Ruwan Zuma Page 49 Hausa Novel
(49) Alhaji Sammani ya dubi ‘yayan nasa ya fara magana kamar haka, “Aliyu Haydar ban yi rayuwa da kai ba amma a ‘yan awannin da na kasance tare da kai na lura kai mutum ne mai hankali, nitsuwa da kuma dattako. Ina da labarin duk abun da Abdul yayi maka tare da kuma matarka bai 6oye mini komai ba, yayi laifi matuk’a wanda nima nayi fushi dashi bana wasa ba saboda yayi amfani ne da k’arfin arzikin da na tara wajen aikata sharri gare ku. Ban ji dad’in abun da yayi ba, kuma na mishi fad’a, sannan na mishi nasiha duk don in nuna mishi laifin da yayi ba kad’an bane. Dalilin da yasa na tara ku a nan shine don in baka hak’uri a kan duk wani abu da Abdul ya muku sannan ina neman mishi yafiya a gurin ku ba don ya cancanci a hakan ba sai don ina tsoritar masa fushin Allah da kuma girman alhakin ku daya d’auka. Abdul yayi nadama ya kuma yi dana sani a kan gur6ata tarbiyyar d’an matarka da yayi, wallahi rana bata gushewa kullum sai ya sanar dani irin tsanar kanshi da yake yi a kan laifukansa a gareku. Ka yafewa d’an uwanka sannan ka mishi jagora ya nemi yafiyar matarka da kuma yaron idan har zasu iya yafe masa. Don Allah kar hakan yasa zumuncinku ya 6aci tun kafin a k’ulla, ku kad’ai Allah ya bani wanda nake fatan ko bayan raina zaku had’a kanku ku zama tsintsiya mad’aurin ki d’aya. Hakan kuma ba zai faru ba har sai kun sasanta junanku kuma kun yi hak’uri da duk abun da ya faru a baya. Rok’on ka nake yi Aliyu Haydar ba wai ina baka umurni bane, sannan a yau idan ka nuna ba zaka iya hak’urin ba wallahi zan fahimceka saboda Abdul ya yi laifin da ya wuce minzali ya wuce gona da iri.” Tun da Baba ya fara magana Haydar kanshi ke k’asa yana jin ina ma basu d’auko maganar ba a wannan ranar, saboda shima a yau ya samu labarin makircin Alhaji Abdul wanda yake jin shi sabo a zuciyarsa. Sannan da ba don a gaban Baba suke ba da ya yiwa Alhaji Abdul abun da yafi na Madu, yanzu ma ya tsani ganinsa balle har ayi tunanin zai iya yafe masa duk da cewa bashi ya cuta ba kai tsaye. Amma ai jinin Laila jininshi ne, Abul danginshi ne na jini sannan d’an matarsa ne. Kuma ko ya iya yafe mishi Laila da Abul baza su ta6a yafe mishi ba dalilin mugun cutar dasu da yayi. Sannan ta yaya zai iya huld’a dashi a karo na biyu har yarda da amincin da Baba yake fata ya wanzu a tsakaninsu? Ai abun kamar da wuya wai gurguwa da auren nesa. Haydar kasa cewa komai yayi dalilin kunya da kuma ganin girman Babansa da Alhaji Shettima da yake yi. Ina zai iya kallon tsabar idanunsu yace ba zai iya hak’uri da d’ansu ba? Ya san cewa Alhaji Abdul yafi samun gurbi mafi yawa a zuciyar Babansu, saboda shi kad’ai Baban yake gani a matsayin d’a, shi kuma rana tsaka da bayyanarsa ba zai sa a yi mishi wannan soyayyar ba saboda rashin sabon dake tsakaninsu. Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji Shettima yin gyaran murya ya ce, “I understand how you feel Haydar, sannan zai fi kyautuwa mu baka lokaci kayi tunani a kan hakan. Sai dai don Allah zamu rok’eka kar ka bari wannan abun da ya faru ya shiga tsakaninka da d’an uwanka, kayi fushi, kayi fad’a amma kar ku raba zumunci. Allah ya baka hak’uri Haydar.” “Amin.” Kawai Haydar ya iya cewa amma bai d’ago kanshi ba. Alhaji Abdul da tun daya shigo gidan yake jin k’aunar k’anin nasa yace, “Kayi hak’uri da duk laifin da na aikata a gareka da kuma dangin matarka, nayi nadama sannan baku cancanci