Kanwar Maza Page 67 Complete Novel By Ayshercool
Page 67
Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ƙuduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita kuma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai.
Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taɓa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki.
Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu.
Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ƙarami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba.
Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karɓar mata ɗan ta, amma ya ce ta yi haƙuri, da ita da Jamila duk ɗaya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taɓa haihuwa ba.
Rashin ɗan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ƙarshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame.
Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta.
Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu’a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.
Laila ce ke satar jiki, ta ɗaukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta shaƙu da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan ɗaukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.
A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ƴar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar ɗan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.
Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin ɗan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.
Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.
Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.
Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da feleƙe, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata haƙuri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.
Ammi ba ta taɓa tanka masa ba, dan a lokacin ta miƙa wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da riƙon abun ta, gefe tana zuwa makaranta.
Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka za a tsallake ƴaƴan bintu na ta su yi sarauta.
Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ƙunci tana baƙin ciki, kwanan ƴar uku ita ma ta mutu.
Nan ta din ga yaɗa cewar, Bintu ce take bawa bokaye ƴaƴanta su cinye, shi ne wannan karon ta haɗa da tata ƴar, tun da dama ƴar gidan malaman tsubbu ce.
Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ƙaunar ɗan sa takawa ba, sannan ya na ɗaukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai ɗau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata ɗan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba.
Iyayen ammi suka yi ta bata haƙuri, da nuna mata dama aure, sai an yi haƙuri ibada ne, ta yi haƙuri da ɗan nan Allah ya bata wani.
A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karɓi abun sa, al’umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naɗa sarki a ‘yaƴan sa, sai aka naɗa ƙanin sa.
Hakan ba ƙaramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taɓu.
Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naɗa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban ɗaki kan ta rasu, shi yana ɗan ƙarami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar ɗan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban ɗaki da marigayi, dan haka shi duk ɗaya ne a wurinsa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ƴa macen, bayan sun gana ɓata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba.
Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba.
Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huɗu da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su ɗaya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haɗu kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka.
Baba Uwani ta yi ta bata haƙuri, ta ɗauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faɗa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuɗi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ƙoƙarin ta wurin kyautatawa baba uwani.
Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ƙanwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiɗen da yake yana cewa “Maraba da kai babana, abun ƙaunata kuma magajina, galadima ɗan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai”
Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam ɗin dariya, wani dunƙulallen baƙin ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran ɗan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu.
Tun daga nan ta fara turawa Mahmud aƙidar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba.
Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.’, za su koma mahaifarsu.
Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta shaƙu da Ade da ƴan rigar, kamar danginta.
Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still ƴa ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so.
A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban ɗaki ta wancan lokacin da ta riƙe shi, ita ma ba ita ta haife shi ba.
A wannan karon, shi ma Sharif ƙarara yake nuna son Adam, saboda soyayyar da yake yi wa mahaifinsa, da yadda mahaifin nasa, ya nuna masa ƙauna.
Jamila kuma ta yi alwashin rusa soyayyar nan, da cigaba da baƙantawa giwa, domin rama abun da ta yi mata, na fara auren Galadima.
Duk yadda ta so raba Mahmud da Adam, ba ta yi nasara yadda take so ba, duk da Mahmud ya fara yadda da abun da take gaya masa, sai dai duk yadda take korar Adam idan ya zo wurin Mahmud ya kasa zuciya.
Tuni Mutanen masarautar, wasu sun fara ɗauka, tare da kiran Adam magajin galadima, har da masu ce masa galadima ƙarami, ko kuma magajin takawa, idan ƴan kan zagi suka yi masa wannan washin, haka galadima zai ta yi musu kyauta.
Hajiya Lubabatu ta samo musu wani hatsabibin boka, malam na kan dutse, suka je wurin sa a kan suna son a nakasta Adam, yadda ba zai moru ba, kuma a saka gaba da ƙiyayya tsakaninsa da Mahmud, yadda wuta da ruwa ba zasu jitu ba, haka suma sannan a saka wa galadima tsanar Adam.
