Fentin Zina Page 38 Hausa Novel
38.*****Kada ka soma wani negative tunani a cikin ranka! Ni mahaifiyar kace bazan taba yin abunda zai cutar da kai ba don haka nike so ka sani yadda na fada din dai haka za’a yi ko a fasa auren gaba daya.Da sauri cikin zabura yace a’a ammy baza’a yi haka ba zan gyara nan din saita zauna nasan kome zakiyi kina da daalilin yin hakan ba kuma zanyi miki musu ko gardama ba.Gyada kai tayi cikin jin dadi tace good naji dadi daka fahimce ni Allah ya maka albarka.Ameen yace. Ammy ta mike ta dauki hand bag dinta ta masa sallama ya mata a dawo lafiya.Lulawa duniyar tunani yayi bayan ta fita yana son gano dalilinta na cewar sai ya zauna a wannan gidan bayan ita da shi duka sun sani wannan ba burin shi bane a cewar shi gara a zauna a mutunta juna yafi. Nan dai yayi ta karanta wasikar jaki daga bisani ya koma tunanin sahibar shi da bai san wani hali take ciki ba gashi ko lambarta baya da ita take ya kuduri niyyar zuwa gurinta da yamma.*****ABDULTun ranar daya je gurin Ameena ta hado shi da guzurin magana yake ta faman jinyar zuciyar shi Koda zai iya jarumtar hakura da ita amma ya kasa gefe daya kuma maryam ta takura mishi rayuwa inda yayi dana sanin aurenta so babu adadi don yanzu abinci bai isa ya ci a gidan shi ba kuma bai isa ya fada mata taji ba, ya rasa ita din wace irin macece sannan shi kanshi yana mamakin kanshi ta yadda baya iya daukar mataki a kan abubuwan da take yi, a ranshi yana jin cewar alhakin Ameena ce ke dawai niya dashi, yasan ya zalunceta ya kasa mata uzuri a rayuwa akan abunda yake jarabawa a gareta wanda yasan babu wanda yafi karfin kaddara gashi wacce yake tunanin kamila ce ashe shigo shigo ba zurfi ta masa, ashe yaudarar shi tayi, ya gano hakan ne tun wata rana….FLASH BACK….Ya shigo falon yana nan dai babu gyara kamar kullum tun bayan barin ameena gidan, yakan ji takaici idan yazo ya samu gidan ba a gyare ba amma yana rasa meyasa a kwanakin nan yake shakkar maryam har wani tsoronta yake ji kuma baya tsallake maganar ta ko kadan.Shiga dakinta daya zama kamar bolar mahaukata yayi yadan rabe ya zauna a gefen gado yana kallonta kudundune cikin bargo, a zuciyar shi yace yau kuma dame tazo oho.Tsintar muryarta yayi tana cewa baby ka kaini asibiti cikina yana ciwo kamar zan mutu. Ta fada tana matsar ‘yar kwalla. Mikewa yayi yace ki same ni a waje ki hanzarta kinga yamma tayi sosai.Zaune suke a gaban likita suna jiran ya karanto musu sakamako sannan ya rubuta musu magani. Likita bayan ya kammala rubuce rubucen shi ya dago ya musu kallon tsap kamin ya maida idon shi kan takardar ya kuma dagowa ya kalli Abdul yayi gyaran murya yace.A sakamakon gwajin da mukayi mun gano cewar sanadiyyar amfani da fake hymen data yi shiya janyo ya narke a jikinta harya haifar mata da cuta(infection) a bakin mahaifarta wanda ya haifar mata da wannan ciwon cikin a yanzu haka zamuyi kokarin daurata akan magani sai kuma mu jira muga warkewar abun, shiyasa wasu asibitocin basu yadda suna dasawa mata fake hymen domin yana da hadari sosai ga lafiyar mace wanda hadarin ya hada da kumburin mafitsara, ciwon ciki mai tsanani da dai sauransu. Abdul ne yadan muskutayace am likita menene shi fake hymen din a takaice. Subn shi likita yayi yace fake hymen wata yana ce da turawa suka kirkireta domin matan da suka rasa budurcin su zasu iya amfani da ita don kada a gane ta taba samun kusanci da wani da na miji.Zufane ya shiga karyowa Abdul yana tsinewa maryam a zuciyar shi sosai kuma ya kuduri aniyyar yau din nan zata bar mai gida ashe dama ‘yar iskace bai sani ba, amma saidai me? Yana daga ido ya kalleta sukayi ido ciki ido da ita ya nemi wannan