hakan daga gareni ba ko da kuwa kai ba jinina bane. Ina rok’an yafiyarka sannan ina neman ka mini izini zuwa gidanka in bawa Laila hak’uri kuma in nemi yafiyarta. Kar kasa a ranka zan k’ara kallon Laila mai nuni da soyayya, wallahi tun ranar da na gane kai k’anina ne na ji na hak’ura da ita saboda k’aunar da nake maka zai iya sawa in bar maka komai ko da kuwa zan rasa raina ne. Hakan yasa na yanke shawarar barin duk wata dukiya da Baba ya damk’a mini ta dawo hannunka, sannan zan yi nisa da ku, nisa mai yawa saboda I want you to feel free and secured. Lu’a Ventures an ginashi ne da sunan da Baba ya rad’awa Ammi, sauran companies d’inmu na kayan gine-gine da kuma yin kwangila duk sun dawo k’ark’ashin ka sai yanda kayi dasu. Sannan zan iya rantse maka da sunan Allah babu haram a cikin dukiyar nan, sai dai a daa na kashe da yawa daga cikinta ta hanyar neman mata da shan giya wanda a yanzu na daina har abada kuma ina so ku tayani da addu’a Allah yasa kar in koma halina na da. Ina son barin duk rayuwar da nayi a baya amma hakan ba zai yiwu ba har sai na samu sauk’i game da sukuni a zuciyata ta samun yafiyarku. Don girman Allah ka yafe mini.” “Na yafe maka duniya da lahira, zaka iya zuwa ka nemi yafiyarta da kuma Abul saboda sun fi cutuwa sama da ni. Bana buk’atar dukiyar ka sannan kar kace kaima zaka tafi domin hakan ba zai gyara komai ba, and Baba will always need you.” Baba da Alhaji Shettima farin ciki ne fal a ransu musamman Baba da yake taraddadin lalacewar zumuncin ‘yayansa, ya ce, “Allah ya muku albarka ya had’a kanku ya kuma shiryi yaron.” “Amin.” Kowa ya amsa kana suka cigaba da tattaunawa game da dukiyar da Alhaji Abdul yace zai barwa Haydar yayin da shi Haydar d’in ya kafe da cewa baya so kuma baya buk’atan hakan. Ganin jayayyar ta yi yawa yasa Baba ya dakatar dasu kan a bar maganar sai daga baya. A nan ya dubi Haydar yace, “D’ana tun lokacin da Ammin ka ta bayyana na nemi ta amince a mayar mana da aurenmu, dalili kuwa bayan 6acewarta da shekara biyu na saketa saki d’aya saboda bana son tana yawo da aurena a kanta. Na san zaka ji haushin rayuwar da muka yi a baya wanda bana fatan a sake furtawa saboda k’azantar dake ciki ta yawaita har ta ta6a d’ana Abdul wanda shima yanzu yake nadamar halayyarsa. Duk yanda na kai ga neman ganawa da ita ta hana k’arshe cewa tayi in barta da halin da take ciki na 6acewarka, a yanzu da ka dawo ina so kai ka mini iso gareta da ‘yan uwanta don in samu aurenta wannan karon cikin mutunci da albarkar iyaye.” Haydar zai iya cewa wannan ne magana mai dad’i da yaji tun zaman su a wannan falon, domin kuwa baya son Ammin shi ta k’are a haka babu aure duk da cewa ita ma rayuwar da tayi a baya ta k’azanta kuma Allah Ya nuna mata kuskurenta ta hanyoyi daban-daban. Ya sani cewa itama ta yi nadamar halin da ta saka kanta a ciki domin yana tuna nasiharta a gareshi akan ya nisanta kanshi daga aikata zina domin tana wargaza rayuwar mutum ta kuma hana shi samun rahamar Allah, hakan yasa ya taso baya ko sha’awar zina balle har ya aikata. Zai d’auki hakan a cikin rahamar Allah saboda daga Babanshi, mamanshi har yayanshi basu kaucewa wannan k’addarar ba. Kenan shi Allah ya ku6utar dashi ya kuma mishi Rahama da har ya bashi Laila ya kuma bayyana mishi ‘yan uwansa da dangin shi a lokacin da bai yi tsammani ba. Murmusawa Haydar yayi yana godiya ga Allah da ya nuna mishi wannan so da k’aunar yace, “Baba