Uncategorized

Jarumar Kannywood Rukayya Dawayya Ta Bada Wani Labari Wanda Ya Zama Wa’azi Ga Sauran Al’umma.

 

  A cewar Jaruma mai suna Rukayya Dawayya, ba zata manta lokacin da ta shigo sana’ar Film ba.  Wata yar uwarta ta shawarceta da su kama hayar wani gida domin tafıyar da rayuwar su cikin Salama.  Bata ki zancenta ba, su ka kama hayar gidan wani bawan Allah a cikin garin Kano.  Kasancewar kowa ya santa domin ta fara haskakawa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood. Jama’a sukan zo kofar gidansu da suka kama haya suna tsokanarsu ga yan film.  

Kodayaushe mai wannan gidan idan ya zo haka yake gani an taru a kofar gidansu.  Da ya tambaya akan me ake taruwa a kofar gidan sai a ka bashi labarin ai yan film ne suka kama gidan, aka ci gaba da zuga shi akan lallai ya kore su.  

Da tsakar dare wannan bawan Allah ya sa su a gaba dole sai sun bar gidan.  Haka su ka tashi suka bar masa gidansa. 

         KARANTA WASU LABARAN

 Kotu ta yanke wa wani dan kano hukuncin Kisa saboda cin mutuncin Annabi da yayi

  AlhamduLillahi Anyi sulhu tsakanin Naziru Sarkin Waƙa da Abubakar Maishadda

  Amfanin Dabino Ajikin Ɗan Adam

 Hanyoyin sace zuciyar budurwa cikin sauƙi

 Kwana da bugun a cewar Jarumar suka samu sana’a Allah ya azurtasu a lokacin sun bar garin Kano.  A haka dai wata rana wani bawan Allah wanda ya santa ya nemi da ta zo ta sayi gidansa don lalurar da tasa shi a gaba.  Haka nan ta samu damar cewa wannan gidan, amma sai dai akwai wanda ke haya a cikin gidan da ta duba taga wanda ke haya ba kowa ba ne face, wanda ya musu korar kare a baya lokacin da basu da shi. Ta tunatar da shi ita ce wacce yayi wa korar kare a wani lokacin da ya gabata. 

Jarumar ta ce bawan Allah nan ya fara bata hakuri dan Allah ta rufa masa asiri. Ta ce masa kada ya damu wannan ma jarabawar ubangiji ce Allah yana ba da arziki ne ga wanda ya so ya kuma hana ga wanda ya so, don haka ita bata dauki abinda ya yi mata wani abu ba kada ya damu ya cigaba da zamansa a gidan da ya zama mallakinta. 

Ta ce har yanzu wannan bawan Allah yana cikin gidan. Tana kira ga masoyanta da ma duk jama’ar musulmi da su kiyaye su rika taimakawa al’umma domin idan ka san yau ba ka san goben ka ba.

Back to top button