Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 34 Hausa Novel

Da kyar ta iya danne kukan da ke taso mata, tsoron Allah na ƙara rufeta tana tuna irin iko da isan mommy akan saleem ashe har za’a iya samu macen da za ta raba wannan iko da isar cikin lokaci kankani haka?Miƙewa tayi ta nufi sashen Mammi, ba za ta zuba ido rayuwar saleem ya cigaba da tafiya a haka ba don salim ya cika mutum cikakke ɗari bisa ɗari ya taimaketa a sadda bata da mai taimako bayan Allah, shi ne namiji na farko da ya fara nuna mata so tsakani da Allah ba tare da kyama ko tsoron tabbatuwar zancen al’umma a kanta ba, ya hana hawayenta zuba ya kuma ƙarfafa mata gwiwa akan jajircewa da haƙuri da rayuwa, ta san babu abin da zai saka saleem saɓawa mahaifiyarshi don ya san darajar ta fiye da kowa face sharrin asiri. Abin da ya sake bata mamaki ya ɗaure mata kai shine ta yaya wacce mommyn ta yarda da ita har ta aura mata saleem ba tare da yana so ba ta zama sanadiyar rabuwarta da ɗanta? Sam bata kawo cewa ko alhakinta bane saboda ta san ita ɗin ba dolen su ba ce da su taimaketa da kar su taimaketa duk wannan tsakaninsu da ubangiji ne yo waenda suka zama dolen nata ma basu mata ba sai bare ne za su mata? Ta saka a ranta son zuciyar mommy ne ya janyo mata wannan wahala da suke ciki, tayi negleting duty ɗinta a matsayin uwa tana ganin dabararta shi zai sa ‘ya’yanta su cigaba da zama ƙarƙashin ikon ta alhali ‘ya’ya ba ababen iko da gadara bane ta manta Allah ne ke da dukkan iko akan bayinsa kuma shi ne ya san abin da yake fili da na ɓoye.Ko da ta isa wurin Mammi bata samu Rayyan ba, zama tayi cike da damuwa tace”Mammi Yaya saleem na cikin masifa”Ta ƙarasa idanunta na cika da kwallah, Mammin ma ta fahimce damuwar Afeefar don Saraki ya sanar da ita komai kuma tausayin Saleem ɗin duk ya rufeta itama.”Yanzu Saraki ya gama sanar mini, nayi mamakin yadda aka dau lokaci bai zo ba har ma aka yi auren Saraki saleem ba ya a kusa da shi ashe abin da ke faruwa kenan, laifin mahaifiyarshi ne Allah ya sa wannan abu da ya faru ya zame mata Aya ya sa ta hankalta”Kai Afeefah ta gyaɗa tana amsawa da “Ameen ya rabbi, Mammi ina so in taimaki Saleem Dukda ban san me Ya Saraki zai yi ba amma ina so in ba saleem gudummawa kaman yadda ya ba ni a sadda na rasa madafa don Allah ki taimakeni akan hakan”Ta ƙarasa a karye.”Me kike tunani Afeefah?”Mammi tayi tambayar cike da kulawa.”Mammi ina so ki yi convincing Ya Saraki akan za ki dinga bashi magani yana saka saleem sha ni kuma zan dinga haɗa zobo ko wani kalar drink da ayoyin da mafificin annabin mu annabi Muhammad (SAW) Yayi mana umarnin amfani da shi don karya sihiri, ko da kurba bibbiyu zai yi Allah zai ba mu nasara kuma ina so zan yi wani abu na sadaka da tawassilin Allah ya dube shi ya dawo dashi hayyacinshi kar mahaifiyarshi ta mutu da damuwarshi”Sossai Mammi ta yabawa hankalin Afeefah ta kara jin kuma tabbas bata yi wa Rayyan zaɓen tumun dare ba, ta gamsu kuma da shawarar don haka ta tabbatar mata zata bata duk wani taimako da take so.Afeefah ta ji daaɗi ta koma ɗaki ta fara neman takardar ta da tayi rubutu akan hakan a sadda malaminsu na islamiyyat ke koyar da su, ta kuwa samu bayan dogon bincike Adu’a kawai take a ranta Allah ya taimaketa.