Page 78
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*
Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”
Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….
(*Ina ma’abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma’ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)
Durƙsawa takawa yayi, ya ɗauki sabir yana juyi da shi, yana murmushi, ya ce “I so much miss you darling, how are you?” Yayi maganar yana sumbatar goshin sabir.
“Paapa, daddy kaga” yayi maganar yana nuna masa in da Mahmud yake tsaye.
Kallon in da Mahmud yake yayi, yana mamakin saurin wayon sabir, ya ɗaga kai yana dubawa ko zai ga su ammi, amma babu kowa sai Mahmud.
Ya kira laila a waya, ta sanar masa da cewa Mahmud ya zo ɗaukarsa, zai fara masifa, ta kashe wayarta.
Mahmud kuma yayi banza bai ce masa komai ba, bashi da wani zaɓi, illa ya je ya saka akwatinsa a boot, sannan ya buɗe bayan motar ya shiga.
Har suka fara tafiya, babu wanda ya tankawa wani, sabir ne dai daɗi ya isheshi na ganin mahaifinsa, ya kasa zama wuri ɗaya, sai ya taka cinyar adam ya miƙe yana taɓo Mahmud “Daddy ka ga papa”
Mahmud yayi murmushi,yana shafo kan sabir da hannu ɗaya.
Takawa ya riƙe hannun sabir ya ce “Ina mimi?”
“Mimi, iman, baba” ya din ga jero wa adam sunaye, adam yana ta murmushi, yana jin yadda yayi kewar ɗan nasa.
Tun daga bakin gate, security suke yi wa adam barka da zuwa, aka ɗauki akwatinsa zuwa cikin gida.
Cike da ɗoki da son ganin mimi ya ƙarasa sashin ammi, ammi ce ta fara taro shi, ta rungume shi, ya durƙusa ƙasa yana gaisheta.
Ammi ta yi masa alamar ya tashi, ta sake rungume shi tana faɗin “Barka da sauka, ya hanya ya makaranta?”
“Alhamdilillah ammi, na same ku lafiya?”
“Lafiya ƙalau Alhamdilillah”
Laila ta ce “Ƴan makarantar bokoko, sannu da zuwa”
“Yauwwa big aunty” yaran laila safiya, anam da haidar, suma suka taho da gudu, suka rungume takawa suna faɗin uncle.
Nusaiba da iman ma duk sannu da zuwan suke yi masa, fuskokinsu, ɗauke da tsantsar farincikin ganin dawowar ta sa, sai dai ya gama rarraba idonsa bai ga mimi ba.
Ya kalli iman ya ce “Amarya ba kya laifi, ya shirye shirye? Kodayake dole a zo a sake wani shirin, tun da na dawo”.
Dariya suka yi gaba ɗaya, yana ta son ya tambayi rumaisa, amma kunya yake ji, kuma dai ya san suna cikin hutun makaranta.
Nusaiba ta kai masa akwatinsa ɗakinsa da yake sashin ammi, takawa ya ce “Nusiaba ina mimi ne?”.
“Wallahi ban sani ba takawa, anty laila zaka tambaya” ya jinjina mata kai. Ya shiga yayi wanka, ya fito falo, an shirya masa abinci a dining, sai dai ammi kanta ta lura yadda yake ta leƙe-leƙe, ta san ba kowa yake nema ba sai rumaisa.
Laila kuma ta zauna ta saka shi a gaba da surutu, ya dubi laila ya ce “Yanzu a gidan nan a rasa wanda zai iya zuwa a cikinku ya taro ni?”
Laila ta ce “To yanzu a ƙafa ka taho? Ba ɗaukkoka aka yi ba?”.
“Amma shi ne yakamata ya je ya ɗaukko ni?”
“Wannan kuma matarka za ka tambaya, da ta shirya hakan”.
Ya kalli in da ammi take, ya ga ba ta jiyo su, ya ce “Yauwwa, wai tana ina ne?”
“Ita wa?”
“Meye haka ne, matata mana”.
