Hausa novels

Aliyu Haidar Hausa Novel complete document

Description/Story:

Aliyu Haidar Hausa Novel Complete Document Written By Kausar M Hassan

 

Description

💫 ALIYU HAIDAR  💫

 

✍🏻 KAUSAR M. HASSAN

 

Bismillahi Rahmani Raheem!

 

“Alhaji dan darajar Allah kayi hak’uri ni bansan laifin da nai maka ba, mai ya kawo maganari saki”???

Cewar yar matashiyar matan dake tsaye a gaban wannan dattijon, wadda ta kasance ita ba fara ba ita kuma ba baq’a ba, shekarunta bazasu wuce 30 ba.

“Hajiya na fad’amaki cewan na’ sakeki saki daya saboda hka idan Allah y baki miji kiyi aure”

Yana gama fad’in yaja rigarsa fuuu y wuce.

Kai kawea ta girgizah saboda tasan tabbas mutum baya tab’a wuce kaddararsa, hakan yasa ta koma d’akinta ta tattara kayanta a cikin jaka ta had’a ta dau mayafinta ta fito, zuciyanta cike da k’una da bakin ciki, tana kawowa tsakiyan gidan d’anta na dawowa dga makaranta, jakar makarantar shi ya yarda akasa, da gudu ya isa gareta.

“Mame tafiya zamuyi ne naganki da jaka a hannu”?

Rage tsayenta tai dea2 nashi tasa hannunta ta dafa kanshi

“Aliyu ba tafiya zamuyi ba, nidea zan tafie, kuma a nan zan barka, ina mai maka nasiha da kazama namiji, kazama mai hakuri da juirya akan duk abunda zai biyo bayanka”

“Mame dan Allah kada ki tafie ki barni, wallahi zan rik’a jin magana, bazan k’ara fasa kwano ko d’aya a gidan nan ba, zan rik’a share ko ina, mame dan Allah”.

Rungumeshi tai tana zubar da hawayen rabuwa da d’anta, wanda yake shine sanyin idaniyanta.

“Aliyu ni wnnn duk baya damuna, ko wanne yaro haka yake, hasali ma ni kullum addu’ah nake maka akan Allah ya shiryaka, nasan kuwa Allah zai amshe addu’ahta”

Gyaran muryan da tajine ya katsie mata zancen da takeyi

“Kai zubairu amso min yaron chan” ya fad’a murya a fusace.

Zubairu dake kusa dasu, yasa hannu yana raba uwa da d’anta.

Zubairu ya amsheshi, hajiya ta juya ta nupie kopan dake fita gidan.

“Mame dan Allah ki dawo kada ki tafie, mame!!!”.

Haka ta fice ta barshi a gidan zuciyoyinsu cike da tarin bakin ciki mara misaltuwa…

Aliyu Haidar Hausa Novel complete document

Page ((2))

 

©Kausar M Hassan

 

Ganin baida mafita sea ta Allah, yasa ya cigaba da huci kaman wani sabo zakin daya fito neman abunci, hannun zubairu ya garzawa cizo, wnda hakn yay sanadiyar sakinshi da zubairu da yay, da gudu y haura gidan saman, ya bud’e wani d’aki wnda da alama wannan shine d’akinshi, banka kopar yay ya maida y kulle da padlock ya hau kan d’an karamin gadonshi ya kwanta ya cigaba da kuka.

Alhj baiji dad’in kasantuwar hakan ba, shi kanshi baisan maisa yay hkn ba.

Cike da tak’aicin abunda ya aikata y kama hanyar shiga d’akinshi. Wata mata na hango fara tas da itah, iya inda akeso mace takai to ta kai, sanye cikin dogowan riga bak’a tasa dan k’aramin hijab, da baqaqen takalmi, chewing gum ne a bakinta tana tauna Karas_karas.

Ganin Alhj da tai yasa taja ta tsaya chack kaman gunkin da aka ajiye.

“Alhj ina hajiya salma”?

