Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 44 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

_💋Boss Bature💋_

Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa “ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba’a son raina nabar ƴa’ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne… ‘

  Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za’ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !?

  gaba ɗaya ya tafi duniyar tunanin ya amince da zancen mahaifiyar shi ko kuwa, shessheƙar kukanta daya ji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa cikin sauri yace “its okey mom,ni banason nayi sanadin da zan zubar da hawayen wani,bare ke da kike mahaifiyata ma,” 

  Ajiyar zuciya alexandra tashiga saukewa jin kalamansa masu daɗin gaske, muryarshi ce tasake katse ta da cewa “pls wipe ur tears mom,” 

  Murmushi ta saki tamkar tana agabansa,hannu ɗaya tasa tana share hawayenta kamar yarda ya umarta tayi,

. bayan ta gogesu tace “baka son ganin hawaye ne? amma meyasa baka amsa kirana duk in na kira wayarka, ko na kira wani nace ya baka muyi waya,a duk lokacin da hakan ta faru ina zubar da hawaye na sosai,

  Murya asanyaye take magana, har cikin zuciyarshi yake jin maganar mommyn nashi,

  “Mommy inaso zan aje waya,i wll call u next time,

Cikin sauri tace “ka haramta mun ganin fuskarka ko? Shikenan my romeo,ka faɗi kome kake so zan maka shi”

  “Komai nace kiyi zaki yi ne”? Ya tambaya yana jiran amsa

  “zan yi maka shi koma menene,”

  murmushi junaid yayi sannan yace”yaya ayaan da jahan suna son wani abu wurin ki, kiyi masu shi, sannan ki dawo gida ki bani kulawar da baki bani ba tun ina yaro,” 

  Murmushi tayi sannan tace”shi kaɗai kake so”? 

Yace “eh,” 

   Jinjina kai tayi tare da cewa”duk abunda kace zanyi saboda in tabbatar maka da cewa ina tsananin ƙaunarka my romeo,sannan koda daga bayane kaga wani abu kana so ka sanar mun, zanyi maka koma menene shi indae acikin duniyar Nan yake, sun jima suna yin wayar daga bisani su kayi sallama, bayan ya ajiye wayar ya dinga jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarshi ga wani irin kwanciyar hankali da yazo mashi yasan cewa duk saboda wayar da yayi da mom in shi ne yasamu wannan natsuwar,

Sai wuraren ƙarfe 4’dai dai sehrish ta farka tana faman yin hamma, ba ƙaramin daɗin baccin taji ba,saukowa tayi daga saman gadon nata ta wuce toilet jim kaɗan tafito da alwalarta, hijab ta dauko ta zura a jikinta sannan ta kabbara sallah, tun tana cikin yin sallar taji ana knocing ƙopar ɗakin nata, don haka tana kammala shafa addu’a ta miƙe a hanzarce ta buɗe ƙopar,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin matar nan ta ɗazu,murya na rawa tace “ina yini,” murmushi Amani tayi tare da cewa “lpy ya kike,”?

“Ina lpy,” ta bata amsa ataƙaice,

dan ta6e baki amani tayi kafin tace”naso ɗazu dana ganki da safe muyi magana amma naga kina cikin sauri ne zaki school,” ta fadi a wayance

  Sehrish tace”eh hakane,” duk tarasa natsuwarta, tsoranta me take son ce mata,

  Amani taci gaba da cewa”Tun yaushe kika fara aiki a gidan nan ne”? Saboda ni ban ta6a ganinki ba gsky,”

  Sehrish tace”banjima da farawa ba,”

  “Amma nayi mamamkin yarda shaƙuwa ta shiga tsakanin ki da mutanen gidan har abbansu ya mayar dake ɗiyarshi,kuma naga kina da kusanci ssae da junaid har yana ruƙe maki hannunki kamar wata ƙanwarsa, bayan matsayinki bai wuce na ƴar aiki ba,”

ɗagowa sehrish tayi a ɗan rikice tana kallonta jin abunda tace,

   Murmushi amani ta kuma saki kafin tasanya hannu ta dafa kafaɗar sehrish tace”idan ba damuwa inaso in baki wata shawara wadda zata amfane ki, domin na lura kinason jefe kanki cikin hatsari, karfa ki ruɗa kan ki,”.

  Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa”ina sauraronki,” amani taci gaba da cewa”ki nisanta kanki daga kowa na cikin gidan nan,ka da ki bari wani ya so ki acikin matasan gidan nan,kuma kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta faɗa tarkon son wani,idan da hali ma ki tsaya a iya matsayinki na ƴar aiki,zaki fi samun kwanciyar hankali,”

  Tun da tasoma magana sehrish ke bin ta da kallo fuskarta ta nuna alamun rikicewa don sam batasan inda zancen matar ya dosa ba,

  “Kada kice na cika ki da surutu,its just an advise in kinyi amfani da ita ke zata amfana,but if u don’t hmmmmm u can even lost ur life……..’ 

Wani irin bugu zuciyar sehrish taji saboda abunda amani tace, na cewa zata iya rasa rayuwarta, tuni jikinta ya shiga yin kerma alamomin tsoro sun bayyana a fuskarta, hankali atashe take cewa”meyasa kika ce haka?saboda me zan rasa rayuwa ta?don kawai naso wani ko wani ya so ni acikin gidan nan”? Ta tambaya tana kallon Amanin,

   Kafin Amani tace wani abu, muryar Azmee ta katse mata hanzarinta da cewa”tsayuwar me kuke yi ne, ke da nace ki kira mun ita don tazo mu haɗu mu fara girkin da wuri”? Ta tambaya tana kallon Amani,

. cikin sauri Amani ta dan basar tare da sakin fara’a a fuskarta tace”dama muna ɗan tattaunawa ne,kinsan bata sanni ba nima kuma haka, so ina gabatar mata dakaina ne don musan juna,”

  Zuba mata ido sehrish tayi kawai baki asake tana kallonta,

  Azmee tace”Hakan na da kyau, sehrish wannan matar yayanku ce Abbas sunanta AMANI,ina fata zaki saki jiki sosai da ita domin kuwa tana da mutunci sosai,

  daƙer sehrish ta ƙaƙalo murmushi tace”Insha Allah aunty azmee,”

   tayi maganar tana kallon Amanin ita ma kallonta takeyi har lokacin,

Azmee ta lura da kallon kallon da suke yi don haka tace”Amani mu wuce kitchen,ke ma sehrish ki ajiye hijabin jikinki ki zo mufara aiki,” 

  Juya ciki sehrish tayi su kuma suka wuce kitchen ɗin, kanta ya gama ɗaurewa da maganganun da Amani ta gaya mata,amma duk da hakan ba tajin zuciyarta zata karaya saboda wasu ƴan kalamanta,hannu tasa tare da tu6e hijabin ta ajiye ta nan saman gadon, sannan ta ɗauko ɗan mayafinta cikin wardrobe tayi rolling ɗinsa,

  A dai dai lokacin da ta fito daga ɗakin ta tunkari hanyar kitchen ɗin sai ga haroon ya fito daga part ɗinsu,sai da taji gabanta ya faɗi don ita yanzu kallon shaiɗan take yi mashi saboda ƙahone kawai babu akanshi,

   Ƙarasowa yayi inda take suna facing ɗin juna yace”mutuniyar ba hello ba hi,laifin me nayi maki ne”? Yayi maganar yana ɗaga mata gira tare da kashe mata ido,

  Tsuke fuska tayi tare da bi zata wuce cikin sauri yasha gabanta tare da ware hannayensa yace”daga kin ƙara motsowa zan rungume………’ kasa ƙarasa maganar yayi gabansa na faduwa ba don komai ba sai don ido biyun da su kayi da SGR wanda ke shigowa cikin babban falon su biyu ne tare da shattima suka shigo,banda omar wanda tun a masallaci suka rabu,

