gaba ɗaya suka kalleshi, su dai sun san ba su yi haka da shi ba.

 

Ya karkace ya ciro kuɗi, dubu ɗari da hamsin, ya ajiye a gaban turaki.

 

Turaki ya ce “Masha Allah, Allah ya sanya albarka, to ba dan ba a shirya ba, ai da sai a ɗaura, mu bashi gidan zama, a wuce wurin ko malam umar?”.

 

Mai sunan baba ya risuna ya ce “Ranka ya daɗe ni yakamata na yi ƙoƙarin samar da mahalli”.

 

Yayi murmushi ya ce “Babu laifi, Allah ya nuna mana”

 

 

Ko da suka taho hanya, Mahmud har gida ya kai su mai sunan baba, a gida suka sanar da mama ai an bayar da kuɗin auren ma, mama ta ce daga zuwa tambaya an biya kuɗin aure? Ta ce to sai a nemo kuɗin malam musa a bashi abun sa, amma ya hau mama da faɗa, a kan dan yayi wa ƴaƴan ɗan uwansa abu, dan me za ta ce a biya shi.

 

Turaki ma wayar ammi ya kira, ya sanar mata su mai sunan baba sun bayar da kuɗin auren iman, dubu ɗari da hamsin, sun sanya watanni shida dai-dai.

 

Ammi ta yi mamaki, dan ita bata ta;a zaton abun a haka ba, ta ce to ba a basu komai na tukici ba, sun kawo kuɗin aure.

 

Turaki ya ce su aika musu daga baya, amma sun zo da kuɗin aurensu sun bayar.

 

Farincikin ammi ya kasa ɓoyuwa, ta nufi ɗakin laila, da suke tare da rumaisa, tana ta koya mata abubuwa.

 

“Laila, rumaisa” suka ɗago suka kalli ammi.

 

“Daga zuwa amsa kiran turaki, sun bayar da kuɗin auren iman, an saka watanni shida”.

 

Ruma tayi murmushi ganin yadda bakin ammi yaƙi rufuwa.

 

“Au shine aka wareni, ban ma san za a kawo kuɗin aure ba, iman yanzu ta rama ta ƙwace mini yaya, dan na auri takawa”

 

Suka yi dariya, laila ta ce “Kaii Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu. Ni dai gayen ya burgeni ranar da na taɓa ganinsa, so gentle”.

 

Ruma ta ce “Taɓ, mai sunan baban ne gaye”.

 

Ammi ta ce “Ya Ubangiji Allah ka sanya ƙarshen matsalar nan ne ya zo, Allah ya sa kar a gaya masa wani abu da zai saka ya ce ya fasa”.

 

Ruma ta ce “Ammi, idan kin ga ba ayi auren nan ba, sai ƙudirar Allah.  Mai sunan baba ba zai taɓa cewa zai fasa ba, sai idan ku kuka fasa auren, duk rintsi kuwa”

 

Ammi ta ce “Allah ya sa, bari ta dawo na gaya mata, Allah sarki ƴar marainiyata, Allah ya kaɗe abun ƙi”.

 

Ƙasan zuciyar ammi, tana ta yi wa iman addu’a Allah ya sa ta dace, dan yanayin nature mai sunan baba, tana bata tsoro, gani take kamar yanayin iman ya nuna tana son shi ba kaɗan ba.

 

Da labari ya iske iman, da ta koma ɗakinta sai da tayi sujudu shukur, sujjadar godiya ga Allah, saboda tsananin farinciki, haka nan a ranta take jin, sassauci zai samu a rayuwarta.

 

A irin kyan da Allah ya yi wa iman, zaka raina abun da aka bayar na kuɗin aurenta, amma jiki na rawa ta kira mai sunan baba.

 

Sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga.

 

“Yaya umar”

 

“Na’am”.

 

“Ashe kuɗin auren zaku kai, na zata kawai zuwa kayi ka amsa kiran da mai girma turaki yayi maka?”.

 

“Na yi garaje ko, na kai kuɗin auren ba tare da kim ce mini kin amince ko a’a ba. Tun da rumaisa ta ce mini, akwai wanda ki ke so”.