Shiru yay jim kad’an tukkuna ya nisa

“Na saketa hajjah rabi, kuma nace idan ta samu miji to tayi aure.

Kirji ta daka cike da nuna rashin jin dad’i fal a fuskanta

“Haba Alhj dan Allah, kayi hkuri ka dawo da ita mana mai yay zafi haka shi ba wuta ba”?

A fusace ya bata amsa

“Kinga na gama magana, kuma bana so a k’ara dawomin da ita farko”

Zatayi wata magana ya ra6ata ya wuce, kai ta girgizah tukunna ta qaraso tsakar gidan, ganin jakar Aliyu da tai yasa ta tabbatar da cewan ya dawo dga makaranta.

“Zubairu!!!” Hajjah ta hau kiran sunanshi

Jiki na rawa ya amsa kiran da take masa

“Na’am hajiya gani” ya karaso kusa da ita cikin ladabi.

“Aliyu y dawo dga makaranta ne”?

“Eh hajjjah ya dawo”

“Yana inane”?

“Yana d’akinshi hajiya”

Alama tai masa da hannu wadda ke nuna cewan ya wuce, da sauri y kama hanya y bar falon.

Hajjah rai a 6ace ta hau gidan saman, dai_dai d’akin aliyu taja ta tsaya, a hnkli ta fara kwan_kwasa kopar.

Aliyu daya riga ya hasala ya fara magana

“Wanene”?

“Aliyu nice mamanka ka bud’e kopan nan”

“Nifa ummi bazan bud’e ba sea abbi ya dawo min da mame”

Shiru tai tukkuna ta qara cewan

“Ka bud’e d’ana zan maka komai kake so kana so kasa mamanka kuka ne, kasan idan bana ganinka bana jin dad’i’

Cikin muryar shagwa6a ya bud’e baki

“Ummi zaki hana anty nana ta daken”

“Na maka alkawari bazata kara dukanka a gabana ba kaji aliyuna jan gwarzo zakin fama, ka bud’e dakin”.

Tasowa yay ya bud’e dakin, da gudu ya fad’a jikin ummi, ummi ta rungumeshi sosai, a jikinta ya matuqar bata tausayi har a cikin zuciyanta”

“Yi shiru d’ana ka deana kuka, ga umminka nan tare dakai, zan baka dukkan gatan da mame dinka ke baka kaji ko”?

Kai ya d’aga tare da cewan

“To ummina”

Murmushi tai masa taja hannunshi zuwa d’akinta.

Tana isa ta tarar da nana zaune a d’akin, cike da hasala ta taso akanshi

“Ummi ya zaki shigo mana da yaron nan a d’aki sarai kinsan bayajin magana ynxn nan zai fara fasa mana kaya”

“Ke”! Ummi ta daka mata tsawa

“Bana son iskanci da d’iban albarka, ke kinsan da ya nai renonki ne, kowanne yaro haka yake, kurciya ce idan yay ta kuma zata wuce, komai lokacine”

Nana ta dubie aliyu ta dubie ummi

“Naji ummi amma gskya nifa…

“Kefa mi? Bazaki zauna da d’an uwanki lpy bane? Tsaya kiji wallahi nai maki iyaka da yaron nan, fice ki bani guri’

 

Baki ta tunzure ta kama hanyar fitah dga d’akin, yayinda ummi ta juya ta dubie Aliyu

“Kada ka damu kaji d’ana mamanka na nan tare dakai”

Mujie in baka chocolate”

Murmushi yay ya saki ranshi, suka wuce chan kuryar dakinta

Yayinda Nana tai d’akinta ta maida ta kulle, zuciyanta nai mata k’una sbd ita a duniya ta tsani aliyu, bata sonshi ko kad’an a cikin rayuwanta…

Meye dalilil”?…

Aliyu Haidar Hausa Novel complete document

 

File Name   Aliyu Haidar… Hausa Novel Doc.
Title   Aliyu Haidar Complete
Author    Kausar M. Hassan
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    13/10/2024
File Size    221KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Aliyu Haidar Hausa Novel complete Document By Kausar M. Hassan

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button