fushin ya rasa shi saima tausayinta daya ji ya ratsa shi sosai.Kyabe fuska maryam tayi tace baby kayi hakuri dan Allah idan muka je gida zan maka bayanin komai wallahi ba laifina bane tsautsayine ya fada kaina kada kayi fushi dani. Ta karasa tare da matsar kwallar data tatso ta don dole.Gyada kai yayi yace kiyi shiru kada kiyi kuka nasan ke din kamila ce baza ki yadda ki saida mutumcin ki da gangan ba, ya samu kanshi da fada a zahiri yana sakin murmushi amma cikin zuciyar shi wutar bakin cikine ke ruruwa ya rasa me yasa ya kasafada mata ainahin abunda ke ranshi so yake yaci mata mutumci ya koreta ya datse alakar dake tsakanin su amma bazai iya ba.Likita ne ya katse masa tunani da cewa ga magungunan priscribtion na nan a rubuce kada tayi wasa domin wannan cutar ba abar rainuwa bace idan bata samu treatment ba zai iya juyewa zuwa cervix Cancer don haka ku kula sosai and ka daga mata kafa sosai wajen mu’amalar aure zuwa lokacin dana dibar muku ku dawo a kara duba ta, Allah ya sawwaka.Mikama likita hannu yayi sukayi shaking hand ya mike Suka masa sallama suka fice.A mota maryam sai kuka takeyi tana fada masa karairayi don duk ya yadda da ita fyade aka mata tun tana karama kuma taji tsoron fada masa ne don girman son da take masa bata so ta rasa shi amma wallahi ba da nufi tayi ba, ire iren wadannan maganganun dai har saida yagaji da jinsu.Kamar an tilasta shi yace na yadda dake kada ki damu, dakyar ya fadi maganar inda makwagwaron shi ya bushe yana jin cewar karya ta shirga masa yayi imanin macen bariki ce kawai keda ilimin sanin fake hymen toh amma dayayi yunkurin fadin abunda ke ranshi sai wani abu ya taso kamar gingirman dutse ya danne sai ya tsinci kanshi da fadin sabanin tunanin shi. Da haka suka iso gida tun daga wannan ranar ta maida shi mijin tace sai yadda take so haka ta hanashi wani katabus a Cikin gidan. Amma duk da haka kullum da tunanin Ameena yake kwana yake tashi acikin ranshi wata ran yayi kuka har ya gaji ya rarrashi kanshi kuma ya rasa wanda zai fadawa yaji dadi gashi anas fushi yake dashi tun lokacin can da suka samu sabani akan Ameena.DAWOWA KAN LABARIShiga falon yayi bayan yayi sallama bai damu da said an amsa ba domin ya san ba za’a amsa din ba, kamar kullum yau ma falon a hargitse yake, kutsa kai ciki yayi kamar zai wuce dakin shi yayi kwanciyar shi sai wata zuciyar ta fada masa ya leka dakinta ta san ya dawo domin ba lokacin daya saba dawowa bane yanzu, yau din ma zazzabi yake ji sosai a jikin shi.Dafa bangon dakin yayi sakamakon sautin daya ji na tashi daga dakin matar shi ta sunnah hadi da dafe kan shi dake barazanar rabewa biyu saboda tsananin azabar ciwon kan dake damun shi.Wasu sautuka ne na muryoyi guda biyu ke tashi daya na matar shi dayan kuma na wata ce da bazai iya tantance wacece ba, kasa kunne yayi a bakin kofar da kyau ta yadda maganar zata iso masa yadda ya kamata.Daga ta cikin dakin maryam tace cike da damuwa tana duban kawar ta, wallahi besty wannan abun ya fara isata ina jiyewa kaina tsoron kada kasana ya rube don ruwan dake zuba mun gaskiya ya soma yin yawa sannan ma har wari yake yi kadan kadan.Kawar tata ta dafa ta tace kawata kenan kada ki damu magani kawai zaki nema dama kashe kudine kuma kina da masu kashe miki. Ga mijinki ga kuma sagir duka fa zasu nema miki lafiya domin lafiyar taki zata amfane su su duka.Hum! Baza Ki gane bane yanzu fa sagir rabona dashi tun sanda yace mu hadu a hotel kamar yadda muka saba na fada masa ga lalurar da take damuna yaja baya dani kon kira shi ma bai cika dauka ba abun yana damuna kuma ina son shi sosai kin sani yanzu ni gaba daya ma na rasa yadda zan bullowa al’amarin