Uncategorized

Akan Aikina Complete Novel Documents

Malam! Malam!! Malam!!! fito kaga i’kon Allah yarinyar nan ta suma, Malam ya fito da gudu yana kallon yarinyar ya kalli Inna Majaifiyarta yace maza ki d’auki Mumtaz ki  ku fito bari in kirawo Alhaji mu tafi asibiti,Sunan yarinyar kenan Mumtaz.

   Kafin Malam ya dawo Inna ta kalli k’afar Mumtaz sai taga jini yana malala kamar ruwa da gudu ta fito k’ofar gida tana kiran Malam.

  Wace ce Mumtaz ?

Mumtaz dai shine asalin sunan ta wanda Mahaifinta ya saka mata saka makon sunan Mahaifiyarshi ne ya saka wa Mumtaz, Asalin Malam Abdullahi Mahaifin Mumtaz y’an jihar Bauchine wanda sun kasance y’an kasuwa ne sosai gidansu suna siyar da kayan masa rufi ta hanyar ne suke samun na cin abinci kuma i’tace hanyar abincin su.

     Kwatsam sai karayar Arzik’i ta samu mahaifinsu Malam Wannan abun ba k’aramin tada musu da hankali yayi ba.

  dalilin da yasa karayar Arzik’i ta same shi shine Mahaifinsu su Malam Wato  Alhaji Jibrin shine yanada wani aboki d’an asalin Maiduguri Alhaji Bukar kusan ma Amininshi shi ne sana’ar Alhaji  Bukar shine siyar da dabbobi daga wannan gari zuwa wannan gari.

    Kwatsam sai wataran Malam Bukar yakawowa abokinshi Alhaji Jibrin ziyara yaga yadda ya bunk’asa da kasuwancinshi na siyarda kayan masa rufi.

    Abun ya tsayawa Alhaji Bukar har yaushe Jibrin zai zama haka a kasuwanci bayan ya fishi tunda ga nan Alhaji bukar ya kafawa abokinshi Jibrin tsana mai tsanani Ya fara bin bokaye don ya raba shi da dukiyarshi,Har yayi nasarar rabashi da komai nashi ya zamo duk abunda ya tab’a sai yayi asararshi tun daga wannan lokacin Alhaji jibrin Mahaifin Abdullahi ya shiga wani mummunan talauci ya zama na koda kayan da zaisa ma sun fara lalacewa sai ya shiga wanka sun bushe sannan ya saka su.

    Ana haka wataran Alhaji jibrin ya fita neman tai mako gidan wani mai kud’i kawai sai ya jiyo kukan wata jaririya cikin bolar kusa da k’ofar wani gida kamar zai wuce kuma sai ya dawo ya duba yaga jaririya ce aka yar kyakkyawa da’ita kamar y’ar larabawa ya d’auketa hannunshi yana kakkarwa ya nufo gida,yana zuwa gida ya nunawa matarshi Adama mahaifiyar Abdullahi da yake ita kad’ai ce matarshi kuma Abdullahi shi kad’ai ne D’an ta don haka koda Alhaji jibrin ya kawo mata wannan jaririya ba k’aramin jin dad’i tayi ba sosai don haka ta rik’e yarinyar da hannu bibbiyu…

WRITTEN BY:      RABI’ATU B. ABDALLAH

NOVEL NAME:   AKAN AIKINA

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         186KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      30- JUNE -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE 

Proceed To Download Akan Aikina Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 1”

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 2”

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button