Laila tayi murmushi ta ce “Tana nan ƙalau tana gaisheka”
Ya tsuke fuska ya ce “Wai meye haka ne? Dan Allah tana ina, ina son ganinta”
“Zaka ganta ne, kai dai ka kammala cin abincin ka huta”
Ya dire cokalin ya ce “ya haka ne? Watanni shida ba ma tare, na dawo kuma kin ɓoye ta”.
“To wai me za ta yi maka ne? Sai mun gama jan aji tukuna”.
Yayi dariya ya ce “Jan aji, wane ajin kenan, ina fatan ba wata rigimar ki ka koya mata, in the name of jan aji ba?”
“You will see” tayi maganar tana dariya.
Mirsisi anty laila taƙi faɗa wa takawa, in da rumaisa take, sai da ta kai ga ya cire kunya ya cewa ammi “Ammi wai ina maman sabir ne?”
Ammi ta ce “A’a bani zaka tambaya ba, ai dama da zaka tafi laila ka bawa riƙo, kuma da zaka dawo ta ce ba ruwana da abun ku, dan haka babu ruwana”.
Wasa² har la’asar, tun yana tambayar har ya haƙura, sai daf da magariba, laila ta ce masa jeka gida, zan kawota.
Da fari bai yadda ba, sai da ta rantse masa tukuna, sannan ya amince.
Da ya je ya tarar da gida ko ina tsaf, duk an sauya fasalin zaman furnitures ɗin, ko ranar da aka kai masa rumaisa, gidan bai haɗu har haka ba.
Yana zaune a falo, yana kallon ƙwallon dole, saboda ya ma rasa abun yi.
Ya ji maganganu ana hawowa sama, da sauri ya tashi tsaye, yana jiran isowarsu.
Laila ce da Iman, sai nusaiba, rumaisa ta duƙunƙune da mayafin lafayarta.
Murmushin sa ya faɗaɗa, suka matsa daga kusa da rumaisa, ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sake rufe fuska tana murmushi, ƙarasawa yayi gabanta ya rungumeta, yana murmushi.
Rumaisa ta rintse ido, saboda wata irin kunya da ta kamata, ganin yadda ya rungumeta a gaban su laila.
Nusaiba kuwa video take yi musu, tana cewa bari muyi ƙara’i tun da bamu yi a lokacin biki ba.
Ya ɗagota yana son ƙare mata kallo, amma ta hana shi damar hakan, sai cukuikuye jikinta take yi, mayafin gashi sai wani irin ƙamshi ne kala² yake tashi daga jikinta.
Laila ta ce “Ku zo mu tafi, kar ya saka mini duka, saboda jan ran da na yi masa, ga ta nan ku cinye juna, ƙarewar ƙauna”.
Adam ya ce “Eh ɗin, Allah ya bada lada, amma an wahalar da mu haba”.
“Da ƙafarka zaka zo nemana, zan rama ne” tayi maganar tana dariya, su iman suka bita suka tafi.
Suna tafiya, ya tsuguno dai-dai tsayinta, ya sake rungumota jikinsa, ya ce “I miss you little mimi”
Kasa magana tayi, kawai taji hawaye na zubo mata, jin tana sheshsheƙar kuka, ya sanya ya ɗagota, ya ce “Yaya aka yi?” Kasa shiru tayi, ta cigaba da kukan.
Ya zauna da ita a jikinsa a kan kujera, ya ce “Gaya mini menene?”.
“Ba kai ne ka daɗe ba, kuma kwanakin suka ƙi cika ba?”
Takawa yayi dariya ya ce “To ni na hana su cikar?. Allah sarki, duk murnar ganina ce har da kuka? I so much miss you dear”
Lafewa tayi a jikinsa, tana cigaba da kuka, cike da shagwaɓa, ganin dawowar ta sa take yi, tamkar a mafarki.