  Cikin sauri haroon ya canza kalamansa da cewa”kin gane dole kisa tsoran Allah acikin zuciyarki idan kinason rayuwarki tayi kyau,amma in kika ce zaki biye ma ƙawayen banza zasu kaiki ne su baro ki,” ya dage sai zuba yake yi mata,juyawa tayi don taga wanene ya shigo saboda ganin yarda haroon yabi ya susuce ya sauya magana,

   hada ido su kayi da shi adai dai lokacin yana ƙoƙarin kawar da nashi idon daga na haroon,har cikin zuciyarta taji wani irin sanyi aranta dama da kewarshi tadawo gidan,ganin shattima na kallonta yasa tayi saurin cewa”ina yinin ku”?

“Lafiyalou Alhmdllh ƴan mata,” ya amsa mata fuskarshi asake,sannan suka wuce upstairs part dinshi,sam takasa janye idonta daga kallon Bayan sgr da takeyi ko kyaftawa ba tayi har suka 6ace ma ganinta,hakan ba ƙaramin fusata haroon yayi ba rai a6ace tace”Ke!!kina a gabana kuma kike kallon wani”? 

  ƴar dariya sehrish tayi kafin tace”Namiji nake kallo,” tana faɗin hakan tabi ta gefenshi ta wuce izuwa kitchen,baki asake haroon ya tsaya yana huci jin abunda tace,aransa yace”lallai ma ƴar shilan can harni zata ce ma Namiji take kallo,hakan na nufin ni kallon ɗan daudu takeyi mun,zan yi maganinta ne! Watan fara shan uƙubarki yayi acikin gidan nan !!zan 6ata maki suna a wurin shi dama kowa na gidan nan”!!! Yana gama faɗin hakan ya gyaɗa kanshi yana sakin shu’umin murmushi ya fuce daga falon.

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)  Shiga kitchen din tayi ta same su har sun fara aikin girkin,sallama tayi masu suka ɗago suna kallonta atare, azmee tace”sannu da zuwa za’a fara aikin ne,”

  Ɗaga kai tayi tare da cewa”eh amma inaso nafara kaima su babban yaya abunsha naga sun shigo tare da wani ynx,” zuru amani tayi tana kallon ikon Allah,

  Azmee tace”toh bari na haɗa maki tare da snacks ki kai masu,” 

  ɗan murmushi sehrish ta saki tana jiranta duk in ta ɗago sai sun haɗa ido da Amani,sai tayi saurin kawar da idonta,

  Bayan azmee ta kammala haɗa mata two cups na coffee a saman tray tare da plate mai ɗauke da snacks ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi ta rike da kyau a hannunta sannan ta juya ta fuce daga kitchen ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya, 

   Wuce wa tayi upstairs tayi a bakin falon ta tsaya tare da yin sallama,muryar wannan abokin nan nasa taji ya amsa mata da cewa”wa’alaikum salam,” sai da ta dai dai ta natsuwarta sannan tashiga ciki gaban ta na faɗuwa kamar kullum,

   Shattima ne kawai ta samu zaune saman 3 seater yana danna wayarshi, 

Ƙarasawa tayi tare da ajiye tray din saman table din gabansa,maimakon ta tafi saita tsaya tana faman wasa da yatsun hannunta burinta kawai taga sanyin idaniyarta tasan cewa zai fito shiyasa ta tsaya,

