Uncategorized

Yanzu-yanzu An Fara Biyan Bashi Na Trader Moni

 

A ranar talata Wanda yayi daidai da 25-Apr-2022 aka fara biyan mutanan da zasuci gajiyar bashin trader Moni Wanda aka buɗe a shekarar data gabata.

 Trader Moni loan tsari ne wanda gwamnatin tarayya ta buɗe domin baiwa yan Nigeria bashi mutum 10 Million amma ba kyauta bane domin kowa sai mutum yadawo dashi, sannan a sake bashi wani.

 A satin da ya wuce ne masu bada bashi na trader Moni suka rinƙa buɗe wa mutanen da zasuci gajiyar wannan bashi na trader Moni Account number na access bank Wanda a cikinsa za’a turo kuɗin wanda za’a basu bashi.

 Sai kuma a yau 26-Apr-2022 suka rinƙa sakawa mutane kuɗin su wanda za’a basu bashi ta wannan Account number ɗin da aka buɗe musu na accees bank suka tura ₦50.000 ga ko wane Account, wanda kuma zasu cire kudin su cikin sauki ta hanyar ziyarar accees bank wanda yake kusa daku.

 Tun daga wannan lokaci zuwa kowane lokaci trader Moni zasu cigaba da turwa waɗanda zasu amfana da wannan bashi kuɗin su ₦50.000 wanda zai baka damar cimma duk wani buri naka da wannan kuɗin kafin lokacin mayarwa yayi.

 Trader Moni sun bukaci duk wanda yake wannan tsari wanda bai sami kuɗi ba ya kwantar da hankali sa kuɗin sa zasu shigo cikin Account ɗin sa ba tare da ɓata lokaci ba.

 Idan kasan baka cikin wannan tsari na trader Moni ka kwantar da hankali zuwa nan gaba zasu buɗe portal domin daukan sabbin wadanda zasuci gajiyar wannan tsari.

 Ku cibaga da kasancewa da Aihausanovels.com.ng Domin samun sabbin update.

Back to top button