Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 54 Complete Novel
*ASM Bk2054*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..Nufo cikin d’akin tay tana d’an yarfe ruwan fuskarta da alama wanke ta tay, a gefen gadon ta tsaya idon ta akan Fatuu da itama ta kafeta da nata idanun, da d’an murmushi tace “sannu kin tashi” itama murmushin take mata ta d’aga mata kai kafin ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya jiki, shiru suka d’an yi suna ta kallon juna Amadu na kallon su da murmushi yar ajiyar zuciya gwaggo tay tace mata ga breakfast nan kai ta k’ara d’aga mata, kina iya saukkowa ne?” Gwaggo ta tambaya a hankali tace mata eh ta fara matsowa zuwa bakin gadon ta zuro da kafafun ta har zata mik’e gwaggon ta dakatar da ita tace yakamata a k’ulle gashin ta kai hannu ta fara tattara mata shi bayan ta gama ta juya cikin kayanta ta d’aukko mata brush da toothpaste ta tambayeta zata iya zuwa toilet nan ma kai ta d’aga mata alamar zata iya amman duk da haka saida ta kai hannu ta d’agota ta nufi toilet d’in da ita Amadu nata kallon su cike da k’auna, Bayan da Haisam ya fito yana shiga reception zai nufi hanyar fita wata mata sanye da farar doguwar rigar uniform kanta d’aure da kallabi ba hijab a jikinta ta sha gaban Haisam tana Fad’in “wa nike gani kaman ango?” dakatawa yay ya kai idon shi kan ta nan take ya ganeta mama ce wadda ta duba Fatuu lokacin da abun ya faru da d’an murmushi ya gaishe da ita yay mata ya aiki bayan ta amsa fuska a d’age tana kallon shi ta cikin glasses d’inta tace “wani ke bai lafiya ko kai?” Fuska a sake yace mata ita matar tashi ya kawo tambayar shi tay Mike damun ta kuma yace “She had a miscarriage” waro ido mama tay “Subhanallahi yaushe hakan ya faru?” Ya bata amsa da jiya ta tambayi yanayin cikin yace mata just 1month ne ruk’e ha6a tay “Oh kace dai tun wannan karan battan aka samu abu bai dad’i ba kuwa” shi dae d’an murmushi kawae yay tambayar inda Fatun take tayi ya fad’i mata tana Amenity da room no d’in ta jajanta mashi kafin sukai sallama ya tafi, tare suka fito bayan tayi brush d’in saida Gwaggo tace ko zatai wanka tace tayi d’azun da asuba, bayan sun fito kan kujera gwaggo ta sata ta zauna ta fara had’a mata breakfast, kakkauran tea da slice bread sai wainar k’wai ta had’o mata ta aje a gefen ta tace ta ci ta k’oshi kallonta tay da d’an murmushi tace mata ta gode, kallon Amadu da har lokacin yana a bakin gadon Gwaggo tay ta tambaye shi yanzu zai yi Karin kumallon ta had’a mashi yace a’a ta bari sai d’an anjima gefen Fatuu ta koma ta zauna cikin sanyin murya Fatun tace ita ba yanzu zata ci ba tana mata murmushi tace sai ta gama, a hankali take cin Abincin akai akai gwaggo ke kai idonta kan ta tay mata sannu ita kuma sai tay d’an murmushi ta amsa suna haka aka turo k’opar Mama ce ta shigo da sallama idonta akan su Gwaggo dake zaune ta amsa mata tunda Fatuu ta kalleta ta gane ta, k’arasowa ciki tay gwaggo na kokarin mik’ewa tace tay zamanta su ai sun saba da tsayuwa, gaisawa suka shiga yi Amadu ma ya gaishe da ita ta amsa kafin ta maido idonta kan Gwaggo tay mata ya mai jiki da fara’a tace mata gata nan da Sauk’i ta maida kallon ta kan Fatuu cike da jajantawa