Fatalwar Delu Part 8
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 8
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
“Kamar ya dole ya mutum, laifin me yayi miki da zaki kasheshi?”. Bayan ta sake barkewa da dariya da fuskar nan tata da ta koma tamkar dodanniya ta ce, “Kaje ka tambayeshi shi yasan abinda ya aikata wanda bai cancanci yafiya ba”. Tunani nake a raina shi kuwa Bukar da shegen tsoron nan nashi ina ya ga kwarin gwiwar da zaiyiwa aljana irin wannan laifi, hala dai tayi kuskure ba shi take nufi ba. “Baiwar Allah fatalwa ko aljana na manta baki fadan sunanki ba, amma dai zan so ace kin yafe wa Bukar duk da bansan laifin da yayi miki ba”. Wata irin tsawa naji ta daka mun, wanda duk juriyata sai da nayi baya tamkar zan juya in sheka a guje, amma sai na dake, domin lalai ya kamata in san wani abu. “Wai kai wane kalar mutum ne? Kana son rayuwarka kuwa, baka da tsoro ne ko baka san muhimmancin rayuwa ba”.
Na ce, “Nasan muhimmancin rayuwa mana, kuma ina da tsoro amma ba can-can ba, a kullum ina tunawa babu abinda wata halitta ta isa tayi mun wanda Allah bai nufa ba, shiyasa nake dai-daita tsorona a zuciyata. Amma tabbas ina da tsoro”. Dake dariya baya da wuya a wajen wannan yarinya sai ji nayi ta sake bushewa da wata dariyar kana daga bisani ta tsuke baki hade da cewa, “Yanzu ma naji ka sake burgeni saboda baka da tsoro kuma ka iya furta magana mai dadi, wasu idan suka ganmu sumewa suke, wasu kuma mutuwa suke ko su haukace, amma kai gashi ka tsaya muna magana da kai ba tare da hankalinka ya tabu ba. Don haka naji ina kaunarka, a bisa haka zanyi ma alfarma guda daya tal, itace kaje gobe misalin karfe daya na dare ku zo tare da Bukar idan ya zo ya bamu hakuri ni da Mamata da Kanina to zamu yafe masa kuma daga ranar zamu daina kashewa ko tsorata kowa a garin nan nasu”.
Ko da jin haka sai na cika da tsananin farin ciki, bansan lokacin da na furta cewa, “Godiya nake aljana, ai na tabbata kyawon nan naki ba zai tafi a banza ba duk da kasancewarki aljana dole zuciyarki zatayi kyau kamar yanda fuskarki take da kyau. Da ke mutum ce ba makawa sai na aureki”. A karo na biyu ta daka min tsawa kana dariya ta biyo baya, daga bisani kuma naji tana fadin, “Ni ba aljana bace, ni fatalwa ce sunan Surayyah don haka ka daina hadani da aljanu ko mutum domin duk na fisu karfin iko, kuma ka sani a yanzu ma dole ka aureni domin naji ina sonka…”. Ai ban gama jin sauran abinda take fada ba saboda wani irin firgici da na tsinci kaina a ciki. Kai amma dai bakin nan nawa wataran sai ya hallaka ni wallahi, ko da yake yanzu ma ai ya hallaka ni saura me kuma?. Tunda wannan aljanar ta ce sai na aureta ta wacce hanya na isa na tsere mata, tunani ne barkatai ke yawo a kwakwalwata, bansan lokacin da na ce mata, “Dan Allah kiyi hakuri karki sa maganganuna a zuciya, duk shirmene. Ni din banza zan iya aurenki wallahi ban isa ba. Ai ke zubin ‘ya’yan sarauta ce, kyawon surarki ya zarce talaka kamata ya tunkareki da sunan so balle aure, domin irinku sai dai saraki ko shugabannin kasa da gwamnoni. Dan Allah ki kalli kanki a cikin madubi zaki gaskata zancena”.