har gara Abdul zaiyi abunda duk nasa ka shi tunda yana karkashin iko nane daga ranar da boka yamun aiki akan shi kinga shi zan iya cewa bani da matsala dashi amma duk da haka hankalina a tashe yake.Mikewa sukayi dukkansu tsaye a firgice suna kallon kofar da aka banko kafin wanda ya banko tan ya bayyana.Kusan zubewa maryam take neman yi a kasa sakamakon tozali dashi data yi da yadda fuskarsa ta sauya a tamke babu ko digon fara’a ga yadda idanun shi suka kada sunyi jajur tamkar an zuba borkono, take zuciyarta ta ayyana mata yaji maganganun da sukayi yanzunnan, wani irin kugi cikinta ya bada sauti tsabar tsoronsa da bata taba tsammani ba ya kamata ta soma haki, itama kawar haki ne na tsorata takeyi.Binsu da kallo yayi daya bayan daya kafin ya tsaida idon shi kan maryam zuciyar shi na tafasa yana jin tamkar ya rufe ta da duka amma yana kokarin daidaita kansa ta yadda bazai yi mummunan abu gareta ba, yace nayi nadamar sanin ki a rayuwata na tsane ki kuma abunda kika yi mun Allah zai mana hisabi ranar kiyama kije na sake ki saki daya.Yana gama fadin haka ya juya zuciyar ahi cike da tarin damuwa da kunci gefe daya kuma nadama ce fal a tare dashi yana da yakinin hakkin Ameena ce ke bibiyar shi don haka yana bukatar neman yafiyar ta da gaggawa, bai iya zama a gidan ba ya fice gaba daya bayan yaja motar shi da gudun tsiya.Gudu yake shararawa a titin har saida yayi nisa sosai kamin ya pafa a gefen titi ya kifa kanshi a steering motar yana mai sakin kuka sosai, ya jima yana kukan har sai da yaji nauyin dake zuciyar shi ya soma raguwa sannan ya tsagaita kukan ya dago kanshi, sanin cewa bai san inda zaije ba ya sanya shi komawa baya kadan inda ya wuce wani hotel ya shiga, direct ya wuce reception ya biya kudi ya karbi key din daki ya haura sama dake gidan sama ne ya bude ya shiga ya ciccire kayan shi ya fada ban daki.Wanka yayi ya fito daure da karamin towel a kugun shi bai nufin shafa koda mai ba tsabar damuwar dake addabar zuciyar shi, kwanciya yayi akan gadon bayan shi yana kallon POP din dakin yana tunani.Maryam kuwa tunda ya fita ta dora hannu akai tana wayyo na shiga uku meke shirin faruwa dani ne? Dan Allah kice dani mafarki nake yi bai kamata inga haka ba, wayyo Allah na yanzu kenan yaya zanyi?..Maryam kenan kaddara ta riga fata amma yanzu ki sani bakin alkalami ya riga ya bushe, yanzu abunda ya kamata kiyi shine ki tashi ki debi ‘yan kayyan bukatunki mu fice daga gidan kafin ya dawo.Da mamaki maryam ta kalli kawar tata tace ban fahimce kiba kamar naji kina cewa mu tafi? A zatona zamu jira ya dawo ne ki tayani rokonsa ya mayar dani daki na kafin kowa yaji ko yasan abunda ya faru.Murmushi kawar tayi tace kekam dai wasu lokutan kina bari kanki yayi murfi. Kina ganin a yanayin da yake idan har ya dawo ya sameki a gidan nan tun kafin ya huce daga fushin da yake yi zai iya karasa sauran igiyoyin dake tsakanin ku shiyasa nace miki muje daga baya zamu san yadda zamu bullowa al’amarin ina fatan kin gane?Gyada kai maryam tayi tace sai yanzu na gane kinsan ina cikin tashin hankali ne banson na rasa shi kinsan dai nan din shine rufin asirina, rabuwata dashi tonuwar asiri nane.Kada ki damu komai zai daidaita.***~**AMEENATana zaune a shagonta kamar kullum da yamma tayi shiru kamar ta fada dogon tunani a jikinta taji kamar ana kallonta a hankali ta dago ta sauke a saitin kofa.Caraf idanunsu suka sarkafe waje daya yayinda yake tsaye ya harde hannayen shi wake daya yana jifanta da wani irin kallo mai wuyar fassara.A tsorace cikin faduwar gaba ta mike ta soma jada baya tana girgiza kai cikin tamke fuska kamar bata taba sanin meye annuri ba………………EESHERT ADAMU