tace “Sannu Amarya ai yanzu na had’u da Angon naki zai fita shine yake sanar da ni kina nan kin samu miscarriage” wani abu Fatuu ta had’iya tay mata zuru da ido Gwaggo kuwa kan ta ne ya kulle cikin ranta ta hau mamakin jin sunan data kira Fatuu Saboda a tunanin ta iya su kadae suka san da Maganar auren to ya akai ita ta sani gashi ba sanin ta ma tayi ba ko a yan’uwan Haisam d’in, kamar Mama tasan zancen zucin da Gwaggon ke yi ta kalleta tace “ai bayan auren nan ya kawo mana ita magashiyan cikin mawuyacin hali hankalin shi a tashe” wata irin kunya ce ta rufe Fatuu ta sadda kai gabanta na fad’uwa gwaggo ma d’an murmushin yak’e tay ta maida idon ta gefe Amadu kuwa dama wayar shi na a hannun shi sai kawae yay kaman yana kira ya mik’e ya nufi hanyar fita, cigaba Mama tay “ai har fad’a saida nay tayi kan yadda ake d’irka ma yara magungunan da suka fi k’arfin su don harda hakan ke haddasa irin wannan aika aikar azo kuma aita jan ido Allah ma yaso ita ba’a dangana da yin d’inki ba, ashe har an samu rabo sai kuma abu mara dad’i ya faru” gwaggo dake ta murmushin yak’e a kunyan ce tace mata “Wllh kam” ta fahimci irin Mutanen ne da bakin su a sake yake komi yazo fad’i suke ba tare da sun ji komae ba,
“To Allah ya maida mafi Alkhairi ai abun ba wuya yanzu kin ji an samu wani ba kamar yaran yanzu fitinannu ne wllh jarabar tsiya gare su” Fatuu tamkar ta nutse a wurin haka taji ba ita kadae ba har gwaggo wata irin kunya ce ta rufe ta saidae ta sadda kan ta k’asa ita kuwa Mama ko a jikin ta tambayar gwaggo tay wai Fatuu d’iyarta ce ta d’ago da d’an murmushi tace mata a’a jikarta ce a wurin ta take nan fa ta hau yi ma gwaggo tambayoyi sai kace yar jarida harda tambayar ta amma dae Haisam d’an manyan mutane ne ko don taga ranar da ya kawo Amaryar tashi har kyautar dubu hamsin yay mata nurse da ta kawo shi wurinta kuma dubu ashirin nan gwaggo ta sanar da ita ko d’an waye harda su ruk’e ha6a tace koda taji ai biri yay kama da mutum sai kuma tace ma gwaggo wai kaman ta san fuskarta a wani wuri tace mata ba mamaki ita attender ce a k’aramar Asibiti Mama tace ba shakka anan tasan fuskar sai k’ara cewa ikon Allah wai su kaman masu d’an rufin asiri ne daga amsoshin da ta bata shi kuma gashi d’an shahararran mai kud’i da aka sani a haka kuma ya auri ita Fatun don taga yanzu auren jari hujja ake ita dae gwaggo sai murmushi take tace mata ai su ba irin wad’annan masu kud’in bane kud’in su basu sa masu girman kai ba kowa na su ne ko mai kud’i ko talaka duk d’aya suka d’au kowa, sosae ta shiga yabon su tana fad’in dama tana jin ana fad’in alkhairan mahaifin shi da kakar tashi ma har a tv tana ganin aiyukan Alkhairin da suke yi harda ce ma Fatuu tayi dace ta k’ara gode ma Allah samun irin wad’annan mazan a yanzu ba k’aramar baiwa bace don tsananin wahala gare su don haka ta rik’e shi gam ta bishi sau da k’afa still kan Fatun na k’asa Gwaggo dae sai murmushi take daga baya ta hau yi ma Fatun tambayoyi tace anyi mata wankin ciki ne gwaggo tace mata a’a jiya har suka bar asibitin da daddare ba’ai ba da yake ta suma ne sai daga baya ta farfad’o Allah yaso bata tambayi dalilin suman nata ba sai ta kalli Fatun tace “kina zubar da jini