“Mimi, meye sirrin ne? Kin ga yadda ku ka yi kyau kuwa, kalli skin ɗinki, duk da dare ne, kin yi fresh ga wani ƙamshi mai daɗi da ki ke yi, i like it baby”
“Baby kuma, kamar wata mijin anty laila, gursumemen dattijo wai baby, ni in dai zaka ce mini baby, sai ka sayo mini feeder, da kayan wasa”
“Ai na sani, ko shekara ɗari za ayi, ba zaki canza halinki ba mimi”
Hira suka sha sosai, rumaisa ta din ga bashi labarin wasu daga abubuwan da suka faru, sai dai tafi karkata ga laabrai masu daɗi da suka faru.
Haka shima ya din ga bata labarin makaranta, sai da suka raba dare a falon, ya ce suje ɗakinsa su kwana, amma ta kada baki ta ce Ba zata kwana a gado ɗaya da shi ba, sai ka ce Anty laila.
“Au kina nufin laila ce mara kunya ko, sai na gaya mata. Kuma banda gulma ba sau biyu kina kwana tare da ni ba?”
“To ai wannan tsautsayi ne, Anty laila dai kama rayuwar turai ta ratsata, take gaya mini ita ɗaki ɗaya take kwana da mijinta, wai tare a kan gado ya rungumeta, ni dai wannan karatun nata ba ɗauka nake yi ba. Dan ba iyawa zan yi ba”
Yayi murmushi tare da shafar sumar kansa, ya ce “Shikenan a sauka lafiya, tsarabarki sai Allah ya kaimu da safe”
Babu kunyar komai, ta wuce ɗakinta.
Sai dai da ta tafi ɗakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta shirya ta kwanta bacci, tana sake ganinsu a tare a cikin idonta, yana magana yana yi mata dariya.
Rungume pillown tayi, ta furta “papa a hankali”
Washegari da wuri ta tashi ta hau aikace-aikace, ta gyara ko ina duk da babu datti.
Ta shiga kitchen ta haɗa abincin karin kumallo, ta leƙa ɗakin Adam.
Ya lulluɓe jikinsa da bargo, saura fuskarsa kawai a ya bari a waje, baccinsa yake yi hankali a kwance, kai da gani ka san a gajiye yake.
Ta kalli agogon ɗakin, tara da rabi na safe, a hankali ta ce ‘Papa baka jin yunwa ne?’
Sai kuma ta tuna lecture malamarsu da ta laila, wai yadda ake tashin miji daga bacci.
Ta rife bakinta da hannunta ta ce “Ni, haka kurum in je in wani kama shafa shi, ina cewa ya tashi, kamar wani mage, ko ɗan jariri, ai gara in daki ƙofa da ƙarfi irin yadda mama take yi wataran a gida, idan haka ne abun, meyass a gida ba a haka ake tashin su Yaya usy ba? Kai anty laila bata da kunya, zaman turai duk ya canza ta’.
Ta gama soki burutsunta, ta koma kitchen tayi wanke-wanke.
Daga nan ta tafi ɗakinta, yin wanka.
Sai dai ko da ta fito daga wankan, bisa mamakinta adam har ya tashi, dan ya ma biyota ɗakin.
“Wai daga zuwana nayi wanke -wanke har ka tashi?” Tayi maganar a ɗan tsorace tana rufe jikinta.
Maimakon ya amsa, kawai ya hau dariya, ta tsaya cak ta ce “Menene?”.
Purple ɗin brezia da ta bari a kan gado, ta shiga banɗaki, ya ɗaga mata ya ce “Meye wannan?”
Kame-kame ta fara tana son faɗar abun da zata kare kanta da shi.
Ya ce “Inyeee mutuniyar, ai kamata yayi a nuna mini, ni dama tun da nayu hugging ɗinki jiya, i feel it but i thought na scam you wanta scam me, ashe na gaske ne, come let me see inyeee”.
Shan kunu tayi ta ce “Papa bana so”
“Meye ba kya so kuma? Ganin kawai”
Ƙarasowa tayi zata karɓi breziar, amma ya riƙeta yana dariya, ta saka hannu ta riƙe towel ɗin ta gam, tana ihu.