 

Iman a ranta ta ce ‘Kai ɗin ne dai, kai nake so yaya umar’.

 

A zahiri ta ce “Ni ba wanda nake so fa”

 

Har cikin kansa ya ji shagwaɓar da tayi masa, ya sake gyara zaman wayar sannan ya ce “To ya aka yi?”

 

“Bugowa na yi, na maka ya ka je gida, Allah ya ƙara buɗi”.

 

“Masha Allah, ayi haƙuri abun talaka na san kin fi ƙarfin hakan”

 

Iman ta ce “A’a ban fi ƙarfin haka ba, Allah ya yassare maka”.

 

“Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, thanks” ya katse wayar.

 

Nothing romantic mai sunan baba ya sani, kawai ayi abun da ya dace, dan soyayya in dai irin yadda Aliyu da Abubakar suke me

Jabir kuwa tamkar zai yi hauka, haka ya ji da aka ce, wai an kai kuɗin auren iman, bai taɓa tunanin da gaske yana son ta ba sai yanzu.

A baya matsananciyar sha’awarta ce take addabarsa, tun ranar da ciwonta ya tashi, yana nan shi ya ɗauketa ya kaita mota.

A baya bai taɓa tunanin jin son ta ba, saboda tana girmama shi a matsayin yayanta, shi kuma ƙanwarsa, tun daga ranar da ya ga jikinta, ya sanyawa ransa lallai sai ya mallaki iman, ko ba komai, idan ka samu irinta a yaranka, ka samu kadara, saboda kyakywar bafulatanar yarinya ce.

 

Washegari, ammi ta bayar order yin girke² snacks, ta ce a kai gidansu rumaisa, ruma ta ce gida za ta je, ayi sabgar nan da ita, saboda wauta ta cewa Iman ta shirya, su tafi tare, laila ta ce ya za ayi ta je kai tukuicin kuɗin aurenta, ban da wauta irin ta ruma.

 

Ammi ta ce laila da sidi sai su kai, sai su tafi da rumaisa, ruma ta ce ga Mahmud, ba sai sidi ya je ba.

Ammi har mamakin yadda Mahmud yake yi wa rumaisa biyayya take yi, duk abun da ta ce masa yayi, ko musu baya yi yake aikatawa.

 

Hakan kuwa aka yi, da shi da laila, da rumaisa, suka kai kayan nan, mama ta din ga mitar wannan kayan sun yi yawa, dan sun kusa kai ɗaya da kuɗin auren, banda uban lemuka da naman kaji.

 

Laila sun gaisa da mai sunan baba, sai dai sama-sama, yaya Abubakar ne mai sakin fuska, sai usman sarkin tsokana.

 

Laila ta daɗe a gidan, suna hira, take bawa mama labarin yanayin zamanta a canada, da iyalinta, take gaya mata a cikin watan, mijinta da yaranta suma zasu zo hutu.

 

Laila ta yi wa mama sallama, ta cewa rumaisa, za ta je ziyarar ƙawayenta da ke Kano, idan Mahmud ne ya zo ɗaukarta, ko sidi sa biya su ɗauke ta.

 

Rumaisa kuwa baki yaƙi rufuwa dan murna.

Yasir ya samu ruma ya ce “Ke, zo mu yi shawara, nifa zan saiwa mai sunan baba akwatunan biki”.

 

Ruma ta ce “Da wani kuɗin?”.

 

“Ke baki san na kusa fara shigo da wayoyi, da computer daga china ba, ni da abokina muke tara kuɗin, yayansa ne zai tsaya mana, mama ma ta san zancen, amma a kuɗin dole ni zan saiwa mai sunan baba akwatunan lefe”

 

Rumaisa ta din ga bayar da shawarwari, na arziki da na shirme.

 

Bayan la’asar, Mahmud ya dawo ya ɗauki rumaisa, suka biya suka ɗauki laila, albarkacin rumaisa, duk da ko a baya, laila da Mahmud ba a ga maciji, amma suka din ga hira yau sosai, hirar da ba su taɓa yi a baya ba.