ne sosae har yanzu?” Kai ta girgiza mata ba tare data kalleta ba a hankali tace “a’a ba sosae bane” tace “akwae gudaji gudaji?” d’an shiru Fatun tay alamar tunani sai kuma ta d’an kalleta tace a’a babu, nufar gado mama tay tana fad’in k’ilan ma ba sai anyi Mata ba to da alama komae ya fice tunda dama cikin k’arami ne sosae, a gaban drawer d’in gefen gadon ta tsaya ta kai hannu ta fara duba magungunan dake sama tana yi tana d’age ido had’i da cuno baki da alama dae kaman bata gani sosae sai da gilashin, bayan ta gama dubawa ta dawo wurin su tace tunda an bata wadancan magungunan tasan za’ayi mata scanning in anga komae ya fita ai shikenan dama amfanin wankin cikin don a fitar da komae koda wani abu ya mak’ale a mahaifar gwaggo ta d’aga mata kai daga baya tace bari ta tafi tana shirin tafiya gida ne aikin kwana tayi zuwa da daddare in ta shigo zata shigo taji yadda sukai da likita gwaggo ta mik’e tay mata rakiya har bakin k’opa tana mata godiya ta tafi, tunda gwaggo ta juyo ta dawo kan Fatuu ke a k’asa inda ta tashi ta koma ta zauna d’akin yay tsit wata irin kunyar gwaggon ce ta lullu6e Fatuu yayin da ita kuma Gwaggo ran ta yay mata wani iri sosae abun ya ta6a mata zuciya jin Haisam har Asibiti ya kawo Fatun wato yanzu da ba aure a tsakanin su kuma Al’amarin cikin bai biyo baya ba shikenan ita ba sanin an aikata zatay ba, sosae jikinta yay sanyi lalle mutum bai isa ya shiryar da wani ba face Allah yaso kaidae kawae saidai kai iya bakin kokarin ka ka had’a da Addu’a amman wani tsananin ka ko sa ido ko wani wayon ka ko dubara duk basu yi wllh tarbiyar yara yanzu sai an dage da Addu’oi don duk yadda kake kaffa kaffa wllh bai hana yaro lalacewa ba tare da ka ankare ba Allah Ubangiji ya shirya mana zuri’a ya tabbatar dasu akan daidai ya taya mu tarbiyyantar dasu kada yaba wani abokin halitta damar canza su daga kan tarbiyyar da akai masu mai kyau ya shirye mu baki d’aya darajar fiyayyen halitta Manzo (S.A.W).
Haisam na fita daga Asibitin gidan Hajiya ya nufa, bayan ya isa yay parking Motar part d’in shi ya nufa yana zuwa Toilet ya shige don yin wanka, after some minutes ya fito k’ugun shi d’aure da Towel ga wani short yana goge sumar shi da shi wata irin yunwa yake ji shiyasa bai tsaya busar da ita da dryer ba shi kan shi saida yay mamakin yunwar don bai cika yin Breakfast da sassafe ba sai wurin 11 haka amman yanzu duka k’arfe takwas da yan mintuna, gaban dressing mirror ya tsaya ya shafe jikin shi da body cream d’in shi mai daddad’an k’amshi bayan ya gama ya shafa roll on ya feshe jikin shi da body spray kala ukku har wani mai ya d’aukko ya matsa a tafin hannun shi ya kai kan kwantacciyar sumar chest d’in shi ya shafe nan take ta k’ara kwanciya luff ya k’ara d’aukko hair spray ya feshe sumar kan kafin ta k’irjin ma ya d’an fesa mata bayan ya gama yan shafe shafen closet ya nufa ya ciro jallabiya da short ya dawo bakin gadon ya fara kokarin sawa, sanye cikin jallabiyar wadda coffee brown ce mai gajeran hannu ya fito bayan ya zura takalma a cikin Corridor ya shigo cikin parlorn dake a gyare tsaf kaman ko yaushe ya nufi kopar ya fita, part d’in Hajiya ya nufa lokacin da ya shiga Parlon ba kowa hakan yasa ya