****Rayyan na fita Asibitin ya wuce kai tsaye ya samu kuwa mommyn na jin jiki yaran sai kuka suke yi, har ranshi tausayinsu yake ji kuma yana jin su ne tamkar su Abeeha, shi karan kanshi a yanzu ya gamsu cewa asiri ne ke dawainiya da abokin shi in ba haka ba ko mahaukaci ai ya san girma da darajar uwa.”Kukan nan me zai yi mata? Ko ba ku san Adu’a shi ne makamin ko wani mumini ba? Ko kukan lafiya zai bata?”Da ɗan faɗa yayi maganan don sun cika mishi kunne, duk shiru suka yi don sun san shi baya ɗaukan nonsense da likitan da ya duba ta yaje yayi magana don anan ɗin ma yana da office kuma yana aiki da nan ɗin Dukda ya fi zama Capital. Daga nan ya shiga ya duba ta tana bacci ya dawo ya kallesu yana so yayi magana da hankalinsu zai kwanta bai iya ba sai cewa yayi “Komai zai wuce in shaa Allah”Daga haka ya zaro kuɗi mai yawa ya basu kana ya fice, yana shiga mota Mammi ta ƙira shi a waya.”Saraki idan ka samu Saleem ko da a waya ne kar ka yi mishi magana da tashin hankali, ka bi shi da lalama kuma kar ka tsananta magana akan mahaifiyarshi da ‘yan uwanshi ka nuna baka damu ba don kar matar tashi tayi yunkurin shiga tsakaninku don akwai abinda nake so kullum ka tabbatar kana bashi yana sha, shi ramin ƙarya a koyaushe ƙurarre ne zai wuce ne kaman ba’a yi ba”Ya gamsu kuma ya san Mammi wani abin zata sama mishi na karya sihiri ya ji daaɗi don bai san ya zai yi ba, ya tabbatar saleem a gidan ba zasu barshi yayi komai na malamai ba bare yace zai kaishi wurin wani malami. A kan ibada da azkar ne zai tsaya sossai ya ga saleem ɗin ya koma yi don tun da chan ɗin shi saleem ba mai wasa da ibada bane kai duk iya ibadarka idan Allah ya nufa kamun asiri na cikin jarabawarka dole sai ya kama ka sai dai ka samu sassauci saboda ka riga ka yi tawasilli ubangiji shine mai yin komai.Kai tsaye gidan Saleem ya je Allah ya bashi sa’a ya dawo don yana horn aka buɗe mai gate a mota ya tsaya ya shiga kiran Layin saleem ɗin ringing na karshe aka sada shi dashi, amsa sallamar kawai yayi ya ce “Ina waje”Yana kai nan ya yanke wayan kusan mintuna uku sai ga saleem ɗin ya fito, ido kawai Rayyan ya kura mishi don kaman ba shi ba ya ɗan yi duhu kuma ya tara gashi sannan fuskarshi babu walwala haka ya iso ya buɗe gefen zaman banza ya shiga ya zauna.”Ya kake?”Saleem ɗin ya tambayi Rayyan yana kallonshi.”Lafiya ƙalau, ka yi wuyar gani.”Murmushi yayi wani dry smile da babu annuri ciki “An tura ni Lagos ne wani aiki shine muka tafi da madame fa, inda nake kuma babu wani service na kirki”Kai Rayyan ya gyaɗa.”No wonder, ya kowa da kowa?””Lafiya ƙalau””mu shiga mana in gaishe da mommy kwana biyu ban leƙa ta ba”Saleem ya ɗan yi shiru don wlh ya manta da ya tura su chan gidan.”Mommy bata nan sun koma tsohon gidan mu””Amma me yasa? Ina haya kuka saka a chan?”Ya ɗan yi shiru “Eh, nan ɗin ya ɗan takura mu ne ga iyayen Sabrina sun dawo shiyasa nace su koma chan”Kai kawai Rayyan ya girgiza duk ranar da Allah ya bashi macen da zata raba shi da Mammi bai san irin hukuncin da zai mata ba don idan bai kasheta har lahira ba sai ya nakasata yadda ba zata taɓa amfani ba har abada.”Ya Mammi da jiki?”Saleem ya katse mishi tunanin da yake yi “Tana ta faɗan kwana biyu baka shigo ba ai, ni kam saleem in tambayeka mana?”Kai yaa gyaɗa mishi “Ya tsakaninka da ubangijinka?”Ya ɗan yi shiru kan ya kalli Rayyan ɗin “ban gane tambayar ba, ina sallah biyar a rana yadda aka umurci kowani musulmi””na sani, ina magana ne akan nafilfili musamman na dare da na sanka da shi da azumin nafila, yau ka ma yi azkar na safe?”Numfashi saleem ya ɗan sauƙe kaman abin na damun shi “A gaskiya na manta rabon da in yi wani azumi da Sallar nafila, azkar ne nake dan yi watarana wani sa’in wani abu ya taso ko bacci ya hana ni amma zan yi kokarin ganin na gyara””Don Allah saleem ka gyara, da karatun alqur’ani kar ka manta ko da baka yi a fili ko baka nuna kana yi ba idan ka ji ƙuncin zuciya ka dinga ambaton Allah zai yaye maka ka ji?”Ya ƙarasa da tausayin abokin nashi, kai ya gyaɗa.”Ka shiga ciki”Rayyan ya faɗa don ganin Sabreenar na tsaye tana kallonsu, ba don tsoronta bane baya so ta fahimci ya san matsalar saleem din kuma baya so ta tambayi saleem ɗin abinda ya wakana tsakaninsu don irin su akwai wayo idan baka iya kama ɓarawo ba aka ce sai ɓarawo ya kama ka.”Gobe zan zo in gaida Mammi”Kai ya gyaɗa “Sai ka zo”Daga haka ya fice shi kuma ya ja motan ya bar gidan.