Bokan ya ce “Sai an kai masa Adam, saboda ya san aikin da zai yi a kan sa, sannan a taho masa da jinin Mahmud a sirinji.
Ta koma gida, ta saka galadima a gaba, wai tana son ta je garinsu, za ta tafi da Adam, galadima ya ce bai yarda ba, ta haɗa baki da malaman makarantarsu Adam, ta je ta ɗauke shi a makaranta, aka shaƙa masa wani abu ya suma, suka tafi da shi wurin boka, tare da jinin Mahmud.
Bokan ya zuƙi jinin Adam, ya haɗa da na Mahmud, ya zuba wani abu a ciki, jinin ya rabu biyu ɗaya ya yi baƙi, ɗaya ya yi ja, ya mayar da jinin jikin Adam, ya bata sauran jinin, ya ce ta yi girki da shi, ta bawa Mahmud da galadima su ci, ya raba su.
Ta ce ai ba iya nan take so ba, so take a haɗa shi da ciwon, da zai nakasa, nakasa ta har abada, da ba zai yi sarauta ba.
Nan ya yi wani ƙulumboto, ya saka wani abu, ya huda wuyansa, ya zuƙi jinin Adam, ta wuya, ya zuba a wani abu, ya ce “Ramin da na yi a wuyansa, ta nan aljanar za ta din ga shan jininsa duk shekara, sai dai babu wanda zai iya hudat, Sannan zan yi wani abu da sauran jininsa, duk shekara za a din ga samun mahaukacin doki, ayi masa, zan haɗa laya da sunansa, wadda za a kai maƙerar da ta shekara goma, a binne, sannan zan saka wannan aljanar, ta zuba masa jinin mahaukaciyar kura a jikinsa, an nakasta shi, nakasa ta fili da zahiri, iya rayuwarsa wannan aljana za ta cigaba da kula da komai, tun da an bata jininsa, sai dai loka-lokaci, za ta din ga buƙatar wani abun” ya wassafa musu abun da za su bayar, suka bayar sannan suka tafi gida.
Ammi ta kaiwa Adam, yana bacci, wai biyo ta yi ta hanyar makarantar su, ta ga an tashi shi ne ta ɗaukko shi yayi bacci a mota.
Ammi ba ta kawo komai ba, ta karɓe shi, ta yi mata godiya, sai dai tun ammi ta na saka ran adam ya tashi, har tsoro ya kamata. Sai dai bayan ya tashi ba baki, sai dai kallo.
Hankalin Ammi ya tashi, ta gaya wa galadima, hankalinsa ya tashi suka tafi asibiti aka ce lafiyarsa ƙalau, ya ce idan zuwa washegari, bai yi magana ba, za a kai shi babban Asibiti, ko ƙasar waje ne a akai shi, sai da daga haka washegarin, tunanin galadima ya sauya, ya ce wai ta ƙyaleshi shakiyanci ne.
Abu kamar wasa, sai da Adam ya yi wata tara, ba magana, ga wani irin bacci, mara kan gado, ammi ta dage addu’a, ta kai shi gidansu wurin mahaifinta aka dage da roƙon Allah, sannan ya dawo yake magana.
Gaba ɗaya galadima ko a jikinsa, ya daina nan-nan da shi, sai dai abun ka da ɗa da uba, soyayyar ba ta dishe duka ba, wataran idan ya gan shi ya na jin daɗi.
A lokacin Mummy ta haifi Fauziyya, mutane ana ta shigowa, Ammi da laila da adam, sun je ganin jaririya, Adam na ganin Mahmud, ya nufi wurin sa yana kiran sunansa.
Sai dai Mahmud ya hankaɗe Adam, sai da ya faɗi ƙasa, ai yana tasowa, sai idanunsa suka koma kamar na mahaukaciyar kura, yana wani irin gurnani, ya shaƙe Mahmud.
Ammi hankalinta ya tashi, duk wanda ya je raba su, sai Adam ya cije shi, kowa ya yaƙushe shi, sai jini ya fita.
Da ƙyar Ammi ta riƙe shi ta na yi masa addu’a, ta ja shi ta tafi da shi sashinta, tana kuka ita da laila, tana tunanin menene ya samu adam?.