“Ni wallahi da baka nan, nafi sakewa”
“Abun har da sharri, kamar ba jiya ki ka gama kuka ba, saboda kin ganni. Anyway, shirya ki zo mu yi breakfast, zamu yi magana”
Sai da ya bar ɗakin sannan hankalinta ya kwanta, ta shirya, ta fito tana wani haɗe rai.
Shi kuma ya ƙureta da ido, har ta zauna.
Taƙi kula shi, tayi serving ɗin sa, ta ja nata ta fara ci, duk yadda ya so ya maze kasawa yayi, dan yana jin daɗin tsokanar rumaisa yaga ta haɗe rai.
“Papa dan Allah ka daina kallona kana dariya, Allah zan tashi”.
“Allah da iko yake, abun ne da mamaki, six months back, a ƙwailarki na tafi na barki, amma in just six months ace lamari ya kankama haka, kuma kin ƙi yarda na tabattar kar in je acuci ake yi mini.
Abunki ras da ke, ai ni yanzu kuma na daina takara da ke, na yarda yafi nawa nesa ba kusa ba, wane ni ma? Ai ni yanzu babu suaran jayayya, zaki iya rainon baby yanzu sosai, kai congratulations mimi, kamata yayi fa mu yi party, tare da celebration, mimi is no more ƙwaila, she’s now a big girl, she can bear a baby, she even wore brezia size nawa ne ma ki ke sakawa, mu je mu sayo dozens of it” ƙarshen ƙuluwa rumaisa ta ƙule, ta jefa masa guntun ƙashin da yake hannunta, ta tashi za ta tafi. Ba dan ya iya shanye dariyarsa ba, ya riƙe ta yana cigaba da ƙyaƙyatawa.
Duk da tsiyatakun da yake tayi mata, ta kasa fushi da zuciya, watannin nan da yayi, ba ƙaramin missing ɗin sa tayi ba, amma dawowarsa ya sakata a gaba da tsokana kamar tayi kuka.
Ta tafi kitchen yin wanke-wanke ya bita, ba abun da yake tayata, ya sakata a gaba da tsokana.
Ruma ta kalleshi, kamar ba shi ne idan ya kamile ya tsuke fuska, ko fara’ar kirki ba ya yi ba, yayi ta muzurai, mussman idan yana cikin shigarsa ta sarauta, amma yadda ya sakata a gaba sai ka ce yaya usy saboda tsokana.
Ya ƙaraci dariyarsa ya koma falo, ya cigaba da kallo, lokacin sallar azahar yayi, ya tashi ya fita masallaci.
Sai dai da ya dawo, har ta kammala girki, ta yi salla ta canza kaya, amma ta kima uban hijjabi, tana so ta ganshi sosai, amma tsiyar da yake mata duk ya takurata.
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “Budurwar, meye haka kuma?”.
“A ina?”.
“Meye na wani saka hijjabi ana zaune ƙalau, wannan abu na farinciki da ya same mu, gaskiya ban yadda ba”.
“Allah papa zan tafi ɗaki na daina fitowa”
Ya ce “Sorry, ke kin san yadda na yi kewarku kuwa, tsokanar da na daɗe ban yi miki ba nake fanshewa. Ya ƙarasa wurinta ya cire hijjabin, tana riƙewa amma ya cire shi.
Kasancewar ba a dining za su ci ba, suka zauna a ƙasan carfet.
Ta janyo kwanukan abinci, da plate biyu, ya ce mata “an daina raba plate, a ɗaya zamu ci” ta tuna anty laila ta ce mata cin abinci kwano ɗaya da miji, yana ƙara soyayya, amma ita ba wannan ya dameta ba, sai tambayarta da tayi, to ba zai yi mini kishiya ba, laila ta ce sai kin kula da abubuwan da na koya miki tukuna.
Ta zuba abinci ta ajiye masa spoon, ya kalleta ya ce “Ke ni fa tun farko a baki ake bani abinci, ba zaki ajiye mini cokali ki maza ba”.
“Ni zan baka abinci a bakin?”.
“Eh mana”
Ta ce “Taɓ papa, ko jajjage baka yi mini ba da ina girki, ko sannu sai ma tsokanata da ka yi tayi, na gama abincin kuma sai na baka a baki, in bawa sabir abinci a baki, in bawa babansa saboda jin daɗi”.