 

Jabir kuwa, Kasa jurewa yayi, ya ɗauki mota, ya tafi gidansu takawa, wani irin kishi, da zafin zuciya yana ta azalzalarsa, ya shiga part ɗin su, sai dai kai tsaye da ya shiga babu kowa a falon, ya tafi ɗakin iman.

 

Tana zaune a kan gadonta tana danna waya, kawai sai ganin mutum tayi a tsaye a kanta, yana huci.

 

Sai da ta tsorata, ta ce “Uncle J, lafiya kuwa?”.

 

“Ban sani ba, tsohuwar munafuka, ni zaki yaudara? Wato dama wancan banzan talakan matsiyacin ki ke so? Ya rasa abun da zai kawo kuɗin aurenki sai dubu ɗari da hamsin, ko da yake babu mamaki, tun da kema tsatson tsiyar ce, ƴar masu kiwo ƙafa babu takalmi duk da babu wanda yake da tabbacin hakan ma, munafuka mayaudariya”.

 

“Uncle j ya zaka din ga zagina ne?, Nifa ban taɓa cewa ina sonka ba, na sha gaya maka a baya”.

 

“Dalla rufe mini baki, har ke wani zaɓi ne da ke, kina wulaƙantacciya”

 

Iman tayi murmushi ta ce “Tun da ni wulaƙantacciya ce, sai ka bari mai sona saboda Allah, ba dan jikina ba, ya aureni”.

 

“Ni kike gayawa haka ko? To ayi auren mun gani, zaki gane kurenki ne”.

 

Ya juya ya fita fuuu, ta zuba bishi da ido, a falo yayi kaciɓis da ammi, ammi cikin tuhuma ta dube shi ta ce “Ahh jabir daga ina kuma?”.

 

“Wallahi baki yi wa kanki adalci ba, a da ne ake aibata ki, nake karewa, ashe haka kike, waccan ƴar matsiyatan ta zigaki kin hanani ƴa, ƴar ma da ba wanda ya san tushenta, balle a san daga gidan uban wa take, nayi jihadi na ce zan aureta amma aka wulaƙanta ni”.

 

Ammi ta ce “Jabir, ni ka ke gayawa haka?”.

 

“Na faɗa, ai kema kin san baki yi mini adalci ba, mun gama magana da ke, ki je ki canza magana, har da yi wa mahaifiyata sharri, saboda tsabar mugunta da son zuciya, ban sani ba ko dan ba ƴar ki ba ce ba, ya sanya kika zaɓa mata talaka matsiyaci”.

 

Ji yayi an ja shi baya da ƙarfin gaske, an sauke masa zazzafan marin da ya kasa gane daga ina marin ya fito.

 

Mahmud ya fuskance shi sosai ya ce “Idan kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri, babarka ce babbar annamimiyar da ta haɗa komai, ita ta zo ta ce ba ta son auren, ta koma kuma ta ce ba haka ta ce ba, idan ka kuma yin mummunar magana a kan ta, sai na yi maka dukan tsiya wallahi”.

 

Duk kallon mamaki suke yi wa Mahmud, banda rumaisa da ta dubi Mahmud ta ce “Ai wallahi duk ɗa nagari abun da zai yi kenan daddy. Kuma mun ji, ni da yayana talakawa ne, amma masu mutunci da sanin darajar kai.

Kuma idan har za a bawa mutum aure saboda nagartar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa, wallahi sai an bawa mai sunan baba sau dubu ba a baka ba”.

 

Jabir ya kalli Mahmud ya ce “Ni ka mara?”.

 

“Waye kai ɗin da ba zan mareka ba?”

 

Jinjina kai yayi ya fita, yana huci, sai dai ya san ko a ido, ba zai iya dukan Mahmud ba.

 

Kasancewar baba uwani tuni mummy tayi bikonta, domin kuwa ta gane cewa dole-dole tana buƙatar baba uwani a cikin al’amuranta, domin sai ta na sanin halin da ake ciki a sashin ammi, sannan za ta san ta ina za ta dinga ƙulle-ƙullenta.

Ita ma baba uwanin Kasancewar ta rayu da mugun son abun duniya, ya sanya babu tunanin komai, ta komawa mummyn.

