Uncategorized

Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Tankwa (Wato Miyar Attaruhu Da Albashi)

Kayan Haɗi :-


  • Shinkafa
  • Attaruhu
  • Albasa
  • Koren tattasai
  • Kwai
  • Plantain
  • Mangyada


Yadda ake hadawa :-

Da farko uwargida za ki ɗora ruwa a wuta idan ya tafasa sai ki zuba shinkafa, idan ta yi rabin dahuwa, sai ki sauke ki tace kimayar tukunya kisa ruwa kaɗan yadda zai turarata, amman fa karyayi yawa don ba ason shinkafar ta caɓe sai ki rage wuta.


Bayan nan Sai kuma ki ɗauko attaruhu ki wanke ki jajjaga, sai itama albasa ki yankata yankan tsaye ki wanketa ki barta a kwando ta tsane sannan ki ɗauko koren tattasai ki yankashi ki ajje agefe, saiki ɗauko plantain ki bare kiyanka shi, daga nan sai ki koma kan shinkafarki idanta turara saiki sauke kibarta a tukunyar tadan sha isaka kafin ki zuba a plaks, sai ki dauko kasko ko tukunya ki zuba mai kisoya plantain dinnan ki ajje agefe, sannan ki dauko tukunyar da zaki yi miyar ki aciki ki zuba mai idan yayi zafi saiki sa albasa idan tayi brown saiki zuba attaruhun dakika jajjaga da albasa da koren tattasan saiki juya, zaki iya sa farin maggi kaɗan idan kina so, ko kisa maggi mai star da sauran kalolin maggin da kikeso, kisa seasoning mai dadi saiki zuba citta da kanunfari kadan wanda dama already anaso  mace ta dake citta, kanunfari, masoro, gyadar yarabawa mai kamshi da tafurnuwa ta dake abinta ta zuba a roba idan zaki yi jar miya ko jallop sai kisa.

To bayan kin zuba  sai ki jujjuya sosai idan miyar ta soyu saiki rufe kirage wutar kibarshi zuwa minti daya. Kina buɗewa zakiga miyar takwanta kayan miyan sun haɗe jikinsu.

Daga nan sai ki dora ruwa ki dafa kwai, idan  ya huce sai  ki bareshi. Za ki zuba shinkafarki a plet saiki sa miyar agefe kizuba plantain dinma a gefe, sannan kisa kwanki a gefe shima kidanyi musu decoration maikyau shikenan girkinki ya kammala sai ci.

Back to top button