Yayi dariya ya ce “To ki bari in baki, ai ni a wurina da ke da sabir, duk ɗaya, baku da wani banbanci dan abun da yake na shiririta kema yi ki ke” kan tayi magana ya ɗorata a cinyarsa, ya ɗebo abinci a cokali ya kai bakinta.
Rufe fuska tayi ta ce “Ayi haka? Kunya nake ji fa”
Sauke hannunta yayi, ya tura mata cokalin a baki, tun tana noƙewa ta saki jiki tana karɓa, ta ce “Da na san haka bawa mutum abinci yake a baki da daɗi, ai da na daina ci da kaina, idan na dafa sai ka bani a baki”.
“Ni zaki saka aiki, yanzu ki ka gama cewa saboda jin daɗi zaki bani abinci a baki, amma yanzu kina gaya mini, in din ga baki abinci a baki. Mara kunya kawai baby mimi an zama lady mimi”
“Wallahi idan ka ce babyn nan kunya ka ke bani, ga abinci a baki ga baby, idan aka ga na koma yin rarrafe kai ne ka ja”
Dariya Adam yake yi, rumaisa ba za ta taɓa girma tayi hankali ba.
“Mimi, kin shiga kin fita kin hana auren jabir da iman, ki ka haɗa da yayanki, kin saka jabir gaba da ni, Jamil ma har na je na dawo bai yi mini magana ba, gaba ɗaya fushi suke yi da ni, duk saboda ke mimi”
“A’a nifa ban hana aurensu ba, kuma can suka ƙulla soyayyar su da mai sunan baba, ban sani ba ina gefe ni ƙarfafawa kawai nayi. Kuma papa kawai fa ban gaya maka bane ba, kar na zama munafuka kai baka san me jabir yayi wa ammi ba, wai saboda ba yi auren sa da iman ba, ka ja maganganun da ya din ga gaya mata? Wallahi sai da Mahmoud ya mare shi”.
“Wane Mahmud ɗin?”
“Daddy” ta bashi amsa. Yayi shiru yana mamaki, ya san rumaisa ba za ta yi masa ƙarya ba, yanzu har jabir zai iya kallon ammi ya ci mutuncin ta, matar da duk da abubuwan da mahaifiyar sa take yi mata, bai hana ta ɗauke shi tamkar ɗa ba.
“Papa ni fa wasu lokutan ba haka kawai nake tsanar mutum ba, da jabir sonka yake tsakani da Allah, kome ammi za ta yi masa, ba zai wulaƙanta ta ba. Shi kuma jamil sake bina yayi, wai sai na gaya masa yadda aka yi anty aisha ta ɓata, da kuma in gaya masa abun da na sani a kan ta, na ce masa ban san komai ba, sai filin da gwamanti ta karɓa a hannun turaki, ake bashi percentage ya sanya anty aisha a matsayin magajiyarsa, shi ne hankalinsa ya kuma tashi, ya ce kaine ka gaya mini”
Adam ya saka hannu ya juyo da fuskar rumaisa tana fuskantar sa, ya ce “Rumaisa, meyasa ba zaki daina yi mini yawo da hankali ba? Yanzu magana ake ta shekara guda da watanni, da ɓatan aisha, ba zaki tausaya mini haka ba, ki daina yi mini ɓoye-ɓoye? Kin bani zane ya ɗaga mini hankali, kuma ban gane komai a ciki ba Please rumaisa” Yayi maganar jikinsa a sanyaye.
“Papa ba laifina bane, laifinka ne haryanzu, ka wuce duk wasu matakai da yakamata, kuma ina iya ƙoƙarina na tallafa maka, ɗaya ya rage haryanzu, nima ba son raina bane in ta wahalar da mijina ba, baban ɗa na”
“Wani mataki ne mimi?”.