  Hannu shattima yasa ya ɗauki cup of coffee din yakai bakinsa yana kurba da alama ba ƙaramin daɗi yayi masa ba,sam takasa tafiya saboda bata ga sgr ba,ganin tayi masa tsaye yasa shi jinkirtawa da shan coffee ɗin da yake yi yace”Ya sunanki ne”? firgit ta ɗanyi tare da kallon shi tace”Sehrish,” jinjina kan shi yayi kafin ya ƙara cewa wani abu sai ga Sgr ya fito sanye da short ajikinshi tare da singlet,nan da nan sehrish ta shiga natsuwarta, wuri ya samu ya zaune gefen shattima, cikin sauri ta ɗauki cup ta miƙa masa hannu yasa tare da kar6a yana dan sipping dinshi a hankali,

  Mayar da idon shi yayi kan sgr yace”wannan fa ban ta6a ganinta ba is she ur sister? Ya tambaya yana kallon shi,

  “U can ask her,” ya faɗi batare da ya dago ya kalle shi ba, murmushi shattima yayi tare da mayar da idon shi kan sehrish yace”kina da connection dasu ne,ko yar wurin Aunt dinsu ce ko uncle dinsu”?

  ɗaga mashi kai tayi alamar”eh” sunnar da kai tayi cikin jin kunyar ƙaryar da tayi,

  Shattima ya kuma cewa”amma Abba yayi maki miji kuwa”? ɗagowa tayi tare da dan zare ido saboda jin abun yace mata,mamakin ta yadda yake ta tambayarta bayan sam ko a fuska baiyi kama da mai son surutu ba shima,

   girgixa kai ta kuma yi tare da cewa”a’a bai mun ba” 

“Because of what?ko babu wanda kike so acikin matasan gidan nan”? maimakon ta bashi amsa sai ta ɗan saci kallon Sgr dake kur6ar coffee din hannun shi,

  Wani irin murmushi shattima ya saki saboda yaga inda sehrish take kallo, acikinsa ransa yace”hmmmm dama nasani,”

  A fili kuma yace”yana da kyau ko’? A firgice sehrish ta mayar da idonta kan shattima tace”Wa”? da ido yayi mata nuni da Sgr, sunnar da kai tayi tana murmushi tace”eh,”

   “Shi bai yarda da mace ba,yace mata matsala ne arayuwar namiji,but i want to ask u something a misali mace ta samu righteous husband kamar wannan lu’u lu’un,wanda ya haɗa komai ga kyau ga ilmi ga dukiya, kina tunanin akwai macen da zata yi gangancin Mallakarsa har ta zama matsala arayuwarshi balle ta 6ata mashi rai”? 

  jikin sehrish tuni ya soma kerma saboda tsoran dogon sharhin da abokin sgr ɗin ke yi mata,babban tashin hankalin ma gashi a kusa duk da yayi tamkar baya jinsu,ammma ae kunnan shi a buɗe suke ba’a toshe ba dole ne yaji abunda suke cewa,muryarta na rawa ta buɗe baki zatayi magana kenan kwatsam taji wannan sanyayyiyar muryar tashi tace”ba kowace mace bace zata so ni dan Allah in fact duk macen da zata soni sai don waɗannan abubuwan daka lissafa,” yayi mgnar again batare da ya kalle su ba, sai ma hannun shi daya zura cikin short pocket dinsa ya ciro wayarsa dake ringing tare da yin picking ya kara a kunnan shi yana magana cikin harshen turanci,

  gaba ɗaya jikin sehrish yayi mugun sanyi kalamansa akwai ƙamshin gsky acikinsu,yanzu ta ƙara gane dalilin dayasa mace sam bata agabanshi,saboda yasan cewa duk wadda zata so shi,ba zata so shi dan Allah ba face sai don wani abu daya mallaka,kamar wannan kyakkyawar surar tashi mai matuƙar jan hankali,da dukiyarsa kuma, 

ga kuma ilmi duka dai😇

Amma har ga Allah ita ba don dukkan waɗannan abubuwan ba take son shi ba,ataƙaice ma tunkan taga fuskarshi tunkan tasan koshi wanene ta afka ma tarkon son shi ta hanyar sunan shi kawai da taji suna faɗi BABBAN YAYA,