Sai dai haka ya wuni yana wannan gurnanin, kamar kare.
Mummy kuwa bala’i ta din ga yi, wai za a kashe mata ɗa, dama adam ɗin maye ne, ya tsotsa a wurin uwarsa, ko kuma a garin yawon bin bokaye, ɗan ta ya haukace.
Magana ta din ga yawo a fada, galadima ya je har sashin Ammi, ya din ga yi mata faɗa, wai ita ta sangarta Adam, har yake yinƙurin kashe ɗan uwansa.
Halin da ya tarar da Adam ɗin sam bai dame shi ba.
Tun daga nan, idan faɗa ya haɗa Adam da yara, sai ya burkice, ya na gurnani, da cizo, idan kuma yayi cizo sai jini ya fita, wanda wannan jinin aljanar take sha.
Wani lokacin idan ana ziga wutar maƙerar nan, haka yake jin ta a cikin jikinsa, yayi ta ihu ya na fuzgar fatarsa, ko kuma idan mahaukacin dokin nan, yana dara, sai ya ji tamkar ƙashin sa ake takawa.
Idan kuwa shakara ta yi, lokacin shan jinin nan ya yi, ya din ga suma kenan, har ammi ta fitar da rai da shi.
Mummy ta din ga tsorata Mahmud a kan Adam, da sai da ta kawo, ba mai kallon wani, juya masa bayan da mahaifinsu ya yi, ba ƙaramin tsaye masa ya yi ba a ransa.
Sai dai ya je ya saka Ammi a gaba, ya yi ta kuka, abun da ake yi musu da tare shi da Mahmud, yanzu sai dai ayi wa Mahmud shikaɗai, hakan ya sanya ya ƙara tsanar Mahmud!.
Roƙon Allah da neman magani, da Ammi ta dage a kai ne, ya sanya ya samu sassauci har ya koma makaranta.
Lokacin da za su shiga jss1, Mummy ta saka aka kai Mahmud boarding, aka raba shi da gidan baki ɗaya, dan yanzu galadima baya iya ƙetare maganarta.
A hankali aka ɗan fara sakin jiki da Adam, cousins ɗin sa suke wasa da shi, kasancewar makarantar su ma ɗaya.
A gidan su jamil, gidan turaki wanda yake wa ga sharif, akwai ƴar sa ɗaya da ya ɗorawa so shi ma, bayan mahaifiyarta ta rasu, mai suna Aisha yake kiranta da fulani, sai dai a bayan idonsa, babar su jamil, ta tsani yarinyar, kamar ba ƴar sarauta ba, saboda azabtarwa daga yayyenta, da kuma uwar riƙonta.
Tun ana yi a bayan idonsa, aka dawo yi a gaban idonsa, ba ya iya cewa komai, wasu lokutan ranar juma’a sai Ammi ta aika a ɗauko mata Aisha, a kai mata ita, ta yi mata kitso, ta saka ayi mata lalle, tana son ƴa mace, laila kuma ta riga ta balaga.
Ana haka Ammi ta haifi nusaiba, ta din ga murna, ta samu ƴa mace, da wata salla suka je gombe, a nan yayan Ammi yake ce mata, ya wuce ta rigar su ade, ya ga kamar da mutane.
Nan da nan Ammi ta ɗau hanya ta tafi, sai dai ta je ta tarar da wata kyakywar bafulatanar yarinya, da ciki.
Suka gaisa da Ammi, take tambayarta, ina su Ade.
Yarinyar ta ce “Ade kakata ce, sun yi gaba, ni daga yaye aka bar ni a wurin yayan babana, to sun tashi zasu tafi can iyaka, in da tushenmu yake, ni dai ban san sunan wurin ba, to mu ma can zamu tafi, da ni da yayan babana ne, da matarsa sai maigidana, sauran ayarin da muka taso tare sun yi gaba, ni kuma na yi nauyi, shi ne aka ce mu zauna in haihu, sai mu tafi, yayan babana ya san in da suke, ina son in ga Ade, kakata”.