“Sauran ma ka tsallake su, ba tare da ka sani ba, wannan ma dan kan ka nake son ka yi surrender ka tsallake shi. Kullum ina yi maka Addu’a, duk wanda na yi wa abu yaji daɗi, sai in ce ya saka ka a addu’a, komai zai zo ƙarshe fa”
Jiki a sanyaye ya ce “Shikenan mimi, Allah ya yi mana jagora”
Ta ɗebo abincin ta kai bakinsa, amma ya girgiza kai ya ce “I loss my appetite, na ƙoshi”.
“Dan Allah ka ci papa, zan yi kuka, kar ka saka na karaya na rigaka miƙa wuya, ba haka muka yi da anty aisha ba”
Cikin mamaki ya ce “You mean you set a deal with her a kaina?” Ta jinjina masa kai alamar eh.
“What was it?”.
“This is not the right time to voice it out, i have to finish it first, but am sorry papa”
Idonsa fal hawaye ya ce “Shikenan miki, baki yi mini laifi ba”
Tuni hawaye ya gangaro mata, ta shafa fuskarsa ta ce “Dan Allah papa kar ka yi kuka”.
“No mimi allow me, it really hurts me, ina jami’in tsaro na kasa bawa iyalina kulawa, har ta rasa ranta mutuwar wulaƙanci, ta haihu a dokar daji, what a mess”.
Ruma da tuni ta fara sheshsheƙa ta ce “Daga baya na gane is not your fault, ka daina dan Allah”.
Ya kwantar da rumaisa a ƙirjinsa, yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma hakan ya bashi damar, zubar da nasa hawayen silently.
A hankali ya ce “Ashe turanci ya fara zama Inyeee”.
Ya zira hannu ya kamo hannun brziar ya ce “ina zamu je celebration ne? A buga cards, da congratulations on your newly developed… Bai ƙarasa ba ta gantsara masa cizo a hannunsa ta tashi.
Dariya yayi, atleast ta rage damuwar da ta shiga yanzu.
***
Yasir kuwa kai da fata ya dage, ya ɗauki lambar iman a wayar mama, kasancewar mama ta kira iman da kanta, tana mata ƙorafin, ta daina zuwa gidan gaba ɗaya, wanda ba iman ba ƙaramar kunya ta ji ba.
Yayi amfani da damar, ya ɗauki lambar, ya yi wa iman magana ta what’s app, bayan sun gaisa yayi mata bayanin shi ne, ya tura mata akwatuna ya ce ta zaɓi wadda take so.
Iman ta ce “Yasir duk abun da yaya umar ya bani ina so, ba zan zaɓi komai ba dan Allah ku ce masa kar ya wahalar da kansa yayi mini iya abun da Allah ya hore masa”.
Yasir ya ce “Amma dai bani ni ne zan gaya masa hakan ba ko? Ai wannan aikin sai ke ko hajiya mama, ni a suwa, dan Allah ki zaɓa amma kar ki gaya masa”
Iman ba ƙaramin burgeta suke yi ba, suna matuƙar son junansu, fiye da tunani.
Ƙin zaɓa tayi, ta ce kowacce aka yi ta gode.
Da yamma mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ana ta cigaba da gini, yana tara kayan lefe, kowa ya fita ya dawo, sai ya kawo wani abun na kayan lefe, kuma ƴan uwa basu gaza ba, da cigaba da kawowa mama gudunmuwa.
Turus yayi ganin wasu kyawawan akwatuna, guda shida da kid, haɗaɗɗu masu kyau.
Mai sunan baba bai tanka ba, sai da mama ta ce “Babana, mutuminka fa ya cika alƙawari ga akwatunanka nan”.
“Meyasa Yasir ba ya jin magana ne? B jari yake tarawa ba, dan me zai kwashe kuɗinsa ya yi wannan hidimar, sonake na ga me zan samu a cika masa, amma ya kwashe kuɗinsa yayi wannan aiki, sai kuma da nace masa ya bari, yanzu kan ya mayar da kuɗin fa”
Yasir da yake tsakar gida, bai ji daɗin abun da mai sunan baba yayi ba, sai dai ko menene shi ya san yaya umar ha cancanci fiye da haka.