ka saka rana in maka jagora zuwa Maiduguri neman auren mahaifiyata a karo na biyu. Allah ya bar ku tare.” Laila ce zaune a falo da yamma tana jiran mijinta wanda take mugun kewa tare da son kasancewa tare dashi ta ji shigowar motarshi cikin gidan, ai da sauri ta mik’e ta bud’e k’ofar falon ta fita zuwa gareshi. Da kanta ta bud’e mishi marfin motar ta rik’o hannunshi ya fito yana dariya, rungumeshi tayi tare da sanya hancinta a wuyanshi tana shinshinarshi kamar mage. “Da alama an yi missing d’ina. I missed you too Matata.” “Ka dad’e da yawa, wallahi don kar ‘yan uwanka su ce ina damunka ne da nayi ta kiranka ka dawo gida.” Ta fad’a a shagwa6ance tana dukan k’irjinshi a hankali. “Matar Haydar kina da sakalci.” Ya ja hancinta ta kai baki ta ciji hannun. “Kin d’auki bashi. Ga kad’an daga cikin ‘yan uwana sun zo gaisheki, mazan suna waje.” Ya fad’a yana juyar da Laila ta fuskanci bakin gate d’insu. Laila daskarewa tayi cikin kunya ganin ‘yan uwan Haydar mata suna kallonsu suna murmushi, domin da alama sun ga duk abun da ya faru. “Baka kyauta mini ba Haydar. Meyasa baka fad’a mini cewa ba kai kad’ai bane?” Ta fad’a a hankali yanda shi kad’ai zai ji tana murmushin yak’e ga bak’in, amma a ciki ranta ji take yi kamar k’asa ta tsage ta shige ciki. “Bismillah ku iso.” Yace dasu yana share Laila wacce take jin kamar ta muntsine shi. “Sannunku da zuwa, mu isa falo.” Ta musu jagora zuwa falo Haydar na take mata baya yana tsokanarta ta shareshi. Cikin d’aki Laila ta shiga ta sanya hijabi sannan ta dawo falo suka gaisa da mutanen cikin fara’a. Yayarsu Aisha ta dubi Laila sosai tace, “Kamar kece mai shagon Laila Beauty ko?” “Ni ce, kina zuwa ko?” Ta fad’ad’a fara’arta ganin Aisha babba ce kamar ta. “Na je sau uku amma sau d’aya na ta6a hangoki a cikin office d’inki. Ina jin dad’in aikin ku wallahi, shiyasa every month a can nake gyaran jiki.” “Na ji dad’in hakan sosai, next time in kin tashi zuwa ki fad’a mini a miki special gyaran mu na Shuwa, duk da cewa ba kowa muke yiwa ba.” Ta k’arisa maganan tana tashi tsaye zata kawo musu ruwa. “A yi haka Aunty Laila? To nagode sosai. In ruwa zaki kawo mana wallahi ki barshi saboda daga gida muke.” Ta fad’a ganin Laila tayi hanyar kitchen. Har Laila zata yi magana Haydar ya shigo tare da mazan wanda su basu samu gurin zama, suka tsaya a tsaye suka gaisheta cikin mutunci tana amsawa cikin fara’a. Akwai wani saurayi daga cikin mazan wanda yana gaishe da Laila ta ganeshi ta ce, “Kamar na gane ka.” Murmusawa yayi ya sosa k’eya ya ce, “Abul classmate d’ina ne. Na ta6a zuwa gidan nan sau d’aya ya mini assignment, amma ya jima fa.” “Allah sarki, ni dai daga ganin fuskarka na gane cewa na sanka. Ya gida ya su Mamanka?” Nuna Aunty Aisha yayi yana cewa, “Ga Maman nawa.” Laila ta dubeta cikin mamaki tace, “Ai idan aka ganki baza a yi tsammanin kin haifi kamar shi ba. Masha Allah.” Aunty Aisha cikin jin dad’in yabata da Laila tayi tace, “Ai kuwa kema baza ayi tsammanin kin haifi d’a kamar Ahmad ba. Ina Abul d’in?” Ta tambaya cikin rashin sanin ainihin abun da yake faruwa, da yake Haydar bai fad’a musu komai ba. Haydar da yake hira da sauran ‘yan uwan nashi amma hankalinshi na kan hiransu yayi saurin cewa, “Yana Maiduguri.” “Ayya. To zamu tafi sai wani lokacin kuma. Tun da yanzu kam an zama ‘yan uwa za’a dinga ziyarta juna Insha Allah. Saka mini numbern ki a nan.” Aisha ta mik’awa Laila wayarta. Sauran