  gaba ɗaya ta tafi zurfin tunani muryar shattima ta dawo da ita daga dogon tunanin nata da cewa”dagaske ne abunda ya faɗa”? ya tambaye ta yana jiran amsa,ba komai yasa shattima sakin jiki da sehrish ba face tun da yaga yarinyar da suka shigo ta gaishe shi da ya kalle ta ba fuskar kowa ya gani ba a fuskarta ba face fuskar SGR bi ma’ana sun dace sosai,saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin yarinyar da ta dace da Sgr ba face wannan yar matashiyar duk da ya lura cewa kamar tayi masa ƙanƙanta,yarinya ce ssae amma kuma tana da duk wani abu da namiji zai buƙata ajikin ƴa mace,🥱

  A hankali sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa”hakane gskya ya faɗi…..” daƙer takai ƙarasa maganarta, cikin sauri tace”kuna buƙatar wani abu”? shiru shattima ya ɗanyi saboda ya lura da chanjin da yarinyar tayi,kuma yasan saboda kalaman sgr ne,may be tana son shi ne da alama, ya faɗi aranshi a fili kuma yace”just its okey zaki iya tafiya,mun gode da wannan,” 

  Murmushi ta ɗanyi sannan ta juya da sauri saboda kukan daya ciyo ta har takai bakin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi, anatse yake yin wayarshi ya jingina bayansa ajikin kujerar,sa kai tayi ta fuce wuri tasamu anan upstairs ɗin ta zuƙunna ta cigaba da shan kukanta jikinta har rawa yake yi,tuni eyes dinta sun canza launi, fuskarta ta tur6une saboda kuka sai faman murzar hancinta takeyi kamar zata 6alle shi,sam ta manta da aikin dake gare su a kitchen su azmee nacan da amani sun taƙarƙare suna ta aikace aikace ba sehrish, gashi Amani sai faman tambayar azmee take yi na cewa har yanzu yarinyar bata dawo ba daga kai ma Sgr coffee,ko mai ta tsaya yi? Ita dae azmee bata ce komai ba, da tacika ta da tambayar ne tace”may be shi ya tsare ta,kinsan ita ke kula da apartment dinsa,

Jin hakan ba ƙaramin tayarwa Amani hankali yayi ba,daure wa kawai take yi tana aikin,

   Hawansa kenan upstairs ɗin ya miƙi hanya yana cikin tafiya yaji shessheƙar kukan ƴar mace,mamaki ne ya kama abbansu ganin yarinyar zukunne ta takure kanta sai faman matse hanci take yi tana kuka,tuni hankalinshi ya tashi ƙarasawa yayi inda sehrish take zukunne,a firgice ta miƙe tsaye lokacin da tayi arba da Abban nasu sam bata lura dashi ba sai da taji takon takalminsa na tunkarota,

   lokaci guda ta rikice duk ta susuce tsoranta mai zata sanar mashi in ya tambayeta dalilin yin kukan nata,

  Ko da ya isa dab da ita sai ya tsaya yana ɗan nazarin fuskarta,tsananin tausayin yarinyar ne ya kama shi,dama ita mace abun tausayi ce musamman in ta kasance ba’a gaban iyayenta ba,babu kowa nata a kusa da ita da zai lallashe ta ya kuma janyo ta jikin shi don jin damuwarta,ya mayar da ita yar shi amma kuma bai da isasshen lokacin jin abunda takeso ko me ke damunta,

   Sunnar da kai sehrish tayi ƙasa murya na rawa tace”ina yini abba,”

  bai amsa mata gaisuwarta ba sai cewa yayi”meya faru ne naga kina kuka?

cikin en ina tace”babu komai,”

hannun shi yakai gefen fuskarta yace”ko da zaki yi ma kowa ƙarya,kada kice zaki yi ma abbanki,ga hawaye nan nagani suna zuba a idonki,kawai dai bakya son faɗamun ne,” shiru tayi bata ce komai ba tana faman wasa da yatsun hannunta,