wuce Bedroom d’inta ya turo kopar ya shiga da yar sallama, tsayawa yay a bakin kopar yana kallon Hajiyar dake kwance tana ta sharar bacci ta rufe rabin jikin ta da lallausan bargo baki a wangame d’an murmushi kawae yay ya juya ya bud’e kopar yana fitowa Saude ma ta fito daga cikin d’akin ta zata kitchen dakatawa yay cikin girmamawa ta gaishe dashi ya amsa mata tay mashi ya mai jiki don jiya bayan Hajiya ta dawo saida ta bata labari kaf tana ta fad’a tana fad’in Haisam bai d’auke su da mahimmanci ba bama kamar ita yanzu ta gane bai damu da ita ba bai k’aunar ta shiyasa ya iya fad’i mata abunda hankalin ta zai tashi harda uban kukan ta ko ta mutu ko tay rai shi ko ajikin shi nan fa Saude ta hau rarrashinta tana bata hak’uri saidae a can k’asan ranta ta ji ma Fatuu dad’i sosae da Haisam ya kasance mijinta duk da bata ji dad’in zubewa da cikin yay ba har Addu’a tay kan Allah yasa auren ya d’ore, umarnin ta kawo mashi breakfast ya bata ta tambayi abunda zata kawo yace wanda ya samu daga haka ya wuce saida ya fita daga cikin corridor d’in sannan itama ta wuce, a parlor ya zauna bai koma part d’in shi ba ta bishi da shi can don yanzu yasan ita matar aure ce, ba’a d’au lokaci ba ta shigo cikin parlorn ruk’e da d’an babban tray saida ta janyo c-table gaban shi sannan ta d’aura mashi tace aci lpy ya jinjina mata kai had’i da furta thanks, kakkauran tea ne a cikin mug sai babban plate mai gidaje da marfi bayan ya bud’e soyayyar plantain ce a gida d’aya sai chips a wani gidan na k’arshe kuma soyayyar wainar k’wai ce daga d’ayan gefen tea d’in ledar biredi mai yanka yanka ce duk da komae d’an daidai ta zuba sun mashi yawa, fara ci yay a nutse yana yi yana d’an kallon Tv a haka har ya gama ya rufe sauran da ya rage ya idasa hayewa kan kujerar ya kwanta sosae yana ci gaba da yin kallon bada jimawa ba bacci ya kwashe shi. Sai wurin karfe goma Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga cotton ta nufo cikin parlorn da sandar ta ta alfarma tana zuwa bakin kujerun tay turus idon ta akan Haisam da ya d’aura hannun shi d’aya ya rufe idon shi yana ta bacci, d’an ta6e baki tay ta wuce ciki a kujerar kusa da tashi ta zauna ta bishi da kallo kaman yaji a jikin shi ya fara motsi ya sauke hannun slowly ya fara bud’e idanun shi suka sauka akan Hajiya da ta tura baki tana bin shi da ido shima kallon ya bita dashi kafin ya yunk’ura ya tashi zaune ya jingina da jikin kujerar cikin muryar wanda ya tashi daga bacci ya gaishe da ita “Gud morning Sweetheart” wata uwar harara ta zabga mashi a d’an fusace tace “ai ka daina yaudara ta kaje can kai ma wata dad’in baki ba dai ni ba” wani kalar kallo yake bin ta da shi idanu a d’an lumshe can yay sigh slowly ya furta “am sorry” k’ara tura bakin tay ta kauda idon ta gefe ganin haka yasa shi jan jiki ya matsa can k’arshen kujerar ya kai hannu ya kamo hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa sai dae ta kasa a fad’ace tace “ai tunda kaga zuciyata bata buga ba sai ka k’arasa ni ta hanyar k’arya man hannun” d’an guntun murmushi yay remorsefully yace “I said am sorry I regret what I did, I dont know what came over me har hakan ya faru” yana Magana yana wani lumshe mata idanu