Mama ta yi ta yi wa mai sunan baba faɗa a kan bai kyauta ba.
Ko da ya fita tsakar gida, ya kalli fuskar yasir, fuskarsa ta nuna bai ji daɗin abun da mai sunan baba ya yi masa ba.
Har dare Yasir sabgoginsa kawai yake yi, ko ɗan shishshigin nan da suke yi wa mai sunan baba, yau bai yi masa ba.
Sai dai da ya shiga ya fita, sai mama tayi ta saka masa albarka tana kwarara masa addu’a.
Har ƙarfe goma na dare, yasir bai shiga gida ba, mai sunan baba ya ɗau babur ya biya shagon yasir, ya tarar da shi yana ta aikin wayoyin mutane da system, shi da yaransa.
Horn ɗin da mai sunan baba yayi ne ya dawo da shi hayyacinsa, ya ajiye wayar hannunsa ya fito.
Mai sunan baba ya bashi galan ɗin man fetur, ya ce “Gashi nan ka zuba a injinka” Yasir ya karɓa ya ce “To na gode sosai”
“Ka rufe shagon nan mu tafi gida, dare yayi goma tayi”
Ya amsa masa da “To, bari na sallami yaran” ya wuce cikin shagon ya sallame su.
Shagon da Yasir yake harkar wayoyinsa da system, har ma da POs mai sunan baba ne ya kama masa shagon, ya saya masa system. Ya ce hauzaifa kuma ya iya ɗinki, shegiyar shirirtar sa ta hana mai sunan baba bashi jari.
Yasir ya rufe shagon, ya hau babur suka tafi gida, a ƙofar gida mai sunan baba ya ce “Yasir”.
“Na’am”
“Ban yi maka faɗa a kan abun da kayi mini dan na ɓata maka rai ba? Kaga jari kake tarawa, bai kamata ace na mayar da kai baya ba”.
“To waye ya bani jarin?”.
“Duk da haka bai kamata dan na baka na dawo na cinye ba, anyway ka daina fushin na gode sosai Allah ya ƙara buɗi, ya sanya ku fi haka, ya sanya maka albarka a nemanka” yayi maganar yana musabaha da hannun yasir.
Yasir yayi murmushi ya ce “Muke da godiya mai sunan baba”
“Nima yakamata na gode, na san ka kashe kuɗi sosai, Allah ya mayar maka da ninkin abun da ka kashe”
Ya amsa da “Amin Yaya”
Suka shiga gida tare.
***
Kwanan Adam huɗu da dawowa, rumaisa ta tarar da shi a ɗakinsa, da travelling bag.
“Ya haka, me nake gani, wannan jakar fa? Ga breakfast can”.
Ya ce “Kin tashi kenan?”
“Eh mana ina zaka?”
“Nemana ake a abuja, zan je na yi booking Flight”
“Daga dawowar taka za ka kuma tafiya?”
Takawa ya ce “Kiran gaggawa ne, suna buƙata ta, ba zan fi sati ɗaya ba”
Haushi ne ya kama rumaisa, kawai ta fice daga ɗakin, ta koma nata.
Bin bayanta yayi yana kiran sunanta, ya tarar da ita a falo, ta cika tayi fam.
Ya zauna kusa da ita ya ce “Wai mimi meyasa ki ke da matsala ne, harkar aiki ne, idan ban je ba ya zan din ga samo mana kuɗi, na biya miki kuɗin makaranta, na saya mana abubuwa”
“To daga dawowarka sai ka kuma tafiya, kullum baka nan ai shikenan”
“To yanzu ya ki ke so ayi?”
“Kawai ka fasa”
“Mimi zuwana yana da muhimmanci, ga kuma karatuna na kammala, akwai aikace-aikace a gabana sosai da sosai, kiyi haƙuri 5days kawai in sha Allah zan dawo”.
“Ni sai dai ka tafi da ni, idan ba haka ba zan yadda ba”.
“To shikenan, zan saka ayi mana booking Flight shikenan”
Ta waro ido ta ce “Dan Allah jirgi zan hau?”
