Novel Document

Kazar Kwanci Complete Novel

Kazar Kwanci Complete Novel Document By Rufaida Umar

Description/Story:

Kazar Kwanci Complete Novel

Written By Rufaida Umar

 

Description Of Kazar Kwanci Complete Novel

 ” Mairamu! Mairamu!!”

 

Matar dake zaune saman kujera ƴar tsugunno dafe da kumatu yayinda ɗaya hannun ke riƙe da buta ta yi firgigit ta farka daga kogin tunanin da ta lula har ba ta san da wanzuwar mutum ba sai jin kiran da ta yi a can cikin kanta. Ta dube shi sai kuma ta yi saurin ajiye butar ta miƙe tana ɗan ɗingisa ƙafarta da ta yi tsami dalilin jimawar da ta yi a zaune ta miƙa hannu domin karɓar ledar da ya shigo da ita tana fadin.

 

“Sannu da zuwa Malam, yanzu ka ke tafe?”

 

Wanda ta kira da Malam cike da damuwa ya girgiza kai, madadin ya miƙa mata ledar sai ya riƙe ya soma magana a tausashe.

 

“Tun yaushe na shigo nake ta sallama ba ki amsamin ba, anya kuwa Mairamu rayuwa za ta tafi a haka? Ki rufamin asiri naji da damuwa ɗaya kar ki haifarmana da wata ki kwanta ciwo.”

 

Kanta a ƙasa ta share kwallar da ya zubo mata.

 

“Toh Malam. In sha Allahu zan kiyaye.”

 

Daga haka ta sa hannu ta karɓi ledar ta kai masa ɗaki sannan ta koma ta zubo ruwa a kwanon tasa ta ajiye mishi a saman ɗan teburin dake falonsa. Shi kuwa koda ya shigo falon kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya faɗa banɗaki, kafin ya fito ta koma tsakar gidan ta yi alwala don tuni an soma kiraye-kirayen sallar Magriba. Shi din ma yana fitowa daga dakin ya nufi hanyar fita zuwa masallaci sai ya dakata ta hanyar juyowa ya kalle ta.

 

“Ki kira Hafsatu ki ce maza ta sa a maido yaran nan gida.”

 

Ta dube shi tamkar za ta yi magana sai kuma ta hadiye ta amsa da toh. Koda ya fita sai da ta gabatar da sallah ta ɗan yi addu’o’inta da ta saba kafin ta dauki waya ta yiwa Hafsatu flashing. Ko mintuna uku ba su cika ba ta biyo bayan kiran. Sai da suka gaisa ta ce.

 

“Babanku yace ki sa a kawo yaran nan gida.”

 

Daga can Hafsatu ta amsa.

 

“Inna ba za’a bari zuwa gobe ba sai na kawo su da kaina? Yanayin Hajara fa har yanzu babu sauki sai ta wuni ba ci ba sha sai aikin kuka.”

 

Inna Mairamu ta numfasa, ta sani dole Hajara ta shiga damuwa tsantsa ta yadda zai wahala lokaci guda ace komai ya wuce a wajenta. Ace har sau hudu ana neman aurenka a fasa? Sati biyu kenan da yi amma har lokacin ba a bar gulma da kuma zunɗensu a unguwa ba. Wasu su ce asiri ne kishiyar uwarta (Inna Mairamu) ta yi mata shi ne dalilin da yasa hakan ke faruwa don ba ita ta haife ta ba. Yayinda wasu ke Allah wadai da masu halin munana zato ga Inna Mairamu da suka yiwa shaidar arziki.

 

“Hello, Inna kina jina?”

 

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.

 

“Ina jinki Hafsatu, hakanan za ta dawo gidan tunda Babanku ya yi umarnin. Zan dai roƙi alfamar ya bari zuwa goben ki taho da su.”

 

“Shikenan Inna, Allah ya nuna mana.”

 

Inna ta amsa da amin kafin su yi sallama, kaf yaran Malam a mata babu wata da ta ɗauke ta tamkar uwa irin Hafsatu. Ita ce babbar ɗiyarsa a mata idan ka cire manyan samarin yaransa su huɗu wadanda su ma a gidan ta tarar da su. Gaba daya yaran Malam su tara ne cif, biyu ne kaɗai yaranta. Hashimu, Sadik (wanda suke kira da Baba Habu), Mustafa, Zakari, Hafsatu, Safiyya da Hajara gaba ɗaya mahaifiyarsu ɗaya sannan mahaifiyarsu ta kasance yar uwar Malam, wannan yasa dangin Malam da dangin mahaifiyartasu a dunkule suke wuri guda, sai bayan rasuwarta ne Malam ya auri Inna Mairamu, dangin Malam kaɗan a cikinsu ne ke sonta, hakanan yaran Malam din, Hafsatu ce kusan tasu ta zo ɗaya sai ko Zakari ɗan baruwansa, amma sauran komai Inna Mairamu ta yi ba ta taɓa wanke kanta a wajensu.

Haka ta dinga hakurin zama har ta haifi yaranta biyu duka mata…

Kazar Kwanci Complete Novel txt

File Name   Kazar kwanci… Hausa Novel Doc.
Title Kazar Kwanci Complete Novel
Author    Rufaida Umar
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    30/10/2024
File Size    150KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦500
Phone No   09034973645
Download Kazar Kwanci Complete Novel By Rufaida Umar 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button