  Murmushi yayi ganin tana ɗan satar kallon shi kamar wata mara gaskiya,

  Cikin zolaya yace”faɗa mun gaskiya kodai aure kikeso ne?kin rasa wa zaki faɗamawa shine kika la6e anan kina kuka ko”? ɗagowa sehrish tayi taɗan zare ido can kuma ta fashe da dariya gaba ɗaya, shima dariyar yayi dama yayi hakan ne don yasata farin ciki yasan mata daga anyi masu maganar aure sai jin kunya da dariya,

  ganin haka yasa shi ƙara cewa”hmmmmm dama nasani,mu aje wannan maganar a gefe nasan cewa akwai wanda kike so acikin ƴa’ƴana don na iya haihuwa gasu nan tubarkalla masha Allah ƴan mata sai rububi sukeyi hada masu kirana awaya duk safiyar Allah suna gaishe ni wai nan suna yi ma kansu ko ƴa’ƴansu kamun ƙafa,ni kuma har yanzu basu kwanta mun araina ba,Amma ke ɗin nan ko ta dabance in har kinaso in baki ɗaya daga cikinsu dole kema ki fara kamun ƙafa daga yanxu,” 

Magana yake a natse sehrish kuwa ta kasa kunne tana sauraron shi,mamaki ya gama kamata yarda Abban nasu sukutun da guda yake fira da ita lallai ba ƙaramin wayayyen mutun bane,

  bayan yakai ƙarshen maganar tashi tace”amma Abba,ni bansan yarda ake yin kamun ƙafar ba,” ta faɗi cikin jin kunya,

  dariya yayi tabi shi da kallo sai taga ya koma mata junaid saboda tsananin kamanceceniyar dake a tsakaninsu don dai shi fuskarshi akwai manyantaka,

Bayan ya tsagaita da dariyar yace”kina nufin baki san yarda ake kamun ƙafa ba in mutun nasan abu,to ki tambayi AZMEE ta faɗa maki zata koya maki,

  Jinjina kai tayi tare da cewa”insha Allah zan tambayeta,”

  Murmushi yayi kafin yace”daga ynx zan fara zuba ido in ga yadda zaki fara kamun ƙafar naki,idan kinyi abu mai kyau sai na duba na gani wanne ya dace acikinsu na baki,idan marks ɗinki yakai matakin A1 to zan aura maki ɗaya daga cikin manyan ne, idan kuma Credit kika samu zan haɗaki da ɗaya daga cikin youngers ɗinsu,amma fa ki sani idan marks ɗinki yazo da matsayin(f)to zan aura maki Haroon ne……….. ” dariyar da sehrish ta fashe da ita ne ya hana shi ƙarasa maganar, zuba mata ido yayi yana kallonta sai ya dinga ganin kamanceceniyar fuskarsu da ta yarinyar sam yarasa gane dawa take masa kama nan da nan kan shi ya ɗaure yashiga mamakin kamannin daya gani kodae idonshi ne ke nuna mashi hakan tabbas fuskarta tayi tamkar photocopy ɗin fuskar ƙanwarsa AZEEMA,

  daker sehrish ta tsagaita da dariyar tace”Abba zan tafi kitchen nabarsu suna aiki,” 

  Murmushi yayi tare da cewa”hakan nada kyau,kwara tun ynx ki koyi girkin shima yana daya daga cikin jarabawar da zan maki don bazan aura ma ƴa’ƴana macen da bata iya girki ba,then idan nasamu free time zan wa junaid magana ya kira mun ke don mu ƙara tattaunawa,”

