Matar Hariji Page 10 Romantic Hausa Novel
Hannu ta daga masa tace “kauce ka bani guri auta ko inci ubanka to ko Abulle yayarku da taji wannan gamin gambizar auren na shashashannan saida ta sallame daga sallar magrib waccan shashashar Zaliha yar uwar dayan itace kawai harda murna to dakai da ita dashi da ita wannan bagidajiyar wlh tallahi uban maqerin babanku zanci nidai wannan mugun irin baiyimin ba inda na shukane ma bazan siya nakai gonataba”Yanda zuciyarsa ke tafasa da kukan Jiddoh din idan ya tsaya zai iya fadawa uwartasa maganar da zata jefashi cikin fushin ubangiji saboda haka ya figi hannun matarsa tana kuka tana komai ya jefata a mota yayiwa motar key ya fice daga gdan a guje.Gidansa ya nufa zuciyarsa a tafashe yana tuqin zuciyarsa na qara kumbura kukan nata shi yafi komai dukan zuciyarsa baisan sanda yaci wani uban birki ba yace “Hauwah ya isa hakaaaa” yanda yayi mgnr da qaraji yasata saurin hadiye kukan taja wata qaqqarfar ajiyar zuciya.Sake taka motar yayi ya shiga unguwar ya taka burki yayi horn me gadin yazo ya bude masa ya shiga yayi parking ya kifa kansa a saman sitiyarin yace “innanillahi wa innah ilaihirraji’un Hauwah idan baki daina kukannan ba zaki tarwatsamin zuciya mu shiga kiyimin wani hukuncin banda wannan” Dagowa tayi idonta sharkaf da hawaye tace “inane nan din Kad…” Rufe Mata baki yayi yace “gdanki ne nan ne gidana da iyalina anan zaki zauna kafin mu tafi Lagos amma banason sunan nan daga yau kidaina cemin Kado sunana Muhammad Lameer” rufe idonta tayi tace “shabdi rahin kunya kenan mu a Rugarmu baa fadar sunan babba” murmushi yayi yace “to kawai ki rinqa cemin babe kinji” batare data damu da abinda hakan yake nufi ba ta fara maimata “babi babe bebe bebi” dariya sosai tasashi wato ita a gurinta komai har ya wucce ta samu abin maimaitawa “babi babe bebe bebi tana nufin duka da haka zatake kirana nikam naga ta kaina” ya fada a ransa tare da bude motar…………A fusace ya juya zai fita ta kamo kwalar rigarsa ta baya tace “wlh bazaka fita ba saika fadamin matsayina a gurinka nagaji da wannan rayuwar quncin dakai Lameer kai banji dadi dakai ta fanni mu’amala ta aure ba kai banji dadin zama dakai ta fannin rayuwa ba kai bansamu lkcnka ba wannan wanne irin jahilin aure ne mara ma’ana da rashi albarka ta baibayeshi ta ko ina Lameer na tsaneka na tsani jininka na tsani zama dakai na tsani komai naka ka rabu dani don Allah Lameer nidai nace ka sakeni kazauna da kucakar matarka”Murmushi yayi Mata tare da dago kanta yace “saurin me kikeyi mmn Fadwah kin dade kina roqona saki naqi yi mikishi saboda abubuwa biyu da nake dubawa amma kidan qara hqr indai zakici gaba da fadamin duk abinda yazo bakinki to inayi miki albishir da saura qiris”Yana fadin haka ya juya ya fice da sauri ya nufi kitchen ya dauki duk abinda yasan zai buqata ya fita ya koma part din Jiddoh ya shiga ya tarar da ita a tsaye tanata kalle kallenta ya shiga kitchen din tabishi ta tsaya tana kallon yanda yake hada komai.Taliya ce ya dafa musu sai tomato soup da taji bushasshen kifi