Dai-dai nan na dakata hade da sunkuyar da kai kasa ina fargabar abinda zai biyo baya. Shirun da naji tayi yasa na daga kai sama na kalleta, ashe tuni tayi girgiza ta dawo kyakyawar budurwa wacce na gani tun farko, nan take kyawonta ya sake cika mun idanu. Dariya naji ta kyalkyale da ita sai kace marar hankali, ta dade tana dariya daga bisani naji ta ce, “Wallahi kayi mun, irinka nake burin aure kuma na samu”. Ta karashen maganar cikin wata dariyar, na dan jima ina nazarin yadda zan kwance wannan mugun tarko da na jefa kaina ciki amma ban hango wata mafita ba, don haka na ce, “To ni zan tafi na kwanta goben zan yi kokari mu taho da Bukar domin neman yafiyarku”. Ina fadar haka ban tsaya jin abinda zata fada ba na juya na fara tafiya sauri-sauri gudu-gudu. Na barta nan tana dariya ina ta sake-sake a raina har na shiga gari na fada shago na kwanta. Shawara daya da na tsayar itace, gobe dole-dole ko a kasa ne na bar garin nan. Idan ba haka ba Allah kadai yasan masifar da zata biyo baya, tunda wannan fatalwar ta fara irin wannan maganganu. A haka dai bacci barawo yayi awon gaba da ni, ko da na tashi nayi sallar asuba ban iya komawa bacci ba ina ta tunanin mafita idan na rasa mashin.
Da safe tun kafin karfe 7 na nemi shagon da Bukar ya kwana, ni na tayar da shi daga bacci a kan ala dole yaje ya nemo min mashin tafiya zanyi. Nan fa ya fara yi mun korafin ai ba wasu mashina sai na jiya, haka na ce muje a sake jaraba na jiyan domin yau nayi rantsuwa sai na bar garin nan nasu. Dake ina dauke da jakata na saka shi gaba muka nufi gidajen masu mashinan. Gidan Dan Ladi muka fara zuwa da kyar muka lallaba shi ya yarda zai daukeni domin ya ce, tabbas ya gano matsalar kin tashin mashin din nasa jiya daga gareni ne, domin bayan barin wajenmu mashin din nasa bai sake mutuwa yaki tashi ba. Nan dai ya fiddo mashin daga cikin gida, amma dan banzan mashin din nan yaki tashi. Har turi mukayi mashin yaki tashi. Dayan kuwa da mukaje yace ya bayar da auron mashin dinsa. Zubairu kuwa rantsuwa yayi wallahi ba zai sake daukata ba yadda ya daukeni jiya mashin dinsa yaita bada matsala yayi asarar kudi da yawa. Ba yadda muka iya haka muka dawo gidan su Bukar jikina duk a sanyayye ba’a samo mashin ba. Har na zauna ina sauraron Bukar ya tabbatar min babu fa yadda za’ayi tunda masu mashina nan sun ki yarda su daukeni wai sai dai in kara hakuri aga abinda Allah zaiyi.
Ni dai sauraronsa kawai nake sama-sama baisan masifar dake tunkaroni da shi din ba, dama so nake sai na bar garin shima in fadi masa yadda mukayi da fatalwa Surayyah da alwashin da suke sai sun kashesa domin yayi taka tsantsan. Bayan tuno maganganun Fatalwa Surayya ai da sauri na mike hade da cewa, “Kai abokina yau fa ko a kasa ne sai na bar garin nan naku”. Bukar yayi murmushi hade da cewa, “Kai wallahi ba zaka iya ba tafiyar akwai nisa sosai, ai ka ga dadewar da kayi a kan mashin da zaku shigo nan kai ganau ne ba jiyau ba”. Na ce, “Eh na ji na gani ni dai kawai a haka zan tafi”. Ba yadda baiyi da ni ba a kan cewa in hakura har a sama wata mafitar amma na ce sam ba zan tsaya ba. Shi kuwa yace wallahi ba zai rakani har can ba, zai dai rakani ya dorani a hanya ya dawo. Na ce na amince muje, ko sallama banyiwa su Inna ba muka hau hanya ni dai burina in bar garin nan.
Mun danyi nisa kadan a hanyar mai jan burji Bukar ya miko min jakata dake rataye a bayansa hade da cewa, “To abokina ni fa iya kacina nan don har na fara gajiya, kai dai da kace zaka iya bisamilla”. Nayi dariya hade da cewa, “Ai kai raggo ne kuma matsoraci”. Shima dai dariyar yayi yace yaji dai, nan dai mukayi sallama na hau hanya shi kuma ya juya. Nayi tafiyar awa guda naji nayi matukar galabaita, kafafuna kamar zasu cire saboda gajiya. Don haka na nemi waje bakin hanya na zauna, gumi ya jikani ni har kishirwa ma nake ji, gashi dan rashin hankali ko karyawa ban tsaya nayi ba. Ba yadda Bukar baiyi dani ba, in tsaya mu ci dumame, amma na ce mu taho kawai, domin na matsu in bar garin. Na kalli hagu da dama na titin, tunda na taho banga mashin ko mota ta wuce ba balle ma insa ran zan samu wanda zai rage min hanya. Mtswwww na ja dogon tsaki, ni dai ziyarar nan kwata-kwata batayi min dadi ba wallahi, In da na sani da ban biyo ba.