****Afeefah yinin gabaɗaya bata zauna ba, musamman Mammi ta ba da aka yi mata sayyayar kayan zobo don ta san saleem na son abin, ta dafa shi ta tace bayan ta gama yi mishi haɗi ta zauna ta yadda idan tana karatun numfashinta zai dinga sauƙa ciki ta fara karanto AyatushifaSuratul tauba aya ta goma sha huɗu 14.Suratul Yunus aya ta hamsin da bakwai 57.Suratul Isra’i Aya ta tamanin da biyu 82.Suratul nahl aya ta sittin da tara 69.Suratul shu’ara aya ta saba’in da takwas har zuwa na tamanin da biyu 78-82.Suratul fusilat aya ta arba’in da huɗu 44.Ta Yi su ne kafa bakwai bakwai, ta yi su da tawassilin cewa Allah zai karɓa har cikin zuciyarta babu kokonto don ba’a yi wa Allah kokonto ta yarda da cewa muddin ya yi amfani da wannan ayoyin na tsawon kwana bakwai duk abin da ke jikinshi sai ya kau. Ba sai a zobo ba ko a cikin ruwan miya ko a cikin ruwan tuwo kai duk abu da mutum zai iya ci muddin aka yi ayoyin nan kafa uku uku ko kafa bakwai bakwai da yardar Allah ko niyyan sihirin ne aka yi maka ba zai kama ka ba bare wanda ke cikin jikinka.A gefe akwai ganyen magarya guda bakwai busassu ta cika farin bokiti surr da kyakyawar ruwa shima ta zauna yi mishi nashi a yayin da Abeeha ke tayata dura zobon a goruna don a sa a frigde. A cikin wannan bokiti mai dauke da magaryan ta shiga karata ayoyin kaman haka: Suratul Fatiha.Ayatul kursiyu.Suratul A’araf aya ta ɗari da shida zuwa ɗari da ashirin da biyu 106-122.Suratul Yunus aya ta saba’in da tara zuwa ta tamanin da biyu 79-82.Suratul kafirun kafa ɗaya.Falak da Nas ƙafa uku uku.Sai ta karanta wannan Adu’a:’Allahumma rabannas azhabal ba’as washfi antas shafi la shifa’un illa shifa’uka shifa’un la yugadiru saƙaman’ kafa uku.Sai ta rufe da ‘Bismillahi Urkika min kulli shai’in yu’uzika wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfika Bismillahi urkika’ shima kafa uku.Hawaye ne ya sauƙo mata bayan ta gama tsaf, ta sa hannu ta share tana Miƙewa tsaye tayi yakini akwai waraka cikin alqur’ani, ta yi yakinin saleem baya bukatar wani boka ko malami da waennan kaɗai Allah zai isar mishi. Sossai Mammi ta jinjina mata don bata bar sashen Mammin ba sai bayan isha, zobon duk a fridge na sashen suka shirya wanda ya kai gora hamsin ta ajiye ruwan ma lungun kujaran da Mammi ke zama a rufe.Sallama tayi wa Mammin zata fita Mammi tace “Ki bi sai ki ɗauka muku dinner ɗin ku daga kitchen na san Saraki yana chan yana jira don tun ɗazu ya yi min sallama”Da Toh ta amsa kan ta fice Mammi ta bita da kallo tana murmushi.A basket yanzu ma ta samu an shirya musu komai da komai ta ɗauka ta nufi sashen, ita dai wannan yanayi da take shiga ta rasa shi don tana tura kofan kamshinshi da ya cika parlorn ya sanar da ita yana ciki kaman kuwa ta chanka daidai don yana zaune kan kujeran dining gefenshi energy drink ne da yake kurba a hankali yana dannan waya fuskan nan babu ɗigon fara’a.Ajiye basket ɗin tayi tana tsoron yin magana ta yi laifi sai ta fara cire kwanukan tana shirya su a kan dining ɗin, ta tafi ta samo cutlaries da plates ta fito da su taje ta ƙaro ruwa da drinks ta kawo ta fara kokarin ajiyewa a lokacin ya ajiye wayanshi ya ɗaga ido ya kalleta sai ta nemi ruɗe wa garin ajiye ruwan goran sai ya faɗi ya Buge cup ɗinshi na energy drink da ta samu a wurin ya ɓare kan wayanshi… Wani irin zaro ido tayi ta zari wayan ta fara gogewa da hijabin jikinta tana furta “Innalillahi…”*Ban yi alkawarin na dare ba amma in har na samu dama za ku ji ni*

Back to top button