sai qamshi yakeyi ya zuba musu a flat daya ya dauka abin na arziqi ne suka fito ya jata dinning suka zauna ya dauki cokali ya juya ya debi yakai Mata bakinta ta kawar dakai ta wanke hannunta tasa ta juya ta diba takai bakinta.Lumshe ido tayi tana tauna abincin a hankali yana kallonta harta hadiye na bakinga ta bude idonta taga ya diba a cokali zaikai bakinsa tayi saurin riqe cokalin ta janye flat din ta tashi ta sauka qasa ta juya masa baya.Ajiye cokalin yayi ya zubawa sarautar Allah ido abincin da yawa amma ko a jikinta ta rinqa cin abinta tana kadakai, tashi yayi ya matsa gurinta yace “bazaki iya cinyewa ba ki bani na tayaki” wani mugun kallo ta watsa masa ta tureshi tace “aa mugunta zakayimin ka cinye nikam ka qyaleni wannan qaton bakin naka mugun lauma zaiyi.Damuwarsa yaji ta gushe gabadaya yayi dariya yace “is ok amma wlh sai kin cinyeshi tas kin yarda?” Daga masa kai tayi taci gaba dacin abincinta, ya miqe ya shiga kitchen din ya zubo wani ya zauna a dinning din yanaci yana kallonta.Cikinta fah ya cika gashi ko rabin abincin bataci ba abinka dame qaramin tanki, juyowa tayi ta kalleshi ya daure girar sama data qasa babu alamun Wasa fuskarsa yanacin abincinsa a nutse yana danna wayarsa, sakeyin qasa tayi da kanta tana cakalar abincin shikuma yana satar kallonta, idan taci abinda zata iya saita dago ta kalleshi.Hardai tagaji ta dago tace “Kado na qosh…..” Hannunsa ya daura a bakinsa yace “sheeeeeet!” Sannan ya miqe ya dauki lemo da ruwa ya tsiyaya a cup ya tsugunna gabanta yakai Mata bakinta ta karba tasha sannan ya sake tura nata abincin yace.“Alqawari mukayi dake zaki cinye saboda haka saikin cinyeshi tass” ai baigama rufe bakinsa ba sai hawaye sharrrr ya miqe ya koma ya zauna saman stool din dinning din yace “oya kiyi ki cinye kiyi wanka zanje masallaci na dawo an fara kiran magrib” miqewa yayi ya shiga daki ta kuma tusa abincin a gaba.Turawa takeyi tana kuka cikinta kamar zai fashe har wani yunqurin amai takeyi tanata jan zuciya, fitowa yayi da sauri baiko kalli inda take a yana daura agogo yace “idan na dawo naga baki cinye abincin nan ba sainayi gunduwa gunduwa da sassan jikinki”Wawuyarku takuwa sake rushewa da kuka dataji yace zaiyi gunduwa gunduwa da ita har tana auna gabobinta yau tasan idan bata cinye abincin nan ba dafgenta zasuyi, Kai abu tun kamar zai yuwu harta kai qarshe kawai ta tusa abincin a gaba ta hade kai da gwiwa ta kurma uban ihu.Daidai lkcn da yake haurowa saman ya qaraso da sauri ganin yanda ta riqe ciki tana kuka wiwi yasashi komawa ya zauna yace “me kikeyiwa ihun bayan kince zaki iya cinyewa?” Cikin shassheqar kuka tace “Qur’anin Allah na dauka abincin kadanne ashe dayawa kuma ai kaine mugu ka zubo da yawa”Wata cafka yayiwa gashinta yace “nine mugu?” Kuka ta rushe dashi tace “eh mana mugun mugaye na saicin alhakina kakeyi ka tsotsemin Inninina kayimin wanka sannan kasani na cinye abincin da kasan yafi qarfina wlh sai munyi hisabi a lahira kai gidansu Ingarido zaa kaika idan ka mutu nikuwa gidansu Hamana”🤣Dariya ce tasashi