“Ƴar ƙauye zata hau jirgi”
Ruma har da tsalle ta ce “Wayyo daɗi, bani waya na kira yaya usy, na gaya masa zan riga shi hawa jirgi”.
Yayi murmushi ya ce “Sai mun sauka tukuna, Ki ɗaukko mana akwatinki guda ɗaya, ki haɗa mana kayanmu”
Tashi tayi da sauri ta tafi tana murna yau zata hau jirgin sama.
Ta waya ta sanar da mama zata raka takawa abuja, amma ba zasu fi kwana biyar ba zasu dawo.
Aliyu ya ce “Yarinyar nan tana sararawa, taɓararta kawai take yi son ranta”.
Rumaisa bakinta yaƙi rufuwa, da ta ganta a cikin jirgi, ta ce “Papa, yanzu idan nayi tsalle a jirgin nan, ya zai yi ƙasa zai yi”.
“A’a sai dai idan yanzu zaki gwada tsallen”.
Ta ce “Haba dai su rainani”
“Gaskiya dai, babbar yarinya kamar wannan mai abun arziki ai sai a rainaki”
“Zaka fara ko?”
Ya ce “Ban fara ba tukuna”.
Ko da suka sauka taxi suka hau, suka nufi hotel ɗin da zasu sauka.
“Papa, to ina gidan shugaban ƙasa yake a nan?”
“Me zaki yi wa shugaban ƙasar?”
Rumaisa ta gyara zamanta ta ce “Zan ce masa dan Allah ya saka a daina sace mutane, wallahi wahala ake sha sosai”
Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba.
Hotel ɗin yayi wa rumaisa kyau, sai dai nanata masa take yi, ko sun koma gida kar su gayawa kowa hotel suka zo a abuja, kar ayi musu kallon mutanen kawai.
Da suka shiga bedroom ta ga ɗaki ɗaya tal, da toilet.
Ta ce “To ina banɗaki, da kuma kitchen da nawa ɗakin?”
“Babu kitchen, a nan zamu din ga kwana tare”
“Kai, ni da kai a ɗaki ɗaya, kuma ba kitchen to me zamu din ga ci?”.
“Saya zamu din ga yi”
“To waye zai din ga kwana a kan gadon?”
“Ke dai kin san ba zan biya kuɗin ɗaki in kwana a ƙasa ba ko? Sai ki nemawa kanki mafita”
Ya ajiye akwatin, ya nemi wuri ya zauna, ya ɗauki wayarsa yana kiraye-kirayen wayarsa, ya ce a kawo masa mota.
Da daddare ya ɗauki ruma suka fita yawo, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ruma ba, duk da dare ne fitar tayi mata daɗi sosai.
Ta ɗauki wayarsa ta kira Huzaifa, tana ta bashi labarin yadda jirgi yake, da abubuwan da ya sai mata.
Usman ya karɓi wayar ya ce “Ke wayar nan a handsfree take?”
Ta ce “A’a”
“To ki ba ya fita dake yawo ba, har kin hau jirgi kina yashe baki, ga uwar tsaraba da ya yi miki da ya dawo, idan. Ki ka kuma kawo mini ƙarar kin yi masa wani shirmen, wallahi kina zaune zai auri wata ya din ga wannan yawon da ita, gara a din ga gaya miki gaskiya”.
Shiru tayi daga baya ta ce sai anjima, ta kashe wayar tana tura baki.
Takawa bai san me suke cewa ba, kuma bai damu da ya tambaya ba.
Suka koma masaukinsu, sai nanatawa take ita fa tunda ta baro gida, ta saba da kwanan kan gado, dan haka ba zata kwana gado ɗaya da shi ba, kuma ba zata kwana a ƙasa ba.
Yayi mata shiru, ya ɗaukko system yana daddanawa.
Ta shiga banɗaki ta fito, ta zauna a gefen gadon tana kallo abun da yake rubutawa a system ɗin.
Ya tashi ya shiga banɗaki, hakan ya bata damar tashi ta buɗe akwati, ta fara canza kaya.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.