  Amsa mashi tayi fuskarta cike da annashuwa tabi ta gefenshi tana faman sakin murmushi ba don komai ba sai don maganar Abban nasu dayace idan marking ta F9 ne zai aura mata haroon hakan na nufin shi kanshi yasan cewa haroon cikon bencin gidan ne 🤣😂😅

  Har juyawa abban nasu yayi yana kallonta a lokacin tayi nisa wurin sauka daga stairs ɗin,ajiyar zuciya ya saki saboda ganin farin ciki a fuskar yarinyar, dama yayi hakan ne don ya mantar da ita damuwar da ta shiga har ta la6e tana kuka,kama hanya yayi ya wuce,dama bedroom ɗin junaid ya nufa,

***************************

Tun ɗazu da suka kammala lunch ɗinsu after Azhar hossana da Camila suka koma bedroom din saman katafaren gadon suka baje suna bacci abun ba’a magana,ita kuwa jahad sam tagaza yin bacci tun  da tayi sallar la’asar tafito daga ɗakin ta tsaya a falon tana zagaye, bakomai take burin gani ba face Ya Omar dinsu ko zafin ciwon ƙafarta yanzu tadaina ji,har wurin ƙarfe biyar da wani abu tana wannan safa da marwar in betwn seater’s ɗin dake a palourn,tana cikin wannan zagayen MARSHAL OMAR ya shigo falon da sallamar shi, sam bata ji shi ba saboda ta juya masa baya tamiƙi hanya tana tafiya,

  Murmushi ya saki ya tsaya yana tunanin wacece acikinsu jahad ko hossana,koma dae wacece ba ƙaramin kyau tayi masa ba acikin kayan,yaji daɗin hakan saboda dama burinshi ya gansu cikin jin daɗi da walwala,ganin bata da alamar juyowa yasa shi yin gyaran murya da ɗan ƙarfi, cikin sauri jahad ta juyo tana faman zare ido don batayi tsammanin ganin mutun ba,nan da nan wani irin farin ciki ya mamaye fuskarta da karfi ta furta”Ya Omar,” lumshe idonshi yayi tare da buɗe su yana murmushi,

  Watsa wa tayi da gudu tamkar zata rungume shi,sai da taje dab dashi sannan taci burki tana dariya,yana ganin hakan ya gane cewa Jahad ce,don da ace hossana ce sai tayi hugging dinshi,

  “Fatan na same ku lafiya”? Ya furta yana kallonta,fuskarta awashe tace”Alhmdllh ya omar,dama tun ɗazu nake jiran zuwan ka, ashe zaka zo da har na fidda rai,

   Omar yace”naso nazo ɗazu to bansamu hali ba,shiyasa na aiko maku da major don ya ɗauko ku,ina fata gidan yayi maku?

  “ya omar ni nama rasa da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wurin yi maka godiya Allah……….”tuni idanunta sun cicciko da kwalla sun soma gangarowa daga cikin idanunta,

  Cikin sauri yace”Why jahad?me yasa zakiyi mun kuka bayan kinsan bana son ganin hawayen ku,sannan bana son godiya kada na sake ji,duk wani abu da nayi maku nayi shi ne don Allah,kuma haƙƙin ku ne dake akaina har yanzu ma ni ji nake kamar akwai sauran abubuwan da banyi maku ba,

..kallon shi kawai take yi yana bayani har yanzu tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Marshal omar,

Cikin shessheƙar kuka tace”ya omar kai wane irin mutun ne?narasa dame zan fasalta ka,kyawawan ɗabi’unka da halayenka da kyakkyawar zuciya irin taka bana tunanin a doran duniyar nan za’a samu mai irinsu,koda za’a samu sai anci baƙar wahala kuma cikin kashi 100 bai wuci asamu kashi biyu ba,kai na musamman Ne ya omar,ina taya iyayenka farin ciki sosai da samun ɗa kamarka,saboda kai abun alfahari ne……..ni bansan da me zamu saka maka ba ya omar,ka bamu kyakkyawar rayuwa ka cire mu daga ƙangin rayuwar da muke ci,a lokacin da muke tunanin cewa kowa ya tsanemu bai son mu mutuwa ma kawai muke jira,sai gashi Allah ya haɗamu dakai,tun a lokacin nasan cewa kai kyauta ne daga Allah………..