qarasa zama yace “waye Hamana?” Shiru tayi tace “wazirin Fir’aunu ne kuma babban babbansu a gidansu😃 Murmushi yayi yace “kintaba zuwa islamiyya?” Turo baki tayi tace “Modibbo Gambaje yana koya mana idan ya dawo daga rani”Murmushi yayi yace “makaranta hudu zansaki ta islamiyya data boko zan dauko masu koya miki a gida sannan ta koyon girki zan kaiki Catherine school sai ta koyan kwalliya da zama da miji” numfashi ta sauke tace “nidai bazani b…” Rufe mata baki yayi yace “aikuwa sai kinje karma ki qara cewa bazaki ba banason musu”Shiru tayi tana riqe cikinta tace “wayyohh cikina” da sauri ya dagota yace “meyene kuma?” Kuka tasa masa tace “kaga kasani naci wannan taliyar yar leda kuma…..” Rufe bakin tayi taqara riqe cikin tana kuka yace “dallah kiyi mgn mene?” Kuka ta Kuma rushewa dashi ta kwanta a jikinsa tace “kashi nakeji kuma babu jejin da zan zagaya a kusa yanzu yaya zanyi”🙈___________📝Riqota yayi jikinsa suka nufi qofar shiga gidan ya bude ya shiga da sallamarsa Mubaraka dake fitowa daga kitchen ta dago domin amsa sallamar ai batasan sanda ta saki flat din hannunta ba saboda tsananin firgici da mamaki.Janye Hauwah yayi a jikinsa ya zaunar da ita saman daya cikin kujerun falon yace “sannu da gda uwargida sarautar Mata ya kadaici” bata iya amsawa ba saboda wani yawu me daci data hadiye daqyar ta matso gabansa cikin macewar gabobi tace “Lameer wacece wannan”Tayi maganar tana kallon Jiddoh wadda itama ita take kallo qurrr tanata zuba santi a ranta na kyawun Mubaraka tayi ajiyar numfashi a ranta tana fadin “dama nice”Miqewa yayi yana cewa “qanwarki ce Ina fatan Isa ya gyara wannan bangaren?” Bata iya cewa dashi qala ba saboda wani baqin ciki da yake turnuqar zuciyarta yaja hannun Hauwah domin su hau saman Amma sai ta noqe tace “tabdi salon naje na taka na fado nikam ka barni anan”Itadai bazata rabu da abin mgn ba ya fada yana figar hannunta da qarfi ta fada jikinsa ya dagata cak tana ihu ya haura saman ya direta a tsakiyar parlourn yayi shigewarsa daki.Tsayawa tayi tana kallon gurin ta zube a gurin tana kallon kowacce kusurwa ta falon cike tsoro da mamaki komai juya Mata yakeyi saboda ko a mafarki bata taba tunanin tsintar kanta a irin wannan gurin ba.Miqewa tayi tana latsa kujerun tana dariya tana cewa “laha’ilallah Kado zo zokaji wlh wanan gumakan na gurin nan duk laushine dasu kamar jikinka” Fitowa yayi ya tsaya jikin qofar ya zuba Mata ido yana kallon inda taken komai na parlourn tana shafawa tana dariyaMurmushi yayi ya matsa ya sha gabanta ta dago ta kalleshi ta nuna masa standard A.C dake tsaye a kusurwar hagu ta parlourn tace “wannan kuma meyene Dana taba naji yanata kwararar da sanyi?” Ajiyar numfashi yayi yajata suka zauna yace “A.C ce” kallonsa tayi tace “tohhh sunanshi kenan ic meyesa bana ganinsa a rugarmu?” Dariya yayi yace “ai bakuda wutar lantarki shiyasa baki ganinsa a rugarku yarinya” “Miqewa tayi tace “aa Kado in zaayi wasa ai wasa banda tsikarin uwar miji da tabarya kada ka qara cemin yarinya danni ba yarinya bace na fada maka…”