Tashi nayi na karasa inuwar da na hango a bakin hanya na ajiye jakar na kwanta gami da yin matashin kai da ita tsabar gajiya kafafuna sai zogi suke. Ni banma san lokacin da bacci ya daukeni ba, amma cikin bacci sama-sama na rika jiyo karar babur don haka na tashi da sauri ina duba gefen da na ga babur din ya tawo. Zuciyata ce ta cika da farin ciki nayi saurin tashi na dauki jakata na karasa bakin titin birjin na yi tsaye ina dagawa mai mashin din hannu. A yadda na gajin nan ina ganin mai mashin din da ya taho shine mafita a gareni, idan naga ba zai tsaya ba wallahi zan iya shiga gabanshi ta yadda dole zai tsaya. Amma cikin sa’a tun daga nesa naga ya fara rage gudu ya hango ni da alama wajena zai tsaya, don haka na kara cika da farin ciki harda furta Alhamdulillah. Don ko nawa ya fadi farashinsa zan iya biya, idan ma kudin hannuna basu kai ba zan kira ko mamana ne ta turo in bashi in muka je wajen masu pos. Bayan ya tsaya na hau mashin din hade da cewa, “Mutumina barka da aiki, dan Allah juyawa zakayi ka kaini wancan garin bakin titi, Tudun sama ko tudun kasa ne ma sunansa oho, ni dai inda zan samu motar Zariya ko ta Kaduna.
Shiru banji yayi magana ba, amma ya tayar da mashin din ya fara tafiya, maimakon ya juya sai na ga ya nufi hanyar komawa garin su Bukar. Nan take na fara fadin, “Kai malam juyawa zakayi ba nan hanyar zamu koma ba”. Amma shiru mutumin baiyi mun magana ba ya cigaba da tuki, a tunanina ko dai kurma ne, don haka na fara taba shi domin ya juyo inyi masa kwatance ko da hannu ne. Amma me! abinda na ji ne ya sa nayi suman zaune a kan mashin din, “Idan ka sake yunkurin barin garin nan ba tare da sanina ba sai nayi maka hukunci mai tsanani duk da ina sonka”. Haka na ji mutumin ya fada da muryar da na tabbata ta fatalwa Surayyah ce. Bayan shiru na dan lokaci ai kamar zan kurma ihu, yanzu kenan duk abinda nake wannan jarababbiyar fatalwar tana biye dani? Lalai na daukko ruwan dafa kaina.
Muna cikin tafiya ji nake kamar na kama hannun mashin din na kifar da mu, sai kuma wata zuciyar ke fadin ai ko faduwa kukayi kaine zakaji ciwo ita dama ba mutum bace ba abinda zai sameta. Eh kuma kwarai haka ne, amma dai raina a tunkushe yake fuskata babu annuri ko kadan, ni tunanina yama kulle na rasa me yake yi mun dadi. Haka ina ji ina gani ya kaini har gaban gidansu Bukar, yana zuwa ya tsaya bai kara ce min uffan ba. Ina sauka daga kan mashin din ya juyo da mashin ya tafi, ni kuwa na nemi waje a kofar shagon Bukar na zauna hade da zafga dogon tagumi. Sai yanzu nake jin haushi dalilin da ya hana in kama mai mashin din nan da kunce gwara da ko faduwa ne muyi duk abinda zai faru ya faru. Bukar ne ya fito daga cikin gidansu, tsaye yayi yana kallona cike da mamaki daga bisani ya ce, “Nura wai kaine kuwa, lafiya me ya dawo da kai ko dai ji kayi ba zaka iya ba ka juyo”. Mtswww, dogon tsaki na ja a karo na barkatai da bansan kaina nake wa ba ko wani. Bukar kuwa ya bushe da dariya, hade da cewa, “Dama ai na fada maka hanyar da nisa sosai ba zaka iya zuwa a kasa ba”…..
Zan cigaba, duk ranar da kukaji shiru a kwanakin nan rashin caji ne ya hanani typing ba guduaw nayi ba, laifin Kedco ne 😁