 

Dan haka ko da wannan al’amarin ya faru, ita ta lallaɓa ta kira Mummy a waya ta labarta mata.

 

 

Ammi kuwa ta rasa meya kamata ta yi ne? Farincikin ɗan da aka rabata da shi, aka cusa masa ƙiyayyarta ya damu da ita, har ya shigar mata faɗa? Ko kuma fargabar abun da ka iya biyo bayan abun da ya aikata ɗin?

 

Washegarin da abun ya faru, shine lokacin da suka shirya tafiya gombe, wanda tafiyar har da ammi, har da laila da rumaisa, nusaiba iman da kuma sabir.

 

Rumaisa taga karamci, kamar su cinyeta, ko ina ta shiga ayi ta nunata ga matar takawa, ga kuma ɗan sa ɗan marigayiya Aisha.

 

Haka zalika sun yi murnar zancen auren iman, da yayan rumaisa, da ammi tayi musu, maman laila ta daɗe rasuwa, sai mahaifinta da ƴan uwanta, kasancewar saukar su iman an ƙara sati guda, ya sanya ammi ta kashe wayoyinta, dan kar ma a kirata a ɗaga mata hankali, a kan abubuwan gidan nan, sai da suka kwana uku, sannan suka dawo kano.

 

Rumaisa ta samu abun arziki kashi-kashi.

 

Mummy kuwa ta rasa in da zata saka ranta ta ji daɗi, domin kuwa alkadarinta ya tasan ma karyewa, tun da labari ya isaketa cewar Mahmud ya mari  jabir, saboda ya kare ammi, abun ya dungunzuma hankalinta ainun, me hakan yake nufi kenan? Asirin giwa ya fara cin sa? Zai karkata ya koma wurinta, domin shishshigin da yake yi a sashinta yayi yawa, dan ko kai kuɗin auren iman, labari ya isketa, shi ne ya jagoranci ƴan uwan su rumaisa har gidan turaki.

Sai dai ta lura, kamar rumaisa ke taka muhimmiyar rawa, wurin rusa mata shirin da take yi, ta hanyar ziga Mahmud, sai dai ta rasa ta ina yakamata ta yi maganin rumaisa. Sannan ta ƙudiri yadda ta ƙwace Mahmud, ba zata bari ya koma ga ammi ba, dan ba zata gama wahalarsa ba, sannan rana tsaka ya koma wurin uwarsa ba, dan idan haka ne, gara ta nakasta shi yadda ba zai moru ba.

 

Mummy na tsaka da tunanin meye abun yi, Hajiya Lubabatu tayi mata dirar mikiya, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, a kan marin da Mahmud ya yi wa jabir.

 

Aka yi sa’a kuwa yana nan, mummy ta ce “Haba lubabatu, mutuwa ma na kunyar idon mahaifi, ya a gabana zaki zo kina zagar mini ɗa? Ai sai ki haɗa su ki yi musu nasiha, tun da duk ƴaƴanki ne”.

 

“Ba wani ƴaƴana, kema ki daina Wannan ƙumbiya-ƙumbiyar, ki fito kan ki tsaye ki daina wannan munafuncin, kina riƙon Mahmud ne da cikar naki muradin”.

 

Mummy ta ce “Ni tsakani da Allah na riƙe shi, sai ma dai tayaki da nake yi, naki muradin ya cika”

 

“Jamila, wallahi kar nake kallonki. Kai kuma zaka ga abun da zai biyo ba, ban da tsabar wulaƙanci, uwar me uawar taka binta ta tsinana maka a rayuwar, da har zaka mari jabir saboda ita? Ƙarya yayi an kama an cuce shi, a kan wannan banzar yarinyar to wallahi ahir ɗin ka, shi da yake jiran gadon sarauta, ai mace ma sai wadda ya zaɓa”.

Mummy ta ce “Lubabatu yakamata ki san abubuwan da ki ke faɗa fa”.