sai kace wata budurwar shi ko matar shi k’in kallon shi tay tana cigaba da tura bakin had’i da kikkafta idanu d’an matsa hannun yay aikuwa ta juyo a fusace tace “Ka gama raina ni Haisam, kai wato har kana da k’arfin halin yi man wannan iskan cin ko” har sai da ya d’an yi yar dariya jin abunda tace cigaba tay “in ba don ka raina mu ba ka d’auke mu maras amfani wai har kasa a d’aura maka aure ba tare da sanin mu ba” rai 6ace tay Maganar yace “kiyi hak’uri Allah ne ya kaddara hakan zai faru ni kaina I never thought zan yi hakan” wani kallo take jefa mashi can tace “uhmm kai ka sani” sakin hannun nata yayi ya maida bayan shi ya jingina da kujerar idon shi na kallon gaban shi ita kuma Hajiyar idonta na akan shi can cikin d’aure fuska ta tambaye shi jikin Fateemar ya kalleta fuska a sake yace mata da Sauk’i tace ta farka ne yace mata eh tun jiya tay shiru can kuma ta sake cewa “ita waccan ta K’asar wajen kunyi magana da ita ne karta ji shiru tunda dae ba yadda za’ai ka tafi kabar yar mutane da ciwo” d’aga mata kai yay sai kuma yace mata sun yi magana jiya tace “kadae zabga mata k’arya tunda naga ka iya ta yanzu” bai ce komae ba ya d’age kan shi kawae yana facing saman Parlon yaji tace in baccin zai cigaba ya tashi ya koma part d’in shi ko a gyara mata parlonta yazo ya kama yi mata bacci ya hana a gyara, sauke kan yay suka had’a ido sai kuma ya mik’e ya nufi hanyar fita yana tafiya a hankali tabi shi da ido har ya fita ta maida jikinta jikin kujerar tay shiru da alamun damuwa akan fuskar ta ta, part d’in shi ya koma ya shige bedroom ya kwanta a kan gado nan da nan wani baccin ya sake d’aukar shi.
Saida Amadu yaga fitar Mama sannan ya koma cikin d’akin yana niyyar komawa bakin gadon Gwaggo ta mik’e tace yazo ya zauna bari ta had’a mashi breakfast d’in yaci yanzu in ba haka ba ba lalle ya samu damar ci ba d’an anjima mutane zasu iya fara zuwa yace to, bayan ya fara ci Fatuu dake gefen shi ta tambaye shi ko yaga wayarta kafin ya bata amsa gwaggo tace gata nan cikin Aljihun ta jiya ma bayan sun koma Fauziyya ta kira ta d’aga ta fad’i mata tana Asibiti shiru Fatuu tay cikin ranta ta shiga raya da ta bi Maganar Fauzy da yanzu cikin na nan ta tabbatar ma inda tasan kiran da Haisam yay mata a waya da yawa ne harda text message bazata bari a zubar ba wani, wani irin sanyi jikinta yay nan take taji wata irin nadama tazo mata da kanta ta zubar da cikinta na halak cikin mutumin da take tsananin k’auna, gaba d’aya ji tay breakfast d’in ya fitar mata a rai ta mik’e ta tattara kayan ta nufi gefen gado dasu gwaggo na ce mata har ta k’oshi tace eh ta tashi ta bata magungunan ta, bayan ta gama sha idasa hayewa gado tayi tay lamo har gwaggo na tambayar ta ko jikin ne tace a’a bacci ne bai ishe ta ba tace ai sai taci gaba ta lumshe ido kaman baccin zatai da gaske amman tunane tunane da zancen zuci kawae take a haka baccin ya d’auketa ba, bayan Amadu ya gama yace ma gwaggo zai tafi sai anjima zai dawo tace to k’ilan ta kira shi ya dafa Abinci ya zauna cikin shiri sukai sallama ta bashi kayan Abincin da aka gama dasu ya tafi. Wuraren k’arfe sha d’aya Fatuu ta farka taga d’akin wayam ba kowa tana kwance aka turo k’opar sai ga Fauzy