suka fita suna yaba k’amshin da gidan yake yi kamar wanda ake gogewa da ruwan turare. Ahmad classmate d’in Abul kuka d’an Aunty Aisha ya riga ya fita amma ya dawo baya ya cewa Laila ta bashi number Abul. Babu musu ta bashi na Kaala Abdi tana cewa, “Abul bashi da waya a hannunshi, amma ga na Kakanshi zaka sameshi ta nan.” Godiya ya mata tare da mata sallama ya fita sauran ma suka bishi a baya suna yaba karamci irin na Laila. Matan ne suke k’us-k’us d’in cewa Haydar ya auri wacce ta fishi shekaru amma Aunty Aisha ta tsawatar musu, tace kar ta sake jin sun yi hirar saboda ba zai ji dad’i ba sannan babu ruwansu a kan private life d’in wani matuk’ar bai sa6awa shari’a ba. Shiru suka yi amma wasu a cikinsu kallon juna suke yi suna dariya a kan cewa maganar bata k’are ba zasu k’arisa a gida. (Mutane kenan kowa da halinsa, sannan ba zai ta6a yiwuwa kowa ya mara maka baya kan abun da kake yi ba, dole ka samu mai kushewa ko da kuwa ciki d’aya kuka fito). Sai da suka watse Haydar ya jawo Laila jikinshi suka koma falo yana bata labarin yanda yinin nashi ya kasance a cikin ‘yan uwansa. Kitchen suka shiga ta bashi juice d’in kankana da madara da tayi ya fara sha ya tsaya da surutunsa. “Laila baki ta6a mana irin wannan abun ba.” “Ka manta dai.” Ta fito ya biyota a baya amma kafin su isa falo ya shanye, hakan yasa ya koma kitchen ya k’aro sannan ya dawo ya zauna kusa da ita yaci gaba da labarin tana sauraronsa da dukkan hankalinta. Ajiye kofin yayi a kan cinyarta bayan ya gama shanyewa ita kuma ta ajiye a k’asa tace, “Sun burgeni wallahi, suna da sauk’in kai ga kuma saurin sabo da mutune. Na san zan ji dad’in kasancewa cikinsu.” Gyad’a kai Haydar yayi cikin yarda da furucinta amma zuciyarsa ta kasa nitsuwa dalilin maganan Alhaji Abdul da yake son ya bijiro mata dashi wanda a da bai kawo mata ba. Gyara zaman shi yayi kana ya dubeta da kyau ya fara magana kamar haka, “Ba lallai bane ki ji dad’in abun da zan furta ba, amma ina so kar kiyi fushi ko kuma ki mini wani zato na daban. Laila an zaunar da ni tare da Alhaji Abdul wanda a yanzu yake Yaya a gareni domin a sulhunta mu, na yafe mishi amma na fad’a musu cutar da ku da yayi bani da hurumin tilastaku ku yafe mishi saboda yayi yawa. Shi da kanshi ya nemi izinin zuwa gurinki don ya nemi yafiyarki tare da Abul, na kuma bashi damar hakan amma sai kin yarda cewa zaki iya ganinshi.” “Bana son ganinshi Haydar, wallahi wancan karon ma don na rasa yadda zan yi ne na nemeshi. Ka fad’a mishi na yafe mishi, kuma ina fatan dalilin yafe mishi da nayi Allah ya ji tausayina ya shirya mini Abul. Ya ci darajarka da kuma girman Babanku da nake gani.” “Nagode Laila. Allah ya biyaki da mafificin alkhairi ya kuma shirya Abul.” Haydar ya fad’a cikin farin ciki wanda har yana mamakin murnar me yake yi. Sai dai tunawa da yayi cewa wai a kan d’an uwansa kuma jininshi ake magana yasa ya tabbatar da maganar Bature da yake cewa ‘blood is thicker than water’.“Amin.” Ta amsa tana kallon yanda farin ciki ya bayyana a fuskarsa. Wai dama ance komin lalacewar hannunka baza ka yanke ka jefar ba. “Zamu je Maiduguri nan da kwana uku neman auren Ammi.” Ya sanar mata yana jawota jikinshi. “Damuwar 6acewarka yasa Ammi ta kasa sauraronshi wallahi, amma ni na sani tana son mijinta bata daina ba. Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu baki d’aya.” “Amin Matar Haydar. Ni fa ina jin yunwa.” “Akwai abinci dana maka tun da rana, mu je in saka maka.” Ta yunk’ura da niyyar tashi tsaye ya dawo da ita jikinshi yana aika mata zafafan sak’onni yace, “Ba wancan ba, wannan.” “Shima akwai idan kana so.” Kwana uku da haka Haydar, Laila, Sabrin, Baba, Alhaji Shettima da wasu ‘yan uwansu maza hud’u suka tafi Maiduguri ta jirgin sama. Laila dai kunyar Baba take ji dalilin ya zo gidansu washe garin da Haydar ya had’u da ‘yan uwan nasa, yayi mata shopping sosai na kayan kwad’ayi wai a bawa Baby. Wannan kunyar yasa ta saka Haydar ya kama musu Hotel daban duk ta cewa ta rok’eshi ya barta ta dinga kwana cikin ‘yan uwanta amma ya nok’e kafad’a yace, “Ina jin tsoron kwana ni d’aya ne, and you’ll never know ko Baby zai buk’aci yayyafi.” Dolenta ta adana kayanta a hotel d’in da ya kama sannan suka dunguma suka wuce family house d’in su inda ita kuma Sabrin zata kwana. Su Baba kai tsaye a falon Kaala Abdi aka yi musu masauk’i tun da dama an san da zuwan su, su Haydar kuwa cikin gidan suka shiga in da ‘yan uwansa suka taru suna jiran isowarsu. Soyayya kam ya gani a ranar har ya rasa in da zai sa kanshi, Ammi dai na gefe kusa da Ummii sai kallonshi take yi tana murmushi kamar wacce aka yiwa bushara da babban kyauta. Laila itama hankalinta na kan d’anta Abul, tana gama gaisawa da ‘yan uwa ta nemi a mata jagora zuwa gurin da Abul yake. Sai da aka bud’e mata gurin da mak’ullin sannan ta shiga ta sameshi yana zaune yana zane a wani sketch book, shigowanta yasa ya d’ago kanshi ya dubeta na wasu sakanni sannan ya koma ga abun da yake yi ba tare da yace da ita uffan ba. Guri ta samu kusa dashi ta zauna tana lek’en zanen da yake yi amma ya rufe yana harararta, ita kuma ta murmusa tace, “Abul babu gaisuwa ne?” “One of my classmate called, kina fad’a musu cewa ina Maiduguri an kulle ni ko?” Ya yi maganar cikin 6acin rai wanda hakan bai sa Laila ta yi ko gezau ba. “Ya tambayeni ina kake nace ka je Maiduguri hutu kuma babu waya a hannunka, shi ya fad’a maka nace an kulleka Abul ko dai you are just assuming things?” Ta kafeshi da ido wanda hakan yasa ya kawar da nashi ba tare da ya amsa mata ba. “Baka son mutane su san halin da kake ciki ne?” Ta k’ara mishi wata tambayar wacce tasa ya dawo da hankalinshi kanta ya ce, “I don’t care. Ki fad’awa Kaala Abdi ya sakeni in koma gida saboda na daina shan kayan maye kuma ba zan k’ara sha’awar yi ba.” “Why can’t you just leave?” “Because I can’t! Kullum idan nayi yunk’urin guduwa sai in ji bazan iya ba, nasan shi yayi mini tsafi ya zaunar dani guri d’aya.” Murmushi Laila tayi wanda har ya bayyana hakwaranta tace, “Kaala Abdi ba ya yin tsafi Abul, addu’a yake maka.” Bai ce komai ba illa tashi da yayi ya shige d’akin da yake kwana ya barta a gurin ita d’aya. Ta jima tana zaune tana tunani sannan ta tashi ta fita bayan ta masa sallama amma bai amsa ba. Laila tana komawa ta samu Mas’ud ya kira wayanta har sau biyu, gefe ta koma in da babu hayaniya ta kirashi, “Kun isa lafiya?” Ya tambayeta. “Lafiya kalau Alhamdulillah. Ka kira bana kusa na je duba Abul.” “How is he?” “Yace baya sha’awar kayan maye Mas’ud, wannan magana tasa naji dad’in da baka tsammani. Baka tunanin ya kamata a sakeshi ya dawo gida? Ni fa ina ganin ya nitsu.” “Dama Kaala Abdi yace ya bar kayan maye har abada, amma halinsa na rashin ganin girman mutane shi suke aiki a kai, and you have to trust him kar ki matsa masa a kan ya sakeshi.” “Na isa