 

“Ba wani, ni ki ƙyaleni, kashedi nayi da babbar murya, idan kallon uwa yake yi miki, to ki ja masa kunne, ya kiyayi ɗa na” Mummy tayi mamakin abun da hajiya Lubabatu ta zo tayi mata, wato hakan yana nufin ita ma tunanin da yake ranta, shine a nata ran, na lokaci yayi da kowa yakamata ya kama gabansa, tun da haryanzu kusan za a iya cewa ita hajiya Lubabatu ba wani benefits da ta samu a tafiyar nan ta su.

 

‘Aikuwa ba zaki samu ba, a hakan zan ƙara zage damtse, ka samu kujerar nan Mahmud, kuma na kawo ƙarshen duk wannan abun, ta hanyar nisanta ka da giwa da ahalinta’.

 

Ta kalleshi ta buɗe baki za ta yi magana, amma ya tashi tsam ya bar mata falon.

Wanda a da, ko gyaran murya tayi jikinsa na tsuma, yake saurarata.

 

Koda rumaisa suka dawo, kamar yadda ammi tayi tsammani, ana ta surutun kuɗin auren iman, wai dan ba ƴar ta ba ce, ta hanata auren jabir, za ta aura mata talaka, tun da laila ƴar yayarta ce, ai mai kuɗi ta aura mata.

 

Ammi dai ta toshe kunnenta, kwanansu uku da dawowa, aka yi saukar Alqur’ani na su Iman, an ci an sha an yi walima sosai da sosai, sai dai mai sunan baba bai je ba, wanda hakan bai yi wa iman daɗi ba sam.

 

Kayan saukar ma da ta ware masa, sai sidi ne ya kai masa gida.

 

Sai daga baya yaje gida, ya ga allon saukar ta ta.

 

A ranar ruƙayya ta ga iman tare da mai sunan baba, ta koma sashinsu, tana koɗa kyawunsa da tsananin kwarjininsa.

 

A haka rayuwa ta cigaba da juyawa, matsaloli suka ƙara tsananta a tsakanin gidajen sarauta, kowa ya ba za komar cimma burinsa, ko ta halin ƙaƙa ko a mutu ko ayi rai, kowa burinsa ya ga ya samu abun da zuciyarsa take muradi.

 

Mijin laila ya zo hutu da shi da yaransu, sai dai yaran gaba ɗaya hausa ba ta ishesu ba, sun fi magana da turanci, ga mijin lailan kansa wani fari sol da shi, kamar ba ya jin hausa, laila sai zuba taɓara take kala-kala, suka tattara zasu koma gidansu na Kano, laila ta ce sai rumaisa da iman sun bita gidanta, ammi ta ce ba za ta kwashe mata ‘ya’ya ba za dai su din ga zuwa.

Ƴaƴan laila kansu, tamkar black Americans, mata biyu sai namiji ɗaya, kyawawa sosai, ranar da Yasir suka kaiwa rumaisa ziyara gidan laila, yarinyar laila ta biyu, ta liƙewa Yasir, hira kala-kala, ta din ga yi masa tambayoyi, mussaman ganinsa da computer, har mamakin yadda yarinya ƙarama take da ilimin computer sosai haka.

Haka mijin laila babu ruwansa, hirar da suka din ga yi da su huzaifa, da yasir, mijin laila ya cewa Yasir idan za a bar shi a gida, zai tafi da shi canada, ya ƙara karatu idan ya kammala diploma da yake yi a kan computer science.

Ya cewa Huzaifa, “kai kuma gashi an ce tela ne, baka cika alƙawari kai ya zmu yi da kai”

 

Huzaifa yayi dariya ya ce “Sharrin yasir ne, ina cika alƙawari, shi da yake hacking ma”

 

Dariya suka yi, ya ce “To kaima zaka bi mu canadan ko kuwa?”

 

Huzaifa ya girgiza kai ya ce “Mama ba zata bari a tafi da mutum biyu ba, shi dai ya tafi”

 

Su duk basu zaci da gaske yake ba, laila take bashi labarin rumaisa kuma zane-zane take yi, nan ya dinga bayanin yadda masu zane-zane suka da muhimmanci a ƙasashen ƙetare.