ta shigo da yar sallama da sauri Fatuu ta yunk’ura ta tashi zaune tana kallonta itama Fauzy da sauri ta nufi gadon ta zaune a gefe fuskarta d’auke da matsananciyar damuwa tayi mata sannu ta d’aga mata kai d’an shiru sukai sunata kallon juna fuskar Fatuu a yamutse kaman zata saka kuka can Fauzy tace “ashe haka abu ya faru harda kwanciya Asibiti tun bayan da muka rabu inata so in kira ki zullumi da fargaba suka hana ganin har dare yayi baki kirani ba kin sanar da ni halin da ake ciki yasa nai k’arfin halin kiran ki saidae kusan sau ukku ba’a d’aga ba tsoro ya kama ni sosae na shiga tunanin to ko lpy gashi na kasa kiran ko Kawu Amadu, sai can dare wurin karfe 11 nace bari in k’ara jarabawa k’ilan ki d’aga tunda lokacin kwanciya ne ina kira sai gwaggo ta d’auka nan take sanar dani wai an kwantar dake Asibiti wayar na gida aka barta wllh sosae hankali na ya tashi bazan 6oye maki ba ko bacci ban yi ba saboda fargabar abunda ya faru har aka kwantar da ke, Aunty Mareeya har ta gane ina cikin damuwa tanata tambayata Mike damuna saidae in ce mata ban jin dad’i kawai don ban san taya zan mata bayani ba” dakatawa tay ta kai idonta kan ledar Karin jinin dake rataye cike da damuwa tace “harda k’arin jini ma akai maki kenan, cikin ne ya fita kika zubda jini sosae?” Kai Fatuu ta d’aga mata alamar eh, girgiza kai Fauzy tay “Sannu, wllh irin abunda nake ta gudu kenan kinga ko a Makarantar hakan ta faru sai an san dalili, to yanzu da su gwaggon suka sani miya faru?” Shiru kaman bazata ce komae idanunta suka ciko da k’walla a hankali suka fara gangaro mata cikin muryar kuka tace “Fauzy na aikata babban kuskure wllh ashe cikin nan na halak ne ba yadda na zata ba” waro ido Fauzy tay with mouth agape a rud’e tace “cikin halak! Kenan kina son kice man Ya Haisam Mijin ki ne???” Cikin kuka ta d’aga mata kai k’ara zaro idon tay ta kai hannu ta rufe baki kafin ta cire cike da Al’ajabi ta tambayeta yadda hakan ta faru nan ta shiga fad’i mata komae da ya faru bayan ta dawo gidan har zuwa yanzu, salati Fauzy ta shiga yi tana yi tana kai hannu tana dafa gaban kanta da kuma bakin ta cikin tsananin tashin hankali ta hau fad’in “ni wllh dama raina saida ya bani anya ba wani abu a k’asa kwata kwata na kasa yadda Ya Haisam zai aikata maki hakan Saboda son zuciya kawae dai bani da wata hujja ne, innalillahi abu dae bai yi dad’i ba wllh aka ce rashin sani yafi dare duhu” sosae ta shiga damuwa har fuskar ta ta nuna idanun ta sun sauya kwalla ta kwanta cikin su sosae Fatuu ke kuka tana fad’in “nayi danasani Fauzy duk da na d’aga wayar Ya Haisam bayan dana je na sanar mashi da hakan bata faru ba, saida yay ta kira na harda message ya turo man yace kar in yi komae in picking kiran nashi amman na k’iya k’in Fad’a maki nay don kar ki hana a zubar na nuna maki sau d’aya ya kira, wllh ban yi zaton na halak bane tunda ni bansan komae ba ai gashi naga kaman ma yayi fushi Saboda hakan ” itama Fauzy k’wallan ne suka fara zubo mata suna cikin haka suka ji karar bud’e kopa duk suka kai idon su kan kopar toilet sai ga gwaggo ta fito idon ta a kan su suma suka bita da ido cike da rashin gaskiya……………
….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.