Mas’ud? Ai ni duk yanda yayi bazan musa ba, ko shekara yace Abul zai k’ara yi yayi daidai.” “Bayan tafiyanku Madu ya zo ya sameni a shago ya nemi mu matsa gefe zai yi magana da ni. Kalti ashe duk shirun nan da muke ji game da case d’in Madu a kotu Alhaji Abdul ne ya shige masa gaba. Shi ya fad’a mini cewa ya biya marayun kud’insu da suke binshi dama saura kad’an, sannan an bar mishi gidansa ba’a sayar ba. Sai dai an k’ar6e shagon yaran da yake hannunsa yanzu ya zama bashi da komai Kalti. Yanzu so yake yi ki saka baki Ummii ta yafe mishi sannan ya dawo su ci gaba da zama kamar da, ya kuma yi alk’awarin canja halayyarsa gareki kuma kema yace ki yafe mishi.” Shiru Laila ta yi tana mamakin al’amarin rayuwarsu da kuma yanda ya canja a lokaci d’aya duk da cewa itama a wani gurin Allah ya kamata da laifi kuma ta tuba. Su kuma su Madu a da sun ci nasara a kanta sun hanata sukuni amma sai gashi yau su suke neman yafiyarta da yardarta. Wai dama an ce duk wanda ya rik’e Allah ba zai ta6a ta6ewa ba. “Tun da na iya yafewa Alhaji Abdul zan iya yafewa Yaya Madu. Ka fad’a mishi na yafe mishi amma shi ya sani bani da wani power a gurin Ummii da zan iya mata magana ta ji, har da laifinsa a ciki wajen ganin na taso babu shak’uwa tsakanina da ita. Tun da tafi sonshi ta kuma fi jin maganarshi yayi k’ok’arin ta koma gidanshi amma ni babu bakina a ciki.” “Kin burgeni Kalti, kuma hakan yayi daidai. You can’t eat your cake and have it.” Fad’in Mas’ud yana dariya a hankali cikin farin ciki. Magana suka k’ara yi na wasu mintuna sannan ta kashe wayarta ta koma cikin mutane ta ga ana shigowa da goro da minti, ko ba’a fad’a ba tasan auren Baba da Ammi aka mayar domin su da shirinsu suka zo bayan Kaala Abdi ya nuna musu cewa zai basu aurenta. Laila ta duba cikin jama’ar don tana son ganin farin cikin da zai kasance a fuskar Ammi amma bata ganta ba, ko da ta tambayi wata ‘yar uwarsu inda Ammin ta ke cewa tayi Kaala Abdi yayi kiranta tun lokacin da ita Lailan ta tafi gurin Abul. Laila ta san a yanzu Haydar na cikin murna saboda yana son a mayar da auren mahaifansa bana wasa ba, hakan yasa shi da kanshi ya kira Kaala Abdi ya sanar dashi halin da ake ciki sannan ya nemi a d’aura musu aure a ranar da zasu zo. Itama Ammi shi Haydar d’in ne ya yi magana da ita a kan ta amince a d’aura auren, dama k’addara ce tasa ta rabu da mijinta ba don ta daina sonshi ba babu musu ta amince har ta fara amsa wayar Baba suna gaisawa. Gida tuni ya zama gidan biki sai d’aura tukwane ake yi ana sauk’ewa, Haydar kam kamar yafi kowa murna domin shiga da fice yake yi tsakanin waje da cikin gida bakinshi har kunne yana mu’amala da ‘yan uwansa ana kuma fad’a mishi sunayensu da kuma dangantakarsu. Da dare Haydar ne zaune a bakin gadon Ammi yana had’a mata kayanta wanda zata tafi dasu Abuja washegari tare da Baba yana mata hira, ita dai tayi zugum tana sauraranshi. Ganin ta dad’e bata yi magana ba yasa ya d’ago kanshi ya dubeta yaga ta zabga tagumi tana kallonshi. Jikinshi ne yayi sanyi ya dakata da abun da yake yi yace, “Ammi ko dai bakya son auren ne?” Girgiza kanta tayi ta murmusa kad’an ta ce, “Bana son k’ara yin nisa da kai ne Ali, tun tafiyar ka zuciyata ta kasa sukuni ina fata da kuma addu’an Allah Ya bayyana mini kai in cigaba da rayuwa da kai, sai kuma gashi daga ganinka yau wai zan k’ara yin nisa da kai. Idan kuma nace maka bana farin ciki da komawana d’akina na maka