 

Rayuwarsu very simple, iya zaman da suka yi a ranar, sun ƙaru da mijin laila sosai da sosai, ya kuma cewa laila, idan har Yasir ya kammala diploma, tayi masa magana ayi wa Yasir visa.

 

***

 

A ranar da rumaisa ta tsaya a gaban kalandarta, ta soke kwana na ɗari da saba’in da uku, a ranar yayi dai-dai da saura kwanank bakwai cif-cif mijinta ya dawo, ji take tamka ta zuƙo sauran kwanakin, dan gani tayi kwanakin ma sun daina yi mata sauri.

 

Duk wani gyaran jiki da laila take yi wa iman na aure, da wanda ta saka ake yi mata, tare da rumaisa ake yi mata su.

Rumaisa kuwa daga ita har iman yadda suka koma ba a magana, domin kuwa sosai ba kaɗan ba, sabayar maman Khadija ta karɓi rumaisa, da maganin girman nono na maman ilham, duk wanda ya san rumaisa a baya, ya ganta yanzu sai ya sake kallonta, ta cika abun ta dai-dai gwargwado, mujewar da ta yi, tayi ƙiba gwanin sha’awa ƴar caraf da ita, ga wani irin kyau da fatarta tayi.

 

Dama iman ba a magana, gata fara tas, ta ƙara da kunun maman Khadija, gashi ita ma ba a barta a baya ba, wurin amfani da maganin maman ilham, abun sai wanda ya gani.

 

 

(Ga mai buƙatar ya murmure, yayi kyau gwanin sha’awa kamar rumaisa, iman da kuma anty laila, sai ku garzaya inbox ɗin maman Khadija, domin mallakar na ku garin kunun sabayar, ku tuntuɓeta kai tsaye ta lambar wayarta 08033411249, tana zaune a bayan Federal Palladan Zaria, haka zalika tana aika kayanta ko ina a faɗin ƙasar nan, da kuma maman ilham mai tula-tula, domin tsantsamw jiki sa kama mutuncin nai, ga masu aure, ƴan mata zaurawa da masu yaye, suma suna iya garzayawa inbox ɗin ta ta wannan lambar 08135613021, tana nan zaune a no. Ai kawo road Kaduna, haka zalika ita ma tana aika kayanta ko ina a Nigeria)

 

Ita kanta mama, sai da tayi mamakin yadda rumaisa ta koma, dan bar sai da ta fara tunanin ko ciki ne da ita, saboda yadda tayi kyau abun ta.

 

Laila da kanta, da masu aiki, suka je gidan rumaisa, suka yi masa gyara sosai da sosai, aka gyara komai, ta cigaba da jaddada mata, ta riƙe abubuwan da ta koya mata, ta kula da kanta.

 

Turarukan rumaisa na aure, ta bayar aka haɗa da na iman, aka ƙara tsuma su, sannan aka yi mata wasu.  Banda sabbin ɗinkuna na kece raini da aka yi wa rumaisa.

Babu babban abun da ya ƙara birge ruman, irin yadda aka yi mata riguna masu breast cut, kuma suke zama cas a jikinta, gashi ta fara saka brezia, murna har da taka rawa, ta sha gyaran gashi, ga lallenta ja da baƙi. Ƴan makarantar bokon su na mamakin yadda wasu lokutan rumaisa ke cin karenta babu babbaka, an hana kowa yin lalle, amma rumaisa ana bari tayi abun ta.

 

Ƙarfe goma sha ɗaya na safe, jirginsu ya sauka a aminu kano international airport.

Sannu a hankali yake tafiya, yana jan akwatin sa, wayarsa yake dannawa yana neman layin laila, dan a wayarta suka yi magana da rumaisa jiya, ta ce za ta turo a ɗauke shi, so yake yaji waye zai zo ɗaukar ta sa.

 

Sai dai yayi turus, da ya ga Mahmud a tsaye, da sabir a hannunsa.

 

Da ƙarfi Sabir ya fara kiram “Papaaa. !paaapaaa” yana miƙe masa hannu, ya tattaka har da ɗan gudunsa na yara masu koyon dabo, ya nufi in da mahaifinsa yake!.

 

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 78 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button