LABARINA (Zango na biyar, kashi na Bakwai)
Sabon shiri, sabon salo, sabuwar fikira.
Shirin ya yi gamon katar tare da afkawa hannun gwanaye ta fuskar rubutu. Wato irin abin nan da ake ce wa komai na babba, daban ne.
Marubuta 1: Nasir S. Gwangwazo, Yakubu M. Kumo.
Marubuta 2: Siddika Habib, da Sidiya Sidiya.
Labari: Aminu Saira
Ɗaukar nauyi- Sarkin waka
Ba da umarni– Aminu Saira
Kamfani- Saira Movies.
1. Tuggu bai yi amfani ba, asarar kujerar sarkin gida da Baba Dan’audu ya yi.
2. Da alama Rabiu zai cika da imani, tabbas Baba Rabiu ya iya acting.
3. Wacce irin kyakkyawar zuciya da karfin hali Ummi take da shi?
4. Dawowar Sumayya zai bude sabon shafi a cikin labarina. .
5. Cakwakiyar Soyayyar Lukman da Ummi da Sumayya, ko ya za ta kwashe ke nan?
KURA-KURAI:
1. kasa gano yadda aka yi da wanda ya saci wayar jami’in gidan yari, kamar nuna rashin kwarewar jami’an tsaro ne a fili.
2. Wacce irin zuciyace da Umma, har yanzu ba ta daukko ba daga fushin da take yi Rabiu.
3. Role din Dan’audu fa tamkar yana rainawa jami’an gidan YARI wayo ne.
Shirin labarina na daban ne cikin jerin shirye-shirye masu dogon zango.
Yanzu za a fara wasan.
Mubarak Abubakar Saulawa
14-10-2022.