k’arya, kana nesa ina nesan ne bana so wallahi.” Ta k’arisa maganar fuskarta zallan damuwa. “Shine damuwar ki?” Ya matsa kusa da ita yana rik’o hannayenta. Gyad’a kai tayi hawaye na cika a idanunta tace, “Shine.” “Ki daina damuwa Ammi saboda duk in da kike a fad’in duniyan nan kina raina kamar yadda na san nima zan kasance a ranki. Dama kuma dole ne akwai lokacin da zai zo ni da ke zamu yi nesa da juna a dalilai irin haka Ammi, amma idan kin tuna cewa ba mutuwa bace sannan kuma zan iya ziyartarki haka kema zaki iya ziyartata zaki ji sanyi a ranki ki gane bamu rabu ba muna nan tare. Idan Laila ta haihu zan baki d’an ki rik’eshi kina kallonshi a matsayin ni.” Ya k’arisa maganan cikin zolaya ba tare da ya gane Ammi ta d’auki maganar har zuciyarta ba. “Shikenan na yarda, Allah ya maka albarka ya k’ara zaman lafiya a aurenku. Ali kai d’a ne da kowacce Uwa zata yi alfaharin samu, Allah ya bar mini kai ya k’ara mini tsawon rai in ga ‘yayanka har da jikokinka.” Dariya yayi ganin fuskarta ta washe tana jindad’i yace, “Ameen Ammina. Ki tashi mu tafi Baba yana jiranki a waje, kinsan jirgin safe kuke dashi.” Gyad’a kai tayi kana ta tayashi suka k’arisa had’a mata kayan wanda duk sabbi ne da Kaala Abdi ya mata bayan ta dawo gabanshi. Shi ya fitar da akwatuna biyun ya saka a motar da zata kaisu hotel ya samu Babanshi yana jiranta a cikin motar. Haydar ya lek’a cikin motar ya dubi Baba wanda daga ganin fuskarsa zaka gane yana cikin farin ciki yace, “Baba Ango.” Dak’uwa Baba ya mishi yana murmusawa yace, “Hingo naka ja’irin yaro.” Dariya Haydar yayi duk da cewa zagin shi aka yi ya d’aga kanshi yana ganin yanda mata suka fito da Ammi kamar wata Amarya har da lullu6i a fuskarta ana wak’a ta yarensu wanda shi bai ma san me suke fad’a ba, amma yaci alwashin koya a gurin Laila domin hatta d’anshi da yaren zai tashi kamar yanda su Abul da Sabrin suka iya. Shi ya bud’e musu k’ofar aka zaunar da ita a gefen Baba wanda annurin fuskarsa ta k’ara k’aruwa, rufe motar Haydar yayi kana ya tura kanshi ta cikin window ya yiwa Ammi kiss a kanta yana cewa, “I love you Ammi.” Rik’o hannunshi tayi ta sumbata tace, “Nima Ina sonka Ali na. Ka kula da kanka don Allah.” “Karki damu Ammi, sai mun yi waya. Allah ya tsare hanya. Take care Baba.” A haka suka yi sallama motar ta tashi suka tafi, Haydar komawa ciki yayi ya shiga sashen da Abul yake don tun da suka zo bai samu ya ganshi ba. Abul yana ganinshi ya murtuk’e fuska tamau yace, “Uban me kake yi a nan? Kar kayi tunanin don ka zama dangi kayi tunanin zan daina tsananka. I still hate you.” “Kana lafiya?” Haydar ya yi kamar bai ji shi ba. Abul juyawa yayi ya shige d’akinsa ya barshi a gurin kamar yanda ya yiwa Laila da duk wanda ya tsani ya ziyarce shi. Kaala Abdi ne kad’ai baya iya yiwa rashin kunya ko musu idan ya sakashi abu. Washe gari da rana Haydar da Laila suka koma Kano tare da su Alhaji Shettima amma ban da Sabrin wacce tace zata yi sati biyu a can. Baba da Ammi kuwa tuni suka isa Abuja har tayi waya da Haydar tana fad’a mishi gidanta yana nan ba’a canja komai ba hatta suturunta da kuma kayan jarirai da suka saya ita da Baba a wancan lokacin. Ummii bata biyo su Kano ba kamar yadda Madu yayi ta rok’anta, k’arshe cewa tayi ta dawo Maiduguri da zama gaba d’aya. Yaran nata basu ji dad’in wannan matakin da ta d’auka ba, amma Mas’ud ya fad’awa Laila su barta na wani lokaci ta huce tukunna sai su