  tun da jahad ta soma kora jawabi ya goya hanneyen shi a faffaɗan kirjinshi ya natsuwa yana sauraronta fuskarshi ɗauke da murmushi,saboda kalamanta ba ƙaramin shigarshi su kayi ba yadda take magana a natse ga wata irin murya dake gareta mai sanyin gaske irin muryar da duk 6acin ran da kake ciki in. Ka ji ta sai ka manta dashi,ae jahad akwai natsuwa ga tawakkali nima na shaida hakan 😘

“Ya omar ka faɗamun dame zamu saka maka?nasan ma babu Ba mu da abunda zamu iya saka maka aduniyar nan face addu’a itace kawai ke gare mu,i will keep pryaing 4 u ya omar hada family ɗinka duka zan saku a addu’ata till the end of my life bazan manta ba aduk lokacin da nayi sallah ko nayi karatun alkur’ani har night prayers ma zan dinga tashi inayi just because u ya omar and ur family,

  ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen fuskarta basu tsaya da kwarara ba,

  Hannu omar yasa tare da zaro handkerchief ɗinsa dake front pocket dinsa dake a t shirt din jikinshi,

  Da hannun shi yasa yana wiping tears dinta a hankali,runtse idonta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa a tattare da ita,

  Muryarshi ce ta tsinkaye ta da cewa”jahad ngde ssae kalamanki kawai da kikayi mun a yanzu ma sun wadatar dani,sannan idan kuna so ku saka mun abunda nakeso shine koda nan gaba kada ku juyamun baya bana son ku canzamin inaso ku tsaya a yarda nasan ku,ina tsananin ƙaunarku sosai bana son abunda zai raba ni daku,inason zumunci ya ɗaure a tsakanina daku daganan har can……

katse shi tayi da cewa”har ina kenan ya omar,”

  Cikin zolaya yace”gidan Aljanna mana,” dariya tayi sosai kafin ta tsagaita da dariyar tace”insha Allah ya omar ba zamu ta6a baka kunya ba,zamu kasance kamar yarda kakeso,”

  Jinjina kansa yayi sannan yace”where’s my hossana banganta ba,ko tana ciki ne? Ya yi nuni da hannun shi,

  Jahad tace”hossana suna ciki tare da wannan nurse camila din sai sharar bacci suke yi tun ɗazu,”

  Murmushi yayi tare da cewa”naso na ganta,”

  Cikin sauri tace”ya omar ka shigo daga ciki mana ka zauna na kira maka ita don itama hossana a ƙagare take data ganka,”

  Omar yace”sauri nake na koma gida yanxu,ki gaishe mun da ita dae,ko kuma zan kira wayane ae akwai telephone sai mu gaisa,” jinjina kai tayi tare da cewa”shikenan zan sanar mata,amma nasan zatayi kuka in taji cewa kazo kuma ka tafi bata ganka ba,

   juyawa yayi yana faman sakin murmushi har ya kusa fita daga falon tace “ya omar,” juyowa ya kuma yi yana kallonta, 

  “Tun jiya inata so in kazo inyi maka ya mai jiki,abun yana araina ɗan uwanka daka sanar mun cewa bai lpy,”

   Omar yace”oh fawan da sauƙi jikin shi sosai,kada ki damu zan bashi waya inyaji sauki ssae sai kiyi mashi ya jiki,”

  Jinjina kanta tayi alamar toh daga nan sukayi sallama ya fuce daga falon,

  Ajiyar zuciya ta saki tare da wuce wa ciki fuskarta asake 😇

****AUNTY BABBA******

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa 

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

Back to top button