Ammi ta ce “Allah sarki, Ade kam tana bani labarinki, ta ce mamanki ma tana wata riga tana aure ko?”
Yarinyar ta jinjina mata kai.
“To ina mijin naki da matar yayan baban naki?”.
Ta ce “Sun tafi kiwo, ita kuma ta je yin itace”.
Ammi ta din ga murna ta ga jikar Ade, kasancewar za su yi kwanaki a can, ya sanya kusan kullum sai ta je, har suka saba da matar yayan baban ade.
Ammi ta sha mamaki, irin yawon da fulanin nan suke da shi, sun yi sanani sun hayayyafa, sun shafe shekaru a wurin, kuma su tashi su yi wani wurin kamar wasu iskokai.
Mijin yarinyar ma, mairamu yana matuƙar girmama Ammi, su yi ta ɗaukar nusaiba suna yi mata wasa.
Ammi kar ta tafi ta bar gida, dan ƙarfin zaman na ta ma, ayi wa Adam Addu’a ne, da nema masa magani.
Bayan Ammi ta koma Kano, tana yawan yin waya, a kan aje a gano mata jikar Ade.
Sai dai aka kira Ammi, daga garin su, aka gaya mata, an kashe mijin mairamu, an kore dabbobinsu, kuma an rasa yayan babanta da matarsa.
Kasancewar ammi ba laifi, tana faɗa aji, ta saka aka kai report wurin ƴan sanda, amma ba wani labari, Mairamu ta tayar da hankalinta, a gidan su Ammi aka yi wa mijinta sutura, aka rufe shi.
Ita ba ta san kowa ba, sai mijinta da yayan babanta, in da suka baro, duka suka taso, ayari sun yi gaba sun bar su, dan su har a lokacin ba ruwansu da abun hawa, kuma ba ta san in da za aje ba, dan ta na da ƙuruciya sosai abun da ta riƙe a in da za su je kawai shi ne kan iyaka, nan ne tushensu.
Saboda tsabar damuwa, ta fara naƙudar dole, aka kwasa aka kaita asibiti, ta haifi yarinaya kyakkyawar gaske, jawur da ita.
Ammi ce ta yi mata role ɗin uwa da na uba, dan ba zata manta karamcin Ade ba.
Ta tambayeta sunan da za a sakawa ƴar amma ta ce ta saka mata duk sunan da take so.
Ammi ta ce “Ta saka mata Khadijah, sunan mahaifiyar ta, kuma ƴar ta da ta taɓa rasuwa, amma take ce mata Iman”.
Ta din ga rarrashin mairamu, tana bata tabbacin, za ta yi ƙoƙari a nemo in da ƴan uwanta suke, kuma a lokacin waya sai gidan manya, balle a sameta hannun bafulatanin daji.
Haka Ammi ta din ga sintiri tsakanin kano da gombe, mahaifiyar laila da ammi ta riƙe, ta cigaba da ɗawainiya da Mairamu, dan a lokacin suma iyayen duk babu.
Sai dai har watanni uku, babu labari a kan in da ƴan uwan mairamu suke, ga ƙuriciya kuma ta yi ta fama da rashin lafiya, ƙarshe Allah ya yi mata rasuwa.
Ammi ta yi kuka sosai da sosai, ta ce sai yayarta ta bata Iman, ya ce ba zata ba, sai ta nemo iznin mijinta.
Ammi ta yi wa galadima bayani, ya ji rauswar yarinyar, kuma ya san ɗawainiyar da Ammin ke ta yi, dan haka ya ce ta ɗaukko ƴar, dan ya san soyayyar da ke tsakanin Ammi da Ade.
Ta zube har ƙasa ta din ga yi masa godiya.
Ta je ta ɗaukko Iman, a lokacin kuma ta riga ta yaye Nusaiba, ya ce ko magani za ta yi, da ruwan nono zai dawo ta shayar da iman, yayarta ta ce kar ta shayar da ita, ta na da ƴaƴa maza, ba ta san me gobe za ta yi ba.
Haka ta haƙura, ta ɗaukko iman, ta zo tana bata madara.