nema mata gida a Kano ta dawo kusa dasu, saboda zata fi samun kulawa idan tana cikin ‘yayanta. Zaman Haydar da Laila zama ne na jindad’i da kwanciyar hankali da kuma mutunta juna, biyayyar da take mishi a yanzu har ya ninka na daa saboda tana tsoron rasa mutum irinsa a rayuwarta. Cikinta kuma ya girma ya shiga wata na tara haihuwa yau ko gobe. Zumunci sosai take yi da Aunty Aisha da sauran ‘yan uwan Haydar wad’anda basa kushe aurenta da shi, tun da a cikinsu akwai masu mata habaici da kuma fad’a mata bak’ar magana cikin wasa wai ai ta haifi Haydar. Madu ya sayar da gidanshi ya samu k’arami ya koma ciki, sauran kud’in kuma yayi jari da yake yanzu an kwace arzikin da yake tak’ama da su, da kyar ya samu Hajja ta dawo gidanshi bayan Mas’ud ya mishi bikonta. Alhaji Abdul ya bar nauyin Lu’a Ventures a hannun Haydar bayan Baba ya tilastawa Haydar d’in ya kar6a, akan cewa shi kuma Alhaji Abdul zai kula da sauran kar nauyi ya mishi yawa. Zumuncin su kuwa har yanzu bai yi gaba ba, saboda in banda gaisuwa da kuma maganan business babu abun da yake shiga tsakaninsu sannan basa ziyartar juna. Hakan yana damun Baba ganin kusan wata shida kenan amma sun kasa daidaita kansu. Ammi ta yiwa Haydar fad’a haka ma Laila tana yawan mishi magana a kan hakan amma baya gyarawa. Wata ranar lahadi Haydar na gida yana matsa k’afar Laila wacce ta kumbura yace, “Kin wuce EDD d’inki fa jiya.” “Mun yi maganar Haydar, na fad’a maka ba lallai bane dama in haihu a wannan ranar saboda kawai tsammani suke yi. Ai haihuwa sai Allah ya kawota, kai dai ka tayani da addu’a in samu in haihu da kaina kar a mini C.S.” “Kina tsoron C.S Laila, Insha Allah ke da kanki zaki haihu.” “Allah yasa. Nagode ka bar matsan k’afar ya daina zogi.” Gyara zaman shi yayi ta kwanta a jikinshi ya bud’e cikinta yana ganin yanda Baby ke naushinta gwanin ban sha’awa da kuma al’ajabi. “Duk ranar da aka ce kin haihu ban san wani irin murna zan yi ba.” Ya kalleta cikin so da k’aunarta. “In baka wani labari?” Ta tambayeshi tana d’aura kwalban Nutella a saman cikinta wanda yayi tozo sosai. “Ina jinki.” Ya bud’e mata marfin ya d’ebo a cikin k’aramin spoon ya bata ta kar6a da hannunta ta fara sha. “Lokacin da nake da cikin Abul na kusa haihuwa kamar haka, muna wasa da babansu yana mini cakulkuli faya ya fashe na fara nak’uda.” Shiru Haydar yayi kamar bai ji ba, ganin shirun yayi yawa yasa ta juyo da kanta tana kallonshi, a nan ta gane bai ji dad’in hirar ba. Gyara kwanciyarta ta yi a jikinshi tace, “Sorry.” “Ki tashi mu je mu kwanta, dare yayi.” Ya taimaka mata ta tashi zaune kana ta mik’e tsaye ta mayar da abun da take sha kitchen, shi kuma Haydar kashe kayan kallo yayi kana ya rufe k’ofar falon suka shiga d’aki. Wanka suka yi tare kamar kullum sannan suka yi shirin bacci suka kwanta. Kamar wanda dama jiranta ake yi ta kwanta mararta ta fara ciwo wanda tana ji ta fara tunanin haihuwa ne yazo kusa, kuma tana son Haydar ya samu nitsuwa daga gareta saboda ya dad’e bai nemeta ba. Kallonshi tayi yana saka mata pillow a bayanta tace, “Akwai hira ne?” Ya dakata daga abun da yake yi cikin mamaki ya dubeta yace, “But mun ce no more sex, saboda kina wahala.” “I know. But I need you.” Yanda tayi maganar kamar wata yarinya ya yiwa Haydar dad’i bana wasa ba yayi murmushi mai k’ayatarwa yace, “An gama Matar Haydar, but stop me idan na fara hurting d’inki. Kin ji?” “Aye Aye Captain.”
Mum Fateey 👌