Kowa ya ga Iman sai ya tankata, saboda tsananin kyan da take da shi, gaya jaririya, amma gashinta irin na larabawa, mai tsawo.
Nan ma mummy ta samu na yi, wai Ammi saboda jaraba, an yarda ƴar shege ta ɗaukko wai tana so, kamar ƴar jari bolan ƴaƴa, ɗan kowa ma sai ta ɗaukko ta ce za ta riƙe, da ganin kyan wannan yarinyar, an san shegiya ce.
Aikuwa aka yadda, wasu lokutan ammi har mamaki take, yadda sirrikanta ke fita.
Jamila ta hurawa galadima wuta, a kan lallai ya sa ammi ta mayar da ƴar nan, duk dan ta cusa wa Ammi baƙin ciki.
Ya kuwa je ya samu Ammi ya ce bai yarda da riƙon ƴar ba, sai da Ammi ta dangana da wurin sarki, da mai babban ɗaki a kan su saka baki.
Mai babban ɗaki ta ce “Dan Allah idan ma ƴar tsintuwar ce, ita ta na so, ƴar ta yi mata kyau Tubarkallah”.
Da ƙyar galadima ya amince, bayan mai martaba ya yi masa ta tas, a kan abubuwan da yake yi.
Iman ta fara girma, ga fari ga kyau, ga uban gashin nan, kullum tana tare da laila da su nusaiba, ga Aisha idan ta zo, amma muddin ta sake suka haɗu da Mahmud, Fauziyya ko ruƙayya, to tabbas sai ta yi kuka, saboda cin zali.
Sai dai duk da haka, ƴaƴan jamila na shiga wurin Ammi, kuma ba zaka ce ba nata bane ba, sai dai suna tsoron laila, dan suka yi mata rashin hankali ubansu take ci, duk da ana yi mata gorin ba gidan ubanta ba ne ba, ta kan ce musu, Jamila ma an riƙeta ba a gidan ubanta ba, dan ita har da Mummyn ma yi take yi, duk yadda Mummy ta so ta saka Galadima ya kori laila abu bai yiwu ba.
Adam kuwa yau fari, gobe tsumma, kusan kullum cikin rashin lafiya, idan ciwon nan ya tashi kuwa, haka zai ta burgima yana ihu, yana neman abun da zai riƙe ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta.
Sashin Ammi ya zama wurin faɗi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting ɗin sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin ɗan ta ya kashe musu ƴa ƴa, amma yaran sun riga sun shaƙu da ita.
Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faɗa, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata ɗa, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faɗan da yake yi masa.
Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai.
Adam ba ya jin daɗin hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro.
Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ƙaddarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ƙauna sama da su.
Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daɗin rayuwa da su, a haka ɗan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ƙasar.
Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taɓa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam ɗin.
Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taɓa ɗaga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaɗowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faɗan sunan sa ba.
A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ƙyae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haɗu da ciwon zuciya da ƙuruciyarta.
Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faɗi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ƙarshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba.
Ɗa da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ƙauna, a baya, Mahmud ma ya ɗimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar.
Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka ɗaga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima.
Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, ɗan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karɓe ɗan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaɗaitawa ƙawarta Lubabatu, ɗan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ƙiyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murɗaɗɗen hali na mahaifin su.
Adam yana girma ciwo yana ɗan raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida.
Ya shaƙu da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ƴar ƙaramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida.
Gefe guda, Samha ta ƙallafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam.
Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ƴan uwanta ke nunawa aisha ƙiyayya, ganinta suke kamar ba ƴar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce ‘yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya ɗaukkota, ko Ammi ta aika a ɗauko mata ita.
Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake muguwa kamar Mummy, saboda waɗan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da ɗaya ba, idan uwar ɗa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa riƙon ɗan sa, babu wanda zai bawa riƙon ɗan sa.
Tun Samha tana ɓoye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba.
Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ƙaninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ƙular da ita sosai da sosai.
Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta roƙe shi ya nemawa Adam auren Aisha.
Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin ɗan ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani.
Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ƙi ya mata ita gaba ɗaya.
Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ƙuduri aniyar ko da bala’i sai ta auri Adam.
Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.